Sashe 63
My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sallar isha'i su Abbah suma sun dawo da mai martaba da kuma Chief duk suka hallaru a babban falon Abbah wanda ba kowa ne yake shiga ba, Abbah yasa a ƙira masa duk mutanen gidan banda baƙin da suka zo,
Razhdeen da Roshan da Yarima Ashmar da Arash da Mohandas da Rakesh da kuma mijin Aunty Yolash Mansur,
a ɓangaren mata ma duk an ƙira su, Ammy da Hajiya Kilishi da Madam Parveen da Minal da ƙanenta, sai Amreesh da Reemah wanda aka ƙara shirya su cikin wani danƙareren swizlace iri ɗaya domin daga falon Abbah za'a wuce da su ɗakin mazajen su,
duk kowa ya hallara banda Aunty Yolash, Abbah ne ya kalli Rukky ita da ba yaro a hannunta ya ce "je ki ƙira mun Auntyn ku...".
Rukky tashi tayi ta fice, kai tsaye ɗakin da Aunty Yolash take ta nufa ga baƙi a falo yanda suke ta shan kallon su wasu kuma suna cin abinci,
Rukky knocking ta fara yi tana ƙiran sunan Aunty Yolash, jin shuru yasa ta buɗe ɗakin ganin ta akan sallaya tayi sujjada yasa ta juya tare da rufe ƙofa, ta koma falon Abbah ta sanar cewa "Sallah take..."
Nan suka sake wani sabon zama wurin awa guda Aunty Yolash bata zo ba, Abbah ya kalli Ammy ya ce "kije ki ƙira mun ita kice ita muke jira..."
Ammy ta tashi ta fice,
Itama É—akin Aunty Yolash ta shiga still ta tarar da ita akan sallaya tayi sujjada,
Ammy ta ce "wani irin sallah kike ne Auntyn yara..."
Ammy ta zauna a bakin gado tana jiran ta ɗago nan ma sai da tayi mintuna kafin Ammy tasa hannu ta taɓa ta tana faɗin "Auntyn yara lafiyar ki kuwa..."
gani tayi Aunty Yolash tayi gefe ta faɗi ƙasi, a ruɗe Ammy ta furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Auntyn yara meya same ki ne?..."
Ammy ɗagota tayi tana tattaɓata ganin bata motsi yasa ta ajiye ta akan sallaya ta miƙe da gudu ta fice a ɗakin,
Da gudu Ammy ta wuce mutanen falon ta fice kai tsaye falon Abbah ta nufa wanda har sun gaji da jira, a ruɗe Ammy ta shiga tana haki, a tsorace Abbah ya miƙe tsaye yana tambayar lafiya kuwa?..."
Nan Ammy ta sanar musu a halin da ta ga Aunty Yolash, a firgice Abbah ya fice shima da gudu haka mai martaba da mijinta da sauran gaba ɗaya duk ɗakin da Aunty Yolash take suka shige, akan sallaya suka tarar da ita, nan Abbah ya ɗagota ya ɗorata akan gado yana faɗin "A ƙira Doctor, ku ƙira mun Doctor..."
Ammy girgiza kai tayi domin tasan babu wani sauran numfashi a jikin Aunty Yolash amma bazata iya sanar da hakan ba,
Roshan ne ya riƙo hannunta yana dubawa ya taɓa sai tin wuyanta ganin babu alamun numfashi kuma duk wasu alamun mutuwa ya gani a tattare da Aunty Yolash,
A ruɗe Roshan ya miƙe tare da ja da baya yana furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un..."
Dafe saitin zuciyarsa yayi jin bugawar da yayi, a ruÉ—e Abbah ya ce "meya faru da ita?..."
Roshan cikin zubda ƙwallah murya na kakkarwa ya ce "a ƙira Doctor ya duba ta...".
Razhdeen shima haka zuciyarsa take bugawa domin halin da ya ga Roshan yasan akwai matsala, Abbah ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba shi da Mai martaba, Mansur yana manne a jikin gini haka jikinsa yake kakkarwa, matan kuwa duk har sun fara hawaye...
Abbah a kiɗime ya ƙira Doctor akan yazo ya duba jikin Aunty Yolash,
Cikin lokaci ƙanƙani sai ga Doctor ya shigo, Roshan da sauri yabar ɗakin yana sharar hawaye itama Ammy fita tayi domin bata son ganin halin da zasu kasance,
Doctor yana duba Aunty Yolash ya fara girgiza kai cikin nuna damuwa ya ce "Allah Ubangiji ya gafarta mata, ta riga mu gidan gaskiya..."
daga nan Doctor ya yi tafiyar sa...
Abbah baya yayi zai faɗi sakamakon hajijiyan da yake ɗaukansa, dasauri Razhdeen ya riƙo shi tare da zaunar da shi a bakin gado,
Mai martaba bai san lokacin da ya zauna akan sallayar dake shimfiÉ—e ba gaba É—aya ya É—auke wuta,
Hajiya Kilishi jan yaranta tayi gaba É—aya suka bar É—akin ganin ko wacce tana shirin zunduma ihu,
Ummy kam da jaririya a hannunta haka tasau yarinyar da sauri Hajiya Kilishi ta tare ta, ta riƙo hannunta suka yi waje, suna fita falo duk suka fara rausa ihu, kuka suke bana wasa ba,
Reemah tana ɗaki ta manne da jikin bango idonta akan Aunty Yolash sai faman ƙaƙƙafewa take, Aunty A'isha ce ta rungume ta sosai a jikin ta, ta kifar mata da kanta akan ƙirjinta ta fice da ita,
Baiwar Allah kuwa lokaci guda ta yanki jiki ta faÉ—i sumammiya, sai da Yayanta Mohandas ya É—auke ta shima ya fice da ita kai tsaye room É—inta ya wuce da ita yaje ya kwantar da ita,
Mansur mijin Aunty Yolash kam a ruɗe yayi kanta yana faɗin "bazaki tafi ki barni ba Khadijah, ina tare da ke duk yanda kika je, ƙafata ƙafar ki wallahi bazan bari ki tafi ki barni ba, meyasa zaki mun haka Khadijah, sai da rayuwa tazo mana mai daɗi shine zaki tafi? meyasa bazaki bari mu inganta rayuwar mu ba, meyasa bazaki bari mu gudanar da zamantakewar Auren mu ba, why Khadijah! why Khadijah!! why Khadijah!!!...."
Lokaci guda shima ya fara amar da jini hannunsa akan ƙirjinsa wurin zuciya, ya kifar da kansa akan ƙirjin Aunty Yolash yana tari shima lokaci guda ya tsaya cakk, kowa yana cikin jimamin rashin Aunty Yolash basu ankara da Mansur ba, sai da Chief mahaifin Baiwar Allah ya ɗora hannu akan kafaɗar Mansur zai ɗagoshi yaga shima jikinsa ya sake, dasauri Chief ya dudduba shi a ruɗe ya ce "shima fa mijin baya motsi..."
Dasauri Razhdeen ya fice ya je ya ƙira Roshan, jiki ba ƙwari Roshan ya shigo da abun duba numfashi yana zuwa ya gwada Mansur, girgiza kai ya yi ya ce "Shima ya tafi..."
A ruɗe Abbah ya miƙe tsaye ya ce "ya tafi ina?..."
Roshan ya ce "ya tafi can..."
Cikin ƙiƙƙina Abbah ya ce "kana nufin ka ce ya bita sun tafi?..."
Cikin kuka Roshan ya ce "eh Abbah..."
Abbah ba abinda yake faÉ—i illah "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un..."
Mai martaba kam babu bakin magana, domin a halin yanzu ba'a cikin hayyacinsa yake ba...
Lokaci guda labari ya baza ko ina na cewa Aunty Yolash ta rasu ita da mijinta,
Kowa ya yi jimamin rashin Aunty Yolash, ga mijinta shima ya rasu sanadiyar rashin ta.
Ƙawayenta waɗanda suka zo bikinta kusan kowa bata yadda akan cewa ta mutu ba,
Cike da mamaki kowa yake jijina lamarin mutuwa lokaci guda ba jinya ba komai ƙarar kwana.
A wannan daren aka sanar wa Æ´an uwan Mansur su ma..
Bayan kowa ya dawo hayyacinsa anan aka sanar cewa za'a bar gawar su sai zuwa gobe ayi jana'izar su, Abbah ne kawai ya ƙi amincewa ya ce "kamar yanda Allah ya ɗauki rayuwar su a yau Jumma'at to dole a daren juma'an nan za'a kai su ɗakunan su na gaskiya..."
Kamar yanda Abbah ya ce haka kuwa akayi, a wannan daren akayi musu wanka aka sallace su, tare da kai su kabarin su, ga kabarin mata ga na miji, sun kwana a É—akin su na gaskiya...
A washe gari labari har a jarida aka bubbuga, a television da ko ina, wasu sunyi tunanin ko hatsarin mota suka yi sai suka ji labari yasha bambam,
Ƴan uwa da abokan arziƙi duk babu wanda bai shiga tashin hankali ba,
sanadiyar haka yasa hawan jinin Abbah tashi,
Ana bikin murnar Aure da kuma haihuwa sai kuma mutuwa ta shiga tsakani.....
Typing âœï¸ Asmeetah writer
*MY ENEMY*
*TAKUN ƘARSHE*
*BOOK 3*
96 to 100
*END OF BOOK 3*
Mutuwar Aunty Yolash ba yanda bai zaga ba, ma sha ALLAH tayi Al'umma sosai, waÉ—anda basu zo Auren ba jin mutuwar ta yasa suka zo ta'aziyya, gidan Abbah mutane ne tam masu zaman makoki ciki da waje, motoci kuwa tsabar mutane ba'a iya shigo da mota cikin unguwar, haka gidan su miji nan ma mutane ne na fitar hankali dake babban mutum ne,
Roshan kam a ɗan kwanakin nan anyi masa mutuwa mai zafi, ga na matarsa Ramlat ga kuma yanzu na Auntynsu mai shigar rai itama kwana ya ƙare, duk babu mai wargi a duk mutanen gidan,
Ummy itama ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, gani take kamar zata ga Aunty Yolash a cikin mutanen gidan, yau kuka gobe kuka ta kasa kwantar da hankalin ta,
Haka Reemah tinda tayi ido huɗu da gawar Aunty Yolash daga nan bata ƙara dawo hayyacinta ba, haka kawai sai tana firgita gawar ce kawai take mata gizo, ga yawan mafarkin ta, gaba ɗaya ta kasa shiga taitayinta,
Baiwar Allah wacce ta farfaɗo har yanzu bata gama tabbatar da cewa Aunty Yolash ta mutu ba, bakin ta ba abinda yake furtawa illah "bata mutu ba ƙarya ne, babu alamun mutuwa a jikin ta kuma bata nuna hakan ba..."
Reemah da Baiwar ALLAH tsabar suna cikin jimamin mutuwa yau har akayi kwana bakwai basu yi ido huɗu da mazajensu ba, suma haka Razhdeen da Roshan basu nemi ganin su ba har yau, domin mutuwar ba ƙaramin jijjiga kowa yayi ba,
Sai da akayi kwana bakwai kafin mutane suka fara raguwa, ƴan ƙasar waje suka fara tattafiya, haka ƴan wasu garuruwa,
a kwana a tashi har aka wayi gari zaman makoki ya ƙare babu mutane a gidan Abbah sai ƴan gidan, shikenam Auntyn yara ta tafi abu kamar a mafarki ya zamto gaskiya,