Sashe 33
My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk zama suka yi suna sauraron Aunty Yolash,
Aunty Yolash ta fara da cewa
"a shekarun baya akwai wasu maza su biyu aminan juna wanda kullum a tare suke, to ɗaya daga ciki yana da wani ɗansa babba mai shiga rai wanda ɗayan abokin yayi alƙawarin cewa idan ya haifi ɗiya mace zai aura masa ita, yayi alƙawarin tin kafin a haifi yarinyar, shi kuwa Yaron jin haka yasa tin daga lokacin ya fara saka abun a ransa, kullum bashi da zancen da ya wuce Allah yasa a haifo masa yarinyar da aka yi masa alƙawarinta, yasa yarinyar sosai a ransa, wasu daga cikin abokansa har cewa suke to idan aka haifo namiji fa? a lokacin ya samu matsala da su duk wanda yace namiji za'a haifa sai ya samu matsala da shi, daga lokacin da matar abokin mahaifinsa ta haihu kafin a sanar masa ta haifu sai da yaron ya ɗauro alwala ya tsaida sallah ya roƙi Allah yasa haihuwar da akayi mace aka haifa domin ba ƙaramin saka rai yayi akan yarinyar ba, a lokacin da aka sanar masa cewa mace aka haifa bai san lokacin da ya dungura goshinsa ƙasi yana sujjada ba, ya gode wa Allah bana wasa ba, kamar yanda abokin mahaifinsa yayi alƙawarin daga lokacin ya damƙa masa ita yana faɗin ya cika alƙawari, ba ƙaramin farin ciki ya shiga ba lokacin,
Hmmm! daga lokacin yaron ya fara rainon yarinyar har ta fara girma, idan ya ɗauke ta tin safe baya maida ita wurin mahaifiyarta sai dare, har lokacin da yarinyar ta cika shekara biyu, itama yarinyar dake ta tashi tana ganinta a hannun yaron yasa itama ta saka shi a ranta, idan bata gà nshi ba a ranar wuni da kwana zatayi tana kuka, tsabar girman alƙawarin da yake tsakanin su ne yasa suka shaƙu da juna bana wasa ba, a lokacin birthday ɗin yarinyar a ranar yaron ya sanya mata zoben alƙawari itama yarinyar aka bata akan ta sanya wa yaron kuma kar ku manta a lokacin tana ƴar shekara biyu fa, wata rana kwatsam sai aka ji labari marar daɗin ji na cewa yarinyar da mahaifiyarta sunyi hatsarin mota, daga lokacin aka nemi yarinyar aka rasa, yaron jin labarin ba ƙaramin shiga damuwa yayi har jiya sai da yayi, nema kuwa babu yanda bai shiga nemanta ba domin a lokacin bai yadda cewa yarinyar ta mutu ba, anan har akayi tsawon shekara da shekaru kowa ya fidda rai akan ta, yaron kuma daga lokacin bai ƙara saka ko wace mace a cikin zuciyar sa ba, bai taɓa neman wata mace da suna soyayya ba hatta kallon mace baya son yi, shi dai ya ɗora ransa akan yarinyar wai bazai taɓa yin aure ba har sai ta bayyana, kuma yanzu shekara 23 kenam...."
Kowa tsayawa yayi yana kallon Aunty Yolash domin basu taɓa jin wannan labarin ba, koda sun ji ma bazasu fahimci labarin waye ba,
Ummy ta ce "Aunty cigaba mana shin har zuwa yanzu bai haƙura da ita ba? sannan kuma bai yi Aure ba? naji kince tsawon shekara 23..."
Pinky ta ce "Allah sarki naji tausayinsa wallahi..."
Rukky ta ce "itama yarinyar ta saka shi a ranta lokaci guda suka rabu duk da bata mallaki hankalin kanta ba..."
Ramlat idonta akan Aunty Yolash ta ce "Allah yasa dai cigaban labarin suna haÉ—uwa da juna..."
Reemah itama idonta akan Aunty Yolash domin tana son jin ƙarshen labarin domin bata so taji cewa har zuwa yanzu basu haɗu da juna ba..."
Minal ce ta ce "cigaba mana Aunty...."
Aunty Yolash murmushi tayi sannan ta ce "lokaci guda yarinyar ta bayyana a gidan su yaron..."
Duk gaba É—ayansu zaro ido suka yi cike da farin ciki suke faÉ—in "wayyo farin ciki zasu haÉ—u da juna Alhamdulillah..."
Aunty Yolash ta cigaba da basu labari da cewa "yarinyar ta bayyana a gidansu yaron wanda abokin mahaifinta ne ya tsince ta ba tare da sanin ko ita wacece ba domin yarinyar ta zama budurwa ta gaske cikakkiya, haka mai gidan ya cigaba da riƙe ta a mazannin ɗiyarsa har yaron gidan ya nuna yana sonta, amma kuma sai dai kash yaron da aka masa alƙawarinta bai gane cewa yarinyar sa bace sannan yayi alƙawarin bazai taɓa sauraron wata yarinya da sunan soyayya ba inba yarinyar sa ba, shiyasa gaba ɗaya baya shiga harƙar yarinyar da aka kawo gidan su, sai ɗan uwansa da ya nuna yana sonta har akayi Auren su...."
Ummy cikin ƙunci da tashin hankali ta ce "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, amma banso haka ba..."
Minal ta É—an ja tsuka ta ce "ni wallahi har naji labarin ya fara fita mun a rai..."
Kowa dai baiyi farin cikin haka ba.
Aunty Yolash ta cigaba da cewa "haka suke zaman Aure har nan da wasu ƴan shekaru yarinyar bata haihu ba, sai lokaci guda mijin da ta aura wata rana ya gano cewa itace yarinyar da akayi wa ɗan uwansa alƙawarinta ta hanyar wata shaidar da zai nuna cewa ita ce,
daga lokacin bai ƙara samun sukuni ba saboda wannan al'amarin kuma yana ganin saboda itace yasa Ɗan uwansa bai yi Aure har yanzu ba, haka shima Yaron yana zaune ya gano cewa wacce ɗan uwansa yake Aure itace wacce yake jira, ya gano haka ta hanyar sarƙarta da kuma zoben alƙawarin da aka musu tin tana ƙarama itama kuma yarinyar tana ajiye da shi, daga lokacin shima bai ƙara samun sukuni ba, ita kuma yarinyar bata san da wannan al'amarin ba, ita damuwar ta sarƙar ta da zobenta dake hannun wancan ɗan uwan mijinta take so ya bata, domin ta hanyar nan take son neman iyayenta, ganin bazata iya jurewa ba yasa ta ƙira ɗan uwan mijin natan akan yazo ya taimaka ya bata sarƙar ta, shi kuwa jin ƙiran daga gareta ne yasa yazo shi, Mijinta kuwa baya nan lokacin haka ta fara roƙon sa akan ya bata sarƙarta da zobe, duk wasu alamun da zai nuna masa cewa itace yarinyar sa ya duba kuma ya tabbatar, ganin a tunaninta bai yadda cewa sarƙar ta bace yasa ta ja shi ɗakinta ta ɗauko Alkur'ani mai girma ta dafa tana masa rantsuwa akan cewa sarƙar ta ce, bata san cewa ya gane itace yarinyar sa ba, ita kuma bata san halin da ake ciki ba, suna cikin wannan halin har zai bata sarƙar kwatsam wasu daga cikin yaran gidan waɗanda basa son farin cikin ta suka feshe su da turare mai sanya munguwar sha'awa wanda a lokacin hankalin su ya gushe suka fita hayyacinsu har suka aikata alfasha dai-dai lokacin da mijinta ya dawo...."
Ƙirjin Ummy ne ya buga jin irin abinda ya faru tsakanin Uncle Deen da Baiwar ALLAH,
Pinky da Rukky kallon juna suka shiga yi...
Aunty Yolash ta ce "a lokacin mijinta yazo ya kamasu daga lokacin ya saka ƙiyayyar su a cikin zuciyar sa sannan ya rabu da matar sa ita kuma matar ta ɗauki ƙiyayya ta ɗorawa ɗan uwan mijin natan, sai dai a lokacin anyi rashin Sa'a juna biyu ya shiga, shi kuma saboda wannan damuwar yasa ya tafi a hanyarsa yayi hatsarin mota, shi kuma mijin yarinyar shima yayi jinyar damuwar da ya shiga daga ƙarshe yayi auren sa,
Amma ita yarinyar har zuwa yanzu bata san cewa wanda ta tsana shine wanda akayi mata alƙawari da shi tin yarinta ba sannan an kasa sanar mata domin a halin yanzu yanda ta tsane shi bazata taɓa yadda da shi ba,
Shin kun san labarin waye wannan?..."
Duk shiru sukayi sai Reemah da Ramlat da suka girgiza kai alamar a'a..
Murmushi Aunty Yolash tayi sannan ta ce "to labarin Razhdeen da Baiwar ALLAH ne..."
Reemah zaro ido waje tayi tare da haÉ—iyan wani irin yawu zuciyar ta na bugun uku-uku,
Ramlat itama sake baki tayi tana kallon Aunty Yolash cike da mamaki.
Aunty Yolash kallon Reemah tayi sannan ta ce "kin ɗauki tsanar duniya kin ɗorawa mata alhalin ita ce take da Razhdeen, wannan labarin zai nuna miki cewa Razhdeen bazai taɓa sauraron ko wace mace ba indai ba Amreesh ɗinsa ba, don haka wannan ƙiyayyar ki janye shi, sannan kada na sake jin wata daga cikin ku ta ƙira cikin ta da shege ko ƙazamin ciki inba hakaba wallahi zan yi mungun samun matsala da mutum..."
Ta kalli Ramlat ta ce "ke ma har zaki iya ce mata ƙazamin ciki? to ina so ki sani cewa Baiwar Allah ba mazinaciya ba ce, wallahi tallahi ko kamo ƙafar ta bakuyi ba a tsoron Allah da kuma yawan ibada, kawai dai ƙaddarar ta ce tazo da haka...."
Reemah tana zubda hawaye tare da murmushi ta ce "Allah na gode maka da kasa cikin jikinta na wanda akayi mata alƙawari ne, Allah yayi hakane domin yasan hakan shine zai kawo ƙarshen lamarin, in ba dan ta hanyar nan ba taya Yaya Roshan zai yi gaggawar rabuwa da Aunty Baiwar Allah har Uncle Deen ya same ta duk da bata san shi ba, amma kuma lokacin da muke gidan marayu tana yawan mafarkin wani mai suna Habeey tin shekarun baya baazan taɓa manta sunan ba, kenam shine Habeey?...."
Aunty Yolash murmushi ta sau tare da faÉ—in "tabbas shine Razhdeen shine Habeey É—inta..."
Ummy tana dariya ta ce "wallahi nima na taɓa jin tana wannan mafarkin a lokacin ma baccin rana take wai Habeey ina so na tambaye ta akan waye Habeey ɗin nan amma na kasa..."
Aunty Yolash ta ce "Naji Mahaifiyar ta ma tace har yanzu kullum sai tayi mafarkin Habeey, duk maganganun da tayi su tana ƙarama sai ta maimaita su, shine Maman take cewa ko zata sanar mata gaskiyar lamarin ne, muka ce ta bari sai Razhdeen ya dawo tukun duk za'a bayyana mata komai..."
Ramlat itama ta tausaya mata da shi kansa Razhdeen sannan tayi farin cikin jin wannan ƙayataccen labarin, kuma tana so ace an bayyanar wa Baiwar Allah wannan kyakkyawar Albishir, sai kuma taji zuciyar ta tayi sanyi yanzu ta cire Baiwar Allah a Bible ɗinta....
Pinky cikin farin ciki ta ce "wayyo farin ciki ashe dai abun alheri muka haÉ—a har akaita azabtar da mu...."
Rukky ta ce "wonderful wayyo zan so muga ƙarshen labarin nan, yanda Aunty Daughter da Uncle Deen zasu ga junan su..."