← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 132

Sashe 17

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk abun ya dame su don For d first time doka ta hau kan su
Gashi zahida ta dage kan cewa bata kashe tania ba
Har mota jabir ya bita yana rarrashin ta cewa washe gari zasu fitar da ita
Amma sam bata jinsa sai kuka
Take tunanin ta ya za'ayi ashween da bakin sa ya sa akamata a wulakance haka

Wasa wasa haka ashween yayi tsayin daka da iya karfin sa har zahida tayi sati guda chur a hannun jamian tsaro ana ta bincike akanta

Hakan ba karamin zame musu abun kunya yayi ba
Musamman ma jamal da kowa ya sani a tarihin sa bai taba fadawa kasa a ko wani irin yanayin case ne wajen murda sharia a kotu ba

Yau ta kasance rana na biyu kuma na kusa da karshe na sauraron kara da shaidu akan zahida
Duk da ashween baya zuwa kotu
Amma lawyer da ya kawo jajirtacce ne wajen aikin sa
don haka ya sa jamal ya rika shan kunya gaban kotu
Yan jarida kuwa sunyi tsayin daka wajen daukar babban al'amarin

Abune na tarihi don a matsayin familyn rodriquez da matsayin barister jamal ba a taba samun case daya so yafi karfin su ba sai wannan

Yawanci jarida ta buga cewa don da chan rodriquez family tafi murqushe na kasa da ita ne shyasa take yawan winning case
Wani fannin kuma sun buga cewa shariar kudi da kudi ake
Saboda haka gar ta san gar "

Rashin samun su nasara yau din ma ya mugun girgiza su duk da ma ba kwarraren shaida akanta tukunna
'Yi shiru baby na im on it "kukan ya isa haka
madam hidayat tace tana shafo kan zahida
A hankali cikin rarraashi

Dago kai tayi tace Mummy..shikenan zai bari akaini prison
Akan wata ? Wayyo Allah na shiga uku,wht will happen to me ,,my beauty"mu..mmy
Pls do something mana ta karashe cikin kuka

Calm down zahida,, Sa hannun ashween akan case din nan ya zama mana babban barazA na
He's got money and words" tunda nake ban taba ganin wannan lawyrs din nashi ba
Amma kar ki damu Zanyi komai ba enda zakije indai ena numfashi ...ena kai,tafada a takaice
Fuska dauke da damuwa

I trust u mummy
Tace sannan ta goge hawayen ta tayi luf kan cinyar ta
Jamal ne ya tinkaro su suit din ma ya rike a hannu Tsaban bacin rai dake tafe da shi
" Me kika aikata haka zahida ?
Ya fada a fusace
Ko kula da yanayin su baiyi ba

Kamr yafa?
Me ya faru kuma jamal
Nan take ya dauko wayar sa ya kunna musu video
40 minutes clip ne na duk abubuwan da suka faru wajen partyn tun kafin zuwan tania har mutuwar ta

Bari hannnun ta ya shigayi tace a ena ka samu wannan?

Bai tsaya amsa ta ba ya dauko wani video 15 minutes clip
Lokacin da take ma tania barazana a shagon ta na spa da na fadar da sukayi a wajen dinner ashween an nuna dai dai ta wanka ma tania mari..

Wtf! Yace a fusace ya bar mata wayar a hannu ya juya baya yana huci

Karbe waya mummyn tayi daga hannun zahida da tuni Zuciyanta ke harbawa sama sama"Kamin bayanin wannan din ma ena ka samu?hjya hidayat ta tambaye sa cikin dauriya

Da kamar bazai amsa ba tsaban bacin rai sai ya danne zuCiyar sa yace Yanzun nan wani unknown number ya turo min akan zasu yi amfani da shi su karya rodriquez family
kinga abunda nake fada miki ko zahida
Duk haukar soyayyar ki da bin mazan ki ya jawo
Gashi Abu kadan na neman tona mana asiri dukan mu
Yhu are ruining my career,. my life zahida

Just stop der jamal haba da Allah hauka ne kuma abun naka? mummyn ta tsawatar masa
Baka ganin hankalin ta atashe ne? So kake ka kashe ta ko me

Bai fasa ba yace" Nima ai nawa a tashe yake mummy tunda mutunci na ya soma zuba gaba daya akan case din nan.

Ko zakice bakiga jarida bane for d past 4 days
Yawancin headline da ni yake farawa
ko yau din nan
Naga wani sabon headline
"The downfall of barister Jarod" me kike so da ni?

Cikin kunan rai yace "Its my dream na zama lawyer how did u xpext me to feel ina ganin yana rugujewa lokaci guda

Shiru ta danyi kafin tace ok
Naji ..kanada gaskiya kaima just calm down

No mummy dont tell me to calm down
Wannan Ba karamin barazana bane ke tasowa mana baki daya
Gashi nasa an bincika min wanda ya turo videon nan har yanzu ba asamu komi akan sa ba
Wht if ba shikadai bane yake da videos irin haka
In ya tura ma su lawyer ashween fa shikenan
Wallhy tamu ta kare "

Shiru duka sukayi suna kallon sa kowa da abunda ke ransa..

Ya cigaba
Yanzu sai ankai zahida prizon zaki ga yadda mutane zasu fara kwakwulu asirin mu suna tonowa tunda na gaza yanzu
Ya karashe maganan sa a raunane fuskan sa dauke da damuwa

A hankali madam hidayat ta dafa sa cikin rarrashi" Bakomai ,kai dae ka cigaba da abunda kake yi
Ni na san me zanyi bari na kira minister tace tana dialing wayar ta
Ko da ta kira yayi ringing sau uku ba daga ba
Tasan akwai wani makar kashiya dan haka ta hakura bata sake kira ba

Jim tayi sannan ta dan Dan tabe baki tace hmmm duniya kenan
Dama inbakayi bani waje
Amma ba komai zamu hade ta wani wajen tafada tana kada kai

Jin hakan ya sa zahida fashewa da wani sabon kukan
Don tasan shine hope dinsu na karshe yanzu kam
don duk ashween ya bi ya toshe musu hanyar samun alfarma

Dama minister Shi kadai ne inya ce akashe shariar zai iya tabbatuwa tunda alkalin case din dan gidan sa ne"
Amma sai gashi bai daga waya ba ..

Zahida kuwa Kuka sosai takeyi tana tunani kala kala a ranta
Bakin ta sai maganganu ya ke fitarwa ita ba zata je prison ba
" ga ta kyakkwa mai aji da kudi,
Kamr zararrriya hakan nan"
Ganin abun na nemar zautar da ita ne ya sa duka suka dukufa suna bata hakuri
Amma ena sai bori take tana rusa ihu ..har baban ta mr abdul fatah saida ta tuna ranar

Mrs rod da duniya gaba daya ta tsaya mata chak
Abun ma mamaki yake ba ta
Ita ne hakan yake faruwa da ita" tace mutane nawa na kashe kuma nawa na batar na murkushe sai gawar wata banzar yarinya ne zai daga mim hankali?

Cikin nazari tayi nisa
alaman tana neman wani mafitar sai sake sake take
Jamal da tuni ya dukufa wajen ba zahida baki
Baiji sallamar da aka yo daf da su ba
" Ash?
Tace tare da Dago kai tana binsa sa kallon mamaki

A haukace ta ture jamal ta yo kansa "Ashween pls dont send me to prison ta tsuguna gaban sa tana rirrrike masa kafa cikin kuka
Tuni zuciyar mrs rod ya soma harbawa tana takaicin saurin karayar zahida akan al'amarin
Kallon kallo jamal ke binsa da shi
Kana ganin kasan ji yake kamar ya shake shi
Don shi ba ta zahida kawai yake ba
Har da bata masa suna da zubar masa da kima da shariar tayi yake jin a ransa
Yya haka? Ka zo ka karasa kashe min yata ne? ,, toh ga fili go ahead
Mummyn tafada tana masa mugayen kallo

Baice uffan ba shi dai yana tsaye
Gamshin jikin sa sai ratsa wajen yake fuskaN sa normal ba alaman wani damuwa

Malam kafadi abunda ya kawo ka in babu kuma just Get out,
bamu bukatar ganin ka jamal ya fada rai abace

Itako zahida kuka kawai take rike da kafar sa tana furta pls..pls ..
Dan karamin murmushi ya sauke kafin ya tsuguna daf da fuskan zahida
Ya kure ta da ido ..da wuri ta sauke kanta gwanin tausayi tana sheshsshekar kuka
Bata hankara ba jitayi ya dago ta sama daf da shi tana fuskan tan sa
" ya isah haka beauty queen its ok..
Ba wanda zai kai min ke prison i promse

Wani dum duka suka ji a kunnen su
Barin ma zAhida data yanke kukan chak tare da dago kai tana kallon sa
Dauke da wani sabon murmushin ya gyada mata kai alaman da gaske yake
sannan ya sa hannu yana share mata hawayen ta
Cikin wani irin tsananin farin ciki ta kankame sa ta kasa cewa komai sai kuka
Mrs rod da jamal da abun ya matukar dauree musu kai suna gefe kowa na nazari
Jamal ne ya soma tambayar sa
" meyasa ka ke so ka zautar da ita ta hanyar mata karya
Bayan kowa yasani kai kake neman jefa ta a prison da hannun ka ?
Ashween Bai jira ya sake cewa wani abun ba ya ce
Kuma nace ba zata je ba yanzu ko?

Meyasa ? Mrs rod ta katse sa itama

Dago zahida yayi a jikin sa ya ya kalleta yace sabida na yafe mata
And she's not spending anoda minute anan wajen
wani kallo suka bisa da shi na mamaki da daure kai
Dan karamin scoff yyi yace
Amma its fine in kuna da plans dinku na cire ta sai na bari ya fada sounding ko ajikin sa
'
Ba musu mrs rod ta ce no, ba komai
Ya fitar da ita din ..ta dakatar da jamal da ga yin maganan da yake shirin yi

Kamo hannun ta yayi Tare suka fice zuwa offishin babban mai kula da wajen
Da shike zallan manya ake kawo wa wajen ba takuri sosai sannan komai a tsaftace yake kamar suna muhallin su

Jamal da ya kasa amincewa da sauyawar ashween din lokaci guda bai jira ba ya bi bayan su
Haka ya dinga bibiyan su yana ganiN yadda ashween yake da mutanen alfarma yaga yadda ake masa biyayya

Nan take aka har harda aka rubuta bail ma zAhida
Daga nan duka suka rusuna suka kau da wani tunanin aran su ..musamman mummyn su mrs rod data gama bari akan hala wani sabon cin mutuncin ya kunso musu yake wasa da hankalin su
Chapter 17 · 0% Book details