← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 132

Sashe 2

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To me ye ne? Tell me,tace tana duban sa
ko ya kula shikam
Dada lume kansA yayi kan cinyar ta idon sa alumshe a hankali yace
Stay ammy"
Kar ki taba rabuwa da ni kinji?
Wallhy bazan iya ba in babu ke. ena ga Zan...zan...sai ya kasa karshewa muryan sa ya soma rawa'
Shiru ne ya ratsa wajen yayin da hjiya shahida (ammy)ta cigaba da sassaita sa tana shafa suman kansa a hankali ba tare da tace uffan ba
Itama
daurewa tayi sosai din tasan meya ke nufi .

Sam ashween Baya so ya sake dandana zafin rashi me a rayuwar sa..
Ita kanta tasan ya shaku da ita shakuwa na ban mamaki
Don Ko da kudin da suka mallaka za'a bayar ace ba ita ta haife shi ba ba mai yarda da hakan

' Ashween ka tashi min nikam zaka karya min tsofafin kafafuwa ta ba fa makai na ajiye ba
WannN na Jikoki na ne..tayi maganan cikin wasa don ta kawar da yanayin su a lokacin

Kamr an tsakure shi ya mike zumbut
Yace too in ba jikan fa?
Ai har yanzu tenure na bai kare ba

Dan zungurin sa tayi tace
Come here..
Share wannan abun a fuskan ka
And promise me bazKa sake min haukar da kamin yanzu ba
shiru yayi baice komai ba sai ma daure fuska dayake shirin Yi
Zaka goge ko nayi tafiya ta?
Da sauri ya sa hannu kamr karamin yaro ya share hawayen san
Baice komai ba

Good ..muje ka ci abinci don tun tuni nake jiran ka

No ammy .na koshi

Meyasa? Kai
Bana son sakalci fa, kaji min iyeyi tashi muje inga guri

Zaman diris yayi ya make kafadun sa "
Im not going untill u promise me nima,

ikon Allah,tace tayi tsaye tana kallon sa
Ehen go ahead ena jin ka
" juyawa yayi gwuwar sa na kasa yace ammy
Na amince bazan sake kuka ba in kika min alkwari bazaki barni ba har abada"
Serious face din daya sa ne ya so ya bata dariya amma sai tace
Promise son"
Oya tashi muje
Allah shi zai bar wanda ya ga dama kar ka damu

Bai saKe cewa komai ba ya bi bayan ta
Suka nufi dininng
Cikin so da kulawa ta sa shi ya cinye abincin sa tas bisa kan tsari kafin suka dawo palour suna taba hirar su

Ammy, ena jasmine ne bangan ta ba tunda na shigo

Uhm well,, kawar ta tazo ne shyasa bazaka ganta ba,
Ok suna daki kenan?

No.

What. ?Cewar sa yan dan yamutsa fuska

Sun fita nace ..na dauka ai ka gansu don basu wani jima ba

'haba ammy, amma kinsan na hana ta wannan yawon tsiyar ko to meyasa kika barta ?

Ahh kaji min dan nan,yo ita kenan kullum daki sai kace amarya? Da sannu na nace taje
Kaga ni bana son dramn ku nan kar kuma ka taba min yarinya ehe

Shiru yayi baice uffan ba don ji yake kamr yayi iska
Ya tsamo ta daga duk inda taje yanzu

Har kusan 6':15 pm
Suna zaune da ammy
Nan ya tashi ya tallafawa kakar nasu zuwa sashin ta ya kammala mata komai da komai kamr yadda kullum ya saba tun kafin ya tafi abroad ..
Sannan ya mata sai da safe ya sauko falo abunsa
"
Can abun bai masa ba ya tashi ya nufi massallaci daganan ya yi tsayuwar sa a farfajiyan gida"

Suman tsaye tayi tana kare masa kallo daga nesa yayin da suke shigowa
Cikin motar salma data dawo da ita
Ita kan ta salma saida ta maida hankalin ta
Don kuwa da ban wani abu ba sai ace wani aljanin suke gani
Ga hasken wutan ko ena tamkar rana haka wajen yake,
Suman Kanshi sai sheki yake hannun sa dauke da tasaddaen classy phone dinsa yana latsawa

Dagowa yayi Kamr ya san ana kallon sa
Charaf suka had ido da salma da shike itace a driver seat
Ba tan tama ta bude kofar ta sauko
Jasmine na biye da ita dauke da gift bag na prada a hannun ta
zuciyan ta sai dum dum yake kamar zai fita ta tsakure gefe shiru,
Fuska ba yabo ba fallasa
Yace susu?
Kece kika girma hakan
Salma da kunya ya rufe ta
A sanyaye tace sannu da dawowa yaya ash

Thank you..ya gida ?fatana kuna lpya right?

Lpya lau
Tace da dan karamin murmushi
Ni zan wuce yaya sai da safe
Ok ..yace a takaice idon sa nakan jasmine da tuni ta sunkuyar da kanta
Daf da ita salma ta zo ke kuma me haka ? cikin rada tafada tana dan pinchin dinta a daba ran ce
Wanda ya sata dada rudeWa ta riko hannun salma tare da dan
'juyawa zata bita kuma

Jasmine!!!
Taji yace

Da sauri ta juya enda salman itama tayi saurin lumewa abun ta

Kamr bazata taka ba haka har ta iso daf
Da shi ta dan rusuna a ladabce tace
"barka da dawowa yaya
ka dawo lpya?
Shiru ya danyi sakamakon wani kira dayake shiga wayrsa
yayi ya sakeyi amma bai daga ba kuma bai kashe ba

Kamr baiji gaisuwan nata ba haka ya sa hankalin sa akan wayar sa
Sai can ba tare da ya kalleta ba yace"
"for whateva reason kar ki sake kaiwa wannan lokacin awaje kinaji na?

Gyada kai tayi murya ciki ciki tace
Naji"
Good ' tashi ki shiga.

Ba musu ta mike ta shige ciki da sauri

Kallon ta yakeyi har ta lume Zuciyan sa gauraye da wani irin yanayin da ya kasa fayyace
wa kansa
Ganin ta kawai yaji nauyin dake kan kirjin sa ya sauka
Ko ena a sasaan jikn sa yayi light bayajin komai
Sai murmushin daya ke sakewa shika dai

Gefen jasmine
Kuwa tana shiga dakin gado ta haye
Da gudu ta fashe da wani irin kuka
' wayyo Allah na
Na shiga uku..
Wannan wani irin azaba ne nakeji a raina?
Lumshe idon ta tayi gam tana kawo lokacin daya barta tsugune ya maida hankalin sa kan wayr sa

To Wace ce wannan take kiran sa?
Meyasa take kirar sa..zir zir wani hawayen ya sauko mata
Tayi wirgi da pillown kasa"he's mine tafada a raunane tana cigaba da sharban kukan ta'kamr ance mata dagasken mace ce ke kiran sa
Saida ta yi mai isarta sannan ta shige bath ta kimtsa kanta
Gaba daya mood dinta ya canza
Tunani kala kala take yi
Ita kadai ..nannauyan ajiyan zuciya tayi tace
"i missed yhu alot ka kara kywu da kwarjini
Ure d most perfct handsome guy ive eva seen so cute"
amma yaya kamr baiyi missing dina ba
Salma kawai fa ya kula'har da cewa ta girma" ta karashe tana tabe baki
Shiru tayi kamr mai tunani can sai ta kashe lamp din ta ta ja bargo ta rufe kanta jim kadan bacii ya dauke ta.

*surriem*
[23/08, 03:02] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_

_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*Page▶2⃣*

5.21am dot ya farka tare da addua abakin sa"la ilah illah wahdahu la sharika- la, lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shai in qadir,subahallh ,walhamdullhi,wa laa'ilah illah wallahu akbar..rabbigfirnii ..sannan ya daura da bismillah ya sauko daga kan gadon sa

Bathrum ya nufa a cikin mintina 12 ya fito a gaggauce ya kimtsa ya nufi masjid'
Gefen ammy kuwa komai ta sanya anyi sa akan tsari musamman breakfast din su na ranar
Don kuwa ita da kanta ta hada masa wasu abubuwan
da shike shi ba mutum bane da ya cika son cin junks ..akasari ya fi ganewa natural flavours na tradional foods kamr vegetables ko fruits.
Don haka ko drinks din daka jera su awajen duka handmade ne bana kampani ko daya.

Wajen karfe 9 da rabi saura Video call suke yi yayin da jasmine din ke rike da setin dresses yakai kala hudu a hannun ta sannan ga wasu chan zube kan gado
'fuska kalar tausayi tace
Haba salma
Munfi awa daya anan in banda tsokana ta ba abunda kikeyi
Pls now""ke ba dama mutum ya neme taimakon ki baki shiru?

Hannu biyu salma ta rike tana jan kunnen ta
'Am sorry jasmine.ke fa wallhy wani lokacin baki san wasa ba
Ai na riga na fada miki kisa normal atampar ki zaifi kamar waccan ta mata nuni da wani chan wanda ta yasar gefe..dark green da ratsin ja
" ohk shikenan
Amma kin tabbata zanyi kyuw?
Oh my god jasmine ..ki sa toh na ganki yanzu..
Ba musu ta mike ta sanya skirt da rigar atmpr a dresing room sannan ta fito da sauri tanayi tana jan skirt din don ya mata das das yabi curve din jikin ta
" wow,
Kinga ni ,i told u wAnnan zaifi
U look terrific .waye ma tayi miki wannan dinki?
Dan murmushi tayi tace
Kathy anthony mana kin manta ne?
Ni wallhy hr wani kunya nakeji ta karshe maganr a shagwaban ce
Sannan suka kwashe da dariya

A hakan har suka rabu enda tayi maza ta kammla kwalliyar ta
ta shirya tsaf ta fito
Tayi kywu sosai duk da ma bata tula make up ba
Sai round cute face dinta ya dada bayyana dimples dinta dake gefe gefe..
Tun daga kan steps ammy ke kallon ta bAta hankara ba sai yauki take tana takowa
Tubarkallh masha Allah ammy ta fada a zuciyar ta tana dan mirmushi

Karasowar ta ke da wuya ta fada kan cinyar ta da gudu
"good morning again most gorgeous ammy in d world

Kokarin dagota ammy take amma sam sai narkewa take ajikin ta tana dariya ciki ciki
Zan ci kaniyar ki fa princess karya ni zakiyi ne
Nan ta dago tace
Wane ni?
Kinyo kyau ne sosai yau "
Ta dan kashe mata ido
Murmushi kawai ammyn tayi ta ture ta gefe
Tana cewa
Bani son shirme bayan kin barni anan tun tuni kinata kwalliyar ki
Karfa kice min wani wajen zaki kinsan yayan ki baiso ko?

No" ammy ni bance zanje ko ena ba fa

Ok fine to, taso muje dinning bari na dubo sa
Dan tabe baki tayi
Sannan ta kalli wristwasch din ta
Karfe 10 da rabi?hmm lallai yaya na hutawa
Toh nima zan biki
Chapter 2 · 0% Book details