← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 68

Sashe 50

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Roshan cikin ɓacin rai ya ce "Reemah tashi ki tafi..."

Ƴar Amana buɗan baki tayi zata yi magana ya yi saurin miƙewa tsaye ya bar falon gaba ɗaya, ficewa ya yi ya nufi motar sa ya shiga already security ya buɗe masa get ya fice a ɗari...

Ƴar Amana fashe wa tayi da kuka, ta juma sosai a zaune bata motsa ba tana kan yin kukan ta taji kamar ana ƙiran sunan ta,
"Reemah! Reemah!! Reemah!!!..."

Ƴar Amana ɗagowa tayi tana kallon sama, cike da mamaki take waige-waige cikin kuka ta ce "meyasa ake ƙiran sunana, waye ne?..."

wani haske taga ya bayyano a cikin hasken taji an fara kaÉ—a jita mai daÉ—in sauraro..

Ƴar Amana tsaya kallon wannan hasken take ga jitar da ake kaɗawa cikin lokaci ƙanƙani taga wata mata ta bayyano a cikin hasken tana riƙe da jita tana kaɗawa fuska ɗauke da murmushi...

itama Ƴar Amana murmushin take ganin yanda matar take kaɗa jitar bata san lokacin da duk wata damuwa ya yaye mata ba, duk da bata san matar ba amma ganinta yasa hankalin ta kwanciya..

Matar zama tayi a yanda Ƴar Amana take zaune dai-dai lokacin da ta dakatar da kaɗa jitar,
ta ce "Reemah kin san bama son ganin ki cikin damuwa, saboda ki faɗa mana me kike buƙata idan aiwatar wa ne zamu aiwatar miki idan kuma shawari ne nan ma zamu baki..."

Reemah karkatar da kai tayi cikin nuna damuwa ta ce "a yanzu damuwa ta shine yanda zan yi Yaya Roshan ya karɓi soyayya ta, ina sonsa sosai..."

Murmushi matar tayi sannan ta ce "Reemah kina son sanin wani abu? inda son samu ne bazamu barki kiyi Aure ba saboda wasu dalilai, kin buƙaci yin Aure kuma zamu bar ki kiyi amma baza mu bar ki kiyi abu ɗaya ba..."

Ƴar Amana cikin tsoro da fargaba ta ce "meyasa to, dan Allah ku bar ni nayi Aure nima na kasance da mijina..."

Matar ta ce "zamu bar ki kiyi amma da sharaÉ—i..."

Ƴar Amana ta ce "meye sharaɗin?..."

"Baza ki taɓa haihuwa ba..."
A cewar matar idonta akan Reemah...

Ƴar Amana ta ce "na yadda da hakan amma nima ina so ku taya ki shawo kan Yaya Roshan domin ina matuƙar ƙaunar shi..."

Matar tayi murmushi ta ce "kar ki damu indai wannan ne amma sai mun ɓullo ta wani siga, sai kin ɓace wa ganin kowa..."

Ƴar Amana ta ce "bangane mai kike nufi ba, taya kenam?..."

Matar ta ce "zamu ɗauke ki zuwa duniyar mu, amma ba wai kin tafi na har abada ba, zamu dawo da ke da zaran Roshan ya kamu da soyayyar ki cikin ƙanƙanin lokaci, zaki na ganin kowa naki amma su ba halin su ganki, zasu nemeki ki rasa mu kuma bayyano wa Roshan da siffar ki ta cikin mafarki har ma a zahiri, zakina masa gizo har sai ya kamu da soyayyar ki sosai duk da mun san yana ji da ke..."

Ƴar Amana cike da mamaki take bin matar da kallo a fili ta furta "Aljana za'a mayar ni?..."

Matar ta ce "ko ba'a mayar ki aljana ba zaki fito kamar siffar aljanun domin babu wanda zai gan ki, idan kin yadda da haka to nan ne zaki magance matsalar ki..."

Ƴar Amana ta ce "ban ƙi wannan ba amma damuwa ta shine bana so nayi nesa da Afaf..."

Matar ta ce "baza kiyi nisa da ita ba, zaki na ganin ta a duk lokacin da kika so, amma ita bazata ganki ba..."

Suna cikin tattaunawarsu suka fara jin motsin shugowar mutum domin yanzu dare yayi, lokacin kwanciyar Roshan yayi, shugowar sa kenam ya tarar falon wayam babu kowa, girgiza kai yayi domin a tunanin sa zai tarar da Reemah ne..."

Ita kuwa Ƴar Amana miƙewa tsaye tayi tana faɗin "Yaya Roshan! Yaya Roshan Dan ALLAH inaso kayi tunani a kaina wallahi bazan wahalar da kai ba..."

Matar kuwa tana zaune sai sakin murmushi take,
Haka Roshan ya wuce bedroom É—insa bai ma san Reemah tana yi ba,

Ƴar Amana da sauri ta juyo tana kallon matar,
Matar ta ce "har mun aiwatar da aikin mu, yanzu wasan zai fara, duk waÉ—annan maganganun nakin Roshan bai san kina yi ba, ko ganin ki bazai iya yi ba balle ya ji mai kike faÉ—a,
Ga wannan jitar yanzu shi kaɗai zai rinƙa jin kaɗa jitar ki, ki rinƙa fito masa a mafarki...."

Ƴar Amana cike da mamaki ta ce "tayaya kenam?..."

Murmushi matar tayi sannan ta ce "na barki lafiya..."
daga nan ta ɓace ɓat...

Ita kuwa Ƴar Amana room ɗin Roshan ta nufa da gudu tana zuwa ta samu har ya kulle ƙofar ɗakin, tsayawa tayi tana kallon ƙofar cikin jin takaici tana tunanin ko ta ƙonƙosa masa ne, hannu takai zata kifar da kanta a jikin ƙofa kwatsam tayi ciki zata faɗi sai da tasau wani ƙara, ta ɗago tana kallon ƙofar da ta ratso ba tare da an buɗe ba, kallon Roshan tayi wanda yake kan sallaya ya idar da sallar lafula zai kwanta, cike da mamaki ta koma waje ta hanyar ratsa jikin ƙofar sannan ta ƙara shugowa tana dudduba jikinta, tunani tayi da cewa "kenam zan iya ratsa jikin gini ma?..."
kamar da wasa a hankali tazo wuce wa jikin bango taga ta ratsa sai ta bayyana ta waje still ta ƙara shugowa tana haka har ta yadda da cewa yanzu ta koma aljana,
a bakin gado ta zauna idonta akan Roshan wanda ya sanya sleeping dress ya kwanta bayan yayi addu'a,
Ita kuwa magana take masa amma sam baya jin ta bai ma san tana É—akin ba,
Bayan bacci ya É—an fara É—aukar sa can yaji wayar sa tana ringing, cikin gaga'ar bacci ya rarumo wayar tare da karawa a kulle,
Ƴar Amana kuwa har wannan lokacin tana zaune a bakin gadon sa,
Roshan jin muryar Abbah yasa ya buÉ—e ido tare da tashi zaune a zabure jin an faÉ—i mata magana kamar a mafarki,

A É—an ruÉ—e Roshan ya ce "Dad you said what?..."

Daga ɓangaren Abbah kuwa cewa yayi "ka fito yanzu mun nemi Reemah mun rasa, kuma duk yanda ya kamata a duba a cikin gidan nan an dudduba bata nan..."

Ƴar Amana duk taji abinda Abbah ya ce girgiza kai kawai tayi tare da sakin murmushi, bata ankara ba taji Roshan yana faɗin "whatttt? Shalele bata gida? ina zata fita taje kuma alhalin security suna nan..."
ɗaga kansa yayi yana duba agogon bango yaga misalin ƙarfe 11 na dare,
a rikice yake furta innalillahi wa inna'ilaihi raju'un ba shiri ya tashi a ruÉ—e ya fice daga É—akin kai tsaye falo ya nufa zai fita waje,
ita Reemah haka take binsa a baya, shiga mota yayi itama ta shige a gurguje yabar part É—insa...

A falo kowa ya fita ana tsattsaye ana jimamin rashin ganin Reemah, mai martaba ne kawai baya nan ya koma ƙasar jidder shi da Aunty Maimuna, sai Aunty A'isha da Ummy aka bari su sai bayan bikin Uncle Deen,
Aunty A'isha ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, itama Baiwar ALLAH ta fito ita da mahaifiyarta cikin damuwa, duk sauran mutanen gidan fitowa sukayi Minal da Rukky da kuma Pinky wanda sai bayan biki kowacce zata koma ɗakin mijinta,
Hajiya Kilishi da Ammy suma zama ya ƙaurace musu, Abbah kuwa sai kai kawo yake a falon yaƙi tsayuwa wuri ɗaya, shima Razhdeen ya fito wanda Abbah ne ya tashe shi shima,
suna cikin wannan halin sai ga Roshan ya shigo a ruÉ—e yana faÉ—in "ina taje Abbah?..."

Abbah ya ce "duk na tara sojojin gidan nan sun sanar mun cewa babu wacce tayi hanyar get, kuma an duba CCT camera gidan gaba É—aya sai muka ga part É—inka ta nufa kuma ba'a ga dawowar ta ba,
Roshan wai kana nufin kace Reemah bata tare da kai?..."

Cike da mamaki Roshan ya ce "daman Shalele bata bar part É—ina ba? but nasan taje amma na barta a zaune a falo daga baya dana koma na tarar bata nan, a tunani na ta dawo...."

Abbah ya ce "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un me ake nufi kenam?..."

Roshan buga goshinsa yayi da hannu cikin damuwa, ya ce "ya kamata mu duba ko ina na gidan nasan tana cikin gidan nan, tinda sojoji sun sanar cewa babu wanda ya fita..."

Abbah ya ce "gidan nan ko part É—in ka? bata fito daga part É—inka ba don haka duk can zamu je mu dubo ta...."

Pinky ta ce "kar muje ta shiga ruwan swimming pool ta kasa fitowa ta mutu a ciki..."

A zabure Abbah ya juyo tare da danƙwalon Pinky yana faɗin "Allah ya tsine wa bakin ki nan da baya faɗan alkhairi...."

Pinky ƙame bakinta tayi tare da sunkuyar da kanta...

Abbah ya ce "me kuke jira ne kuzo mu tafi..."
Duk suka nufi hanyar waje shima Razhdeen yana jan ƙafa wanda bacci yaci idonsa haka ya bi bayan su...

Ƴar Amana kuwa tana tsaye ba abinda take sai dariya tana faɗin "ashe dai kuna sona, hahaha na hana kowa bacci woo ni shalele, kaima Yaya Roshan dole ka damu da ni tinda ka nuna bazaka Aure ni ba to kuwa yau ba bacci wollah..."
ta gama yin didimar ta a falo daga bisani ta wuce room É—inta da gudu tana faÉ—in "wayyo Afaf É—ina inason ganinki..."

tana shiga room ɗin ta tarar da Biju Mama sai shan baccin ta take ga fida a bakin ta yanda ta riƙe sosai idan ta ɗan motsa sai ta fara zuƙan fitar ta wanda yake cike da madara a ciki....

Ƴar Amana haurawa saman gado tayi cikin farin cikin ganin Afaf, tasa hannu tana shafa sumar kanta tana faɗin "Biju Mama kinyi musu wayo ke kina shan baccin ki, su kuma suna can yawon nema na, Biju Mama ina sonki sosai kuma inason Yaya Roshan idan ba haka nayi ba Yaya Roshan bazai daina nuna cewa baya sona ba...."
Chapter 50 · 0% Book details