← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 68

Sashe 49

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Madam Parveen ta ce "Amreesh naga kin shaƙu da yarinyar nan sosai duk da ke kika haife ta amma dole zan gaya miki abinda ake ɓoyewa a cikin gidan nan, akan ƴarki Afaf da kuma Reemah..."

Baiwar Allah cike da mamaki take binta da kallo ta ce "me yake faruwa ne Mommy, me ya faru da Ƴar Amana ta da kuma Afaf?..."

Madam Parveen sai da ta sauƙe nannauyar numfashi kafin ta sanar mata duk halin da ake ciki da kuma abinda ya faru lokacin da suka zo ɗaukar Afaf..."

Baiwar Allah lokaci guda hawaye har ya wanke mata fuska ta ce "daman nasan baza'a rasa aljanu a jikin Ƴar Amana ba, aljanun ta kuma sai suka haɗa ta da yarinya ta, Allah sarki Ƴar Amana indai Afaf ce farin cikin ta to ni na bar mata ita duniya da lahira, domin duk wanda ya nuna yana son jininka to babban masoyinka ne..."

Madam Parveen jinjina kai tayi sannan ta ce "shikenam kin sadaukar da Æ´arki?.."

Baiwar Allah ta ce "na sadaukar da ita indai ba cutar mun da ita za'ayi ba, nasan zata fi samun kulawa sosai a wurin Ƴar Amana fiye da yanda zan bata, kuma Ƴar Amana tin Afaf tana jaririya take riƙe da ita kamar yanda na riƙe ta lokacin da take jaririya why ni bazan bata nawa ba, don haka zanje na sanyata cikin farin ciki..."

Ta ƙarasa maganar tana kallon yanda Afaf take ta wasan ta ta ce "Biju Mama zo ma za na kai ki wurin Auntyn ki..."

tasa hannu ta É—auke ta suka fice a É—akin,
Madam Parveen binta kawai tayi da ido tare da girgiza kai tana jinjina lamarin nan...

Baiwar Allah tana fita falo kai tsaye ɗakin Ƴar Amana ta nufa, tana shiga ta tarar da ita zaune akan gado ta rungumi pillow sai kuka take ga kuma Ummy a gefenta sai rarrashin ta take...

Baiwar Allah tsayawa tayi tana ɗauke da Afaf idonta akan Reemah tasan duk akan Afaf ta shiga damuwar nan, cike da tausayawa Baiwar ALLAH ta ƙira sunan ta tare da faɗin "Ƴar Amana..."

Reemah ɗagowa tayi tana haɗa ido da Baiwar ALLAH tare da Afaf tayi saurin tashi daga kan gadon ta nufi yanda suke tsaye tana ƙoƙarin karɓan Afaf duk da Yarinyar tayi wayo 2 years amma ɗaukar ta ake kamar jaririya,
Baiwar Allah tana murmushi ta miƙa mata ita tana faɗin "ga nan ƴarki na kawo miki ita..."

Ƴar Amana dariya ta soma yi tana faɗin "Nagode sosai wallahi ina matuƙar ƙaunar ta, dan Allah Aunty Baiwar ALLAH ki bar mun ita, wallahi zan kula miki da ita sosai...."

Baiwar Allah dafa kafaɗarta tayi tana murmushi ta ce "kar ki damu Ƴar Amana ta, na bar miki Afaf..."

A ruɗe Ƴar Amana ta ce "wai da gaske Aunty Baiwar ALLAH? wayyo farin ciki nagode sosai, shikenam Biju Mama ta zamo tawa har abada..."

Haka Ƴar Amana take sumbatar Afaf akan goshi tsabar farin ciki..

Ummy itama tana zaune bata san lokacin da ta tsinci kanta cikin farin ciki ba, lokaci guda kuma ta maida idonta kan Baiwar ALLAH sai taji tausayinta domin tasan tana buƙatar ɗiyarta a kusa da ita amma ta sadaukar da ita....

Baiwar Allah juyawa tayi ta fice daga ɗakin ganin hawaye yana shirin zubo mata domin itama tasa Afaf a ranta sosai, tana fita falo hannunta akan fuska yanda take ƙoƙarin share hawaye zata wuce taji an riƙo hannunta,
da sauri ta sauƙe hannun tare da ɗaga kanta tana kallon wanda ya riƙe ta,
Razhdeen ne ya riƙo ta yana ƙareta da kallo murya ciki-ciki ya ce "why are you crying?..."

Girgiza kai tayi tare da faÉ—in "ba komai..."

Ya ce "Please i need to know who make you cry, idan har kina son ganin farin ciki na ki sanar mun abinda yake ranki...."

Baiwar Allah gani tayi bazata iya riƙe kukan da ya kuɓuto mata ba yasa ta rungumi Razhdeen tare da kifar da kanta akan faffaɗan ƙirjinsa ta fashe da kuka.

Sauƙe numfashi yayi yasa hannu ya ɗauke ta kai tsaye part ɗinsa ya nufa da ita, a hankali ya haura upstairs sannan ya miƙe hanyar room ɗinsa, yana shiga falo ya wuce da ita bedroom ɗinsa bai sauƙe ta a ko ina ba sai akan katafaren gadonsa, a tsakiyar gado ya zaunar da ita shima ya hau ya zauna yana fuskantar ta, yasa hannu ya tallafo fuskar ta ya ce "Reesh! Me ya same ki?..."

murya ciki-ciki ta ce "ban san halin da Ƴar Amana da Biju Mama suke ciki ba sai yau, na sadaukar da ƴata, na bar mata ita har abada domin ta nuna mun ta fini sonta sosai, kuma tayi ɗawainiya da Biju Mama tin tana jaririya..."

Razhdeen sauƙe numfashi yayi yana riƙe da fuskar ta ya ce "to meya sakaki kuka? shin sadaukarwar da kikayi ne yasa kike kuka ko kuma me ye?..."

Baiwar Allah ta ce "Ni bazan ɓoye maka ba nima ina son Biju Mama, bana so na ƙara yin nisa da ita, ina so yarinyata ta shaƙu da ni sosai, amma bayar ta da nayi a Ƴar Amana duk ban faɗi ƙasi ba tinda duk ɗaya muke amma babban damuwa ta shine aljanun da suka raɓe su, ina tsoron aljanu sosai..."

Razhdeen jawo ta yayi jikinsa yana rarrashin ta ya ce "kar ki damu zamu sake haifan wasu ai, kuma sannan aljanun ba masu cutar wa bane ki kwantar da hankalin ki Biju Mama ai tana tare da mu tinda a wurin Sarah take, naji Abbah da Uncle suna maganar cewa zasu haÉ—a Roshan da Sarah...."

Baiwar Allah ɗagowa tayi lokaci guda ta saki ranta cikin fara'a take faɗin "Ma sha ALLAH! inason haɗin nan sosai, kuma sun dace da juna, kasan Ƴar Amana tana son Yaya Roshan, shi kuma abinda yasa bai ɗora ransa akan ta ba saboda marigayiya Ramlat ce amma nasan shima yana sonta...."

Razhdeen hannu yasa ya É—an ja kuncin ta yana murmushi ya ce "taya kika san Roshan yana son Sarah?..."

Baiwar Allah kwantar da kanta tayi akan ƙirjinsa tana faɗin "na fa zauna da Yaya Roshan, na gama sanin duk wani take-takensa abinda yake ɓoyewa da kuma sirrin cikin zuciyar sa, na gama yin bincike na na gano cewa yana son Ƴar Amana sosai, tin kafin na tafi na gama sanin haka kuma itama tana son sa, amma kuma jaririnsa wa zai riƙe masa ?..."

Razhdeen ya ce "baza a rasa ba..."

Baiwar Allah kasancewar ta da Razhdeen ya ƙara je fa ta cikin shauƙi, haka kawai sai sakin murmushi take,
ta ƙira sunansa a hankali "Habeey..."

Ya amsa mata cikin kulawa.
Ta ce "yaushe ne Auren mu?..."
Murmushi yayi shima ya ce "ƙarshen watan nan ranar da Ramlat zata cika wata uku a ranar twins ɗina shima za'a Aura masa Sarah..."

Baiwar Allah ta ce "kenam kai da shi za'ayi bikin rana É—aya ?..."

Ya ce "of course my wife, kinga ana bikin mu zamu koma U.S domin zan koma wurin aiki na shima Roshan zai koma Egyph shi da matar sa da yaransa Biju Mama da kuma Boy..."

Baiwar Allah ta ce "kenam duk yara biyun zasu tafi?..."

Ya ce "to waya sani ne sai lokacin yayi komai zai bayyana..."

Baiwar Allah sai da ta ɗan yi shiru na wani lokaci sannan ta ce "ni sai a bar mun yaron zan riƙe shi...".

Razhdeen ya ce "ke da zaki fara aikin soja..."

A zabure Baiwar ALLAH ta É—ago tana kallonsa gira a haÉ—e ta ce "wani soja? impossible wallahi haka naji Daddy na yake faÉ—a Ni kuma bazan iya ba..."

Ya ce "zaki iya mana ke fa jaruma ce..."

Kamar zata yi kuka ta ce "Ni kawai bana so, ku daina mun zancen nan..."

Dariya ya yi yana bubbugan bayanta irin na rarrashin nan, da haka suka wuni a É—akin..."

Roshan yana part ɗinsa a zaune kan kujerar falo misalin ƙarfe 8 na dare ya haɗe kansa da gwiwa yana tunanin abubuwa da dama,
Bai ankara ba yaji an dafa kafaÉ—arsa ta baya dasauri ya É—ago yana kallon wacce ta É—ora masa hannu,
Cikin sassanyar murya ta ƙira sunan sa "Yaya Roshan...."

HaÉ—iyar yawu yayi idonsa akan ta ya ce "Shalele ya akayi ne?..."

Ƴar Amana cikin damuwa ta ce "meyasa bazaka dawo yanda kake a baya ba, bana son ganinka cikin damuwa, wanda ya mutu ya tafi kenam ba halin dawowa dan Allah Yaya Roshan...."

Sauƙe numfashi ya yi tare da faɗin "ki kwantar da hankalin ki bawai ina jimamin mutuwar bane har yanzu komai na barwa Allah, haka Allah yaso da ni kuma ina fatan hakan shine mafi alkhairi a rayuwa ta gaba ɗaya..."

Ƴar Amana jinjina kai tayi sannan ta ce "ma sha ALLAH! to yanzun tunanin me kake?..."

Girgiza kai yayi sannan ya ce "kawai dai haka ne idan na kasance ni kaÉ—ai...".

Cikin nuna damuwa ta ce "shin kana son kasancewa da ni? bana so ka rinƙa zama a haka..."

Ya ce "Shalele daman ai a tare muke..."

Girgiza kai tayi tare da faÉ—in "ba irin wannan tarayyar ba, ina nufin tarayyar zaman Aure..."

Murmushi ya yi sannan ya ce "Reemah kenam, kamar yanda nace bazan ƙara yin Aure ba har ƙarshen rayuwata to na faɗa ne da zuciya ɗaya, har cikin raina bana buƙatar zama da wata mace a mazannin matar Aure ...."

Ƴar Amana hawaye ne ya fara gangaro mata ta ce "Yaya Roshan ina tunanin lokacin da ka ƙini saboda ganin idon Ramlat ne ashe duk ba haka bane tinda ga shi yanzu bata duniyar gaba ɗaya amma still ka furta baka sona, meye a jikina wanda ban cancanci a soni ba, Yaya Roshan mena maka ne? shin da me duk matan da kaso suka fini? basu fini komai ba but meye matsalar?..."

Roshan ya ce "Reemah kina ji ba, tashi ki tafi bana son maganar Aure yanzu..."

Ƴar Amana tana kuka ta rirriƙo hannayen sa tana faɗin "Yaya Roshan dan Allah, wallahi ina sonka sosai, dan Allah ka cika wa zuciyata burin ta, shin meyasa bata dacen samun abinda take so, taso Yaya Razhdeen bata dace ba, sannan kuma yanzu tana shirin fashewa saboda tsananin ƙaunarka amma kana shirin hanata abinda take so..."
Chapter 49 · 0% Book details