← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 68

Sashe 8

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Al'amarin Razhdeen da Baiwar ALLAH ya wuce misali domin a halin yanzu gaba ɗayan su ba kaya a jikin su sai ma rufe kansu da suka yi da mayafi, kowa yana bawa junan su saƙonni, domin ba ƙaramin shiga yanayin uƙuba suka yi ba, sai fitar da numfashi suke amma a halin yanzu gaba ɗayan su babu wanda yasan mai yake aikata wa, duk basu san me suke yi ba domin hankali ya rigada yayi gaba domin har yanzu wannan turaren lokacin sa bai ƙare ba, da zarar ƙamshin ya washe a lokacin suma zasu dawo hayyacinsu..

Lokaci guda Baiwar ALLAH tasau wani irin ƙara haɗe da kuka tana ambatar sunan "Yaya Roshan! Yaya Roshan!! Yaya Roshan!!!..."
sunan ne kawai yazo bakinta take furtawa amma ita kanta bata san mai take faÉ—i ba balle tasan a halin da take ciki...

Shima Razhdeen ganin kansa yake a cikin gajimare ya kasa daina abinda yake aiwatar wa, ko ambatar sunan Yaya Roshan da take yi shi sam baya jinta, bai san a wani duniya yake ba, da za'a barshi a tunaninsa cewa zaiyi bashi da rai ya zama matacce domin a cikin gajimare yake ganin kansa...

★★★★★★

Ƴar Amana kuwa tana cikin halin kuka sai ga Madam Blessing ta shigo har ɗakinta ta zauna a kusa da ita a bakin gado, yanda tayi tagumi sai zubda hawaye take ga yanda zuciyar ta yake ta bugawa haka kawai bata san dalili ba.

Madam Blessing ce ta dafa kafaÉ—arta tare da ambatar sunanta "Sarah..."

A firgice Ƴar Amana ta ɗago tana kallon Madam Blessing ido a shashshanye domin tin safiya bata ci komai ba..

Madam Blessing ta ce "kina yarinyar ki ƙarama amma kina jefa kanki cikin matsalar da zai sanya miki hawan jini ko ciwon zuciya, nasan dai matsalar ki abu ɗaya ne bazai wuce akan Ogah Razhdeen ba,
shima a kwanan nan ya shiga wani irin halin da na kasa gane masa, a halin yanzu bai iya control kansa ba balle yazo ya baki lokacin ki, kin daina zuwa school saboda baya kai ki, kin daina cin abinci sosai saboda baya nutsuwa ya ci shima, baya zuwa yanda kike yanzu kema kuma kin kasa zuwa yanda yake, amma duk laifin sa ne da ya gagara gane halin da kike ciki alhalin yasan ba iya magana zaki yi ba, shin inda bana zuwa nan gidan sai dai ya fito ya samu gawarki kenam?....."

Ƴar Amana tsaya kallonta tayi wuya a karye kamar marainiyar da ta rasa gata,

Madam Blessing ta cigaba da cewa "Sarah nasan soyayya ta shige ki tin ba yau ba, na fiskance ki kina tsananin ƙaunar Razhdeen, amma kin kasan sanar masa don babu yanda zakiyi tinda yanzu baya tsayawa ya baki lokacin sa balle kiyi masa alamu da hannu,
Bazan iya juran ganin ki a cikin wannan halin ba kina ƙaramar yarinya dole zan same shi yasan abinda ya dace, sannan zan sanar masa cewa kina sonsa in zai tsaya ya kula da ke toh gwara haka...."

Ƴar Amana jin Madam Blessing ta ce zata sanar masa tana sonsa yasa tayi saurin riƙe hannunta tare da girgiza mata kai alamun "A'ahh ta bar shi kawai...."

Madam Blessing ta ce "to shi ya kasa ganewa, idan kuma wani ciwo ya kamaki fa? to ni saina gaya masa..."

tana kaiwa nan ta fice a É—akin,
Ƴar Amana kuma ta cigaba da zubda hawayen ta.....

★★★★★★★

Roshan ya iso gida cikin ƙoshin lafiya haka motar su ta rinƙa tsallake gate gate a jere har suka yi parking a wurin ma'ajiyin motoci, Ummy uwar masu gida ya tarar ta fito jin sauƙar mota daman tana jiran isowar sa ta fara masa oyoyo, yanzun ma nufan yanda yake ta je tayi masa oyoyo tare da karɓan jakar sa suka nufi babban falon gidan kafin ya wuce part ɗinsa.

A falo ya tarar da kowa da kowa anata shan hira ga baƙi ƴan uwa har sun zozzo, a ciki har da Aunty Yolash, duk tashi sukayi suna tsokanan sa da cewa "Ango yasha ƙamshi, Ango ya iso mijin Amarya..."

Roshan zama yayi akan kujerar falon domin yanada son mutane, haka ya fara gaggaisa wa da su, anata tambayarsa Amarya...

Duk family su ba ƙaunar Baiwar ALLAH suke ba hasali ma ganin laifin Abbah suke yi da ya Aurawa ɗansa yarinyar da ba'a san asalinta ba, yanzu kuwa jin zai ƙara Aure ne yasa kowa ya shiga yin farin ciki,

Da yawan mutanen falon baƙin sunata masa complain akan Baiwar ALLAH ta cika baƙin hali, bata son ƴan uwansa, dalili shine tinda suka zo bata zo ta gaishe su ba sannan ta hana aje yanda take,

Sam Roshan bai ji daɗin hakan ba, yafi son kowa ya yabi matarsa amma sai ya ga akasin haka, itama Aunty Yolash da take ji da Baiwar Allah yau ta kawo complain ɗinta a Roshan ta ce "yarinyar nan wai zan yi mata gwaninta musamman na aika Ummy akan zanje nayi mata gyaran jiki irin na Amare, nayi mata gyaran Uwar gida amma ta aiko cewa ita bata so ai raina na ɓaci wallahi, shiyasa banje part ɗinka ba tinda nazo..."

Wasu daga cikin mutanen ne suka ce "mu kam munje amma taƙi buɗe mana ƙofa haka muka juyo, ita dai baƙin kishi zai hallaka ta saboda kowa yasan kishi ne, za'a kawo mata mai asali da tushe wacce zata haifa mana yara ƴan dagwai-dagwai tinda ita juya ce bata haihuwa, Aure shekara biyu...."

Roshan ganin bazai iya juran maganganun nan ba yasa shi miƙe wa yana faɗin "Bari naje part ɗina, zan same ta da maganar Insha Allahu...."

Hajiya Kilishi ce ta sauƙo tana faɗin "Ina kuma zaka je Roshan ga abinci yanda aka haɗa maka na taryan Ango..."

Sakin murmushi yayi sannan ya ce "mutane sunyi yawa anan kawai a aika mun can part É—ina domin nasan Ammata bata yi ba saboda ban sanar mata ina kan hanya ba...."

Hajiya Kilishi ta ce "to shikenam Insha Allahu za'a biyo ka da shi..."

Ya amsa tare da fita zai nufi yanda yake da matar sa ga kuma Ummy Æ´ar rakiya tana É—auke da jakarsa haka suka fita tareda, suka shiga mota zasu je domin da É—an rata a tsakanin su,

Roshan ne ya kalli Ummy sannan ya ce "Razhdeen ya zo ne?..."

Ummy ta girgiza masa kai alamun "a'ah..."

Roshan ya ce "why? naga motar sa fa a other side sannan na shiga ciki ban gan shi ba..."

Ummy ta ce "zai iya ajiye tasa ya É—auki wani motar ai...."

Jinjina kai Roshan yayi tare da faÉ—in "na gamsu yanzu dai muje..."

Roshan yana shiga part ɗinsa yaji zuciyar sa tayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske, riƙe saitin zuciyarsa yayi tare da sunkuyar da kai, Ummy ta ce "Yaya Roshan meya faru ne?...."

Ya girgiza kai ya ce "ba komai, let us go..."
Suka buÉ—e tare da fice wa....

Sai da suka zo bakin ƙofa sannan suka buɗe gani yayi falo yayi fes-fes sai ɗaukan ido yake sai dai babu kowa a falon...

Ummy zama tayi akan kujera shi kuma ya É—auki jakarsa ya nufi room É—insa...

A wannan lokacin turaren ya wa she babu sauran ƙamshin da ya rage,
Baiwar Allah da Razhdeen suna nan a yanda suke babu ƙwari a jikinsu, sai yanzu hayyacinsu ya fara dawowa, Razhdeen ne ya ɗan motsa yana shirin tash, jikinsa gaba ɗaya ba ƙarfi haka ya ƙara komawa kanta duk bai san akan mutum yake ba, hasali ma ya ɗauka a gidan sa yake hakan ma kan gadonsa...

Roshan ne ya dawo falo yana faÉ—in bari naje É—akin Ammata nasan yanzu haka tana ta shan bacci....

kai tsaye ya nufo room ɗin Baiwar ALLAH cikin rashin sa'a yana tura ƙofar ta buɗu,
Fuska ɗauke da murmushi da sallama a bakinsa ya shiga, yana kaiwa idonsa kan gadonta zuciyarsa ta wani irin bugawa da ƙarfin gaske, a tsorace ya ja da baya yana jero Addu'o'i....

Wannan Addu'o'in bai sauƙa a ko ina ba sai a kan dodon kunnen Razhdeen da Baiwar ALLAH wacce yanzu take mutsil-mutsil tana shirin buɗe idonta,

Razhdeen a hankali ya buɗe idonsa jin anata addu'a, idonsa ne ya sauƙa akan fuskar Baiwar Allah a ruɗe da firgici yayi saurin tashi daga kanta yana zazzaro ido waje haka zuciyarsa take harbawa da ƙarfin gaske, cike da mamaki yake bin ta da kallo yana tunanin taya hakan ta faru duk da har yanzu bai san ya aikata wani abu ba bayan wannan,

Dasauri ya waiwaya ya kalli bakin ƙofa yanda yaji sallama yaga Roshan a tsaye idonsa akan su bai san lokacin da hawaye yake zarya akan fuskarsa ba,

Itama Baiwar ALLAH buɗe idonta tayi wanda ta fara gani shine Razhdeen dake gefenta ko kaya babu a jikinsa itama a ruɗe cikin tashin hankali ta miƙe zaune tana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Allahumma ajurni fi musibati ƙalu innalillahi wa inna'ilaihi raju'un...."

Cikin tashin hankali ta ce "na shiga uku mai mai mai mai zan gani haka,?..."
Buɗe baki tayi zata ƙara magama idonta ya sauƙa akan Roshan dake tsaye a bakin ƙofa, da sauri tasa hannu biyu ta toshe bakinta tana shirin yin ihu,

Roshan cikin tashin hankali haka ya juya ya koma falo bai ce musu komai ba, ga hawaye ya ƙi tsayuwa har sai da ya je falo ya nemi kujera ya zauna tare da yin tagumi...

Ummy ganin a halin da Roshan yake ciki ne yasa ta tashi taje kujerar da yake ta zauna tana rirriƙe shi kamar zata yi kuka tana tambayarsa "meya faru ne Yaya Roshan? Dan ALLAH ka sanar mun mana bana son ganin ka a cikin wannan halin...."

Roshan shiru yayi bai ce komai ba, ji yake zuciyarsa kamar ta faso ƙirjinsa ta fito tsabar bugawar da yake...

Ummy ta ce "to tinda ka kasa sanar mun ni zanje na gano menene..." Zata tashi yayi saurin riƙo hannunta tare da zaunar da ita still bai daina hawayen ba kuma ya kasa cewa komai...
Chapter 8 · 0% Book details