← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 68

Sashe 52

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan kwana biyu Roshan yana kwance akan katafaren gadonsa dake yanzu ya dawo ainihin É—akinsa dake part É—in Abbah, yana shan baccin safen sa dake yau ranar weekend ne,
a cikin bacci ya fara jin sautin jita, ɗan buɗe idonsa yayi yana jiyo sautin miƙewa yayi zaune yana bin bakin ƙofa da kallo daga bisani ya sauƙar da ƙafafunsa ƙasin carpet ya miƙe tsaye ya nufi hanyar waje, hannu yasa ya buɗe ƙofar ɗakin wani irin sanyi ne ya fara hura shi da ƙarfin gaske, haka ya fice a ɗakin yana fita yaga ya bayyana a cikin wani hayaƙi kamar wanda yake cikin gajimare, babu kowa babu komai sai gajimare ga yanda ake hura iska kamar zai ɗaga shi sama,
wani irin haɗiyar yawu Roshan yayi cike da tsoro da fargaba yake bin wurin da kallo yanda kasan barza'u, yana juya bayansa yaga ɗakinsa ya ɓace babu komai sai hayaƙi, kallon ƙasa yayi yaga akan gajimare yake tsaye, a wannan lokacin hankalin sa ba ƙaramin tashi yayi ba, haka jikinsa yake ɓari ga sanyi ga tsoro, lokaci guda yaji an dakatar da kaɗa jitar sai wurin yayi tsit,
ta bayansa ya ji an furta "Yaya Roshan..."

Da sauri ya waiwaya ganin Ƴar Amana riƙe da jita yasa shi ja da baya yana zazzaro ido,
Ta kuma cewa "Yaya Roshan ga Shalelen ka shin baza kayi farin ciki ba ne?..."

Roshan binta yake da idanuwansa waÉ—anda suka shashshanye kamar mai jin bacci haka lips É—insa yake kakkarwa a hankali ya furta "Shalele..."

Ƴar Amana tana sanye da farar doguwar riga har ƙasi babu takalmi tana riƙe da jitar ta, wanda itama akan gajimaren take.

Roshan ne ya matso dab da ita ga hawaye yanda yake gangaro masa haka yayi saurin rungumota jikinsa yana kuka yana faɗin "Shalele meyasa zaki tafi ki barni cikin ƙunci? so kike zuciyata ta buga? so kike kema na rasa ki? idan har na rasa ki na tabbata rayuwata bata da wani amfani mutuwa nima zanyi...."
Sai da ya gama rungumar ta bayan ya gama sambatu yana hawaye ya ɗago da kansa ya riƙo gefe da gefen fuskarta da hannayensa biyu ya ɗora goshinsa akan nata kamar zasu haɗe baki ya ce "Shalele meyasa zaki tafi ki bar masoyin mijinki? kinsan irin damuwar da nake ciki kuwa? Shalele nayi miki alƙawarin zan Aure ki, zamu yi Aure Shalele..."

Itama Ƴar Amana kuka take ta ce "Yaya Roshan ni ɗin taka ce, sannan kaima nawa ne, ina matuƙar ƙaunar ka, sannan ina so mu kasance a tare har ƙarshen rayuwar mu..."

Roshan ya ce "to kin san da hakan meyasa zaki tafi ki bar Ni?..."

Ƴar Amana ta ce "Yaya Roshan ka kasa sanar cewa kana Sona zaka Aure ni, bazan iya kasance ni ɗaya ba tare da kai ba Yayana, kayi zurfin ciki ka kasa sanar wa, bazan iya ganin wannan takaicin ba hakan yasa na ƙaurace wa kowa..."

Roshan ya ce "Shalele yanzu ne dai-dai lokacin da kowa zai fahimci yanda nake ƙaunar ki, yanzu ne dai-dai lokacin da zan mallake ki a mazannin matata ta Aure, yanzu ne zan yi Auren da zan kasance cikin farin ciki na har abada, Shalele you are my life..."

Itama Ƴar Amana kuka take sosai goshinsu a haɗe ta ce "You are my life Yayanaaa..."

Wani irin haske ne ya fara bayyana a jikin Ƴar Amana, lokacin ganin juna ya ƙare daman an bata lokaci ne wanda zata kasance da Roshan,
A ruÉ—e ta É—ago da kanta tana kallon Roshan gaba É—aya idanuwansu sun yi jawur tsabar kuka, a rikice take faÉ—in "Yayana lokacin tafiya ta yayi, Yaya Roshan zan tafi..."

Roshan riƙe ta yayi sosai yana faɗin "Babu yanda zaki je Shalele, bazan ƙara yin nesa da ke ba, bazan barki ki tafi ba..."

Ƴar Amana sama ta fara yi haske yana shirin rufe ta gaba ɗaya tana kuka tana faɗin "Yaya Roshan! Yaya Roshan zan dawo gare ka..."

Haka shima Roshan ya riƙe hannunta yana jawo ta a yayin da haske yake ɗauke ta sama har ta zama haske gaba ɗaya lokaci guda ta ɓace...

Wani irin ihu Roshan yayi tare da ambatar sunan ta "Reeeeemmaaaahhh...."

Dai-dai lokacin da ya farka daga bacci a ruɗe ya tashi zaune yana fitar da numfashi da ƙarfi-ƙarfi, gaba ɗaya ya haɗa gumi haka zuciyar sa take bugawa fatt! fattt! fattt!!!.
A hankali ya ke furta "Shalele! Shalele meyasa kike tafiya ki barni, yanzun ma kin tafi ko? my Shalele I want you inside me...."
Daƙer ya dawo hayyacinsa haka yasa hannu ya dafe goshin sa domin kansa ba ƙaramin ciwo yake ba,

Ga fuskar sa yanda aka tsara masa kwalliya kamar irin matan ƙauyen nan
fuskar nan tayi fari tsabar yawan pawder dake farar powder ce sannan aka ɗauki red jan baki aka guggurza masa akan lip sai bakin yayi jawur, aka ɗauki baƙin kwalli aka zana masa gira, aka goga masa aishado mai colour red a saman idanuwansa, gaba ɗaya an cakurkuɗa masa fuska da makeUp
Dai-dai lokacin aka fara knocking, murya ciki-ciki ya amsa da "Yes..."
turo ƙofar aka yi sai ga Ummy (uwar masu gida) ta shigo da tumbin cikin ta wanda ya girma, ƙarasa shiga tayi ta tsaya tare da faɗin "good morning Masoyi..."

Roshan tashi yayi ya zauna fuska É—auke da murmushi ya amsa mata da cewa "morning to you Maman baby..."

Ummy sake baki tayi tana kallon Roshan wanda yanzu tayi ido huÉ—u da shi, ai bata san lokacin da ta tintsire da dariya ba, dariya take kamar zata shiÉ—e har da kama ciki idonta akan Roshan...

Roshan cike da mamaki ya tsaya kallon ta gaba ɗaya ya rasa akan me take wannan uban dariyan, ganin dariyar ya ƙi ƙarewa ne yasa shi faɗin "wait! wai akan me kike dariya? sannan me yake tafe da ke?.."

Ummy daƙer ta dakatar da dariyar ta ta ce "Yaya Roshan, Yaya Roshan...." nan ma ta ƙara tintsire wa da dariya, daƙer ta samu damar cewa "Yaya Roshan wai kaje ayi breakfast yanzu..." ta ƙara tintsire wa da dariya,
Shi dai girgiza kai yayi ya tashi ya bi ta gefenta ya ce "mahaukaciya..." ya fice a É—akin,
ita kuwa sai da ta ƙare yin dariyar ta mai isar wa kafin ta fice itama tana mamakin ganin kwalliya a fuskar Roshan, sai yanzu kuma abun yake ɗaure mata kai, da wannan tunanin ta sauƙa falo...

Roshan kuwa yana sauƙa falo ya tarar da Razhdeen yana ɗauke da Biju Mama akan cinyarsa sai kuma Baiwar ALLAH a gefensa suna shan soyayya kamar yanda suka saba kullum domin yanzu basa ɗau tsawon mintuna basu haɗu ba, bacci ne yake raba su, baccin ma sai kowa yayi bacci kafin su ma su kama makoncinsu amma ba'a son ransu ba domin in da son samu ne a ce makoncinsu ɗaya.

Roshan tsaya kallon su yayi ta bayan kujerar da suke ya jinjina kai tare da faÉ—in "sannun ku masoya ku koda yaushe bakwa É—an rabewa ne?..."

Duk juyowa suka yi da murmushi akan fuskokin su haɗa ido da Roshan yasa ƙirjin Baiwar ALLAH bugawa domin ba ƙaramin tsorita tayi ba tayi zaton Aljan ne ya fito musu ganin wani irin kwalliya na ƴan ƙauye a fuskarsa, jan bakin duk ya zazzaɓo ƙasin lips ga yasha jan aishado da girar sa har da su barbaɗa kumatu 🤣.
Baiwar Allah ruƙo hannun Razhdeen tayi ta ƙanƙame ido a zazzare tana kallon Roshan, wanda shima Razhdeen idonsa akan Roshan ya ce "my twins meye haka kuma?..."

Baiwar Allah da ta fahimci Roshan ne bata san lokacin da dariya ya ƙwato mata ba, haka take dariya kamar ranta zai fita tana nuna Roshan da yatsa tare da faɗin "wai daman Yaya Roshan?..."

A wannan lokacin Roshan ba ƙaramin ƙuluwa yayi ba rai a haɗe yake bin Baiwar ALLAH da kallo ganin dariyar da take masa ga ya baro Ummy itama,
Razhdeen kasa cewa komai yayi sai ido da yake bin Roshan da shi..

Ƴar tinny ce itama ta tsaya a gaban Roshan ta zuba masa ido ta ce "Yaya Roshan ka koma mace ne?..."

Wani irin kallo ya watsa mata, Ƴar tinny kuwa dariya ta tintsire da shi tare da barin wurin da gudu...
Sai ga Minal itama ta fito tana riƙe da hannun yaronta ganin Roshan yasa ta ƙamewa a wurin, buɗe baki tayi ta ce "woooowww yau ɗin comedy za'ayi mana a gidan ne, kaii wayyo nayi niyyar fita unguwa yau amma na fasa saboda kar ayi banda ni...."
Itama ta kwashe da dariya, sai ga Pinky da Rukky su ma sun fito yin breakfast, suna ganin halin da Roshan ya kasance suma ba magana sai dariya, gaba É—aya falon ya kaure da dariyar su,
Baiwar Allah da Ummy da kuma Minal da Pinky da Rukky har da Ƴar tinny wacce ta dawo daga yin gulma taje ta sanar wa Mommynta cewa Yaya Roshan ya zama Dodo duk dariya suke masa ba ƙaƙƙautawa, sai Razhdeen shima wanda yake zaune yana ƙunshe da dariyar sa wanda bai bari ya fito fili ba,
Ammy wacce ta fito daga kitchen tana jera kayan breakfast a dinning table jin dariya yayi yawa a falo yasa itama ta fito tana faÉ—in "wai me yake faruwa ne?.."
haÉ—a ido tayi da Roshan cike da mamaki ta ce "wannan É—in waye?..."

Roshan abun mamaki ya bashi jin itama Ammy abinda ta furta..

Hajiya Kilishi sauƙowa tayi daga upstairs tana son ganin meke faruwa ne domin Ƴar tinny ta sanar mata cewa Roshan ya zama Dodo,
tana sauƙowa ganin Roshan yasa ta zaro ido cikin rashin sanin abun cewa yasa ta faɗin "AAAA'UZUBILLAHI MINASHAIƊANIN RAJIIIINN,
INNA ASHANA MINAL BALBALINA...."
Da iya ƙarfinta ta furta hakan cikin tsoro,
Jin abinda Hajiya Kilishi ta furta ne yasa itama aka fara kwashe mata da dariya, hatta Ammy sai da ta É—an dara.

Roshan ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba domin ya dudduba jikinsa bai ga abun dariya ba, amma haka ake ta masa dariya, cikin fushi da ɗaga murya ya darara tsawa tare da faɗin "Ya Isa haka! wani irin rainin hankali da wayo ne wannan, kun sakani a gaba kuna mun dariya shin na haukace ne? Ni mahaukaci ne ko kun ganni ina tsine-tsine a bola ne?..."
Chapter 52 · 0% Book details