← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 132

Sashe 102

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai abun ya taba zuciyan mamy don kusan kullum tana kiran sa taji ya suke sai yace mata lpya lau.tace wato ashe karya yake min? Ta tabe baki ta jinjina

Itama jasmine din bata barta ba sai da ta mata fada sosai na boye mata gaskiyan lamarin har saida aka kai ga haka.

Nan ta sa mai aiki ta kaita site din ta na da ,gashi sam ta boye halin da take ciki na ciwon ciki.

Sai da Ta shiga room din ta ta kimtsa tsaf
Ta kwanta ,nan ne ta shiga kukan zuci ta rasa me ke mata dadi a duniya baki daya.

Tana tsoron mamy ta san ta zubda ciki sannan ita kanta tasan tana bukatar kulawa

Karfe 10 saura ashween ya iso abuja
Baiyi kasa a gwiwa ba ya je gidan su salma direct.

Bayan ya gaida umma da jiki ya fita waje ya tsaya a farfajiyan gida
A ganin sa koda zasuyi wani rikici da jasmine kar su tada mutanen gidan hankali

Da kyar salma ta ajiye call din da suke yi da kamal don sosai ya tsara mata yadda zatayi maganan da ashweeen har ya fahimce ta..

Taci kuka sosai abun da yafi damun ta zubda cikin da kawarta tayi, a ganin ta to shi jariri mai laifin sa?
Haka dai ta daure ta fito tsaye ta hange sa yana jeka ka dawo ya kasa zama.

Tace sannu da zuwa yaya ash,
Murya kalar damuwa Yace salma pls ena jasmine?
Sai tayi murmushin karfin hali tace zauna nan tana zuwa yaya

Nan ne ya dan rusuna suka zauna ahakan ma sai leke yake yi ,
Sai tayi boyayyen ajiyan zuciya
Tace yaya,?

Ya dago ya kalle ta,

Tace kayi hakuri dan Allah ka kwantar da hankalin ka,a duniyan nan tamu ni mai laifi ne,kaima kuma haka ne, sannan babu wanda yafi karfin kuskure a rayuwar sa,

Yace haka ne salma.

Tace yay jasmine bata gidan nan,
Amma tana garin nan..

Bai bari ta sake magana ba A daburce yace a garin nan a ena kenan
Kinsan wajen dan Allah kimin kwatance naje mana

Nan ne ta fashe da kuka sosai. Dan dolen sa ba don yana good state of mind ba ya zauna ya shiga bata baki duk da baisan meyasa ta fara kukan ba

Anan ta cije ta bashi labari kaf abunda ya afku tsakanin ta da jasmine jiya zuwa yau da asubah

Yayi shiruuu Har wani sosa kansa yayi tsaban takaicin dake bin hanyoyin jinin sa
Gaba daya sai yaji kamar an tsaga zuciyan sa dan zafi da ciwo
Yana so yayi ihu ya ce makansa karya ne jasmine bata kashe masa dansa ba amma sai ya danne zuciyan nasa...ya sun kuyar da kansa kasa

Nan Salma ta shiga bashi hakuri ,jikin sa yayi sanyi ya kuma mutu zuciyan sa sai ta karaya
A raunane yace, bakomai salma ki daina kuka kema kinji
Allahn da ya bamu kuma ya amshe shi zai sake bamu wani
I have to go and see her bansan jasmine tayi fushi har haka ba
Yanzu Nasan tana gida barin je kawai salma. u take care ok?
Ta amsa murya a sanyaye tana binsa da ido
Tausayin sa ya gama balbale ta tasan dauriya ne irin na maza yayi har ya ke iya furta wannan kalamai

Yana tafiya har Wani bugu zuciyan sa keyi take ya soma hawaye shikadai
Har ya kai kusa da kofar gidan mamy bai dena ba idon sun gauraya sunyi jajir.

To amma Yasan in yayi garaje bazai cimma burin sa ba ,don yana so ko yaya ne jasmine ta bashi dama ya fada mata gaskiyar wacece zahida awajen sa.

Ya kudira yau din sai ya gaya mata sannan ya bata hakura ko zai samu sauki ma zuciyan sa.

Anan bakin gate yai horn aka bude ya shiga ciki ya tsaya
Mai gadi ya aika akayi magana da jasmine din

Da shike sakon yazo mata half, rabi da rabi, kawai ance madam ana kiran ki, bata san ko waye bane kawai ta sa hijabi fito falo ba kowa tabi dakin mamy nan ma shiru alaman tana wanka
Sai ta dawo ta leko ta waje..duk tunanin ta ko ma salma ne.

Bata ganshi ba amma shi ya ganta da sauri ya karaso ya damke hannun bazata ta ya jawo ta gefen

Jin shi din ne ya sa ta fashe da kuka tace ka kyale ni"ni ka sake ni

Cikin firgici da tashin hankali ya juyo ta tare da dan jijjiga ta yace why?jasmine Meyasa zaki kashe babyn mu ..

Cikin kuka da kokawar kwace kanta tace ka sake ni an kashe din.
Just leave me alone

Ena dai Danka ne damuwar ka ?
Ai kaji ance na zubar da mistake din naka ko? to ai
Magana ya kare saura ka fice kaje chan kayi rayuwar ka da wacce kake so.

Shi duk wannan ba damuwar sa bane cikin dauriya yace jasmine,please let me xplain give me a chance dan Allah ko 5 mint ne,
I think u shud know what happen but pls ki nitsu ki saurare ni

Ta fincike hannum ta daga nashi tace banayi,
i hate u,
Ni Bana bukatan wani xplanations dinka,its over.
Sai yayi shiru yana kan kamo hannun ta tana ficikewa
Ta soma hawaye tace ai
auren alkwari ne dama is not ur fault

Na fahimce ka U just took advantage of that to fool me kana nuna min ka damu da ni na karya just to used me don samun biyan bukatan ka.

And u know whats worst?Dama tunda nice nake son ka, takai masa duka kan kirji tace
Im so stupid in love with u, ta kuma ja sheshekar kuka tace but its over now ai kayi ma kanka zabi ni ba komai bane a wajen ka.

Alkwarin ammy is no longer there tsakanin mu
To da shi ma ya na kare a hannun girfrnd din naka bare yanzu babu.
And u still expect me na rike cikin ka? The bigest mistake of ur life ,kan fuskar sa tace u can
Go to hell na zubar din.
Sai ta fashe da kuka mai ratsa zuciya jikin har ta na rawa..

Shikam Duk ya rikice ya rasa ya zaiyi mata, burin sa kawai ta nitsu ko da kadan ne ya fada mata gaskiyan lamarin sa

Hawaye sun gama wanke fuskan sa bai motsa ba ya dada kamo ta kusa da shi yace"kiyi hakuri im wrong jasmine nasan bana miki adalci
Amma Na roke ki just listen to me once kiji abunda zan fada miki mana kiyi hakuri dan Allah.

Cikin masifa Tace bazan ji, nace ka kyale ni ko

Ya cigaba yana kakkamo ta tana fizgewa tana dukan hannun sa da iya karfin ta cikin kuka,

Can ya jawo ta jikin sa ya matso ta yace jasmine na amince kimin duk wani hukunci bayan kin saurare kar ki azabtar da ni haka.
pls just 1 last chance ki saurare ni

Still Tace no, kawai kyale ni har na mutu bazan saurare ka ba
mayaudari,maci amana kawai.mugu ta karashe cikin kuka

Ganin in yabi na rartashi abun bazai kare ba sai yayi kokarin jan ta da karfi zuwa motar sa don su bar gidan ko zata saurare shi a hakan

Yana kamo hannun ta tsala ihu tana cewa ya sake ta,ita bazata bishi ko ena ba.

Cikin haka suka ji ance me nake gani haka?
Mamy na kara sowa ta kuma cewa Ka sake ta ne ko sai nazo na saba maka?

A Lokacin ashween ya gama daburcewa shika dai yasan abunda ke masa zafi aran sa

Jasmine ko sai fiffincikewa take a hannun sa shikuma fir yaki sake ta

A fusace mamy ta kara so ta bangaje hannun sa ta ja jasmine gefe tana kallon sa sai tace" ashween na tambaye ka mana?

Ya sunkuyar da kai kasa yayi shiru baice komai ba

A raunane Cikin bacin rai Mamy tace da gaske ne tulin lokacin nan da ku kayi aure akwai wata yar iskan yarinya agidan ka tare da jasmine?

Nan ma Yayi shiru baice komai ba.

Cikin tsawa tace bana son silence just answer me"

Hawaye ne sabbi taf kan fuskan sa ya dago a sanyaye yace haka ne.

Tayo murmushin takaici tace, kuma kace zaka aure ta ko?

Cikin dauriya yace eh nafadi hakan mamy amma..tayi saurin dakatar da shi tace
Look young man dama abun dana ke so naji kenan da ga bakin ka ,
Ga hanya ka fice min a gida na dis minute
Kar ka dawo min nan sai da takardan sakin jasmine.

A razane ya dago ya kalleta dat minute ya zube kasa kan gwiwar sa yace mamy na rokeki kiyi hakuri dan Allah ki saurare ne ,pls let me explain kar ki raba ni da jasmine.
Ta masa shiru tama kau da kai
Kuka sosai ya fashe da shi har yana kamo kafan ta amma tana shiru sai hawan diri take zuciyan ta ma mata zafi da balbalin masifa

Chan ta juya ta kalli jasmine din dake numfashi sama sama tana kuka tace ke wuce ki shiga ciki
Ta juya ta kalle sa shikuma tace in kaga dama kayi ta zama anan ni dai naga ya maka takardan saki kadai zai sake hada ni da kai.

Ya mike tsaye dan harga Allah yanzu kam he cant bear d pain anymore

Ganin jasmine ta juya zata shige ciki ya sa yayi wani wawan yunkuri ya chakumo ta jikin sa.

Duk jikin sa rawa yake har hancin sa yayi ja yace mata kar ka tafi jasmine pls ki saurare ni ,
I truly love you, in kika barni ya zanyi da rayuwa ta, i cant just live witout u, pls listen,all i want is just 1 chance dan Allah,dan Allah kar kimin wannan hukuncin.

Ta bishi da kallin tausayi For the first time kalman i love u ya fito a bakin sa
Tabbas tasan kuma da gaske ne don a lokacin tasan yanayin yaudara ko wasa ba zai shigo ba.

Amma sai ta kasa cewa komai tana kallon sa yana mata kuka kamar karamin yaro yana maimaita kalma daya tayi hakuri ta saurare shi.
Chapter 102 · 0% Book details