← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 132

Sashe 3

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ah ah, ki tashi kije chan kijira ni dai ena zuwa ammy tace...amma ko ta kula
Nan ta soma chune fuskan ta tana maganan cikin kiriniya da shagwaba
Ammy kuwa ta biye mata ta fada ta sake na natawa amma sam taki jin ta
Suna Cikin haka wani sassanyar qamshi ya dosu su' wayr sa ce makale a kunnen sa

A hankali yake magana fuskan sa dauke da wani annuri da annashuwa gaba dayan su saida suka juya suna kallon shigar tasa data masa bala'in kywu
Simple jumpa ya sa fara ta yadi shara shara
Hannun sa dauke da wata kafurar wristwatchh na hublot wacce hasken fatar sa ya dada sata yin baki ajikin sa 'baisa hula ba don haka suman kansa suka zube kadan a bayan kunnen sa sai
sheki yake
Ko ya daga kai Yana magana yana dosu su"
' gefen ammy yayi ya daura mata light peg a gefen kuncin ta
Yana cewa" sai na ganki
And dont be late please
Sannan ya katse wayar

Ido hudo suka yi da shi lokacin gaba daya yanayin jikin ta ya sauya
Duk da asirtaccen murmushin daya jefa mata
Itako Wutar kishi ba karamin huruwa yake a ranta ba
' yanzu nake cewa zan duba ka
Kaga sai kaga nan ma

"yh,na tsaya waya ne ammy
U look great ..ya fada ma ammy amma idon sa nakan kallon jasmine
Ganin haka yasa ta dan dukawa kasa
A ladabce tace
Ena kwana yaya ?
Katashi lpya,,

Lpya lau..ya fada a takaice tare da mikewa tsye yana rike cikin sa
Ammy am so hungry.

Ahh Muje mana
Dama ai kai kawai nake jira ka fito
Princess shall we?
Nan hankalin ta ya dawo daga nisan tunanin bacin ran data ke ciki a lokacin

Ba tace uffan ba ta mike tabi bayan su
Sama sama ta ke cin abinci don kuwa tunda ya zauna kira ke faman shiga wayar sa
Gashi sam ta kasa tantance namiji ne ko mace ne
Idon ta fam ya cika da hawaye amma ta kasa sauko da su sai ma dura ma cikin ta ruwa data keyi
Sosai suke tadin su na kaka da jika mai kama da na đa da uwa ita da ashween suna ta dariya

Shirun da tayi ne ya sa shi kai kallon sa kanta
Shi dai sosai abin ke damun sa sai yaga kamar a takure take
Dan haka ma ya mike tsaye"yace ni zan fita ammy
Amma bazan dade ba zan dawo

Nooo way ,tace tana dan hararar sa
Zauna ai ba mu gama maganan mu ba

Wani sanyi jasmine taji aran ta da ammyn tace haka amma tayo xugum tana wasa da spoon
Toh ena jin ki ammy

First of all
To kai din ena zaka yanzu bayan nace ka huta na sati agidan nan

Zanje na siya abu ne kawai i need some toiletries ammy

Ok yayi'

Dama maganan waliman ka dana hada
Auntyn ku hajiya hadiza
Tun jiya take famr son taji ra'ayin ka amma kamin shiru ko kunyi waya ne
Dan jingina kai yayai da chair
Yace
Na kira ta da safe ammy
Amma gaisawa kawai k
Mukayi na sanar da ita na iso lpya
She called me tun ena japan har tai min addua

Dats nice tace atakaice..
Toh ya ake ciki
How do yhu want it kasan wannam duk dan kai zaa shirya sa ko?

Yes ammy
Ni ai bani da matsala ko yau ne ma am ready
Dan rau tayi da ido tace
Ready?
Uhm ,uhm
I want it to be a grand welcoming party
So ena son ka gayyace kowa da kowa naka

Dan murmushi yayi yace done .
Angama ammy ur wish is ma command

Kema haka princess cewar ammy tana maida kallon ta kan jasmine dake kai kawo a zuciyan ta

Ye..sss ammy tace a sanyaye
Nan ta mike tayi dakin ta sum sum
Kallo duka suka bita da shi ba wanda ya iya tanka mata
Yana dauke kai suka hada ido da ammy
Waccw ta sake dan karamin murmushin daya sa shi jin kunya

Na tafi nikam..

Zo nan...bangama ba

Ba musu ya juya yana kallon ta
Nace ba ..
Why dont yhu take your sis along
Ai sai itama amata toileteries din ko?

Ah' a
Ammy ki bari ba yau ba ..zan kaita intana so yanzu am in a rush

Ok toh a dawo lpya tafada tana kokarin haurawa sama

Cikin Babbar motar sa ya shiga kirar matrix marron ya fice bai tsaya ko ena ba sai wani katafaren ma'aikata mai suna k and k agro-chemicals industy
Kai tsaye ya mike wata office ya kusa kansa ciki tare da sallama
A tsaye ya tarda shi yana jeka ka dawo cikin suite dinsa baka wanda tayi ma dark skin dinsa kywu sosai
My man"...suna hada ido ya fada suka kwashe da dariyA ya zago cikin sauri sukayi musabaha suka rungume
Juna
'Welcome back bro..so dama da gaske kake yi?
Na dauka irin abun kan nan ne sa kasaba

Toh yanzu dai gani na taho so whats up'

Kalau am just glad Ka dawo dai finally

Yeah alhmdullhi ..abu kamar wasa yanzu dai
Kasan me ?

No sai ka fada

Wai welcome partyn nan da nake gaya maka aunty na ta na shirin hada min shine yanzun
Suka dago da magana
And yhu know akwai abubuwa agaban mu"

Dan shiru kamal yayi kamr mai nazari sannan yace
Tashi muje gida mu karasa achan
I have an idea..

Ba musu ya tashi suka nufi gidan su kamal din
..
Gefen ammy kuwa ta gama sanar da kusan duk friendly business patners din ta na ciki da waje don
Ta gama sawa a ranta ranar ne zata nuna ma ashween clients dinta ta kuma sake masa dukkan harkokin ta na business itama ta huta tunda tsufa ya kamata sosai

Zaune Cikiin wani tunanin akayo sallama
'doctor?tafada tana mikewa da kyr
Ah zauna hajiya shahida
Ya jikin
Doctr sikirat lawal tafada

Toh jiki dai alhmdullhi doct tafada tana dan dube dube
Bayan sun kammla gaisuwa nan ma ta dan mata tambayoyi game da kanta kamr yadda suka saba..
Ammy tace
Yawwaa likita nace yanzu zamu dinga haduwa a office dinki kawai saboda yaro na ya dawo kasar nan gaba daya and you know very well ba na san su gane me nake ciki ko?

Haka ne 'ajiya
Amma nidai har yansu ena shawartn ki da bayyana musu ko da mashi babban ne
Gudun kar wata rana wani abun yafaru unxpected.i think thy dersv to knw d truth

Ah' a likita ,insha Allahu bazai faru ba ai ena kiyaye wa likita
Gaskiya bazan iya sanya ma yara na wannan dawainiyar ba .nasan su sarai zasu daura wani damuwa akan su 'cikin ranta tace musamman ma shi babban da kike tunanin zai iya rike wa

Toh Muyi sauri kafin yaro na ya dawo yace bazai dade ba
Ba musu likita ta shiga mata kwaje kwaje
Sannan ta bata magani kamar yadda suka saba
Ita da kanta ta taimaka hajiya shahida har zuwa site dinta
Sannan ta samu ta kwnta
Jim kadan bacci mai nauyi ya kwashe ta..

Jasmine da ke dakin ta ba abunda suke kullwa illa yadda zasu fuskanci babban taron yaya ash dake gaban su
" komai sun fara tsara yadda zasuyi shi itada aminiyar ta salma kama daga spa, gyaran gashi..
Make up,dresses,shoes jeweries ..hatta gift saida suka tsara yadda zasuyi masa ranar

Misalin karfe takwas na daren ranar kamal ya soma broadcasting event dinsu a media
Yana tura iv ma family and friends musamman yan mata wato slay queens ke kokuwar samun wannan Ivn duk da ma wasun ta social media aka sanar da su,
Ko kafin yagama ajiye wayar sa ya amsa kirar mata sunfi akirga kowacce da salon ta na neman samun shiga hidiman

Karshe kashe wayar sa yayi ya dauko dayar wacce private ce ba kowa ya san shi da shi ba ya kira
" cikin murmushi mai kama da dariya yace "Ash akwai chwakakiya
Ladiea are on dis team 100%
Dan karamin tsuka yayi yace
Chan musu.
Just make sure kasan kalar da zasuyi matching da plans din mu dai
I want highly classical and unique girls
Kasan zahida ta wuce yadda kake tsammani ko?
Ni wallhy duk fargaba nake bansan ko tania zata iya ba gobe in munje

C'mon ash ,
Have faith mana,kamal yace' komai zai zo mana cikin sauki
Ita zahidar sarauniyar ena ce ?
I dont think tania is less agaban wata ya mace kaima kasan ta hadu iya haduwa

Yh naji...Allah ya kaimu goben
Ya katse wayar sa
Juyawar da zaiyu sukayi ido hudu da jasmine wacce tuni ta tsane gefe daya fuskn ta a dan daure
Wani zazzafan ajiyan zuciya yayi a boye
Sannan ya mata hannu alamn ta karaso
Ba musu ta taho sum sum. Jiki a sanyaye hannun ta dauke da paranti
" haddaen french fries ne da egg souce wanda yaji nikakken namar kaza'
Gefe guda kuma glass jug ne
Mai dauke da fresh apple and cocunut juice
Chapter 3 · 0% Book details