← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 132

Sashe 15

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

don harga Allah dazun wasu abubuwan data yi harda na ganganci aciki....tana kammalawa daure da pepper red towel ta shigo wajen washin machine dan ta tsoma kayan ta ciki
Nan ne ta lura da dan stain din dake jikin skirt din
Cikin sauri ta kame baki
Ohh God! Allah ya sa bai gani ba "
Bayan ta kammala shirin ta simple makeup tayo ta sanya gown din atamfa mai dogon hannu
Lokacin ne takejin sallamr talatu
Shigo tace a takaice
' dauke da tray ta tsaya sakamakon tsare ta da ido da jasmine tayi
Wannan fa?
Ehmm dama oga ashweeen ne yace bayan azahar na kawo miki abinci
Dan karamin tsuka tayi a ranta kafin tace
Ok ajiye
Ba musu ta ajiye zata fice jasmine tace
Ki matse min kaya na a machine pls
Toh, tace sannan ta wuce
Zama tayi kan abincin don kua yunwa dama takeji sosai
' tunani kala kala ke zuwa ranta
Wani bin in ta tuna yadda ashween ke nuna ya damu da ita sai tayi murmushi
Wani bin kuma inta tuna yadda take jin sa azuciyar sa take sai fargaba ta lullubeta
'tare da sauke ajiyan zuciya
Tace 'hmm so maso wani kenan
Allah ya sa zuciyata ta samu sauki ta dena rudin kanta akan ka ruhi..
Nasan kana kula ni ne kawai a matsayin sister ka Kwalli daya a duniya"ba don wani abu ba
Batafi wani cikakken minti 15 a hakan ba talatu ta dawo dauke da gogagen bedsheets a hannun ta
' kallo daya jasmine ta mata ta cigaba da cin abincin
"Da yaushe kika cire min bedsheet din nan

,kallon rashin fahimta talatu ta maido mata
Tare da cewa wallhy ban cire miki ba
Ni ma cewa kawai yayi na goge miki in ya hushe sai na kawo

Wa kenan? Ta ajiye spoon ta mida kallo kan talatu
Wacce ba musu tace "Ogah,

Shi ogan ne ya wanke kenan kome?

Uhm,ai lokacin bakki lpy ne'naga shine tuntuni dakin nan na kula dake
Ya jikin? tafada tana dan sosa kai

Dakata anan' Ni bance ki min bayani ba jeki...jasmine tafada tana rau rau da ido

Sum sum ta fice
Oh my god tace tana maida kanta kan sofa hade da lumshe ido cikin jin dadi
He's done so much ko wa ya sashi oho
Shyasa mana naga dakin yamin daban
haba
Nasan dai wannan ba gyran talatu bane

Haka ranar ta wuni jiran ko zai dawo ko ma ta kalle shi ta ji sanyi a ranta amma shiru
Har karfe 10 saura na dare bai shigo ba
"Hala ma yanzu yana chan tare da yan matan sa ni ena nan ena whalar da kai na
Zuciyar ta ya raya mata a yayin da take jingina bayan ta da window
' lumshe idon ta tayi cikin tunani
take wasu zafafan hawaye suka biyo baya
Haka kawai takejin mummunan kishin sa da haushin sa lokaci guda a ranta...
Takai minti 10 a hakan
Sannan ta laluba ta koma kan gado ta yi kwnciyar ta

Gefen tania kuwa bakar riga tasa doguwa mai diso dison ja wanda ya mata kyuw sosai
Suman kanta ta watso su gefe kamar yadda indiya keyi sannan ta zuba make up din ta irin na kece raini
' waya takeyi kusan minti 50 amma sam ba ajin meta ke cewa
Tana kammalawa ta kulle ko ena tsaf, du wani abun amfani kamr su document da sauran su ta killace sa ta kama hanyar zuwa gidan gonar zahida

Wuri ne mai dumbin tarihi a rayuwar su rodriquez family don anan sama da kashi 80 na arzikin su ya fara tashi ...

Fadin kywun tsari da haduwar wajen bata lokaci ne
Don haka makil yake da yan uwa da abokan harkan ta anata shagali
' wata figiggiyar mata ce kusan age mate din zahidan take cewa
Beauty queen banga bakuwar na mu ba fa har yanzu
Kinsa na taho da zuga na
Sunata jira
Ajiye wine glass wata ma agefe tayi
Tare da cewa nifa ayita ta wargaje kawai yau din nan da bala'i na zo nan wajen
In fa tsoro take a aika aje a dunkulo mana ita koya kuka ce?
Shewa ne ya karaade wajen
Ana ta kace kace

Ku tsaya ku tsaya zahida ta fada cikin dariya

'ku kwantar da hankalin ku mahaukaciya ce zata zo
Nan ma aka sake fashewa da dariya alaman yawancin su a buge suke
Jabir ne ya shigo
Ba jira ta karaso wajen nasa
How far ? Tace tana duban sa alaman tana sauraro

Kalau "ya dada matsowa gefen kunnen ta "
Na bincike sa da kywu ki kwantar da hankalin ki baisan da patyn nan ba fa"
Yanzu haka ma suna tare da kamal suna meeting kinsan kwanan nan zaa fara world olympics

Ohhhhhh perfect ta fada cikin wani nishadi tana sake murmushi
ya dube ta yace
' ke
Wai me zaki ma yar mutane haka ne
Naga kin wani dage sai hade hade kike yi ba sauki

Oh jabir ,forget it
Kawae zan dan koya mata manners ne
Ai ta tsokano tsuliyan dodo tunda tasa shi ya ci min mutunci gaban workers ena
Hmmm toh kiyi dai a hankali
If not zata sake fada masa ya miki wanda yafi wancan

Shhhhh no way, tafada tana dariya mai ban haushi
Ai zan dealing da ita ne in such a way dat sai na mata izini tayi magana nan gaba

Zahi....

Ehhhhh ,ta dakatar da shi da cewa

Just enjoy ta ce sannan ta wuce tayi gaba abunta
tsaban wani farin ciki dake bin zuciyar ta a lokacin
Oder wine tasa aka sake karowa aka baza ma mashaya sai shewa mata keyi ana rawa jifa jifa
Karfe 11 da minti 58 wacce ake kira da preetyhot ta yi ihu tana cewa i wish
yarinyar nan yanzu zata diro da sai na yayyan ka ta tanayi tana gwadawa da hannun ta .
Wani shewa aka sake bugawa
Ana mata tafi

12.00pm aka bude kofar wajen
Duk da basu sani ba mafi akasarin su saida sukace wow
Ganin yadda tania ta hadu
Dadin abunda ya sa kowa ya maida hankalin sa kanta saboda
Excatly irin shigar da zahida tayi shima ita tayi harta dan kunne da takalmi

Chak wajen ya dauke akayi shiru kowa da abunda ke sakawa a ransa
Wasu sunyi tunanin special quest ce kawai
Wasu suna kawo ko kanwar zahida ce
Amma ba wanda yayi tunani itace namar da suke jira tuntuni
Taku cikin jan aji da kasaita take har ta iso gaban zahida wacce numfashin ta ya kafe yana neman daukewa tsaban bacin rai
' ido da ido suke kallon juna fuskr tania dauke da wani shu'umin murmushi
'chan ta fashe da wani busashen dariya mai kularwa ganin yadda zahida ke bari har lashess dinta na rawa

' how dare yhu " zahida tace a hatsale

Shhhhhhh karki sake ki min tsawa
Zuyi tayi tana ma sauran yan matan wulakntaccen kallo sannan ta juya tamaida kallon tattare da sake dan karamin dariya tace ""hmm waht a kingdom party
Wayannan bayin ki ne ko kuwa yan cirani ne?

What? Preetyhot tace rai a bace

Nan fa mata suka soma mikewa tsaye alaman sun soma fahimtar wasan
Wacece wanannan zahida ?

Rai a bace tace ai ba sai na gaya miki ba "don itace mahaukaciyar da takeji zata hada shoulders dani
Just lokat at her
Tuni figagiyr cikin su ta karaso tana kare ma tania kallo
Don rainin hankali ma irin kayan ki ta sa? Ke wacece ?waye uban ki

Itama tania watsa mata harara tayi ' sunana tania ubana kuma sherrif
Wai tambayar kayan dana sa kike? nop, kiduba da kyau ai bansa kaya ba
Dan dafe kai tayi kamr da gaske
Ta cigaba " tunda na shigo nan na lura kuchakai ne ku baku da wardrobe choices,besides nazo hidimar mahaukata ai saida shigar hauka

Don shi mahaukaci zaki iya fahimtar da shi wani abun ne kawai inka maida kanka siffar sa,

Hannu ta mika zata zuba mata mari
Dam ta rike ta suna watsa ma juna kallon banza

Sosai wajen ya kaure da surutai wasu matan ana taro su zasu shiga fili

Ya isah haka ku kyale ta,rainin yayi yawa
Ku gwada mata ku ba mahaukata bane ita din ce ita kadai

Hmmm na nawa kuma? tania
Ta fada hankali kwance

Meke faruwa anan jabir ya fada yayinda yake kara sowa tare da zugar sa shima
Ganin yadda kowa ke tura wa tania bomoboman mugayyen kallo ya sa ya fahimci komai
Duk da ba wanda ya amsa shi

Ke ,,yace da niyyar juyo tania nan take ta buge hannun sa da karfi

A fusace zahida ta chakomau gwalbar giya zata rafka ma tania
ta tayi sauri ta kare kanta suna kallon kallo"
Buuuura uba ,,to hannun ki ya sake taba wanann anan sai na kashe ki ..

Heyy calm down sis ya fada yana zare hannun zahida daga jikin tania

Riko hannun ta yayi cikin sigar rarrashi' ki kyaleta
Muga gudun ruwan ta
Kiyi aiki da basira mana zahida

Gyada kai kawai tayi
Nan ta ja gefe
Hayakin taba wani ke busawa
Sosai ba ruwan sa sai kallon tania yake
Yanayin yadda tania ke kauce wa hayakin tabar ya burge zahida
Don Har wani yamutse fuska take tana korewa alaman bata so
A dabaran ce ta masa signal kan ya kara matsawa daf
Ba musu ya biye mata
Daga gefe kuwa sai kus kus ake
Jabir ma na tsaye duk dai maganar bai wuce kan tania da tayi tsayuwar ta a tsakiyan su hankali kwance

Busa Hayakin daya sake na karshe sai ta soma tari
Tun tanayi tana kakkaucewa har ta soma yi sosai ba tsayawa
Dariya ciki ciki suke mata
Ba mai ce mata sannu
Wasu burin su kawai akashe su mata lilis su huce haushin kiran su bayi da mahaukata data yi
' rike kirjin ta ta yi sai tari take
Cikin wajen jabir ne ya fara nuna damuwar sa da shike yana da mugun son mata
ganin abun yaki tsayawa
Har ta kama kan desk alamn tana bukatar ruwa
Chapter 15 · 0% Book details