← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 68

Sashe 5

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Roshan jin irin waɗannan kalaman da rabon da yaji su tin lokacin da yake soyayya da marigayiya budurwarsa Mariam, ƙwaƙwalwarsa ne ya fara juyawa jin sautin irin muryar Mariam kuma irin kalaman da take masa sak irin wanda Ramlat tayi masa....

Ramlat tana tsugune kai a ƙasi ta kasa ɗagowa,
Sauƙe nannauyar numfashi yayi sannan ya ce "Nagode sosai, tashi ki zauna ..."

A hankali ta tashi ta zauna,
Yana kallonta ya ce "Meyasa kike ɓoɓɓoye fuskar, shin meye amfanin kwalliyar? ko dai ba'a ni akayi wa ba?..."

Murmushi tayi ta cikin mayafin sannan tasa hannunta waɗanda suka sha jan lalle da zanen baƙin lalle ta buɗe fuskar...

Yana kallonta bai san lokacin da ya furta "Ma sha ALLAH..."

Bata ƙarasa buɗe fuskar ba ta dakata haka yasa hannu ya yaye mayafin fuskar gaba ɗaya, cike da mamaki ya ce "amma ke ban sanki ba, aka ce Ramlat zan Aura..."

Murmushi tayi sannan ta ce "Ni ce Ramlat É—in ai..."
Ya ce "ban yadda ba, ke kinfi Ramlat kyau sosai.."

Ɗagowa tayi tana kallonsa sannan ta miƙa masa hannu ga yanda tafin hannunta ya sha jan lalle...

Kallon hannun yayi fuska ɗauke da murmushi shima ya ɗora tafin hannunsa akan nata, riƙe hannunsa tayi a cikin nata sannan ta ɗora hannun akanta idonta akan sa shima ɗin ita yake kallo ta ce "wallahi Yaya Roshan Ni ce Ramlat Amaryar ka kuma Uwar ƴaƴanka zuwa nan gaba Insha Allahu..."

Jinjina kai ya yi sannan ya ce "na yadda..." tukun ta sauƙar masa da hannun....

Baiwar Allah kuwa tana zaune akan kujerar falo ta kasa katse ƙira sai kukan da take tayi ita kaɗai domin alamun shima Roshan son yarinyar yake...

Tana cikin wannan yanayin sai ji tayi an buɗe ƙofar falo an shugo, ganin wanda ya shugo ne yasa tayi saurin miƙe wa da sauri tana zazzaro ido, ganin Razhdeen yasa tayi saurin katse wayar,
cikin ƙiƙƙina take ƙoƙarin cewa "me me me ya kawo ka gi gi gidan nan?..."

Matsowa yayi gaban ta sannan ya goya hannayensa akan ƙirji ya zuba mata ido, duk da har yanzu akwai hawaye shaɓe-shaɓa akan fuskar amma bai damu da sanin dalilin kukan ta ba...

Da sauri ta goge hawayen fuskar sai da ta dai daita nutsuwar ta kafin ta buÉ—i baki ta ce "Mijina baya nan..."

Yayi saurin katse ta da cewa "wurin ki nazo..."

Wani irin bugun zuciya taji lokaci guda ta tuno da saƙon da ya aiko mata daga nan ta ƙara ɗaure fuska cikin fushi ta ce "me ke tafe dakai?..."

Ya ce "nazo ne game da sanin yanda rayuwa ta take..."

Cikin zafin rai ya ce "Rayuwarka? to ina ruwana da rayuwar takan, da rayuwar ka da rashin sa duk bai dame ni ba..."
ta juya zata bar wurin yayi saurin riƙo ta ya zaunar da ita akan kujera sannan ya ɗora ƙafar sa a gefen ta ya sa ta a gaba tare da ƙura mata ido fuska ba annuri,

Ya ce "ina Amreesh?..."

Hararar sa tayi sannan ta ce "wata ƙila tana ƙarƙashin gado na..."

Cikin ɓacin rai ya damƙo dantsen ta tare da ɗagota yana faɗin "to muje ki nuna mun ita..." ya fara jan ta suka nufi bedroom,
ƙoƙarin ƙwace wa take tana faɗin "meye haka Razhdeen? Ni ka sake ni shin ka manta cewa ni ɗin matar Aure ce? ka sake ni nace...." ta fizge hannunta tana huci ta cigaba da cewa "kana nufin bedroom ɗina zaka shiga? ɗakin kwanciyar Aure na zaka shiga?..."

Cikin zafin nama ya riƙe hannunta tare da yin wurgi da ita yana faɗin "and so what..."
Kanta ne ya bugu da jikin kujerar ta riƙe kanta tana shirin yin kuka..

Ya ƙarasa yanda take ya ce "ki fa ɗa mun aina Amreesh take? bana son shirme da rainin wayo, a wani wuri take sannan a gurin waye?..."

Baiwar ALLAH cikin É—aga murya ta ce "wai wata Amreesh kake fa É—a ne haka?..."

Ciro sarƙa yayi a cikin aljihunsa ya ɗaga mata shi idonsa akanta ya ce "ina neman mai wannan sarƙar shin tana ina?...."

Baiwar ALLAH zaro ido waje tayi cikin nuna farin ciki takai hannu zata karɓa yayi saurin kawar da sarƙar tare da faɗin "ina tambayar ki tana ina?..."

A ruɗe Baiwar ALLAH ta ce "sarƙa ta ce fa, wallahi sarƙa tace ina nema ban gani ba tin shekaran jiya, ka taimaka ka bani dan ALLAH...."

Razhdeen jinjina kansa yayi jin irin rainin wayon da take shirin masa, ya zaro mata ido sannan ya ce "bana son shirme, nasan wannan sarƙar ba taki ba ce, shin aina kika samu?..."

Baiwar ALLAH fashe wa tayi da kuka ta ce "wallahi sarƙa tacee ...."

Bata ƙarasa maganar ba taji wani irin zazzafar mari akan fuskar ta har sai da taso shiɗe wa,
Ya miƙe kamar zai yi kuka yake faɗin "Meyasa kike son yin wasa da rayuwa ta? kin gama raina mun wayo da kuma hankali, na gaya miki mai wannan sarƙar ita ɗin rayuwa tace kuma farin ciki na, ki gaya mun aina zan same ta, zan iya sadaukar da rayuwa ta domin na ceceta daga halin da take ciki, nasan Amreesh tana nan a raye, amma tinda bazaki iya sanar mun gaskiya ba shikenam zan fita na nemo ta da kaina...."

Ya juya a fusace har ya buɗe ƙofa yaji ta ce "Uncle Deen Ni ce mai wannan sarƙar, idan ka rabani da sarƙar nan tamkar ka rabani da rayuwa tace, wannan sarƙar ina ɗaukar sa a mazannin uwata da kuma ubana, Meyasa zaka mun haka, tinda na tashi ina ƙarama nake ganin wannan sarƙar babu wanda yayi yunƙurin rabani da shi sai kai? me nayi maka haka? na rasa iyaye na tin ina ƴar shekara biyu zuwa uku amma inasa ran zan same su ta sanadiyar wannan sarƙar...."

Nan ta fashe da wani irin matsanancin kuka mai cin rai...

Razhdeen tin da ta fara magana ya tsaya yana sauraronta, zuciyarsa ce ta fara bugawa da ƙarfin gaske jin tana maganar ta rasa iyayenta sannan ta ambaci ta ɓata tin tana shekara biyu zuwa uku kuma lokacin da Amreesh ta ɓata tana ya wannan shekarun,
Numfashinsa ne yake ƙoƙarin ɗage wa, dasauri yake girgiza kai tare da faɗin "I can't believe you...."

Juyawa yayi ya nufi yanda ta miƙe tsaye tana kuka, ganin ya nufo yanda take gadan-gadan ne yasa ta haɗiye kukan ta fara ja da baya gudun kar ya sake dukan ta,
Ji tayi ya riƙo ta tare da jawo ta jikinsa yasa hannunsa ta bayan rigar ta ya zuge zip ɗin rigar,

Baiwar ALLAH ganin haka yasa ta zazzaro ido waje tana tutture shi cikin tsoro da fargaba, amma ta kasa domin yayi mata wani irin riƙo ne wanda bazata iya ƙwace wa ba....

Shi kuwa Razhdeen abinda yake son gani shine wannan tambarin zanen bindigar bayanta, buÉ—e rigar yayi sai breziyyar da yake ciki bai damu da ganin wannan ba domin shi abu É—aya yake son gani,
Abunda ya fara gani shine tambarin zanen, a firgice ya zaro ido waje yana kallon zanen,
Ga yanda ya rungumeta sosai a jikinsa...

Ɗaker ta tattaro ƙarfinta ta ture shi baya tana sauƙe numfashi, tare da masa wani irin kallo na rashin fahimtar abinda yake nufi da ita,
Ƙara fashewa tayi da kuka tana faɗin "nifah matar ɗan uwanka ne, shine kake son cin amanar sa?...."

Razhdeen tsabar hankalinsa ba'a jikinsa yake ba haka ya buÉ—e baki kamar wanda zai yi magana amma ya kasa sai ido da ya zazzaro yana kallonta,
A ruÉ—e yake son faÉ—in "R R Res Reesh?..."

Kar kata kansa yayi yana leƙa wani dabon baƙin tawadar da yake tsakanin wuyanta da kunne domin wannan da shi aka haife ta, yana leƙawa ne domin ya ƙara tabbatar wa da Amreesh ɗin ce,
Ganin wannan ɗin ma hujja ce yasa ya dafe goshin sa sakamakon hajijiyan da yake shirin ɗaukar sa, har idanuwansa sun kaɗa sunyi ja lokaci ƙanƙani,
Haka yake furta sunan "Reesh! Reesh!! Reesh!!!...."

Baiwar ALLAH girgiza kai tayi ganin Razhdeen yana shirin zauce wa yasa ta rufa da gudun gaske ta nufi room ɗinta, tana shiga tasa sakata tana sauƙe numfashi daƙer, ga rigar ta a zuge sai kakkare ƙirjinta take da hannu bibbiyu....

Razhdeen jin hajijiya yana son kayar dashi yasa yayi saurin durƙusawa a ƙasin carpet yana riƙe da kansa, sai ambatar sunan Reesh yake.....

Typing ✍️

*MY ENEMY*

*TAKUN ƘARSHE*

*BOOK 3*

11 to 15

________________★★★★★★

Razhdeen cikin yanayin damuwa da tsananin bugun zuciya haka ya tashi jiki ba ƙwari yake jan ƙafa da ƙer ya fice, tariyo abubuwan da ya gani yake tayi abu kamar a cikin mafarki, kai tsaye part ɗin Abbah ya nufa anan ya tarar da Abbah shima ya shirya zai bar ƙasar domin akwai Meeting ɗin da suke son gudanarwa a cikin satin nan, sai ana washe gari ɗaurin Auren Roshan zai dawo,
Ganin Razhdeen idanu yayi jawur yasa shi faÉ—in "lafiya kuwa Razhdeen meya faru da kai?..."

Razhdeen babu bakin magana haka ya nemi wuri ya zauna yana dafe da goshi cikin ƙarfin hali yake girgiza kai ya ce "kaina ciwo..."

Abbah zuwa gefen sa yayi ya zauna tare da dafe kafaÉ—arsa ya ce "look Razhdeen ban saba ganinka a cikin wannan yanayin ba, dole na damu idan na ganka a cikin matsala, saboda haka ka gaya mun meke faruwa?..."

Razhdeen É—ago kansa yayi yana kallon Abbah lokaci guda ya fara zubar da hawaye yana faÉ—in "Dad my Reesh..."

Abbah haÉ—e gira yayi sannan ya ce "au yau kuma da abinda ka tashi kenam? meyasa bakinka bazai furta sunan wata mace ba sai Reesh? Amreesh ta mutu, inda tana raye to da yanzu ta bayyana sakamakon irin neman da akayi mata har gidan rediyo da television, kaga malam idan zakayi Auren ka kayi amma babu wani labarin Amreesher..."

Girgiza kai Razhdeen yayi idonsa akan Abbah yana fargaban sanar masa cewa Baiwar ALLAH ita ce Amreesh domin a halin yanzu tana Auren É—an uwansa twins, zuciyar sa harbawa kawai take ya ce "Reesh tana raye bata mutu ba..."
Chapter 5 · 0% Book details