← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 68

Sashe 31

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fusace Ramlat ta ƙarasa shigowa ciki tare da faɗin "ke baki da hankali ne? akan gadon mu na Aure zaki zo kiyi seƙe-seƙe dake ke ba ƙaramar yarinya ba..."

Reemah cikin lumshe ido wacce bacci yake ƙoƙarin ɗaukar ta ta ce "yau anam zan kwana..."

Ramlat ta ce "amma ba'a cikin É—akin nan ba ko?..."
Reemah gira a haÉ—e ta ce "ke nifa kin takura ni, shin aina zan kwana wanda ya wuce nan, ai kuwa yau da Yaya Roshan nayi niyar kwana a É—akin nan...."

Ƙirjin Ramlat ne yake bugawa da ƙarfi-ƙarfi domin al'amarin Reemah ya fara bata tsoro...

Roshan jin surutu yasa shi buÉ—e idonsa tare da faÉ—in "me yake faruwa ne?..."

Ramlat tana tsaye ta ce "gata nan a kusa da kai, ban saniba ko yau an haÉ—a Aurenka da ita anyi ne..."

Roshan kallon yanda take a kwance yayi ya ce "ƙanwata ya akayi ne?..."

Reemah tashi zaune tayi tana tura baki ta ce "nazo ana korata shikenam, daman kwana nazo taya ku amma matarka shine take faÉ—a mun maganganu ko..."

Shima tashi zaune yayi yana binta da kallo ya ce "yi haƙuri ƙanwata kwanta kiyi baccin ki..."

tana turo baki ta koma ta kwanta, shi kuma tashi yayi ya riƙo hannu Ramlat suna shirin barin ɗakin, Reemah ta ɗago ta zauna tana faɗin "iyyeeee! tafiya zaku yi ku barni ni kaɗai kenam, ai wallahi duk yanda ku ka je sai na biku...."
ta ƙarasa maganar tana shirin tashi,
Roshan ya ce "kinga kwanta mun dawo to..."

Ya kalli Ramlat ya ce "kuje ku kwanta tare ni zan kwanta akan doguwar kujerar nan..."

Ramlat fuska a É—aure sai fushi take tayi tana kumbura kamar zata fashe, ji take kamar ta rufa Reemah da duka, haka ta hau gadon ta kwanta tare da jan mayafi ta rufe kanta ga kuma Reemah a gefenta itama ta ja mayafi a kanta domin bacci take ji,
Roshan kuwa kashe hasken É—akin yayi zai bar musu É—akin yaji Reemah tana cewa "Yayana ka ce akan doguwar kujera zaka kwanta yanzun ina zaka je?...."

Roshan ya ce "zan koma other room ne naje can na kwanta nima akan gado..."
Reemah tana cikin mayafi ta ce "to tunda akan gado kake son kwanciya kazo nan ka kwanta a tsakiyar mu...."

Roshan zaro ido waje yayi yana kallon ta yanda ta rufu,
Girgiza kai yayi sannan ya ce "shikenam zan kwanta akan doguwar kujerar..."

ya rufe É—akin ya zo yabi kan kujerar É—akin ya kwanta, su suna kan gado shi kuma yana kan kujera da haka har bacci ya É—auke su, sai iya Ramlat ce ta rage da idonta sai faman kuka take ta sha a cikin mayafin, ta daÉ—e bata yi bacci ba tana kuka itama daga baya baccin ya É—auke ta,
A haka har sallar asuba Reemah ta hanasu sakattt......

Typing ✍️

*MY ENEMY*

*TAKUN ƘARSHE*

*BOOK 3*

46 to 50

Washe gari
Duk a dinning suka zauna zasu yi breakfast su uku Roshan da Ramlat da kuma Reemah wacce tayi musu ƙarfa-ƙarfa,
Roshan ne da Reemah kawai masu hira amma ita Ramlat takaici kamar ta hallaka, sai faman hararar Reemah take,
Roshan ne ya É—ago yaga yanda take ta mata kallon banza, tsaya kallon ta yayi daga bisani ya ce "me hakan yake nufi?..."

Juyowa tayi tana kallon sa fuska a É—aure tana turo baki ta ce "cin fuskar ne yayi yawa, bazan iya jure wa ba..."

Reemah ce ta juyo itama tana kallon ta cikin rashin fahimta, sannan takai idonta kan Roshan tana son sanin abinda take nufi...

Roshan ne ya ce "idan kin yi haƙuri sauran kwana nawa ne ya rage, bana son yawan complain fa..."

A fusace Ramlat ta miƙe tsaye tana faɗin "ai dole ka ce haka saboda ni ba komai bace a wurin ka, daman nasan ba Sona kake ba dole ce tasa ka Aure ni, to bazan iya ba, idan ana son na cigaba da zama a gidan nan to sai dai a ja mata kunne akan shiga tsakanin ma'auratar da take, ita mahaukaciya ce? ko jahilci hauka ne, ina ga bata je islamiyya ba shiyasa jahilci da rashin tarbiyya yayi mata yawa..."

Bata ƙarasa ba taji Roshan ya darara mata tsawa tare da miƙe wa tsaye a fusace yana nuna mata yatsa tare da faɗin "ya isa haka! idan ita jahila ce kina nufin kice duk har da mu jahilai ne ko? hakane tinda tsatson mu ɗaya, ina so nayi miki warning akan wannan kishin nakin..."

Cikin ɓacin rai Ramlat ta ce "dakata Yaya Roshan, me kake nufi ne? kana nufin kace bazanyi kishi akan ka ba? gaskiya ni ina kishi akan ka ne saboda tsananin son da nake maka, kai kuma sam bana gabanka balle kayi kishi da ni amma ita Baiwar ALLAH da kake masifar sonta ai kana kishi da ita tinda har kuka kayi cir da idanuwanka...."

wani irin kallon takaici yake mata cikin fushi ya ce "idan kinga zaki iya zama dani a haka to sai kin cire wannan kishin nakin, idan kuma bazaki iya ba ga nan hanya...."

ya ƙarasa maganar yana nuna mata hanyar waje dai-dai Lokacin da idonsa ya sauƙa akan Baiwar ALLAH wacce take tsaye a bakin ƙofar falon tana tsaye ta zuba musu ido...

Daga nan Roshan bai ƙara furta komai ba idonsa akan Baiwar ALLAH.
Ganin haka yasa Ramlat juyawa tana kallon bakin ƙofa fuska duk ya jaƙale da hawaye, ƙirjinta ne yayi wani irin bugawa ganinta...

Reemah wacce take zauna cikin izzah ko É—agowa ta kalle su bata yi ba sai ma cigaba da yin breakfast É—inta jin faÉ—an akanta ake,

Baiwar ALLAH ƙarasa shigowa ciki tayi tazo ta tsaya a gaban su idonta akan Roshan tana son isar da saƙo Ramlat tayi saurin katse ta da cewa "ke meyasa kanku baya ja ne? anya ƙwaƙwalwar ku bana kifaye bane? especially ke marar zuciya mutum ya ce baya yinki amma sai ƙoƙarin cusa kanki kike, yanzu har takai kina shigo mun ɗaki ba excuse, idan kika tarar da mu a cikin wani yanayi fa?...."

Baiwar ALLAH goya hannayenta tayi akan ƙirji tana kallon ta ta ce "yanayi kam ai na rigada na riske ku a ciki, sannan kun ci sa'a tinda a iya falo na tsaya bance zan taya ku kwana a ɗaki ɗaya ba...."

Ramlat gaba ɗaya ta gama ƙuluwa ta ce " to ina so ki fita daga shirgin mijina domin baya hulɗa da ƙazamai masu aikata alfasha, sai ki je ki nemi uban cikin ki kuje can ku cigaba daga yanda ku ka tsaya..."

Roshan idonsa ya sauƙar kan Ramlat jin abinda ta furta, kasa cewa komai yayi domin shi bai cika son hayaniya sosai ba, yanzu zai iya jawa kansa ciwon da zai dame shi..

Baiwar ALLAH tana shirin zubda hawaye tayi saurin kawar da fuska tana ƙoƙarin matse hawayen, murmushin yaƙe tayi tana kallon Ramlat ta ce "karfa ki manta har yanzu akwai igiyar Aure na da Roshan..."

Ramlat kwashe wa tayi da dariya tare da faÉ—in "rabuwar Aure kuwa na nawa tinda a gaban kowa yayi sakin..."

Baiwar ALLAH cije lips ɗinta na ƙasi tayi ta ce "kin taɓa jin anyi saki da ciki? Roshan ya sake ni amma ban saku ba har sai na haifi ɗan dake ciki na, kinga kuwa har yanzu a mazannin mijina yake..."

Ramlat ta ce "ai dai zaki haihun koh? to ki haihu kiga in Auren zai zauna tinda na tabbata bazai taɓa maida ke ɗakinsa ba..."

Ramlat ta ƙarasa maganar tana ɗaga mata gira ɗaya...

Roshan ne ya katse su da cewa "ku dakata mun da wannan shirmen nakun..."

Ramlat ta maida idonta kan Roshan tana faÉ—in "taya zan dakata? wallahi yau sai an faÉ—a mun matsayi na a cikin gidan nan, idan har ina matsayin matar ka ce ta sunnah to ina so daga yau ka ja wa waÉ—annan masu zuciyoyin kare kunne kada su sake zuwa yanda kake..."

Roshan kallon ta yayi cike da mamakin ta ya ce "to Fatima Bintu mahaifiya ta kenam, naji zan bi zaɓin ki..."

Ramlat tana turo baki ta ce "Ni dai ka zaɓa idan su ka zaɓa to inason sa ni yanzu idan kuma haukar su suke to inaso kayi mana iyaka da su, domin bazai yu ba, ita wannan yarinya saboda ta raina mun wayo da rashin mutunci har da kwana mun akan gado to bazan iya ba..."

Roshan cikin ɓacin rai ya kalli Reemah sannan ya ce "Reemah..."

Reemah ta maida idonta kansa gaba ɗaya Ramlat ta gama ƙular da ita, haka zuciyar ta yake ta hargutsuwa, itama kallon sa take,

Ya ce "taso ki zo nan..."

Reemah tashi tayi ba mu su taje gabansa tana hararar Ramlat, itama Ramlat É—in wani irin harara take wurga mata,
Roshan ya riƙo haɓarta suna kallon juna ya ce "Reemah kina so na? zaki Aure ni ?..."

Ramlat a zabure ta ja da baya tana zaro ido waje cike da mamaki take bin su da kallo tinin idanuwanta har sun cicciko da ƙwallah, Baiwar Allah kuwa idonta akan Ramlat tana sakin murmushi ganin halin da ta shiga lokaci ƙanƙani, ita ko kaɗan bata damu ba domin tasan hakan zata faru....

Shi kuwa Roshan idonsa akan su idan ya kalli Ramlat sai ya juyar da idonsa kan Baiwar Allah domin a tunanin sa hakan shi zai kawo maslaha a tsakanin su, kuma tin yanzu Ramlat ta fara nuna kishinta akan Reemah shiyasa yayi haka domin ta yi kishin da gaske, sannan bugu da ƙari cin mutuncin ta da tayi a gabansa har tana ƙiranta da jahila....

Reemah kuwa idonta akan Roshan ta kasa furta komai,
Ƙara maida idonsa yayi kanta still ya ce "kodai bakya sona?..."
Reemah murmushi tayi sannan ta ce "ina sonka sosai Yayana..."
ta ƙarasa maganar tana kallon Ramlat domin ta ƙara ƙuntata mata...
shima murmushi ya sakar mata, cikin jin kunya ta rufe fuskar ta tare da juyawa da gudu ta nufi hanyar fita daga falon..
Chapter 31 · 0% Book details