Sashe 30
My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rukky ta ce "ahhh kuma fa hakane amma ai taci sunanta Aunty Daughter..."
Minal ta ce "dan ubanku ai Auntyn ku ce tinda ta auri Yayan ku..."
Pinky ta ce "kuma fa hakaneee..."
Minal ta É—ago tana kallon Baiwar ALLAH ta ce "yawwa ni Aunty Daughter me ya hanaki zuwa wurin party ne kam?..."
Baiwar ALLAH ta ce "wallahi Aunty Minal kaina ne yake ciwo shiyasa banje ba..."
Rukky ta ce "wai kina nufin kice iya ke kaÉ—ai aka bari a gidan?.."
Pinky ta ce "ni ban lura da ita ba wallahi saboda abubuwa sun sha mun kai, ni yanzu bazan iya tantance su waye suka je da kuma waɗanda basu je ba, har a cikin ƙawayen mu..."
Baiwar ALLAH murmushi kawai ta saki kanta a ƙasi tana wasa da yatsun ta, can ta ɗago tana waiwaye tare da faɗin "wai ni ina Yaro nane..."
Minal ta ce "ga shi can yanata shan baccin wahala..."
Baiwar ALLAH ta ce "Ayyah yaron kirki ai da an bar mun shi..."
Minal ta ce "gaskiya ne ai kuma da kin je wurin party ba shiri..."
Duk suka kwashe da dariya....
Ummy dake zaune a tsakiyar gado sai danna wayarta take tin shugowar Baiwar ALLAH bata É—ago ba balle tasa musu baki a hirar su...
Rukky cike da mamaki ta ce "ikon ALLAH! wai yanzu duk ɗin mu kowa zai kama ƙasar da zai je da Aure ko?..."
Pinky ta ce "daga gobe ne fa, duk kowa zai watse gaskiya zamuyi missing ɗin juna, gwara ku Aunty Minal da Rukky a ƙasa ɗaya zaku zauna tinda duk mazajen ku a ƙasa ɗaya suke hakan ma gida ɗaya uwa ɗaya uba ɗaya, zaku na haɗuwa kusan kullum, ni da Ummy ne sai Allah, ni ƙasar Saudiyya Ummy kuma ƙasar Jidder...."
Minal ta ce "ai gwara ita Ummy tana kusa da Uncle duk da ba'a gida ɗaya zasu zauna ba amma nasan zata na yawan zuwa masarauta ga kuma ƙawarta Reemah..."
Pinky ta ce "Allah sarki Ni kaɗai ce zanje wuri a baƙunta babu na gida..."
Rukky ta ce "kina tare da Æ´an uwan Ammy ai..."
Pinky ta ce "Ammy ai kishiyar uwa ce, ban shaƙu da ƴan uwanta sosai ba..."
Minal ta ce "sai ki É—auka tamkar uwar ki ce, kina musu biyayya kuma..."
Pinky fari tayi da idonta tana faÉ—in "ai Ni gidana ni É—aya ne..."
Minal ta ce "kowa ma ai gidansa shi É—aya ne, kina nufin baza kina zuwa musu ziyara bane?..."
Pinky ta ce "zan rinƙa zuwa mana...."
Ummy ce ta ɗan ja tsuka tare da sauƙa daga kan gado zata fice..
Minal ta ce "ina kuma zaki je..."
Ummy tana harare -harare ta ce "ni bana iya zama inuwa É—aya da mutum..."
Duk sun san da wacce take, kuma itama Baiwar ALLAH tasan da ita take,
Minal rai a ɓace ta ce "duk wanda yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake, wai ni Ummy yaushe kika zama hakane? wallahi kwata-kwata kin chanza, yanzu kin zama mahaukaciya..."
Ummy ta ce "na daÉ—e da zama mahaukaciya ai tin yaushe..." ta juya zata fita, Minal tayi saurin cewa "ki dawo kizo ki zauna..."
tsayawa Ummy tayi ita bata fita ba sannan bata juyo ciki ba, har Minal ta tashi ta fice taje ta ƙira Aunty Yolash suka shigo tare,
Aunty Yolash cewa tayi "me yake faruwa ne?..."
Nan Minal ta sanar mata cewa "Aunty wallahi Ummy bata da hankali, gava ya ƙi ƙarewa ita da Aunty Daughter, kuma duk laifin Ummy ce, bata mata magana, yanzu haka fita take son yi wai bata son zama inuwa ɗaya da Aunty Daughter, kenam ita ba'a isa a gaya mata taji ba?..."
Aunty Yolash riƙo hannun Ummy tayi suka ƙarasa ciki ta zaunar da ita itama ta zauna tare da faɗin "Uwar masu gida meye matsalar ki ne?..."
Ummy ta ce "idan na tuno da abinda ya faru ita da Uncle Deen ne sai inji raina yana ɓaci...."
Aunty Yolash ta ce "dan ƙaniyarki ina ruwanki da batun nan, ko shi Roshan baya mata wannan ƙiyayyar, amma ke saboda shashanci sai kace ke ce mijin da akayi wa laifin, idan haushin ne sai ki sauƙe haushin ki akan ƴan uwanki tinda su sukayi silar faruwar haka, kuma ko shi Roshan bai isa ya bata laifi ita da Razhdeen ba sai dai yaƙi gaskiya, kuma dan ubanku daga ke har Roshan ɗin yanzu haka idan ku ka tsaya aka feshe ku da turaren nan bazaku san lokacin da zaku aikata wani abu ba, duk da yana ɗan uwanki jini ɗaya hankalin ku gaba ɗaya zai gushe, an gaya miki cewa ba laifin ta bane, an gaya miki da yaren Hausa sannan an sanar miki da yaren English uwa uba an nuna miki video yanda abun ya faru, to tinda haushin ta kike mai zai hana ki ɗauko wuƙa ki caka mata in yaso sai mu san ƙiyayyar da gaske kike nuna mata, kuma abun nakin har da son kai wallahi, baki ji haushin ƴan uwanki ba sai ita saboda bata da iyaye daga sama ta faɗo, to bari kiji ko wani ɗan adam a rayuwa baya taɓa tsallake ƙaddarar sa, tin kafin mutum yazo duniya ƙaddarar sa take a rubuce, Allah ne yasa zata samu cikin jikinta ta hanyar nan babu yanda ta iya saboda haka ƙaddarar ta yake, bata isa kuma ta tsallake ba, itama kanta ba'a son ranta take ajiye da cikin nan a jikinta ba, kuma duk damuwar da zaki shiga da shi Roshan ɗin bazaku taɓa kai rabinta a shiga damuwa ba, inda kin san irin damuwar da take ciki wallahi da ke bakida bakin magana, idan kuma baki yadda da ƙaddara ba to imanin ki bata cika ba, domin cikar imani shine ka yarda da ƙaddara mai kyau ko akasin haka,
Ummy inaso ki sani fa gidan wani zaki je kuma tafiya mai nisa zakiyi, ba tare zaku zauna ba yanzu baki sani ba shin zaku ƙara haɗuwa ne ko kuma bazaku ƙara ganin juna ba, ita fa mutuwa bata sallama, babu kyau ki tafi gidan miji kina mai jin haushin wani a cikin ranki, Pinky da Rukky sun aikata laifi kuma sun nemi yafiyar wanda suka yi wa laifin daga Daughter har Roshan da Abbah duk sun nemi yafiyar su kuma an yafe musu, yanzu Razhdeen suke jira duk lokacin da ya dawo shima zasu nemi yafiyar sa akan abinda suka saka shi ya aikata a bisa dole,
Don haka kema Ummy inaso a yanzun nan ki bawa Daughter haƙuri ku rabu lafiya da juna...."
Baiwar ALLAH itama tana zaune hawaye sai gangaro mata yake,
Itama Ummy zubda hawayen take tana wasa da yatsun ta, ga Pinky da Rukky su ma yanda suke kuka domin duk su suka jawo komai...
Ummy jinjina kai tayi tare da faÉ—in "shikenam Aunty Insha Allahu komai ya wuce...."
Aunty Yolash ta ce "masha Allah! yanzu kiyi mata magana..."
Ummy tashi tayi ta koma gefen Baiwar ALLAH ta zauna tare da riƙo hannun ta tana faɗin "Aunty Daughter Dan ALLAH kiyi haƙuri a bisa mis-understanding ɗinki da nayi, gaba ɗaya idanuwa na sun rurrufe tare da kunnuwa na, na kasa tantance baƙi da kuma fari, duk da video da na kallah naga ba laifin ku bane amma shaiɗan bai daina cusa mun ƙiyayyarki a cikin zuciyata ba, na faɗa miki maganganu marasa daɗin ji kuma duk kin jure dan ALLAH ki yafe mun, kiyi haƙuri komai ya wuce, mu koma kamar yanda muke a baya, ni a wurina Roshan da Razhdeen duk ɗaya ne a wuri na, AM so sorry please...."
Baiwar ALLAH tana kuka babu bakin magana sai hannu da tasa ta rungumi Ummy, itama Ummy hannu tasa ta rungume ta tana kuka,
É—agowa tayi suna kallon juna Baiwar ALLAH ta ce "ba komai, na yafe miki nima inaso ku yafe mun..."
Ummy ta ce "ai ke babu abinda kika yi mana, kinada kyakkyawar zuciya..."
Ummy takai idonta kan tumbin cikin Baiwar ALLAH sannan ta É—ora hannunta akai ga shi yanda ya girma sosai,
Ummy rufe idonta tayi lips É—inta na motsi hannu akan cikin alamun addu'a take yiwa cikin...
Bayan sun gama sai ga Pinky da Rukky su ma sun matso kusa da Baiwar ALLAH suna faɗin "Aunty Daughter Dan ALLAH muna mai ƙara neman yafiyar ki akan mummunan abubuwan da muka miki..."
Baiwar ALLAH share hawayen ta tayi tare da faɗin "haba dai ai mun daɗe da wuce wannan layin, yanzu banida damuwa da kowa a cikin ku sai Ƴar Amana..."
Aunty Yolash ta ce "ita wannan ai ƴar juju ce, yanda kasan mai aljanu haka take, ta nuna tana son Razhdeen kuma yau ga yanayin da aka ganta ita da Roshan a wurin taro, amma kar ki damu zan san yanda zan yi na shawo kanta, dole ta haƙura itama, ƴar banzar yarinya ga ƙarantar shekaru sai iya shege..."
Duk murmushi suka yi,
Baiwar ALLAH ta kalli Pinky da Rukky ta ce "meye to kuke kukan, ku matso ku ji..."
Duk rungumar su Baiwar ALLAH tayi, itama Ummy rungumar Baiwar ALLAH tayi duk suka haÉ—e kayuwan su...
Aunty Yolash ganin haka yasa tasau murmushi tare da ficewa daga É—akin domin yau babu alamar kowa zai kwanta yin bacci....
Ƴar Amana kuwa tinin ta isa part ɗin Roshan ta fara buga musu gate, sai da ta ɗan juma kafin taji motsin mutum anzo buɗe mata,
Ramlat ce ta buɗe cike da mamaki take bin Reemah da kallo, sai kallonta take tayi daga sama har ƙasa ta ce "ke kuma fa a wannan daren?..."
Reemah ta ce "inason ganin Yayana..."
Ramlat ta ce "mai zai zauna yayi har zuwa wannan lokacin bai yi bacci ba..."
Reemah ganin bazata iya juran yin magana ba yasa ta ratsa ta gefen Ramlat ta wuce ciki, cike da mamaki Ramlat ta bi bayanta da kallo daga baya itama ta shige ciki,
Ganin bata ga Reemah a falo ba yasa ta faÉ—in "to tana ina kuma?..."
zuciyar ta na harbawa ta nufi bedroom É—insu tana sanye da sleeping dress, tana shiga ta tarar da Reemah kwance a gefen Roshan wanda ya juma da yin bacci..