← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 132

Sashe 122

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kuka Jasmine tace zan fada mamy amma kiyi hakuri dan Allah

Tace ni baruwa kawai kiyi magana ena jin ki, nan jasmine ta daure ta tsayar da hawayen ta amma sai ta sunkuyar da kai kasa tace mamy cikin nan na yaya ne don ni bantaba fita da kowa ba sai shi..daga nan tayi shiru

Mamy dake jin maganan kamar wani almara sai tace ki kace yaya? Wani yayan?

Jasmine Ta dago boldly ta kalli mamyn tace yaya Ashween ne.

Mamy ta sa hannu akai cikin wani irin shock tace what? Sai aka bar ta kai a daure ta kalli nan ta kalli nan tace,Ashween!?toh how ,when?nace
Garin yaya?naga dai Ashween baiya ma zuwa gidan nan kwata kwata.

Sai jas ta tari numfashin ta da cewa a'ah mamy ai ni nake zuwa na same shi dama..
nan ma ta sunkuyar da kai cikin wani kukan tayi nuni da ashraf dake wajen shima tace wallhy gaskiya nake fada miki nidai nasan cikin yaya ash ne
Kuma Yaya ashraf ma yasan komai ko jiya ma maganan da yazo gaya min kenan,yace min har wajen yaya ash din ya taba bina don ya tabbatar...
Sai ta karashe maganan murya kasa kasa tace mamy ki tambaye shi zai fada miki ko yaya ashraf?

Aka bar ashraf da zare ido yana kallon jasmine din don bai san har zata iya furta magana har hakan ba

Mamy ta sake juyi cikin wani mamakin ta kalle sa shima tace ashraf?wato Kaima Kasan sa cewa jasmine tana fita gidan nan har zuwa wajen Ashween shine baka fada min ba?

Kafin ya amsa Nan abba ya sa baki yace ashraf, ka fadi gaskiya yadda kasan zaka mutu" ba maganan wasa akeyi anan ba haka ne ko ba haka bane?

Da shike duk rashin kunyar sa yana daraja baban na sa hakan don dolen sa ya ma jasmine shaida ya amsa da cewa eh suna fita da ashween
Yace a gidan ammy take samun shi
Ni na sha ganin su tare sai dai kawai bansan abun hakan yake ba ne.

Mamy ta dafe kirji ta sallame ta kwaso salati tana bin kowannen su da kallon mamaki

Wani turirin kunya ke tsatsafo mata tun daga dunduniyar kafar ta har tsakan kanta sai ta dan lumshe ido tana ji kamar a bude mata kasa ta shiga ta boye don wannan abun kunya.

Abban ashraf kam sai yayi murmushi a ransa yace yaran zamani kenan,dama duk wanda ya shiga tsakanin ma'aurata karshen sa jin kunya
don ko da kuwa kanada gaskiya in tayi musu zaki sai a mance da kai.

Mamy ta kasa cewa komai ta nemi waje ta zauna don jasmine ta gama kure mata tunani.

A ranta Tace ohhh, ciki har wata2 da kwana uku agaba na?sai naga kamar yarinyar nan ta sake agidan nan ashe tana chan sake da mijin ta,
Ashe toh an dade ana yi kenan ban sani ba.
Hmmm Lallai yaran zamani abun tsoro ne, uhmmm tohmm ban isah ba ai gwara maza Ashween ya zo ya dauke matar sa kafin ayi nisa..tabbb ni yau naga duniya dan ba kara.

Jin kowa yayi shiru jasmine ta dan kara sautin kukan tana cewa mamy kiyi hakuri wallhy ba laifin shi bane duk laifi na ne kar ki masa fada kinji mamy, ni na yarda barin sake kara fita a gidan nan ban fada miki ba dan Allah kiyi hakuri

Mamyn batace komai ba sai suka kalli juna da abban ashraf wanda ya gama gano kunya ne ya hana mamy sake magana a wajen

Sai tayi boyayyen murmushi tace yi min shiru awajen,yanzu ne kika san da haka?sai da kika dauko min ciki zaki ce min bazaki kara ba? wato har ni zaki na zagawa agidan nan ko jasmine?
Bakomai tashi kije ciki da kaina zan kira ashween din a idon ki kina gani bazaki koma gidan san ba..

Jasmine tuni ta fada kasa ta tsala ihu ta soma bori tana birgima cikin kuka tana cewa mamy dan Allah kiyi hakuri kar kice hakan wallhy ena son shi,ni gaskiya zan koma wajen shi ai yace bazai yi auren ba kuma ni kadai yake so ...

Borin nata abun kunya abin dariya amma mamy sai ta danne tace sai ta dan jijjiga ta yadda ita ma tasa jiya taji tsoro da fargaba sosai ranta
Tace nace ji tashi ki je ciki ,shi zai zo nan ya same ni shima.bani zaku mayar shasha ba..

Jasmine zata kara wani maganan abban ashraf yace mama na tashi abun ki,kukan ya isa haka, ai kema kinga da laifin ki kar ki sake aikata irin haka kinji?
Duk abunda zakiyi kar ki nayi a boye kinga in badon akwai wanda suka sani ba da ba mai yarda da ke..

Cikin kuka tace ayi hakuri abba nasan nayi kuskure,amma nidai dan Allah kar a raba ni da yaya na wallhy ena son shi.
Abban saida ya kasa danne murmushin sa
Yace jeki toh ki kwanta maza tashi..

Mamy dake makale da guntun dariya ,kunya da mamakin jasmine din tace barta kawai,ai jasmine bata jin magana ne kwata kwata musamman ma nawa.

Jasmine Ba musu ta tashi tana kan matse ido tana kananun magana ciki ciki don har ga Allah wani haushin mamyn yanzu take ji take kamar ta yi tsuntsu ta gudu a gidan

Nan Ta haura sama suna binta da ido
Fuskan su dauke da murmushi duka

Sai dai Banda ashraf wanda tun lokacin da jasmine ta sa yayi mata shaidan cikin ashween dan dolen sa ya kamo da wani bakin ciwon zuciya da bacin rai mai daci.

Anan duk idon sa sun gauraye da bakin ciki don haka ne ma bai iya cewa komai ba.

Bai tashi ba ya sunkuyar da kansa yana kan jin hirar su mamyn
Abba yace kingani ko hadiza ai saida na rokeki tum wuri ki maida masa matar sa kika ki baga irin ta ba,?

Mamy tace gaskiya ne alhj yau nima naga kuskure na
Insha Allah kuma na dauko darasi daga dan ba kara.

Yace alhamdullhi,
Tace yanzu ni zan kirashi yazo nan ayi magana sai a maida ta kawai tunda cikin satin nan zamuyi tafiya muma.

Abban ashraf yace wannan yayi dai dai, Allah ya shige mana gaba.

A sulale ashraf ya tashi suna kan hirar su ko takan sa basuyi ba bare su san meya ke ciki

Yana shiga dakin sa ya daka ihu mai dauke da kunan rai yana maka ma katifan sa duka cikin bacin rai.

Yace wallhy ba a isa amun haka ni kenan na tashi a tutan babu?
Sai ya rarumi wayar da ya dauki videon su yayi screen shoot na wasu wurare suka dawo hotuna
Nan ya tashi a gaggauce ya soma shirin zuwa paris.

A ganin sa wannan ne kawai ya rage masa hanyar da zai hana komawar auren Ashween da jasmine,

Ba yadda mamy batayi da shi ya gaya mata mai ya kawo tafiyar gaggawa ba amma sam yaki yace yana so ya samu wani abun ne akan lokaci shiyasa zai tafi

Tun kafin ace wani karfe
2pm ya bar nigeria ya nufi paris neman zahida abun sa..

Mamy kam shiri ta shigayi na abubuwan da zata tarkata jasmine da shi kafin su sami layin ashween din.
Don daga ita har jasmine
Din sun neme sa ba su same shi ba

Barin ma jasmine da ta gama rudewa mamy tace zata raba ta da mijin ta.
Karshe text kawai ta tura masa cewa dan Allah ya zo tana cikin matsala.

Har dare jasmine bata fito ba tana kan fushin ta da mamy gashi har yanzu ba wani motsi daga wajen habibin ta.

Bayan isha'i sai tayi wanka ta dauko sabon nightien ta da suka siya kwanan nan da shi da su kaje ukraine zuwan si na karshe

Dark royal blue ne mai tsansi mai dauke da dan fingilin riga mai tsiririn hannu kuma iya rabin cinya ta ciki.

Sai haddaden jacket dinsa na waje anyi masa vneck mai kyau shi sai ya dan zarce daf gwiwar ta ta haska sosai kalar ya fito da farin fatar ta

Tana jikin mirror tana kan masifa aranta cewa duk tsiya wallhy bazata zauna ba sai tabi mijin ta.
Nan Ta kama suman kanta da suka dada cikowa duk sanadiyar shigar cikin tana daurewa sannan sai
Ta juya zata haura gado.

Ko isa kan katifar bata gama yi ba wayar ta yi karar alaman shigar tex
Ta dauka cikin sauri ta bude tsaban murna bata saya wani suturce jikin ta ba ta fice a dakin ba ko takalmi tayi bayan balcony nan hanyar da ta saba fita a sace.

Ba tan tama Shine a tsaye sanye da baki da ash suit mai guntun hannu bisa ga dukkan alamu yanzun dirowar sa nigeria sai yaga sakon data turo masa tun safen shine ya taho kawai bai bi gida ba.

Da uban gudu take saukowa yana kallon ta har ta zo ta fada kirjin sa suka kankame juna

sai kansa ya dan daure ya dan dago smilling face din ta dake faman jera masa sannu da dawowa,yayi kissing lios dinta ligthly yana dada kallon yadda tayi matukar kyau cikin kayan baccin yace princess wato kina jin dadin ki dinga birkitamin zuciya na ko?meke damun ki yanzun i saw ur tex wai kina cikin matsala
Ni kuma ena jirgi yau,gashi tun jiya ban samu na zauna ba

Ta dan sake jingina jikin sa a shagwabe tace toh dama bazaka dawo din bane,yayi murmushi ya dan dada riko ta jikin baice komai ba sa sai tace uhmmmmm
Yaya, dama so nake kazo sai mu tafi gida ni na gaji da nan.

Yace kamar ya jasmine? ba munyi magana ba, ai nace zanzo na samu mamy da kaina na sake gwadawa
Nan ta dago tana kallon sa sai ta sa fuskan kuka tace uhm,uhm,kar ka wani same ta kawai mutafi ni yanxu nake so ni wallhy sai na bika.
Ya shiga lallabata amma sam tako ta kuma turje

Sai Abun ya soma damun shi ganin jasmine lallai da gaske take yi ita sam sai dai su gudu.
Chapter 122 · 0% Book details