← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 68

Sashe 62

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowa da kowa ya hallaru ga abokan Angwaye da Æ´an uwa, har Madam Blessing itama tazo ana jiran mai za'a fara gudanar wa,
wani dogon kujera aka ajiye a gaban hall da table da wata ƙatuwar jita, Razhdeen ne ya yi surprise a Reemah yanda ta iya kaɗa jita har tayi makaranta akai yayi alƙawarin idan lokacin Auren ta yazo sai kowa ya ji sautin kaɗa jitar ta,
Razhdeen ne ya tashi daga yanda yake zaune yazo gaban hall tare da ɗaukan lasfika ya fara sanar wa kowa cewa "wannan jitar ba'a kowa na tanadar ba illa Ƴar uwata jinin jikina wato Amaryar twins ɗina Reemah,
wannan kyauta ta ce a gareta domin tanada wata baiwa wanda ba kowa ne yasan da haka ba, sannan na tanadar da wannan jitar ne saboda ita, ina neman Alfarmar ta da ta fito ta kaɗa wa masoya zazzaƙar jitar ta mai saka mutum cikin shauƙi, wannan shine surprise ɗina a gare ta...."

Lokaci guda wuri ya kaure da tafin hannayen mutanen wurin,
Razhdeen ne ya juya zuwa wurin da Reemah take a zaune, da murmushi akan fuskarsa ya miƙa mata hannu,
ɗagowa tayi tana kallon sa itama murmushin take ta ɗora hannunta akan nashi ta miƙe tsaye, yana riƙe da hannunta suka nufi wurin jita tana taku a hankali dake takalmin ta mai tsini ne sosai,
har sai da ya kaita wurin jitar tukun ya sake mata hannu...

Dasauri Reemah ta juya tana kallon sa ta ce "Uncle Deen..."
ya katseta da cewa "Please my Sarah, inaso kowa yayi alfahari da gimbiya ƙanwata..."

Jinjina kai tayi cikin ƙwarin gwiwa ta zauna akan kujerar ga jita a gabanta,
Roshan shima cike da farin ciki da É—aukin son jin kaÉ—a jitar ya zuba mata ido...
Itama Baiwar ALLAH da murmushi akan fuskar ta take kallon wurin da Reemah take domin itama shaida ne akan baiwar kaÉ—a jitar da Reemah take da shi...
Reemah zama tayi tana tunanin shin idan ta fara kaɗa jitar taya zata fara rera waƙar? ita jitar kawai ta iya kaɗawa amma bata iya waƙar ba, bazata iya bin sautin kiɗan ba,
babu yanda ta iya haka ta fara kaɗa jitar, tin daga farkon sautin mutane suka fara ihu ana tafa hannaye, anan Reemah ta samu ƙwarin gwiwa nan ma ta dage sosai ta fara kaɗa jitar a nutse mai jan hankali, haka take kaɗawa kowa yayi shiru domin sautin irin mai ratsa zuciya ne,
Akwai sauti kala-kala wanda Ƴar Amana ta iya su amma wannan sautin na daban ne, ta zaɓe shi ne saboda ta tuna lokacin da suke rayuwa a gidan marayu, idan wahala tayi wahala takan kaɗa wannan sautin ne saboda ta fi samun nutsuwa,
Baiwar Allah jin kalar sautin da take kaɗawa ne yasa itama ta tuno da wahalar da suka sha a gidan marayu, lokaci guda ta fara zubda hawaye, wanda itama Ƴar Amana zubar da hawaye take idanuwanta a lumshe, duk wanda yaji wannan sautin sai ya zubda ƙwallah saboda lokaci guda sautin yake kashe zuciya,
Ƴar Amana kaɗa jitar take a hankali dai-dai lokacin da wata sautin murya ta fara fitowa tana bin sautin kiɗan, a hankali Ƴar Amana ta fara buɗe idanuwanta domin tasan muryar Baiwar ALLAH ce, saboda ita kaɗai ce ta iya bin sautin kiɗan nan take rera waƙar, murmushi tayi domin hakan yasa ta zaɓi wannan sautin saboda tasan indai Baiwar ALLAH taji sai ta rera waƙar ta, domin ita ta ƙirƙiri waƙar kamar yanda Ƴar Amana ta ƙirƙiri sautin,
Haka ƴar Amana ta cigaba da kaɗa jitar itama Baiwar ALLAH miƙe wa tayi tsaye tana rera waƙa...

Wasu ma'aikata ne suka kawo wani abu mai tsayi na fitar da murya, zuwa tayi ta tsaya a wurin bakinta a saitin abun idonta akan Ƴar Amana, lokaci guda suka sau wa junan su murmushi nan suka fara, wannan tana kaɗa jita mai daɗin sauraro wannan kuma tana rera waƙa da zazzaƙar Muryar ta,

Razhdeen cike da mamaki ya sake baki yana bin Baiwar ALLAH da kallo, dasauri ya dafe kansa yana tariyo kalar muryar nan haɗe da sautin da yake sauraro a cikin mafarkinsa a kwanakin baya, already ya gano Ƴar Amana ita ce mai sautin amma har zuwa yau bai samo mai muryar ba sai yanzu da Allah ya nuna masa, a hankali ya furta "Reesh! daman ke ce? ke ce daman? muryar ki ce how comes ban san da hakan ba sai yanzu?...."

Haka yake ta maganar zuci cike da mamaki, bai damu akan Ƴar Amana ba shi damuwar sa da kuma abinda ya firgita shi shine Baiwar ALLAH, tayi masa tsantsar bazata bayan ya bata labarin duk halin da ya kasance a baya hatta sautin Muryar da yake ji amma bata taɓa sanar masa cewa ita ce kuma tasan ita ɗin ce, tinda a labarin har da ƴar Amana...

Roshan jikinsa ne yayi mungun sanyi shima jin waƙar da sautin duk kashe jiki gare su, na tausayawa ne kuma kamar labarin wahalar da suka sha ne a cikin waƙar, sauran kaɗan ya zubda ƙwallah...

Kaf matan wurin babu wacce batayi hawaye ba, hatta mazan wasu sunyi hawaye wasu kuma jurewa kawai suke,
Suma Baiwar ALLAH da Ƴar Amana duk kuka suke domin kaf labarin su ne a cikin waƙar...

Aunty Yolash da Aunty A'isha da Aunty Maimuna da Ammy da Hajiya Kilishi da Madam Parveen da Minal da Pinky da Rukky da Ummy da sauran duk kuka suke...

Sun daɗe suna waƙar kafin suka dakata ko wacce tayi nisa a kuka duk sun ɓata fuskar su da hawaye, Baiwar ALLAH tana tsaye idonta a lumshe sai kuka take, ji tayi an dafa kafaɗarta ta baya, a hankali ta juya ta buɗe idonta a nutse haka take bin ƙirjinsa da kallo har ta ɗage kanta sama ta haɗa ido da Razhdeen wanda shima ita yake ta kallo fuska ɗauke da damuwa a hankali ya furta "ke ce?..."

ÆŠaga masa kai tayi alamar eh lokaci guda ta fashe da kuka, tasa hannu ta rungume shi shima rungumarta yayi sosai a jikinsa...

Ƴar Amana itama kifar da kanta tayi akan jitar kuka take sosai kamar ranta zai fita, Roshan ne ya taso yazo yanda take cikin tausayawa yasa hannu ya ɗago ta tare da rungumar ta sosai a jikinsa, itama zagayo da hannayenta tayi ta bayansa ta rungume shi sosai tana kuka...

Daƙer kowa ya dawo cikin hayyacinsa suma Amaren aka rarrashe su duk kowacce ta koma wurin zamanta ita da mijinta,
Daga bisani Aunty Yolash ta fito tana sharar hawaye, itama ta gudanar da wa'azinta na gaske mai ratsa zuciya, Aunty Yolash wa'azi tayi sosai kuma daman Malama ce tanada haddar Alkur'ani akanta da fassara ga littafai na hadisai da A'halari kaf litattafan musulunci kusan ko wanne tayi karatu akansa,
nan ma sai da kowa ya zubda ƙwallah domin wa'azin ya shafi imani ne da kuma mutuwa...

Wasu Æ´an mata da yawa sunyi tunanin party za'ayi sai suka ga akasin haka, wata kam kuka ta fara yi tana faÉ—in "nayi tunanin zamu zo mu kwashi rawa ne ashe kawo mu wurinda zamuyi ta kuka akayi, har tsoro da fargaba ya kamani wallahi, yanzu zan fara yin Sallah akai-akai tinda ita mutuwa bata yin sallama..."

Sai da Aunty Yolash ta kammala wa'azin ta itama har da sharar hawaye tukun ta dakata haka, kafin ta sauƙa daga mambari sai da mai ɗaukan photo ya ɗaɗɗauke su a photo ita da Amare da Angwaye, ƴan uwa duk zuwa suka yi akayi photuna sosai ko wacce sai da akayi photo da ita, mijin Aunty Yolash shima fitowa yayi akayi photon da shi,
daga bisani Aunty Yolash tayi musu sallama akan zata koma gida sakamakon ciwon da kanta ke yi tsabar hayaniya,
anan ta bar su, mijinta ne ya É—auke ta a mota ya komar da ita gida,
Sojoji ne suka buÉ—e musu gate suka shige har can cikin harabar gidan, kafin su fito daga cikin motar sai da suka É—an sha hirar su,
Aunty Yolash ce ta sanar masa cewa "Mijina zan je na sha magani sai nayi sallah naga ana shirin ƙiran mangarib kafin mutanen gidan su dawo..."

Mansur ya ce "amma kisa a ranki cewa yau zamu kasance a tare gida É—aya, za'a kai ki É—akin mijinki kema..."

Murmushi tayi sannan ta ce "yau za'a kaini É—akina, Allah Ubangiji yasa na tarar da alkhairi..."

Ya ce "insha Allahu alkhairi zaki tarar har ƙarshen rayuwar mu..."

Ta ce "to sai da safe..."
Yayi saurin katse ta da cewa "sai da safe kuma? naga a yau ne ko wacce za'a kaita É—akin mijinta..."

Cikin zolaya Aunty Yolash ta ce "Au hakane fa ashe, amma kafin nan nasan duk zamu hallara a babban falon Abbah saboda gudanar da nasiha..."

Mansur ya ce "hakane shikenam sai zuwa anjuma..."
Ana suka yi sallama cikin so da ƙaunar juna,
Aunty Yolash tana shiga falo ta tarar wayam ba kowa haka ta nufi É—akin da ba'a fiye shigar sa ba domin bata son hayaniya kuma yanzu mutanen gidan zasu dawo,
Bayan ta shiga bedroom ta ajiye gyalenta da jakar hannunta ta shige toilet ta ɗauro alwala sannan ta zo ta zura hijab har ƙasi ta tsaida sallah,
tayi raka'a uku na sallar mangarib sannan tayi raka'a biyu na lafula tana son godewa Ubangijin ta da ya nuna mata ranar Auren ta da mijin da take matuƙar ƙauna,
A sujjadar ƙarshe ta fara jero Addu'o'i tana godewa Ubangiji.....

Sai yanzu kowa ya fara dawowa gida jiki ba ƙwari, Amare suna dawowa aka nufi wani ɗaki dasu saboda su huta ko wacce ta dawo hayyacinta, kowa yayi farin cikin gudanar da walimar da akayi saboda ko ba komai mutane da yawa sun ƙaru, sun ilmuntu, wasu da dama masu aikata miyagun ayyuka sun shiryu, masu wasa da Sallah sun tsorita jin wa'azin da aka gudanar, imani ya shige su sosai....

Aunty Yolash tana kan sallaya ta roƙi kowa akan bata son ganin mutum a ɗaki saboda tana buƙatar hutawa, har akayi sallar isha'i ta tashi ta tsaida sallah..

★★★★★
Chapter 62 · 0% Book details