Sashe 13
My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abbah ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "Daughter an samu iyayen ki, Roshan shine ya bayyana ki a yanzu don haka ki kwantar da hankalin ki...."
Baiwar ALLAH kamar a mafarki take jin wannan batun, gaba ɗaya kanta ya kulle, nan ta fara kuka, ta rasa gane shin kukan farin ciki take ne ko kuma na baƙi ciki tunda duk tana cikin yanayin su, ga baƙin cikin halin da ta tsinci kanta sai kuma halin farin ciki da ta tsinci kanta a yanzu,
leɓɓenta ne yake motsi tare da kakkarwa tana son yin magana amma ta kasa, kallon Roshan tayi tana kuka, shima ita yake gani sai kuma ta bashi tausayi,
Daƙer ta iya buɗan baki ta ce "Iyaye na? suna nan da ransu daman? daman basu mutu ba?...."
Lokaci guda ta ƙara fashewa da matsanancin kuka...
Abbah rarrashinta yake tare da faɗin "kiyi haƙuri Daughter Insha Allahu zan sanar wa iyayen ki cewa kina hannuna, tinda a baya muna da kyakkyawan alaƙa..."
Baiwar ALLAH girgiza kai ta soma yi tana kuka ta ce "dan ALLAH Abbah inaso ku mun wata alfarma dan Allah, ban taɓa neman alfarma a wurinka ba sai yau..."
Abbah ya ce "ina jinki Daughter ko meye kike so zaki samu Insha Allahu..."
Baiwar ALLAH ta ce "kayi alƙawarin haka Abbah?..."
Abbah ya ce "nayi miki alƙawari..."
Baiwar ALLAH ƙara fashewa da kuka tayi tana faɗin "bana so a sanar wa iyaye na cewa an same ni, inason ganin su amma banaso su san cewa ni ɗiyarsu ce..."
Abbah ya ce "miye dalilin yin haka Daughter?..."
Ta ce "a halin yanzu idan suka ganni maimakon suyi farin ciki sai dai su ji ƙunci sakamakon halin da na shiga, idan suka ji na aikata zina shin da wani ido zan kalle su, bana so ranar farko dana ga iyayena su fara jin takaici na,
Dan ALLAH Abbah kada ku sanar musu..."
Abbah ya ce "Nima kaina ina so ko zaku gana da juna ya zamana su ganki cikin ƙoshin lafiya, amma a halin yanzu banaso iyayenki su ganki a haka kina kukan jini, sannan kina cikin damuwa sosai, yanzu inaso ki kwantar da hankalinki ki daina shiga damuwa, idan hankalinki ya kwanta kika samu nutsuwa zan gayyato iyayenki da su zo ku gana da juna, ni kuwa nayi miki alƙawarin babu wanda zai sanar musu cewa kin aikata wani abun ɓatanci in ma da gaske ne domin sai nayi bincike tukun...."
Mai martaba murmushin farin ciki yayi sakamakon yanzu Abbah ya fara sauƙo wa...
Ummy ce ta tashi tare da barin falon ta haura saman room ɗinta, ba jumawa ta sauƙo hannunta riƙe da M.P da memory a ciki, tana zuwa ta miƙa wa Abbah...
Abbah ya kalle ta sannan ya ce "wannan fa?..."
Ummy ta ce "Uncle Deen ne ya bani ya ce idan ka dawo na baka, amma ni kaina ban san meye ba..."
Abbah karɓa yayi tare da kunna wa daman iya recording ne a ciki na maganganun mahaifin su Baiwar ALLAH, kowa nutsuwa yayi ana sauraron recording ɗin....
Sai da suka saurara gaba ɗaya, Abbah ba ƙaramin regretting yayi ba, duk jiki sa yabi yayi sanyi kamar ba rai a jikinsa, ga idanuwansa yanda suka yi jawur, domin a labarin gaba ɗaya duk babu laifin Chief Suraj Mahendra,
Abbah abinda yake furtawa shine "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, ya ALLAH, rashin sani yafi dare duhu...."
Mai martaba ya ce "daman ai zaman gava bashi da daɗi musamman a wurin ka da kake ɗan musulmi jikan musulmai bai kamata ba, gashi dai shi Christal ne amma bai ɗauki rayuwa da zafi ba domin wata rana in mu ne wata rana bamu bane, mu rinƙa tuna kwanciyar kabari, shi rayuwan nan ba komai bane illa ruɗanin dake cikinta, a gaskiya shawarar da zan baka yanzu shine kaje ka samu Chief Suraj ka nemi gafarsa, domin yayi maka halacci a duniyan nan wanda da wuya ka samu masu irin halinsa na kirki, gashi dai duk ƙiyayyar da kake nuna masa bai hana Allah Ubangiji ya ɗora maka ƙaddarar zama da jinsin su ba, ɗiyarka ta bi ɗansu wannan ma jarabawa ce, sannan jininka ya haɗu dana ɗiyarsu har alaƙar Auratayya ta shiga tsakani nan ma jarabawa ne Allah ya ɗora maka, yanda ta faru tsakanin Fir'auna da Annabi Musa kenam, ya ɗora ƙiyayyarsa akan yara maza yasa duk macen da ta haifi namiji a kashe jaririn amma da aka haifi Annabi musa sai Allah ya ɗora masa son Annabi Musa a ransa yana jaririn, to kuwa kaga babu wanda yafi ƙarfin Allah ya jarrabe shi da jarabawar rayuwa...."
Abbah ya jinjina kai sannan ya ce "Insha Allahu gobe zan je har ƙasar U.S na je na same shi na bashi haƙuri a bisa hukuncin da na ɗau a rashin sani, Ni ina ƙin nashi amma shi yana jan nawa a jikinsa Allah sarki...."
Aunty Yolash ce ta yi magana itama tana faÉ—in "Yaya to akan maganar auratayyar tasun kuma fa? shi Roshan yace bazai iya zama da ita ba, kenam haka za'a barta cikin damuwa?..."
Abbah ya ce "taya zan barta cikin damuwa?..."
Ya kalli Roshan sannan ya ce "Kai kace ka rabu da ita ko?...."
Roshan kawar da kansa gefe yayi yana hasasho yanda ya tarar da su kwance akan gado zigidir babu kaya a jikinsu, da sauri ya fara girgiza kai tare da faÉ—in "Ehh...."
Abbah ya ce "to shikenam..."
Ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "to kinji Daughter amma shin kina son Razhdeen?...."
Dasauri Baiwar ALLAH ta ɗago tana kallon Abbah tare da girgiza kai tana hawaye ta ce "ko da maza sun ƙare a doron ƙasa bazan taɓa Auren Razhdeen ba, domin shi ya jefani a cikin wannan matsalar, bana son sa wallahi...."
nan ta ƙara fashewa da kuka,
Abbah ya ce "it's okay, insha Allahu baza ayi miki dole akan abinda bakyaso ba shiyasa na tambaye ki, amma tinda bakya so shikenam, amma yanzu meye a ranki?..."
Baiwar ALLAH tana sharar hawaye ta ce "shawara É—aya na yanke shine zan rabu da kowa a cikin su, kawai inason barin gidan nan..."
Abbah ya ce "ina zaki je Daughter bayan kin ce bakya son haÉ—uwa da iyayenki yanzu?..."
Baiwar ALLAH shiru tayi ta cigaba da kukan ta na jini...
Abbah cewa yayi "shikenam zan duba lamarin kar ki damu, yanzu dai akai Amarya É—akin mijinta sannan kowa ya je ya nemi wurin makwancinsa dare yayi...."
Sannan Abbah ya kalli Baiwar Allah ya ce "uwar masu gida kizo ki kai Daughter É—akinta anan part É—in...."
Ummy bata yi ƙasa a gwiwa ba ta tashi ta nufi Baiwar Allah sannan ta ce "tashi muje..."
Baiwar ALLAH tashi tayi suka shiga room É—in da take kafin tayi Aure, Ummy tana shigar da ita ta juyo ba tare da ta furta komai ba, domin a halin yanzu bata son yi mata magana....
Baiwar ALLAH saman gado ta haura ta fara sharara kuka ba ƙaƙƙautawa gaba ɗaya yanzu bata ma ɗaukin ganin iyayenta saboda matsalar da ta shiga....
Su Hajiya Kilishi da Aunty Yolash da Maamie da Aunty A'isha da su Pinky duk raka Amarya su kayi part É—in Roshan...
Shima Roshan É—in nufan part É—insa yayi shima,
Abbah da mai martaba su kuma fita sukayi suka nufi hospital ganin Razhdeen....
A wannan daren Baiwar ALLAH kwana tayi bata rintsa ba, daman yau waran kwana uku zuwa huÉ—u kenan bata samun yin bacci ba...
Misalin ƙarfe 12 na dare Amarya tana zaune akan gado dake room ɗin Roshan, shi kuwa yana falo a zaune kan kujera, damuwa ce ƙarara akan fuskarsa rabuwa da yayi da Ammata tamkar ya rasa wani ɓangare ne na jikinsa domin ba ƙaramin sonta yake ba, amma zuciyarsa tana bashi cewa dole zai rabu da ita saboda budurcinta ɗan uwansa ya riga shi karɓansa a mazannin ta na matarsa, bazai iya zama da ita domin zaman ƙunci zasu shiga daga ita har shi ɗin, gwara kawai ya sallamar da ita ba dan zuciyarsa na so ba...
Haka shi kaɗai yake ta tunanin Baiwar Allah da kuma baƙin cikin da yake fama da shi a cikin zuciyarsa, shi kan sa Razhdeen ba ƙaramin tsanar sa Roshan yayi ba, baya ƙaunar ya sake buɗe ido ya gà nshi...
yana cikin wannan tunanin ya tuno ashe dai an kawo masa mata, ya barta ita kaÉ—ai acan..
Tashi yayi yana jan ƙafa ya nufi room ɗinsa, da sallama a bakinsa ya shiga, amsa masa tayi cikin so da ƙauna, ba ƙaramin farin ciki ta shiga ba jin shugowar sa domin har ta saddaƙar cewa bazai shigo ba...
Zama yayi a bakin gado yana kallon gefe guda sai yake tariyo Baiwar ALLAH lokacin da take Amarya itama kamar haka aka kawo ta fuska a rufe, lokaci guda ya ƙanƙame idonsa zuciyarsa na tafarfasa....
A hankali ya kalli yanda Ramlat take sannan ya ce "ki tashi kije kiyo alwala..."
jiki a sanyaye ta tashi ta nufi bathroom ta É—auro alwala sannan ta fito, tana fitowa ya ce mata "jira Ni..."
Shima ya shiga ba jumawa ya fito tareda alwalarsa yazo ya samu ta shimfiÉ—a musu sallaya, tsaida sallah suka yi sukayi raka'a biyu sannan ya tottofa mata Addu'o'i tare da tambayar akan abinda ta sani game da addinin ta cikin sa'a duk ta bashi amsa, yayi farin ciki sosai ganin cewa ba jahila ya Auro ba, haka ya tashi yaje ya É—auko ledar gashashshen naman kaza da lemuka kala-kala sannan ya zo ya baje musu shi, cikin jin kunya Ramlat take É—an tura a bakin ta dan ma yana lallaminta akan ta ci...
Bayan sun kammala duk brush suka yo sannan yaje ya É—auko mata kayan bacci a cikin akwatunan Auran ta har sai da ya tallafa mata wurin cire kayan amarcin ta sannan ya sanya mata sleeping dressing duk da a cikin damuwa yake amma hakan bai hana shi bata kulawa ba, shima kayan bacci ya zura sannan ya jata suka nufi gado,
(Ganin an kashe hasken ɗakin ne yasa nabar musu ɗakin, amma naji alamun motsi-motsi a cikin mayafin fa 😂).
★★★★★★★