← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 68

Sashe 45

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abbah ya ce "shikenam zamu zuba ido idan uwar yarinya ta buƙaci ƴarta duk za'a san yanda za'ayi saboda baza'a hanata ƴarta ba ...."

Sai da suka gama tattaunawa daga bisani kowa ya watse a falon, already Razhdeen da Roshan sun shirya akan gobe zasu nufi ƙasar U.S,
Roshan ɗaukar matar sa ya yi suka nufi part ɗinsu da ƙaton cikin ta..

Shi kuwa Razhdeen room ɗin Reemah ya nufa, yana shiga ya tarar da su akan gado duk sunyi bacci, Reemah rungume da Afaf da haka bacci ya ɗauke su, zama yayi a bakin gado yana ƙare su da kallo, idonsa akan Reemah sai sakin murmushi yake ganin yanda take matuƙar ƙaunar ƴarsa, ya ƙara maida idonsa kan Afaf tare da kai hannunsa yana shafa sumar kanta lokaci guda ya zufafa tunani yanda akayi aka same ta, abunda ya shiga tsakaninsa da Amreesh yake tunowa, da irin matsalolin da suka fuskanta tin farkon haɗuwar su,
wani abu idan ya tuno sai yayi murmushi especially farkon haɗuwar su ganin farko da ta suma, da kuma rufe ta da yayi a ɗakinsa har tsawon sati guda, sai kuma ya tuno da itama ta so shi kamar ta mutu, har ta bayyanar da hakan tin tana kwance a asibiti a ranar Auren ta sai kuma ya ji ƙunci a ransa da Allah yasa ba shi ne ya Aure ta ba,
A yanda yake jin soyayyar Amreesh a ransa gani yake bazai iya haƙura da ita ba, abinda ya shiga tsakanin su ma sai ya ƙara jin ƙaunar ta a ransa,
haka yake ta tunanin Amreesh hannunsa a dafe akan sumar kan Afaf, bayan ya dawo daga dogon tunanin yakai lips É—insa kan goshinsa ya sumbata, sannan ya shafa kan Reemah itama yabar É—akin...

Yana sauƙa falo kai tsaye ainihin part ɗinsa ya nufa dake cikin babban falo, haurawa yayi bayan ya haura sai da ya tsaya yana kallon layin part ɗin Roshan yana murmushi ya girgiza kai sannan ya wuce part ɗinsa wanda ya sha gyara sosai, duk furnitures ɗin ɗakinsa an canza, ba ƙaramin kyau yayi ba, tsaya wa yayi yana ƙare falonsa da kallo wanda ya juma bai shige shi ba sannan ya wuce bedroom ɗinsa, yana shiga ya rage kayan jikinsa ya shige bathroom ya watsa ruwa a jikinsa tare da yin brush sannan ya fito ya sanya ƙananun kayansa already yayi sallar sa abunda ya rage masa shine bacci, hakan kuwa akayi ya miƙe akan katafaren gadonsa, sai da ya juma yana tunanin Baiwar ALLAH kamar yanda ya saba kullum kafin nan bacci ya yi gaba da shi....

★★★★★★

Misalin ƙarfe 8 na dare Ramlat ta idar da sallar isha'i har da lafula tana zaune akan sallaya haka kawai sai zubda hawaye take,
Roshan ne ya shigo ya dawo daga masallaci ya cire jallabiyan sa duk bai lura da halin da take ciki ba, kallon yanda take yayi tare da faɗin "mai kike buƙatar ci?..."

Kanta a sunkuye tana hawaye ta ce "babu..."
Kallon ta ya yi jin kalar amsar da ta bashi, nufan yanda take yayi yaje ya zauna a bakin gado kusa da ita yana fuskantar ta, hannu yasa ya ɗago da haɓar ta suna facing juna, ganin hawaye kwance akan fuska yasa shi cewa "meya faru?..."

Ta ce "Babu komai..."

Ya ce "bana son ƙarya fa, haka kawai zakiyi kuka?..."

Ta ce "Yaya Roshan haka kawai nake jin yin kukan..."
ta riƙo hannayensa tare da karya wuya ta ce "Yaya Roshan nasan na ɓata maka rai, kayi fushi sosai akaina saboda kishi na, ina neman alfarmar ka dan ALLAH ka yafe mun, wallahi bazan ƙara ɓata maka rai ba, bazan ƙara nuna kishina ba, Baiwar ALLAH ta bar maka saƙo akan cewa ka Auri Reemah, nasan saboda ni ne yasa baka amince ba har yanzu, amma nasan Reemah tana sonka sosai, nima yanzu na amince ka Aure ta, zan riƙe ta hannu bibbiyu, zanyi ƙoƙarin faranta maka rai, dan ALLAH kaima ka amince ka auri Reemah, mahaifinta ya mun halacci a rayuwa zanso zama da ita, kishi ne ya rufe min ido yasa na kasa gane wannan amma yanzu na bawa zuciyata ruwan sanyi, dan ALLAH Yaya Roshan...."

Roshan cike da mamaki yake binta da kallo ya ce "duk mai ya kawo waÉ—annan maganganun?..."

Ramlat tana kuka ta ce "Yaya Roshan ka yafe mun?..."

Jinjina kai Roshan yayi sannan ya ce "na yafe miki..."

Ta kuma cewa "kayi mun alƙawarin zaka auri Reemah?..."

Shiru yayi bai bata amsa ba sai ido da ya zuba mata...

Ta ce "Please Yaya Roshan..."
tayi magana tana fashewa da kuka..

Roshan ya ce "it's okay nayi miki alƙawari...".

Sakin murmushi tayi tare da tashi daga kan sallaya ta rungume shi sosai a jikin ta tana faÉ—in "ina sonka sosai Yaya Roshan...."

Shima rungumarta yayi yana rarrashinta da haka tayi shiru ya É—auke ta suka fita, kai falo suka nufa wurin dinning zasu yi lunch É—in dare....

★★★★★

Acan ƙasar U.S
Baiwar Allah yanzu ta zama ainihin Amreesh ɗinta, domin idan ka ganta bazaka iya gane ta ba saboda farin da ta ƙara tayi kyau sosai, ga jikinta ya murmure ta zama dirarriyar mace wanda hips ɗinta ma abun kallo ne, ƙugunta ba ƙaramin cikowa yayi ba, uwa uba breast ɗinta kamar bata taɓa haihuwa,
ta samu hutu sosai duk abinda take so shi ake mata, kulawa da gata duk tana samun su, hankalin ta a kwance yake tana tare da mahaifiyar ta da mahaifinta cikin ƙoshin lafiya,
bata wani saka damuwar kowa a ranta, ta cire kowa a ranta, har mantawa take da tayi zaman Aure balle ta tuno da wani Razhdeen ko Roshan,
mutum ɗaya zuwa biyu ne kawai a ranta yanzu wanda koda yaushe tana kan tuna su, na farko ƴarta wacce ta haifa kullum tana ranta ko sau ɗaya bata taɓa cire ta a ranta ba, itace wacce idan tana tunanin ta take hawaye sai kuma Ƴar Amana itama ba sosai ba...

Saboda ta tsani jin labarin Razhdeen yasa kwata-kwata ba'a mata maganar sa,
Amma akwai dabara É—aya da ake mata wanda ta sa abun a ranta ba tare da tasan ko waye ba,
Kullum Madam Parveen takan bata labarin mutumin da akayi alƙawarin ta a shi da irin kulawar da yake bata amma ba'a sanar mata cewa Razhdeen bane,
tasa mutumin a ranta sosai wanda take muradin son ganinsa amma anƙi nuna mata shi.

Akwai wani ƴar Babynta ƙato wanda aka siya mata tana yarinya, a jikin bebin akwai memory a ciki wanda duk recording maganganun da take yiwa Razhdeen ne tana yarinya, tana magana ana mata recording, har maganar Aure da komai da komai idan tanayi akanyi mata recording, to shine aka saka a jikin bebin kana kunnawa recording zai fara aiki, sai kayi tunanin Bebin ne take magana,
A yanzu wannan Bebin koda yaushe Amreesh tana riƙe da shi, kullum saita kunna maganganun da take yiwa Habeey ɗinta tana ƙarama idan taji ita kaɗai sai tayi ta dariya, domin abin na yarinta ne, kuma yana ɗebe mata kewa sosai most especially idan Madam Parveen ta tafi wurin aiki da Daddynta ita kaɗai a gida sai ta kunna Muryar ta tayi ta sauraro da maganganun Habeey ɗinta,
Ji tayi haka kawai take son jin Muryar Habeey, da irin rarrashin ta da yake idan tana shagwaɓar kuka, kulawa na musamman yana bata sosai, hakan yasa ta saka shi a ranta kuma take son ganinsa,
tayi tayi Mommynta ta sanar mata aina Habeey ɗinta yake amma Madam Parveen taƙi sanar mata, Amreesh tayi akan a nuna mata ko photonsa ne amma anƙi nuna mata, tayi akan a haɗa ta tayi waya da shi amma anƙi bata number sa, hakan haka yasa tayi kuka sosai amma sai dai a rarrashe ta tayi shuru...

Yanzu iya Habeey ne kawai take jin ƙaunar sa a zuciyar ta duk da ta ce bazata ƙara yin soyayya ba amma saboda Habeey yasa ta janye ƙudirinta,
Kuma itama tayi alƙawarin indai yana sonta har yanzu to itama zata aure shi,
Chief ya sanar mata cewa saboda ita yasa har yanzu bai yi Aure ba yana jiran dawowar ta, hakan yasa Amreesh ta ƙara saka shi a ranta, ta bisu akan a sanar wa Habeey cewa ta dawo amma anƙi bin maganar ta, kullum addu'ar ta shine Allah ya kawo mata Habeey....

★★★★★

A yau ne su Razhdeen suka sauƙa a airport dake ƙasar U.S shi da Roshan..

A yau ne kuma aka sanar wa Amreesh cewa yau Habeey yana kan hanyar sa ta zuwa gare ta, dake su Chief da Madam Parveen duk sun san da zuwan su,
Amreesh tsabar farin ciki haka ta fara tsalle tana hawa kujera tana durƙowa ƙasin carpet kamar wata yarinya ƙarama, haka ta kunna waƙa ta ƙura volume take rawa kamar ba jini a jikin ta, daga bisani taje ta ɗauro alwala sai da tayi sallollin lafulolin ta na godewa Ubangiji kafin ta tashi musamman aka ƙira wacce zatayi mata makeup na musamman, ga wedding gown fari sol kamar yau ne ɗaurin Auren ta, kwalliya na musamman aka tsara mata ba ƙaramin kyau tayi ba, yanda kasan shugaban ƙasar england ne zai zo, babu wanda zai ganta bai yabe ta ba,

Dake yau su Minal sun zo gidan Chief jin labarin su Uncle Deen suna hanya ita da Rukky da mazajen su Mohandas da Rakesh kowa ya hallaru a falon gidan,
Razhdeen da Roshan ne suka zo gidan da Æ´ar rakiyar su sojoji wanda Chief ya tura akan aje a É—auko su a airport..

Suna shiga falo kowa farin cikin ganinsu yake, Musamman Minal da Rukky ganin Æ´an uwansu sun zo,
Chief tsabar farin ciki haka duk ya rurrungume su,
Razhdeen dai gaba ɗaya hankalinsa ba'a jikinsa yake ba, shi damuwar sa yayi ido huɗu da Amreesh ɗinsa sai faman leƙe-leƙe yake, duk babu wanda bai fahimci haka ba sai tsokanansa ake ana dariya...

Ita kuwa Amreesh tana room É—inta a zaune a gaban mirror tana kallon kanta sai zabga murmushi take, an gama shiryata tsab kamar wata amarya,
Minal da Rukky ne suka shigo da sallama a bakinsu tare da tsokanan ta suna faɗin "Amaryar Habeey bakya laifi, to yanzu dai Habeey yana buƙatar ganin Amaryar sa..."
Chapter 45 · 0% Book details