← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 68

Sashe 12

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mai martaba ya ce "matar takan zaka na wulaƙantawa haka, ai duk laifin da tayi maka bai kamata kazo mana da ita ta haka ba, wannan rashin ɗa'a ne da tarbiyya...."

Abbah yana kallon Roshan cikin takaici shi ba abun ya rufe shi da duka ba ya ce "kana hauka ne Roshan?..."

Roshan kallon Abbah da mai martaba yayi sannan ya ce "kuyi haƙuri dan ALLAH ku zauna..."

Mai martaba zama yayi haka shima Abbah, ita kuwa Baiwar ALLAH ta kasa É—agowa...

Aunty Yolash cike da mamaki take bin al'amarin da kallo domin itama bata san me yake faruwa ba, amma tasan a yanda taga Baiwar Allah har da kukan jini tasan akwai babban matsala kawai ta ɓoye mata ne,

Ummy itama kawar da kanta gefe tayi cike da takaicin Baiwar Allah, Pinky kuwa ƙunsar dariya take domin abinda take son gani kenam, Rukky kuwa sai yanzu abun yake damunta domin ba ƙaramin tausayi Baiwar Allah ta bata ba ga Uncle Deen a gadon asibiti shima ta silar haka ya samu hatsari...

Roshan ne ya kalli Abbah sannan ya ce "Dad da farko ni nace ina son wannan yarinyar, yanzu kuwa nace bana sonta, sannan kamar yanda aka ɗaura igiyar Aure na da ita yanzu ina so a since wannan igiyar domin daga yau na kawo ƙarshen alaƙata da ita...."

Cike da mamaki Aunty Yolash da Hajiya Kilishi suke kallon lamarin abun ba ƙaramin kulle musu kai yayi ba, Aunty A'isha da Maamie kuwa sun kasa fahimtar komai sai dai ido, gwara ita Maamie ta shiga yanayin farin ciki jin Roshan yana faɗin zai saki Baiwar ALLAH, yanzu Ramlat ita kaɗai zata zauna ba kishiya....

Itama Ramlat abun ya ɗaure mata kai matuƙa ...

Mai martaba ya ce "Roshan zauna..."

Roshan ya zauna rai a ɓace, sannan mai martaba ya kuma cewa "shin meye dalilin ka na aikata haka?..."

Roshan ya ce "kawai bazan iya rayuwa da ita ba ..."

Abbah tsawa ya daka masa tare da faɗin "your very stupid Roshan, meye amfanin mu idan bazaka iya sanar mana damuwar ka ba? shin su waye suka ɗaura maka Aure? mune sannan idan matsala ka samu da matar ka a mu zaka kawo ƙara, mu kuma sai mu dubi abinda ya dace ayi...."

Roshan idonsa ne ya cicciko da ƙwallah idonsa akan Baiwar ALLAH wacce take kife a tsakiyar falo har yanzu ta kasa ɗagowa, girgiza kai yayi sannan ya ce "kawai na gaji da zama da ita ne shiyasa nake buƙatar rabuwa da ita...."

Mai martaba ya ce "Roshan shin sasanci kazo ayi ne ko kuma rabuwar Aure? bai kamata ace kayi saurin yin saki ba, gwara idan laifi tayi a ja mata kunne sosai in yaso kuje ku cigaba da zaman Auren ku..."

Dasauri Roshan ya ce "Rabuwar Aure nake so ayi...."

Abbah ya ce "idan baka sanar mana dalili ba wallahi bazaka sake ta ba ..."

Roshan ya Ciro takardar saki a cikin aljihun jallabiyarsa ya miƙa wa Abbah yana faɗin "Abbah kayi haƙuri ga takardar sakin ta nan...."

Abbah idonsa akan Roshan ya ce "taurin kai zaka mun ko Roshan?..."

Roshan tashi yayi ya miƙe tare da nufan yanda Abbah yake ya miƙa masa takardar yana cewa "Gashi Abbah na sake ta saki uku..."

Tsabar ɓacin rai Abbah ya ɗauke shi da mari har sai da ya faɗi ƙasin carpet ya ɗago yana kame da fuska...

Ramlat hawaye ta fara zubarwa ganin yanda aka mari Roshan tamkar ita aka mara domin taji zafin haka sosai a ranta...

Ummy ganin tana kallo bazata bari a cutar mata da ɗan uwa ba akan gaskiyar sa yasa ta miƙe tsaye tare da ambatar sunan Abbah...

Abbah juyowa yayi yana kallonta ya ce "ke kuma fa, ko rama masa zakiyi?..."

Tana kuka ta ce "Abbah inason yin magana da kai..."

Abbah ya ce "su waye baƙin ki anan? duk iyayenki ne don haka ki faɗi abinda zaki ce ...."

Roshan ɗagowa yayi yana girgiza mata kai alamar kar ta gaya, amma Ummy sam ta nuna bata gànshi ba ma,
Ta ce "Abbah meyasa ita É—in bazaku tambaye ta akan laifin da tayi ba?..."

Abbah ya ce "bana son iskanci ki fa É—i meye zaki ce?..."

Ummy ta ce "dalilin da yasa Yaya Roshan zai rabu da Matar sa shine ya kamata a É—aki ita da Uncle Deen suna aikata alfasha...."

Abbah wani irin dimmmm yaji, kansa ne ya fara juyawa, kamar a mafarki yake jin wannan batun...

Mai martaba shima cikin firgici ya ce "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un..."

Aunty Yolash zaro ido waje tayi tana jinjina batun..
Haka itama Hajiya Kilishi abun yayi matuƙar ɗaure mata kai..
Pinky da Rukky kallon juna suka yi,
Aunty A'isha ba abinda take furta wa a cikin ranta illah "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un..."

Ramlat itama zuciyar ta ne yake bugu domin tayi matuƙar mamakin jin wannan batun, bata yi tunanin Baiwar ALLAH zata iya aikata zina ba kuma da Auren ta...

Roshan dafe goshinsa yayi yana kallon ƙasi domin har cikin ransa bai so Ummy ta faɗi wannan kalmar a cikin mutane ba...

Abbah kamar ba jini a jikinsa ya maida idonsa kan Baiwar Allah har zuwa yanzu bata É—ago ba..
A hankali ya furta sunan Baiwar Allah da cewa "Daughter..."

Baiwar Allah kasa ɗagowa tayi saboda tana fargaban haɗa ido da mutanen falon, Abbah ya sake ƙiran sunan ta yana faɗin "ki ɗago maza ki kalle ni, shin abinda aka fa ɗa gaskiya ne ?..."

shiru Baiwar Allah bata ɗago ba balle ta bada amsa, Abbah ne ya ƙara cewa "ɗago mana Daughter nah..."

Baiwar ALLAH a hankali take motsi tana shirin ɗagowa jiki duk ya mutu, ga wani irin yunwan da ya kama jikinta sosai, da ƙer ta ɗago tana kukan jini, durƙusawa tayi a gaban Abbah tana fuskantar sa fuska a jiƙe da jini..."

Abbah gaban sa ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ganin yanda Baiwar Allah take kukan jini, duk kallonta suke shima Mai martaba ya ce "kukan jini kuma?..."

Aunty Yolash bata san lokacin da kuka ya yanko mata ba domin tana matuƙar jin tausayin Baiwar Allah especially kukan jini da taga tana yi...

Abbah ya sauƙa daga kan kujera ya zauna a ƙasin carpet ya riƙo hannunta tare da furta "Daughter! Daughter!! Daughter kukan jini kuma? kina tare da cuta amma ban sani ba? tayaya hakan zata faru?..."

Baiwar Allah tana kuka ta ce "Abbah na aikata laifi babba, nasan hukuncin aikata zina a matar Aure jifa ne da duwatsu, dan Allah Abbah inason mutuwa, inason barin duniyan nan..."

Abbah shima hawaye ne suka fara gangaro masa tare da girgiza kai yana faɗin "Daughter nasan da hankalin ki bazaki taɓa aikata hakan ba, ni ban yadda da wannan ba dole sai nayi bincike akai, saboda haka ki share hawayen nan sannan zamu je hospital a duba lafiyar ki domin ke amana ce a gare ni, bayan zuwan ki gidan nan naje har gidan marayu na rubuta takarda tareda yin signing cewa na ɗauke ki a mazannin ɗiyata, na gaza samun iyayen ki saboda ke ƴar Amana ta ce, kuma na karanci duk wani ɗabi'un ki da halayenki nasan abunda zakiyi da kuma abinda baza kiyi ba, dole sai nayi bincike akai kafin na yadda....."

Abbah ya kalli Roshan ya ce "Aure da zargi haramun ne don haka bani takardar ta..."

Ummy ta ce "Abbah ba zargi bane da idonsa ya kama su..."

Abbah ya darara mata tsawa da cewa "kiyi mun shuru nace..."

Abbah yana karɓan takardar ya buɗe yana faɗin "ba saki uku ba shikenam..." Abbah ya karanta sakin da yayi mata saki biyu ne...

Ya kalli Roshan ya ce "kace saki uku?..."

Roshan ya ce "saki biyu nayi mata daga baya zan ƙaro ɗayan..."

Abbah har zai rufe takardar ya ga wani rubutu a ƙasin sakin,

An rubuta :
"Ni Roshan matar da nake tare da ita wato Baiwar Allah ɗiyar Chief Of Defence Staff ce (C.D.S) Chief Suraj Mohandra Marka, wato shugaban sojojin ƙasar Austaraliya na yanzu, yarinyar da akayi wa alƙawarinta a Razhdeen tin kafin ta ɓata mai suna Amreesh........

Abbah cike da mamaki ya furta "whattttt!!!!"

Abbah É—agowa yayi yana bin kowa da kallo ya kasa faÉ—in komai...

Aunty Yolash ce ta taso ta karɓi takardar a bayyanai take karantawa yanda kowa zai ji, yanda saƙon yake a rubuce haka ta karanta....

Baiwar ALLAH zaro manya-manyan idanuwanta tayi waje tare da juyowa da sauri tana kallon Aunty Yolash.........

Typing ✍️

*MY ENEMY*

*TAKUN ƘARSHE*

*BOOK 3*

21 to 25

Abbah da sauri ya juya yana kallon Baiwar ALLAH wacce idonta ke kan Aunty Yolash, cike da mamaki da kuma rashin fahimta take binta da kallo tana son sanin abinda take nufi,
Abbah a hankali ya furta "É—iyar Chief Suraj Mahendra marka?..."

Duk kowa a cikin falon shuru yayi kowa yana jinjina batun, da kuma jiran matakin da Abbah zai É—au,

Pinky kam a cikin ranta cewa take "shikenam in ba'a kore ta don fasiƙancin da suka aikata ba, ai za'a kore ta ko dan ƙiyayyar dake tsakanin Abbah da mahaifinta..."

Aunty Yolash haka zuciyarta yake bugu tsoronta kar Abbah ya kore ta,
Mai martaba shima babu abin cewa kowa jiran Abbah yake akan batun,

Abbah kallon mutanen falon yake ɗaya bayan ɗaya yana jinjina kansa, abinda ya fito daga bakinsa shine "Ikon ALLAH kenam! kana naka Allah na nashi, tsawon shekaru ina gava da mahaifinta, na kuma tsani haɗa zuriya da shi, a karo na farko ɗiyata Allah ya ɗora mata son ɗan su, har takai yanzu suna can zaman Aure, a karo na biyu kuma Allah ya ɗora mun son ɗiyar su wanda har na ɗauke ta a mazannin ɗiyata ta ciki na, har takai na Aura wa ɗa na ita a rashin sani, gashi dai kuma bana ƙaunar ahalin, amma sakamakon yanda nake jin Daughter a raina bazan iya tozarta ta ba saboda ita abar tausayi ce, tin tana ƙaramar ta take cikin ƙuncin rashin iyaye, duk gatan da ƴaƴa suke samu daga wurin iyayensu ita sam bata samu wannan gatan ba, ƙiyayyata sai dai na nuna a iya mahaifinta a halin yanzu amma ita na cire ta a layi...."
Chapter 12 · 0% Book details