← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 68

Sashe 19

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daman Ƴar Amana indai zata saka wando mai belt to Madam Blessing ce take ɗaura mata shiyasa har yanzu bata iya ɗaura wa ba,
Aunty Yolash ce ta tsuguna tare da sa hannu zata ɗaura mata, Ƴar Amana sake wandon tayi ita kuwa Aunty Yolash bata yi gaggawar riƙo wandon ba sai kawai wando ya sulale har ƙasi, da sauri Ƴar Amana tasa hannu ta rufe fuska saboda tsananin kunya,
Aunty Yolash tana dariya ta ce "inna'ilaihi ya haka kuma, ta riƙo wando zata ja mata shi sama Allah yasa tana da pant a ciki, sai da ta zo sai tin cinyar ta da wandon idon Aunty Yolash suka sauƙa akan zanen dake kan cinyar ta, ƙara zaro ido waje tayi ganin zanen kamar na masarautar ƙasar Jidder,
Aunty Yolash hannu tasa tana murtsika idanuwanta ko dai mafarki take ganin da gaske ne yasa ta saka hannu a kan zanen tana shafa gurin cike da mamaki.

suna cikin wannan halin sai ga Aunty A'isha ta shugo É—akin tana faÉ—in "ina Auntyn yara ku fa ake jira a falon kun juma...."

Cike da mamaki Aunty A'isha ta ƙaraso yanda suke ganin Ƴar Amana tana rufe da fuska da hannayenta biyu ita kuma Aunty Yolash tana durƙushe tana riƙe da wandon Ƴar Amana bata gama jansa sama ba,

Aunty A'isha ta ce "ha'a bata iya saka wandon bane?...."
Aunty Yolash ce tayi saurin riƙo hannun Aunty A'isha ta durƙusar da ita ƙasi tana nuna mata zanen kan cinyar Ƴar Amana,
A tsorace Aunty A'isha ta ja da baya tare da zazzaro ido waje tana faÉ—in "wannan ai tambarin masarautar mai martaba ne, ya akayi naga irin zanen akan cinyar yarinyar nan ?...."

Aunty Yolash cike da mamaki take faÉ—in "kuma zai iya kasance wa Reemah ce...."

A zabure Aunty A'isha ta ce "Reemah kuma? ai lokacin da aka haifi Reemah ba'ayi mata wannan zanen ba...."

Aunty Yolash idonta akan zanen ta kuma cewa "zai iya kuma kasancewa Razhdeen ne yasa ayi mata, tinda ta É—au tsawon lokaci a wurin sa..."

Aunty A'isha hannu na kakkarwa ta kai kan haɓar Ƴar Amana ta ɗago da kanta suna kallon juna, itama Ƴar Amana kallon Aunty A'isha ta tsaya yi ganin yanda ta ƙura mata ido, lokaci guda Aunty A'isha taji wani irin yarr a jikin ta, haka zuciyar ta take bugun uku-uku...

Aunty Yolash ce ta É—aura mata belt É—in wando tare da É—agowa ta dafa kafaÉ—ar Aunty A'isha tana faÉ—in "kar muyi gaggawar yanke hukunci sai mun tsawar ta bincike tukun, in ma ita ce za'a gano, idan ma ba ita bace duk dai gaskiya zata bayyana da yardar Allah...."

Aunty A'isha jinjina kai tayi tana zubda hawaye ta juya zasu fita,
Aunty Yolash riƙo hannun Ƴar Amana tayi suka fita tare....

Suna sauƙa falo Abbah ya ce "bacci ne ya ɗauke ku a ɗakin ne?..."

duk zama suka yi ba tare da kowa ya furta komai ba,
Aunty Yolash zama tayi a kujerar da take kusa da Razhdeen tana riƙe da hannun Ƴar Amana zata zaunar da ita, Ƴar Amana idonta ta sauƙar akan wanda yake zaune kusa da Aunty Yolash,
a ruÉ—e ta zaro ido waje ganin Razhdeen,
shima Razhdeen ɗin idonsa ya sauƙar kan Ƴar Amana wanda ko motsi baya iya yi...

Ƴar Amana cike da farin ciki tana washe baki haɗi da kuka ba tare da ta dubi waɗanda suke falon ba tayi tsalle ta fa ɗa jikin Razhdeen...

Cike da fargaba Aunty Yolash ta ce "wayyyyyooo ta kashe shii...."

Razhdeen jin yanda ta fa É—a jikinsa bai san lokacin da ya ce "Asshhhhh....."
abunda ya iya furta wa kenam..
Ita kuwa Ƴar Amana rungumar sa tayi sosai tana kuka ba tare da ta dubi halin da yake ciki...

Duk kowa na falon tsaya kallon su suke da murmushi akan fuskokin su ganin yanda suka shaƙu da juna sosai ...

Baiwar ALLAH tin shugowar Ƴar Amana ta zazzaro ido waje tana binta da kallo, a ruɗe ta miƙe tsaye tana zazzaro manya-manyan idanuwanta baki a buɗe ta gagara furta komai...

Idon kowa sai ya koma kanta, a tunanin kowa sun yi zaton ko dan saboda ta rungumi Razhdeen ne yasa,
Roshan shima idonsa akan Baiwar ALLAH haka yake jin bugun zuciya kamar zai fasa ƙirjinsa, wani sabon kishi ne ya ziyarci cikin zuciyar sa...

Ƴar Amana kifar da kanta tayi akan ƙirjin Razhdeen tana kuka bata ma lura da Baiwar ALLAH ba,
A ruɗe cikin kakkarwar murya Baiwar ALLAH ta soma faɗin "Ƴ Ƴ Ƴar Amana...."

wannan sunan ne ya daki dodon kunnen Ƴar Amana dake kwance akan Razhdeen, sunan da rabon da taji an ƙirata da shi tin tsawon shekara uku yanzu...

Baiwar ALLAH ce ta ƙara nanata sunan "Ƴar Amana..."

Ƴar Amana jin sunan da gaske ake ƙiranta ba gizo ba yasa ta juyo da sauri tana kallon yanda ake ƙiran sunan,
Ganin Baiwar ALLAH a tsaye yasa itama ta miƙe da sauri tana zaro ido, baki a buɗe kamar wacce zata yi magana haka ta ƙura wa Baiwar ALLAH ido,
Baiwar ALLAH cikin kuka ta ce "Ƴar Amana ta...."

Itama Ƴar Amana shirin yin kuka take haɗe da dariya, haka ta rufo kan Baiwar ALLAH da gudu itama Baiwar ALLAH tafo wa tayi suka rungumi juna sosai kamar bazasu ɓanɓaru ba, duk ɗin su kuka suke domin ba ƙaramin kewar juna suka yi ba...

Kowa a falon cike da mamaki suke binsu da kallo.
Baiwar ALLAH ce ta ɗago kan Ƴar Amana tana kuka ta ce "Ƴar Amana daman zamu sake ganin juna? daman ashe da rabon zamu sake ganawa da juna, Allah nagode maka daka bayyano mun Ƴar Amana ta, ina kika shiga ne inata neman ki, nayi kewar ki sosai...."

Ƴar Amana itama kuka take sai yanzu take ƙara jin takaicin rashin iya maganar ta domin tana da maganganu tarin-tarin a bakin ta,
ganin bazata iya cewa komai ba yasa ta ƙara rungumar Baiwar ALLAH sosai,
sai da suka gama koke-koken su da kukan su tukun hankalin su ya koma kan mutanen falon,

Abbah ya ce "Daughter ya isa haka ku nemi wuri ku zauna..."

Baiwar ALLAH tana riƙe da hannun Ƴar Amana suka zauna a tare wuri ɗaya...

Abbah ya ce "daman kun san juna ne?..."

Jinjina kai Baiwar ALLAH tayi...

Abbah ya ce "aina ku ka san juna?...."

Baiwar ALLAH anan ta kwashe labarin zaman su a gidan marayu tin suna yara har kawo Ƴar Amana da akayi tana jaririya, da kuma wahalar da Yallaɓai ya basu har aka sace Ƴar Amana, da jinyar da tayi Madam Aliya ta kaita asibiti har zuwa wannan lokaci bata ɓoye musu komai ba, sannan ta ƙara da cewa "sai yau Allah ya haɗa ni da Ƴar Amana...."

Kowa ya jinjina labarin su, abun tausayi kowa sai da ya tausaya musu banda Mamie da ta toshe kunnen ta da earpiece ta ƙura volume waƙar da take ji, duk abubuwan dake faruwa bata san mai ake tattaunawa akai ba...

Aunty A'isha gaba ɗaya hankalin ta ya kasa kwanciya, jikinta ne yake kakkarwa kamar zazzaɓi ne yake shirin rufan ta, tasa a ranta cewa Ƴar Amana ɗiyar ta ce, tin daga labarin ta da taji ta ɓata ne tana jaririya...

Aunty Yolash ce ta lura da halin da Aunty A'isha ta shiga gaba ɗaya ta ƙanƙame jikinta sai rawar sanyi take tayi...

Aunty Yolash itama taji hakan a ranta ta ce "am Daughter ina so nayi miki wata tambaya..."

Baiwar ALLAH itama Aunty Yolash É—in take kallo,
Aunty Yolash ta ce "akwai wani zane akan cinyar Sarah shin kin san da shi ko kuma babu a lokacin da take jaririyan?..."

Cikin rashin fahimta Baiwar ALLAH ta ce "wata Sarah?..."

Aunty Yolash ta ce "au to Ƴar Amana...."

Jinjina kai Baiwar ALLAH tayi tare da faÉ—in "tabbas akwai zanen masarauta akan cinyarta kuma tin tana jaririya da aka kawo ta dashi ne...."

Aunty Yolash kallon Aunty A'isha tayi suka haÉ—a ido, nan da nan idon Aunty A'isha ya kaÉ—a yayi jawur...

Aunty Yolash girgiza mata kai tayi akan ta dakata kar ta nuna alamun komai...

Abbah ya ce "toh Alhamdulillah tinda Allah yasa yanzu kun ga junan ku, ke Allah ya bayyanar miki da iyayenki itama ki tayata da addu'a Allah ya bayyano mata da nata..."

Abbah ya kuma cewa "ina so na kawo ƙarshen rashin fahimtar juna da ake a cikin gidan nan domin abun ya ishe ni haka, tsakanin Razhdeen da Roshan, to shi dai Razhdeen ba shine mai matsalar ba domin tsawon watanni ba'a cikin hayyacinsa yake ba..."

Abbah ya kalli Roshan sannan ya ce "ga wannan memory inaso kaje ka saka a jikin plasman akwai abinda nake son gani..."

Roshan ba mu su haka ya karɓi memory sannan yaje ya saka a jikin plasman tare da maida film ɗin da ake kalla zuwa USD...
ya koma yaje ya zauna.

Abunda aka fara kalla shine a lokacin da Pinky da Rukky suka je suka ajiye kwalin gift a bakin ƙofar falon part ɗin Roshan sannan sukayi knocking tareda guduwa....

Pinky da Rukky ganin haka yasa suka zazzaro ido waje cike da fargaba da tsoro haka zuciyoyinsu suke bugun uku-uku...

Daga baya Baiwar ALLAH ta buÉ—e tare da É—auka tayi ciki...

Abbah ne ya danna stop tare da kallon su ran a ɓace ya ce "mai ku ka ajiye..."

Baiwar ALLAH itama idonta akan plasman ganin ba Razhdeen ne ya ajiye ba yasa tayi kallon yanda yake a zaune...

Pinky kame-kame ta fara yi ganin haka yasa Abbah ya darara musu tsawa, a ruÉ—e Rukky ta ce "wallahi Abbah zan gaya maka gaskiya,
kyautar Abaya ce muka rubuta cewa Uncle Deen ne, sannan akwai letter a ciki..."
duk ta zayyano abinda suka rubuta a cikin takardar...

Jinjina kai Abbah yayi sannan ya danna remote suka cigaba da kallo,
Iya wurin da aka yi abinda bai dace ba aka yanke,
already sai da Abbah ya kalli video nan tass kafin ya yanke wurin da akayi ta'addanci tukun,
Gani suka yi Baiwar ALLAH ta fito ta shiga mota security ya fita da ita...

Nan ma Abbah stop ya danna sannan ya kalli Baiwar ALLAH ya ce "Daughter ina kike je a lokacin?..."
Chapter 19 · 0% Book details