← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 132

Sashe 23

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga ranar ya zama kamar an huro wutar fitina a zuciyar ashween haushi take basa tunda ta amsa tana son ashraf agaban ammy don haka ma ya yanke baya shiga damuwar ta
Yanzun Sosai ya sake yana harkan rayuwar sa da zahida baiya ko boyewa kamr da chan
Sau dayawa yakan ba ammy waya su gaisa
Wani lokaci har ya kawo ta gidan

Tun jasmine tana kishin abun har ta soma danne zuciyarta itama ta sake
Ta fara bada kulawa ma soyyayar su da yay ashraf
Sai dai basu haduwa don sam ammy ta masa katanga da zuwa hira wajen jasmine
"
Kwanaki na ja jasmine Sosai tayi rama cikin dan kwana biyun don aganin ta ashween ya riga ya kufce mata kenan har abada
" musamman inta tuno zahida ga kywu,ga kudi da aji,sai taji wani shaukin son ta cire duk wani digon son ashween aranta
Hakan yasa ko zahida ta zo gidan sau dari ne bata fita,haka ma cikin su ammy ba wanda ya kula ya ce ta fito
Don tuni ammy ta fahimce komai game dasu amma sai ta zuba musu ido kowa ta kyalesu ...

Shiru shiru salma ba labari yasa jasmine dada shiga damuwa,
Yau kusan wata biyu kenan
Komai ya lafa mata ,alhamdullhi yanzu wani abun bataji aranta game da shi
Gaba daya ta mika almarin ta ga ubangiji...sai ya zamo ma bata kaunar ganin sa duk iya kokari tanayi kar ma su hadu tagan sa

Ji takeyi ena ma ace son data ke masa ya koma kiyayyya.. Kullum tana gode ma Allah a ganin ta tunda baisan tana son shi bama komai ya zo da sauki

" Shiko ya kasa fahimtar ta musamman data biye masa itama tana boye kanta
Amma sai yayi tunanin yaranta ne kawai ke damunta
Hakan yasa sai yayi kamar bai masan ta nayi ba .

duk da abun na damun sa sosai amma ko sau daya bai taba nuna mata ba
Sai ma dada jan jikin sa yake yana dulmuyar da ita akan cewa eh da gaske ne baya yin ta ..
Tsawon wata uku kenan ba abunda ya zanca..

Exams over👅👯🏻‍♀

*surriem*
[23/08, 03:02] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_

_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*Allah ka kare mana yan uwa musulmai a duk enda suke,ka kuma bi kadin wayanda aka zalunta a hanyar jos,ya ubangiji ka saka mana😪😪😪*

*Page▶14*

Ashween ne Zaune a asibiti kamar da gaske
Kamal ya tinkaro sa
Yana dariya ciki ciki kamar munafiki ya sai yazo ya tsuguna daf

' daure fuska ashween yayi ya kau da kansa
Wanda ya dada sa kamal fashewa da dariya,

Da Allah ni ka kyale ni,banson iskanci fa
Ya fada a fusace

Ok calm down ..mr zahida rod
Wallhy dramar ce take bani dariya
Lallai yarinyar nan yar iska ce ji enda tayi lumui ta kwantaa asibiti ta hanaka motsi? Hmm

Mswwww kayi na kudin ka fa kamal,
Itama Ba barin ta nayi ba ta san hali na sarai,so nake ta sa hannu akan wancan abun dana fada maka shiyasa kaga ena bata lokaci na anan din im so tired..yafada sounding serious

Ka kara hakuri kamal ya dafa shi ..fuska ba yabo ba fallasa
Ya labarin ita madam hidayat din? Yaushe xata dawo daga china?

Ashween yace, In four weeks time,amma kafin nan insha Allahu na kammala komai sai dai next plan
Gyada kai kamal yayi yace " insha Allahu roh
Barinje na duba babyn namu ....ya mike ya shige cikin room din yana dariyar tsokana

Zahida dake kallon karasowar su ta glass din kofar Kifi kifi ta so mayi da ido ,tana nishin karya "shiko kamal sauya fiska yayi ya dube ya yace
Sannu zahida luv ,.hw r u feeling now?
Tace, Fine ,sai yanzu kake zuwa ko ai ka kywta

Dan tabe fuska yyi yanayin tsokana yace " so kike ki hada mu biyu ki nakasa..abokina fa har ya rame pls get well mana kar shima fa ya kwantaa
Dariya tayi cike da jin dadin maganan
Amma sai ta marairace fuska tana duban sa
" bayan sai nayita ihu anan kafin yazo kusa dani,.ash is so lazy kamal.. ta karashe a shagwabe...

Ashween Murmushi kawai yayi baice komai ba,
Don shi ya san me take nufi,. Amma ya riga yayi alkwari har ya mutu ba abunda zaisa wani abu mai kama da romance ya shiga tsakanin sa da ita...ko da kiss ne

Hmm karki damu kamal yace
Ki warke kawai..kinji?
Kamar baby haka ta gyada kai
Jefa jefa suna hira,har suka watse

Gefe guda bangeren asibitin
Ammy ne zaune a counseling room tare da doc
" zugum tayi
Bayan ta kammala karanta sakamakon gwajin ta
Kallon nitsuwa doc ta mata sannan ta ce
Kinada sauran lokaci hajiya shahida
Kar ki manta farincikin ki is important a wannan stage din
Kiyi kokari kibi kai'dojin maganin dana kara miki yanzu in akayo haka ba matsala insha Allahu

Murmushin karfin hali ammy tayi tace
Hakane doc,kullum kina fadan haka karki damu insha Allah zAn yi kokari

Dan shiru doc tayi...daga baya tace tun da nake bantaba ganin mace mai karfin zuciya kamr ki ba hajiya,
Sau dayawa mutane masu dauke da brain tumour ke qarar da rayuwar su ta hanyar damuwa da kunci tun kafin ciwon ya yi halinsa
Amma ke kam sabanin haka ne ,,na miki murna

Murmushi kawai tayi ta ce" nagode kwarai ..kema ai kina iya bakin kokarin ki Allah dai ya saka miki da alkahiri..

Bakomai hjy en akwai matsala a kirani anytime

Insha Allahu ..Sai anjima sukayyi sallam ta wuce gida

Tun daga ranar ammy ke kokarin danne zuciyar ta
Amma ena waNi bin damuwa da tunani na cin karfin ta tasan mutuwar ta yazo ba shakka
Kullum tunanin ta rayuwar ashween da jasmine
Musamman Da yanzu ta lura ko maganan ma ba sosai sukeyi ba.

Kwana na tafiya kullum tana dada kirga ranakun ta ne ,..don likita ya tabbatar mata tana mataki na karshe

Amma Haka take daurewa ta danne duk wani alama ,.tana cin abinci ta tana shan maganin ta amma duk a boye ba wanda ya lura da halin da take ciki

Bangaren su zahida kuma Yau kusan sati guda kenan media tana news akan familyn madam hidayat wanda mafi aka sari sun samu tallafawar kara bude ido ne ta wajen ashween, yanzu haka jabir ne zaiyi wani gagarumin concert na tallafawa yan mata wanda basu da galihu karkashin wani companyn kamal...

Daga gidan hajiya hadiza kuwa ashraf tsungune yayi kansa kasa yana kukkuni
"Mamy amma wannan ba adalci bane
Ni banga wani abun jira anan ba ,kawai dai ana neman a hanani yarinya

Yi min shiru da Allah'
Toh ai sai kayi tayi, sau nawa zan kira jasmine din baki da baki tace min ita bata muradin auren ka,ta nuna sa da dan yatsa tace ashraf
Kaine kake tilasta ta,

Wani cunkusashhen bacin rai ne ya durmuye sa amma sai ya danne zuciyan sa don hargowa take kamar zata fashe nana ya sake cewa" Mamy ai dama basai tana so ba ,ke fa yar uwan ammyn ta ne. kawai ni in za'a bani kawai a bani....

Wani mugun kallo ta bisa da shi ta ce
Lahhhhh ta dafe kirji
" zaka mata na dole ne ,? Toh bisimillhi

Amma dai Kar ka manta idan jasmine ba amince ba na tabbata hajiya shahida babu abunda zatayi akai..gwara ma ka saukaka rashin kunyar dake damun ka kaje chan in kun shirya da ita to sai kazo min da magana ni ba ruwana da iskanci
Bude baki yayi zaice wani abun ta dakatar da shi dacewa tashi,oya. .oya ..fice min naga wuri
Bai ce komai ba "Sum sum ya wuce waje rai a bace ai kuwa
Bai tsaya ko ena ba sai gidan su jazmine din

Sosai ta sha Mamakin ganin sa don kuwa ta san rabon sa da zuwa yakai 3 months kenan yau

Lpya kuwa ?
Ta fada tana dan tura sa waje kar wani ya hango su
Bankade hannun ta yayi yace" Ai dole zAki min wannan tambayar?jasmine Ashe ke munafuka ce

Cikin mamaki tace ni kuma yaya ashraf me namaka na munafur ci?

Ohh..tab...baki ma sani ba ko, ai dama bazaki sani ba tunda kin mayar dani shasha sha..wawa uhm

Ranta ne ya soma baci amma sai ta dago calmly tace
Ban fahimce ka ba fa har yanzu?

Tswa ya daka mata " Meyasa a gabana kike gwada min kokarin ki akan maganar auren mu alhalin ke kike cewa su ammy baki son auren? Answer me ya karashe a tsawace

Shiru tayi tana kallon sa , don tuni taga alaman bacin rai sosai tattare da shi ,ko tsayuwa mai kyw bayayi

Gashi Tarasa me zatace don batayi tsammanin maganan zaije kunnen sa da wuri ba

Kayi hakuri yay ashraf, ni ba wai cewa nayi bana so ba,
U just misunderstood me

Cikin kunan rai yace"da Allah malama kimin shiru ..ko tausayi na bakiyi jasmine ko dan kinga sonki tayi min illah ne ? Aure fa nace ba wasa ba...
Nan idon sa ya ciko da kwalla ya soma binta da wani irin kallo ....nasan baki dauki komai da muhimmanci game dani ba shiyasa kike min haka
Amma ba komai ,
Zan baki dama kije kiyi tunani na miki alkwari duk abunda kika yanke a zuciyar ki ,zan karba ..kaiwa nan ya juya ya tafi ya barta anan tsaye

Durus ta tsaya kallon sa har ya lume ,mamaki da tausayin sa ya kamata lokaci guda,
Dan tabe baki tayi cikin ajiyan numfashi tace" ohh ni jasmine wallhy
Ba laifi na bane, zuciyata ce ta ksa aminta da soyyayr ka yaya ashraf..don ban taba tunanin da gaske har haka kakeyi ba .gani na jiki na kawai yake so"

Juyawa tayi tana tafiya cikin nazari tace "But I think i will give him a real chance..tsakani da Allah ko dan naga in dagasken yake.
Inshi ne miji na Allah ya bayyana alkahirin dake ciki
Ta karasa magananta tare da shiga cikin main hause
Chapter 23 · 0% Book details