← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 132

Sashe 34

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan kadan ya kurba drinks din ta ya ajiye
Sai wani kallon sa take ,ba daga ido
Cikin haka har ya kai ga a hankali ta soma tunanin shi din bana ta bane,zuciyar sa na wata ce ba ita ba "duk da ma tasan zAsuyi aure nan da kwana kadan
Tabbas zahida ce a zuciyar sa ,
Take ta soma jin wani zafi aranta mood din ta ya sauya
To meye sa ammy zata takura ma yaya ya aure wacce bai so? Auren alkawari kenan zaiyi da ni?tace Wayyo Allah Na shiga uku

Ni kenan an raba ni da soyayyar yaya ashraf har abada ba wanda zai so ni kenan sai dai nawa soyayyar yaya ash ya zamo min makamin cutar da kaina?

Wani dada langwame fuska tayi ta cigaba""Ammy ke kika hada wannan abun
Pls come back ammy na, yay ash bani yake so ba kikace ya aure ni kuma wallhy ena son sa bazan iya jurewa ba....nan wasu zAfafan hawaye suka biyo kan kuncin ta,.again

""Jasmine... ya fada a dan tsawace
Wai meye haka ne dan Allah ...kukan nan bazai kare bane?
Wai ko so kike kiga na bar miki gidan kafin .....

Jin hakan daya fada ma ya kara dada hura mata zafin dake ranta
Luf tayi da kanta akan cinyarta tana kuka abun ta,
Iya surutu da fadan yayi amma sam taki kulasa karshe da kansa ya hakura ya koma kan sofa ya same ta

Daf da ita ya zauna ya riko ta ,fizgewa take alaman tayi fushi"don itakam kishin sa ne da tunanin matsayin da zAta koma awajen sa in sukayi aure ke damun ta yanzu

kan sa ne ya dada kullewa har ya soma tunanin ko don fadan daya mata ne ya sata ke fushi haka.

Bai hakura ba Cikin lallashi ya raba kanta da kan cinyar ta ya jawo ta jikin sa,
Yadda taji ya rungume ta yasa ta sauke karamin numfashi
Sai wani zirr take ji a brain dinta Musamman data ji ya kwntar da murya yana bata hakurin laifin da baiyi ba

Da kyar tayi shiru ta dena kukan amma tana lafe kan kirjin sa shikuma ya jingina da sofa idonsa a lumshe
Jin ta shiga Wasa da dan yatsun sa yasa yace".me ya saki kuka jasmine ,nine?

Dan shiru tayi chan sai tace bakai bane

Da sauri yace to waye ne?
" Nan ma ta shiga muhawara da zuciyan ta """tunda aure na zaiyi
In fada masa ena son sa in yaso yaa san yadda zaiyi dani ?No' ai shi baya sona to meyey na fada masa? Ai sai ya raina ki ,,,wani bangaren yace
Shifa na miji ne zai ma iya auro ta daga baya,na rasa soyayyar yay ashraf na rasa na yaya ash? Tabbbb kenan na cutu ?

.. nan ta budi Baki da azamanta ba kunya tace
Yaya ni bana son....au. ..
Sai maganan ya dauke mata chak a baki ganin yadda ya dago ta ya susutar da oily eyes dinsa ya zuba a nata

Ehem? Baki son meye jasmine ki fada min
..
Cikin dauriyar da batasan zata iya ba tace bana son auren nan
Ni yaya ashraf nake so"
Nan take hawaye suka biyo baya

Wani irin mugun duka kirjin sa yayi lokaci guda idon sa suka rine
Kamar ya wanka mata mari haka yake ji don kishi....amma sai ya danne zuciyar sa yayi calming din kansa ya riko hannayen ta,kamr baiji komai ba

Toh Kiyi hakuri bani nace zN miki dole ki aure ni ki bar ashraf din naki ba,
Ammmy ce, ko kin manta ke kika amsa mata kin amince? Ko zaki karya alkwarin nata ne?

Cikin jin kunyar abun da tayo ta sunkuyar dakai ba tace uffan ba,
Zuciyan tane ke cike tam da haushin kasa danne tunanin ta a kowani lokaci inta na gaban sa..

Chan ta budi baki Murya dishi dishi tace im sorry,

yaya naga wai kaima kanada wacce kake so ne ai kuma fa aure zamuyi

Nan ya tari numfashin ta shima yace
Haka ne,enada wacce nake so
Amma ke bazaki so ki cika ma ammy burin ta bane?

Duk da amsar ya kona mata rai
Haka ta daure ta gyada kai ta koma ta kwanta jikin sa

Shiru ne ya ratsa wajen,kowa da abunda ke masa zafi
Ganin zai iya jefa kansa matsala ya sa ya kauda tunanin tan

Nan ya takura ta suka ci noodles din
Har yayi nasara hankalin ta ya dan kwanta kafin ya fice a dakin

🙂😌

*suriem*
[23/08, 05:42] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_

_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*Page▶22*

Hakan rayuwar su ya kasance a gidan
Yau ana saura kwana biyu kacal da cika sati da rasuwar ammy

Hjy hadiza da har yanzu bawai jimamin mutuwar ammyn ya sake ta bane amma hakan ta daure ta soma shirye shiryen auren jasmine da ashween kamr yadda ammy ta bukata

Bangaren Ashraf kuwa ba yadda baiyi ba don yaji shirin meye mamyn shi keyi amma sam taki gaya masa komai
gashi ya jira jin amsar jasmine har ya gaji ya zuba mata ido, don shi mutuwar ba wai ya damesa chan chan bane.

Toh amma ba yadda ya iya a dole Mutuwar ammyn ya sa shi dakatawa da maganar don yasan yanzu jasmine bata hankalin ta sosai ,
tunanin sa tunda yanzu ba wanda zai tsawatar masa mutuwar ammyn ai tamkar an share masa hanyar saukin samun nasarar auren ta ne

Duk lokacin da ya tuno ashween kuma gani yake kamar bai isa ya hana shi jasmine ba
don karara yake nuna gabar sa a fili da shi.

Gefen Ashween kuwa yana iyakan bakin kokarin sa wajen kula da jasmine duk da cewa kullum sai tayi kokarin ballo maganan bata son auren nasu, a duk lokacin data fada hakan kuwa shima sai ya nanata mata itama cewa akwai wacce yake so kuma ba ita ba ce.

Duk da Abun na matukar damun sa don iya sanin sa jasmine dinsa shi kadai take so to meya faru?
Yana cikin wannan halin wayar sa ta buga kara ganin kamal ne ya sa
Bai bata lokaci ba ya dauka
bayan sun Gama gaisuwar su
Ya tambayesa salma,don yanaji jasmine din ke complain rashin samun layin ta kwata kwata

Na kamal yace ' wallhy akasi aka samu amma zansa ta neme ta kafin nazo,

Mekake nufi kafin kazo ita bazata zo bikin kawar tan bane?

Uhumm mubar wannan maganan tukun,, zahida fa zata kashe min aure jiyan nan da kyar na kalmaso salma"duk ta bi ta isheni da kira wai layukan ka basu shiga in kaji ta tamkar zata tashi sama.

Dan Karamin tsuka yaja sannan yace
Ai nafada mata bana bukatar disturbance bata ji ne kawai,
Kuma kaga bana son tasan ammy ta rasu before she starts thinking odawise..don wallhy yanzu yadda nakejin kaina zan iya mata illah.

Ohh my god ash, Hakane nasan baka bukatar ganin ta ,toh amma
Tace min dai nan da kwana uku zata dawo nigeria kuma zata shigo yola
ranar jummu'ah nan agidan ka zata sauka kamar yadda ta saba

Cikin halin ko enkula yace ""Kyaleta tazo mana ,ai ena dai dai da ita

Nan suka dan taba hirar su kafin ya tashi ya nufi dakin sa,
Ko minti biyar baiyi ba yaji turowar kofa dakin sa a hankali tare da sallama,jasmine ne a tsaye
A ladabce ta gaishe sa,sai kallonta yake don kuwa hijabin data sa bakaramin kyu ya mata ba,
Light make up ta danyi wanda ya sa ta dada fresh,tayi so cute and innocent

Dan lokaci ya dau yana starring akanta Chan ya ce, ena fata lpya dai ko?ko kina bukatar wani abu ne.

Tace, Dama mamy ne ta aiko da driver ni zan wuce

Wani garas yaji maganan a kunnen sa don har wani ciwon kai ne ya soma masa a take,
Uhum, toh Allah ya kiyaye inkinje ki gaishe ta..taKe care
Ya fada ba yabo ba fallasa
Dan karamin murmushi ta mayar masa tace toh yaya,sannan ta juya ta fice ,

Saukar ta kawai ya keji daga steps amma sai yaji kamr ya rugo da gudu ya bi bayanta su tafi tare
tunanin sa kawai kar ashraf yace zai kula masa ita a bayan idon sa,
Tuni ya zaga jikin windown ya cigaba da kallon ta
daga sama yana gani har ta lume cikin motar suka bar gidan

Itama Guntun hawayen ta ta share don tuni take jin wani mugun missing dinsa a zuciyar ta,

duk da ma tana kokunton samun soyyayr sa a rayuwar ta
wannan karon duk lokacin da sukayi sharing tare cikin sati dayan nan yasa ta sake jin wani zazZAfan kaunar sa a ranta

Cikin tunanin sa Bata hankara ba har suka iso gidan mamy,
A hankali ta sauko ta najin kanta daban sai sum sum takeyi

Gani na farko da hajiy hadiza ta mata yasa ta jin hawaye cikin ranta tace" hmm duniya kenan kowa akan hanyar sa yake 'Allah ya jikan ki hjya shahida,
Ji yadda yar nan ta jeme lokaci guda kamr bata da lpya, ohhhhhh
Allah ka bamu da sauki,

Tana kan jimamin haka jasmine ta rusuna ta gaishe ta, murmushi tayi ta kamo hannun ta tana mata jagora cikin gidan

Nan ma Basu ko kammala gaisuwar ba kiran ashween ya shigo
Enda ta tabbatar masa isowar jasmine din lpya
"
Daki mai kyau ta ajiye ta da kayan ta, domin tayi kokarin
Komi anyishi yadda ranta zai so duk da ma bazama zata yin ba..

Itako jasmine zugum take zauna gefen gado tayi tagumi
edan bata tuno ashween ba to salma take tunani"

Washe garii da safe bayan kammala shirin ta don ko fita ba tayi anan dakin tayi komai har breakfast da da kyr ta iya ci ita kadai

Ba laifi mamy ta sa baqin ta na larabawan sudan suka soma dan gyarata emergency dai dai gwargwado
komai ya tafi dai dai da shike a daki take wuni bata leka ko ena ba
kafin ace rana na biyun
Take fatan jikin ta ya dada yin sumul da tsantsi
sai dai har yanzu damuwan dake tattare da ita yana nunawa
Chapter 34 · 0% Book details