← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 68

Sashe 4

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abincin ya fara ci idonsa akan ta sai da yayi Three spoon sannan ya dakata tare da ɗora hannunsa akan nata hannun dake ajiye kan dining, a firgice ta ɗage hannunta ta miƙe tana shirin barin wurin yayi saurin riƙo ta tare da janyo ta kan cinyar sa,
Bubbugar sa ta fara yi akan ƙirji tana ture shi ga yanda hawaye yake gangaro mata, a halin yanzu ba ƙaramin jin haushin sa take ji ba, riƙe hannayen ta yayi duk biyun da hannun sa ɗaya tare da mannata sosai a jikinsa yanda bazata iya ƙwace wa ba, matso da fuskar sa yayi sai tin nata yana goga mata dogon hancinsa akan nata hancin, haka numfashin su yake haɗuwa, cikin takaicin ta ƙanƙame idonta tana jin yanda yake goga mata amma ta kasa aikata komai sakamakon riƙon da ya yi mata..
Bayan ya gama da wannan ya zo yana hura mata iskar bakin sa akan fuska sannan ya ce "Sarah.." ya ƙira sunan ta cikin sigar rarrashi, ya cigaba da cewa "Am so sorry please, kina fushi da ni ko? aina kika ji wannan ciwon?..."

Buɗe idonta tayi tana masa wani irin kallon haushi, haka take masa kallon up and down haka ta tattaro ƙarfinta ta ture shi baya tana daga kan cinyar sa haka kujerar tayi baya da su suka tafi zuuu suka doku a ƙasi ita tana kansa shine a ƙasi, tashi tayi ta rufa da gudu ta haura ɗakin ta tana kuka...

Madam Blessing da take gyaran falon tana kallon su ita kaÉ—ai sai dariya take tayi, da haka ya tashi tare da kar kaÉ—e jikinsa dan ma akan carpet ne, ya girgiza kansa sannan ya yi waje zai je yanda ya shirya tafiya...

★★★★★★

A can ƙasar Jidder
Ramlat sai shirye-shirye take tayi Roshan yana hanyar zuwa domin taji Mai martaba yana cewa Roshan yana jirgi, farin ciki kamar bazata mutu ba, har sabon kaya tasa aka É—inka mata na taryar Roshan ga yanda taje aka tsara mata kwalliya na musamman, tin yanzu aka fara shirye-shiryen biki an sanar wa Æ´an uwa da abokai yau sauran kwana biyar biki...

Bayan awa ɗaya da mintuna sai ga Roshan a gidan mai martaba, a part ɗin mai martaba ya fara sauƙa suka gaggaisa cikin aminci, sannan Roshan ya je part ɗinsu da suke sauƙa shi da Razhdeen idan suka zo, daga baya kuyange suka kai masa kayan abinci kala-kala da kayan fruits na musamman, ga ɗakin da ya sauƙa a gyare an gyara ko ina tsab-tsab, ɗakin sai ƙamshin turaren wuta yake na masarauta, sai da ya tsaya ya kalli room ɗin ganin yanda ya tsaru ba ƙaramin burge shi yayi ba, da murmushi akan fuskar sa ya fa ɗa saman gado yana huta gajiyar hanya, ta falon ɗakin kuma an gama shirya kayan abinci akan dinning dake room ɗin falo and bedroom ne sai bathroom ta ciki, yana kwance yaji ana knocking a hankali ya furta "who?..."

Wata ce daga cikin Æ´an matan masarautar ta ce "an kammala haÉ—a kayan abincin..."

Yana daga kwance ya ce "Ok thanks..."

Bayan ya gama hutawa ya tashi ya shige bathroom ya watsa ruwa a jikin sa sannan ya fito ya chanza kaya tare da feshe jikinsa da turaruka kala-kala ya shirya tsab sannan ya nufi falo, kai tsaye dinning ya nufa ya je ya ci abinda zai iya ci sannan ya ɗan taɓa kayan fruits daga baya ya taso yana goge bakinsa da tishu,

Sai da ya ƙara shiga bathroom ya shige toilet yayi brush tare da ɗauro wa alwala ya fito yabar ɗakin gaba ɗaya, bai tsaya a ko ina ba sai a masallaci....

Ramlat kuwa tana can part ɗin ta tana zaune a gaban madubi tana sanye da sari mai bala'in tsada irin wanda ƴan India suke saka wa a lokacin biki, ta rufe kanta da mayafin sarin wanda duk bakin sarin yake zagaye da duwatsu masu sheƙi da ɗaukar ido kai ka ce a yau ne ranar bikin ta, ga tayi wani irin gyaran gashi na musamman a gaban gashin an manna mata wani irin dutsi mai kama da ɗan kunne mai sheƙi, Ramlat ba ƙaramin kyau tayi ba, duk da Black beauty ce amma kyan ta ba zai misaltu ba, haka lips ɗinta yake ta wal-walin maiƙon glowlips.
wata mata ce take ta bayanta tana shirin ɗaura mata sarƙa mai kalan sarin ɗin jikinta bayan ta sanya mata sarƙa,
matar kana ganin ta kasan ɗaya ce daga cikin kuyangen masarautar, haka ta ɗauki turare ta feffeshe ta da shi sai wani irin ƙamshi take bada wa, ga wasu ƴan matan masarautar su uku suna tsaye ko wacce sai yabonta take, dake sune masu rakata wurin Roshan...

Suna cikin wannan halin sai ga Aunth A'isha ta shugo Amaryar mai martaba tana ganin Ramlat ta zaro ido tare da faÉ—in "wayyo gimbiyar mata kinga irin kyan da kika yi kuwa? haba Ramlat ashe haka kike da irin wannan kyau amma shine bakya son yin kwalliya?..."

Ramlat ta cikin madubi take kallon ta da murmushi akan fuskarta ta ce "da gaske Aunty A'isha nayi kyau sosai?..."

Aunty A'isha ta ce "ai wallahi ko maƙiyin ki bai isa yace baki yi kyau ba, kinyi shiga irin na ƴar India sai kika sa je da su..."

Ramlat ta ce "Aunty A'isha nifa baƙar mace ce su kuma ƴan indian farare ne tas, kuma inda kece kika yi irin wannan shigar tasun baza'a banbance ku ba saboda kema fara ce tass..."

Aunty A'isha tana dariya ta ce "baki ji ance baƙar fata gimbiyar mata ba, baƙa sarauniya ce, sannan baƙa gimbiya cee, ke kyakkyawa ce asalin kyau, domin ke ɗin Black beauty ce..."

Suna cikin wannan hirar sai ga Mamie ta shugo tana ta kallon ƙasƙanci wa kowa daga ƙarshe taja dogon tsuka, ta ƙarasa gaban mirrow yanda Ramlat take,
Maamie tsaya kallon Ramlat tayi daga baya ta ce "wannan É—in Ramlat ce ko kuma Amarya mai martaba yayo ban sani ba?..."

Murmushi Ramlah tayi sannan ta ce "Ni ce mana Aunty Maamie, yau É—in ke ce a É—aki na?..."

Maamie ta ce "Oh laifi nayi dana zo ɗakin ƙanwata wacce muke uwa ɗaya uba ɗaya? nake ga yau sauran kwana biyar ki tafi gidan mijinki shine nazo miki nasiha, ko dai nayi laifi?..."

Girgiza kai Ramlat tayi sannan ta ce "a'ah bakiyi laifi ba, ai daman kece kika ƙi ni duk da muna uwa ɗaya uba ɗaya, maganar nasiha kuma sai dai mu nemi yafiyar juna kawai domin duk wani nasihar da ya kamata naji duk naji su daga bakin Aunty A'isha...."

Wani irin kallo Maamie ta watsa wa INDO sannan ta juyo tana kallon Ramlat ta ce "Oh ni ban kai nayi miki nasiha ba kenan?..."

Ramlat tana kallon Maamie ta cikin madubi ta ce "Nasihar ki bazai wuce akan kada na zauna lafiya da abokiyar zamana ba, da kuma wulaƙanta miji duk nasan wannan nasihar takin tinda shi kike yi anan gidan mijinki, Ni kuma bazan iya bin wannan nasihar ba kinga kuwa ba amfanin gaya mun su..."

Maamie ta ce "shikenam tinda bakya buƙatar jin nasihar tawan, amma wannan kwalliyar da kika yi sai kace shugaban ƙasar America ne ya zo..."

Ramlat tayi murmushi tare da juyo wa ta kalli Maamie sannan ta ce "Hmmm! Maamie kenam ai Roshan yafi ƙarfin wannan matsayin a cikin zuciya ta, idan akwai matsayin da ya wuce na shugaban ƙasar America to Roshan ya wuce wannan ma...."

Maamie ta ce "Hmmm!! Dakyau, to Allah ya baku sa'a, Allah ya kaimu ranar bikin kuma..."

Murmushi Ramlat tayi sannan ta ce "Amiin inda gaske kike..."

Maamie bata juyo ba balle ta kalle ta haka ta bangaje Aunty A'isha ta wuce...

Aunty A'isha girgiza kai kawai tayi ba tare da ta furta komai ba...

Maamie tana fita sai ga wata ta shugo tana faÉ—in "Aunty Ramlat zamu iya kai ki yanzu saboda mijin nakin ya dawo, kuma mun kammala masa gyaran muhallin sa..."

Aunty A'isha ta ce "to kije ki sanar masa cewa za'a kawo Ramlat idan a shirye yake..."

Yarinyar ta amsa cikin girmamawa ta fice....

_______________ Roshan bayan ya koma room É—insa ya sake tarar da an kwashe kayan abincin dinning an gyara wurin tsab,
zama yayi akan kujerar falo yana kallon Film É—in da ake showing a plasman,

Jin sallama ata bakin ƙofa yasa ya waiwaya yana kallon wacce ta shigo, durƙusa wa tayi har ƙasi ta ce "yallaɓai wai ka shirya a kawo Amaryar?..."

Kallon ta yake cikin rashin fahimta ya ce "okay..." abunda ya iya furtawa kenam, ta tashi cikin farin ciki ta fice zata je sanar wa...

Wayar sa ce ta fara ringing yana dubawa yaga suna "Suger wife" ya bayyana akan screen É—in wayar,
Murmushi yayi sannan ya ɗauka tare da furta "Ammata nah amun afuwa na iso ban ƙira ki ba..."

Daga ɓangarenta ta ce "D fatan ka isa cikin ƙoshin lafiya..."

Ya amsa mata da cewa "ina cikin ƙoshin lafiya, Allah yasa ke ma haka..."

Ta ce "lafiya ƙalau ya Amaryar mu?..."

Kafin ya bata amsa yaji anyi sallama an shigo da Ramlat ga Æ´an mata biyu suna gefe da gefen ta Æ´an rakiyar ta,
Ramlat tana rufe da fuska da mayafin sari É—in ta kamar wata amarya,

Roshan ganin su yasa ya sake baki yana kallon su, a cikin ransa yake faÉ—in "duk wannan hidimar na miye? ko dai yau ne ranar Auren?..."

Yana riƙe da waya ga bai kashe ba itama Baiwar ALLAH bata katse ba jin shuru yasa itama tayi shurun tana sauraron mai zai faru domin taji anyi sallama..

Ramlat zama tayi a kujerar da Roshan yake dake 3 seater ne, su kuma waÉ—anda suka rakota sallama suka musu sannan suka fice,
Bayan sun fita ne Ramlat ta zamo daga kan kujerar fuska a rufe ta durƙusa cikin sassanyar murya ta ce "Amincin Allah ya tabbata a gare ka ya Amintaccen zuciya ta, fatan ka iso cikin ƙoshin lafiya ya ma'abocin son ibada da haƙuri da juriya, ina maka fatan alkhairi da cin nasarar rayuwa...."

Baiwar ALLAH jin kalaman nan daga cikin waya yasa zuciyar ta bugawa da ƙarfin gaske nan danan hawaye ya fara gangaro mata ga wani irin kishi da ya ziyarto ta...
Chapter 4 · 0% Book details