← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 68

Sashe 47

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Roshan cije lips ɗinsa na ƙasi yayi tsabar takaici haka ya dafa kafaɗar Razhdeen yana faɗin "my man please tashi mu koma Nigeria..."

Razhdeen idonsa akan Amreesh ya ce "Reesh Please help me, bazan iya rayuwa ba tare da ke ba, ina matuƙar ƙaunar ki..."

Amreesh ta ce "Daddy ka ce su tafi dan ALLAH, ko kuma na tafi na bar muku gidan gaba É—aya..."

Roshan cikin ɓacin rai yake faɗin "My man tashi mu tafi, ka roƙi Allah ya fitar maka da sonta a cikin zuciyar ka, Allah zai baka wacce ta fita, bata sonka banga amfanin tilasta mata ba ...."

Razhdeen babu yanda ya iya haka ya miƙe tsaye idonsa akan ta sai da ya ɗau mintuna kafin ya ce "shikenam zan tafi Reesh! amma ki sani cewa ina nan akan baka ta na cewa bazan taɓa yin Aure without you..."

Kowa na wurin bai ji daɗin abinda ya faru ba, gani suke tinda yanzu tasan shine Habeey zata iya haƙura amma sai suka ga akasin haka...

Amreesh idonta a lumshe ta ce "Go away from me...."

Roshan riƙo hannun Razhdeen ya yi suka nufi bakin ƙofa zasu tafi,
Chief ya dakatar da su da cewa "baza ku koma Nigeria a yau ba, Mohandas zai kai ku wurin masauƙi a other house ɗina..."

Shima Mohandas miƙe wa yayi cikin jin haushin ƙanwarsa zasu fita a tare,
Har zasu fita suka ga Razhdeen ya tsaya cakk suma Roshan da Mohandas tsayawa suka yi tare da juyawa su ga meke faruwa sai gani suka yi Amreesh ta rungume shi ta baya,
Razhdeen kasa juyawa yayi ganin yanda aka rungume shi amma ya tabbatar da cewa Amreesh ce,
kuka take a hankali take furta "Habeey i hate you too much..." ta ƙara wa kukan ta volume sosai,
riƙo hannunta yayi tare da zagayo da ita ta gabansa suna kallon juna daga bisani ya rungume ta sosai shima ya ce "I hate you my Reesh..."

Bugan ƙirjinsa tayi tana dariya domin lokacin da take ƙarama idan tace masa I love you shi kuma cikin wasa sai ya ce mata I hate you da haka ta koya itama take ce masa i hate you....

Cikin farin ciki Minal da Rukky suka fara tafa hannayen su tare da faÉ—in "wow congratulation so nice wannan salon soyayyar ya yi kabce da yawa...."

Madam Parveen itama bata san lokacin da ta fara dariya ba,
Duk haka kowa ya kasance cikin farin ciki lokaci guda,
Shima Roshan bai san lokacin da ya tsinci kansa cikin farin ciki a yayin da yake baƙin ciki rashin mutuncin da tayi wa twins ɗinsa ba...

Haka suka juya cikin falo cikin farin ciki, Razhdeen da Amreesh a kujera ɗaya suka zauna suna riƙe da hannun juna.....

A wannan ranar ne first sight of love da Razhdeen da Amreesh suka kasance, wanda ya kasance iya su biyu ne a falo kowa ya tashi ya bar musu wuri bayan an gama tattaunawa akan batun,
Ba ƙaramin shauƙi da kewar juna suka tsinci kansu a ciki ba, lokaci guda soyayyar Razhdeen ta dawo wa Amreesh ɗanye shakaf fiye da yanda ta so shi a baya, wannan so shi zai kai su har ƙarshen rayuwar su..

★★★★★★

Washe gari da safe Razhdeen da Amreesh suna zaune akan kujeru a wurin shakatawa dake bakin swimming pool na gidan Chief, ga wani lema a saman kujeru yanda rana bazai taɓa su ba, suna shan hirar su kamar babu wata ƙiyayyar da ta shiga tsakanin su,
Amreesh tana zaune sai ga wani zazzafan hawaye yana gangaro mata, a ruɗe Razhdeen ya taso ya zauna a kujerar dake gefen ta ya riƙo hannunta cikin kulawa yake faɗin "wannan hawayen tamkar mashi yake a cikin zuciyata, ganinsa tamkar ana caka mun a tsakiyar zuciya ta ne..."
yana kaiwa nan ya riƙo fuskar ta da hannayensa biyu sannan ya kai bakinsa saitin fuskar ta tare da zaro harshen sa ya fara lashe hawayen fuskar ta, tas sai da ya lashe hawayen da ya gangaro mata,
Ita kuwa abun dariya ya bata hannu tasa ta bugi ƙirjinsa tare da ture shi tana faɗin "kai Habeey meye haka kumaaa..."

Murmushi yayi sex eyes ɗinsa akan kyakkyawar fuskar ta ya ce "da zaki cigaba da zubar da hawaye haka ni kuma zan cigaba da shanye su domin bazan taɓa barin hawayen ki ya zuba ƙasi ko da ya ƙwayar zarra, domin hawayen ki na da matuƙar mahimmanci a rayuwa ta, asarar sa kuma dai dai yake da rasa rayuwa ta..."

Murmushi tayi itama ta ce "Ni kuma bana buƙatar ganin ƙarshen rayuwarka sai dai kai kaga ƙarshen rayuwa ta, ina matuƙar ƙaunar ka Habeey, bana so mu rabu da juna, ina so mutuwa in ta zo ta ɗauke mu tare, ina so soyayyar mu tayi ƙaurin suna ta kuma bayyana kamar Mahadi, ina so soyayyar mu ta cigaba da gudana a cikin jijiyoyin jikin mu sannan al'umma suyi alfahari da mu tare da zuriyar mu ga baki ɗaya...."

Razhdeen jinjina kai yayi sannan ya ce "bazan iya misalta miki yanda girman soyayyar ki take a cikin zuciya ta ba amma zan nuna miki yanda soyayyar mu zata cigaba da gudana a cikin jijiyoyin mu..."

Amreesh sauƙe numfashi tayi tare da faɗin "okay show me how..."

Razhdeen ajiye wata glass cup yayi a gaban sa tare da tsiyaya ruwan bottle a cikin cup ɗin, ya ciro wata sabuwar reza a cikin poket ɗinsa ya ɓare ledar jiki sannan ya ɗago hannun Amreesh tare da buɗe tafin hannunta fari tass mai ɗauke ido,
Idonsa akan fuskar ta ita kuwa idonta akan hannunta yanda ya riƙo babbar yatsar ta ya ɗora reza akai,
zaro ido waje tayi murya na kakkarwa ta ce "H H H Habeey mai zaka yi kuma, yanka ni fa zaka yi...."

Idonsa akan fuskar ta ya ce "kina tunanin zan iya cutar da ke ne?..."

Da sauri ta girgiza masa kai, ya ce "to rufe idonki idan kina jin tsoro..."
kamar yanda ya ce haka tayi,
lips É—insa na motsi a hankali ya furta "Bismillah..." ya É—an dirza rezar akan yatsar ta,
a ɗan ruɗe tasau ƙara tare da buɗe idonta taga yanda jinin ta yake zuba a cikin glass cup da ya ajiye, nan da nan ruwan cikin ya canza launin ja,
idonta takai kan fuskar sa tana kallon ikon Allah baki ya gagara rufuwa,
Bayan jini ya É—an zuba a cikin cup haka ya sa bandej ya manne wurin yankuwan,
ɗagowa yayi shima yana kallon ta shima miƙa mata reza yayi yana ɗaga mata kai alamar ta karɓa, itama karɓa tayi cike da mamaki da rashin sanin dalilin yin haka,
Ya ce "kamar yanda na miki kema ki mun, ki zuba jini na a cikin wannan cup É—in da yake É—auke da jinin ki..."

Miƙa mata hannun sa yayi tare da saita yatsarsa akan cup ya damƙi hannunta mai riƙe da reza ya ɗora rezar akan yatsar yana faɗin "ki yanke ni mana..."

Haka hannun Amreesh yake kakkarwa tana girgiza kai ta ce "ni ni ni bazan iya baaa..."

Murmushi ya yi tare da faÉ—in "ke fa matar soja ce ina so ki zama jaruma, idan kina sona da gaske ki yanke ni, amma idan bakya sona shikenam daga yanzu nasan matsayina..."

Amreesh tana shirin yin kuka Razhdeen yayi saurin dakatar da ita yana faÉ—in "kada na ga hawaye akan fuskar ki domin idan ba haka ba zan iya mutuwa yanzu saboda na sanar miki cewa hawayen ki mashi ne lokaci guda zai iya cakar zuciyata, idan kuwa ya caki zuciyata to mutuwa zanyi....".

Dasauri Amreesh ta goge guntun hawaye da yake shirin zubo mata,
ta ce "Habeey dan ALLAH ka dakatar da wannan abun ba zan iya yankan hannunka ba..."

Razhdeen ya katsar ta da cewa "sai dai idan bakya so nane, nasan inda kina sona da bazaki tsaya yin jayayya da ni ba..."

Amreesh rufe idonta tayi a hankali ta dirza rezar sai ga jini jajawur yana zuba a cikin glass cup sai ya haɗe da nata ruwan ya ƙara yin jaa sosai.

Razhdeen ganin idonta a rufe yasa ya kai lips ɗinsa kan ɗan ƙaramin bakin ta yayi mata wani irin hot kiss, da sauri ta buɗe ido tana bin sa da kallo bata san lokacin da tasau murmushi ba,
Ɗaukar cup yayi yana juyawa da spoon jinin ciki ya gama haɗe wa kamar lemon juice, idonsa akan ta yakai cup ɗin bakinsa yana sha kamar juice itama kallonsa take cike da mamaki haka suke kallon juna, sai da yasha yayi rabi tukun ya miƙa mata yana ɗaga mata kai alamar itama ta sha..
Karɓa tayi ba musu ta ɗora bakin cup akan lips ɗinta itama ta fara sha har sai da ta shanye gaba ɗaya, tana gama shanye wa kuka ya yanko mata tinin ta fashe da kuka tare da rungumar Razhdeen sosai a jikin ta, shi kuwa haka yake bubbugan bayanta yana rarrashi...

Sun kai mintuna a haka, Roshan ne yazo ya tarar da su a haka shima ya juma yana tsaye idonsa a kansu sai sakin murmushi yake domin yanzu babu soyayyar Amreesh a cikin zuciyar sa da taimakon Ubangiji domin tin daga lokacin da Baiwar ALLAH ta bayyana a mazannin Amreesh daga lokacin ya fara roƙon Allah ya cire masa sonta a cikin zuciyar sa, yanzu dai a hankali komai ya dai daita, bazai ce baya sonta ba amma irin soyayyar Aure ko sha'awa babu ita yanzu,
sai da ya juma shima a haka yana maganar zuci daga bisani yayi gyaran murya, duk É—agowa sukayi tare da juyawa suna kallon Roshan,
Da murmushi akan fuskar sa ya ce "sannun ku masoya..."

Amreesh kawar da kanta gefe tayi cikin kunya, shi kuwa Razhdeen tsaya kallon Roshan yayi daga bisani ya ce "ba dai tafiya ba ko?..."

Roshan ya ce "dole zan tafi mana yanzu ake sanar mun cewa Ramlat ta haifi É—a namiji..."

Razhdeen ya ce "congratulation dole tare zamu tafi domin bazan bar ka ka tafi kai É—aya ba...".

Itama Amreesh cewa tayi "gaskiya duk tare zamu tafi, su Ramlat an zama Mama, ma sha ALLAH dole zamu je ganin jariri..."

Roshan idonsa akan Amreesh ya ce "meyasa bakya tambayar Biju Mama ne?..."
Chapter 47 · 0% Book details