Sashe 41
My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ummy ce ta É—auki yarinyar,
Hajiya Kilishi ta ce "ko dai tana cikin toilet ne, mu jira ta fito...."
Kujera aka bawa Mai martaba da Abbah suka zauna, sauran kujerun kuma Aunty A'isha da Aunty Maimuna da Ammy ne suka zaune sai Hajiya Kilishi, Reemah da Ummy kuma a bakin gado suka zauna,
Suna zaune har minti talatin shuru babu labarin Baiwar ALLAH, Mai martaba ya ce "lafiya kuwa har yanzu shuru?..."
Roshan da Yarima ne suka shigo a tare, ganin yanda akayi shiru ne yasa Roshan cewa "lafiya kuwa?..."
Hajiya Kilishi ce ta ƙara cewa "to kun san wankan jego sai a hankali....."
Abbah ne ya katse ta da cewa "ke dallah haba ko wankan mutuwa ne iyaka ci, ki tashi ki shige kije ki dubo mana ita..."
Hajiya Kilishi tashi tayi taje ta buÉ—e toilet ta shige ciki, ba jumawa ta fito tana zazzaro ido,
Abbah ya ce "yadai?..."
Hajiya Kilishi "wallahi bata nan..."
A zabure Abbah ya miƙe yana faɗin "bata nan kuma?..."
Mai martaba ya ce "to ina kuma taje ta bar jaririya?..."
Roshan wani dimm yaji cike da mamaki ya ce "whattt?..."
Kallon jaririyar yayi dake hannun Ummy,
Zaro wayar sa yayi zai ƙira number ta, bugu ɗaya yaji wayar tana ringing a cikin gadon jaririya, nufan wurin yayi yasa hannu a ciki ya ɗauki wayar yana jujjuya wa, idonsa ne ya sauƙa akan wata takarda, cike da mamaki yasa hannu ya ɗauki letter, ganin takarda yasa zuciyar kowa bugawa,..
Aunty Yolash ce ta shigo da sallama a bakinta cikin farin ciki ta shigo tana faÉ—in "a gafarce mu sai yau muka zo ganin Æ´ar jikallen mu..."
Aunty Yolash ganin kowa fuska ba annuri yasa ta tsaya ta ce "lafiya kuwa? ..."
Ummy ce ta ce "Aunty yanzu muka shigo muka tarar da Aunty Daughter bata nan, ga jaririya sai kuka take..."
Aunty Yolash ta ce "subhanallahi to ina taje?..."
Abbah idonsa akan Roshan ya ce "meye a cikin takardar nan?..."
Aunty Yolash ce tasa hannu ta karɓi takardar ta buɗe da sauri, a fili ta fara karantawa kamar haka:
"Assalamu alaikum! Abbah na dan Allah kuyi haƙuri daman na ƙudurta a raina cewa duk lokacin da na haihu zamana a gidan ku ya ƙare sakamakon abinda ya faru a tsakani na da Razhdeen, idan yarinyata ta taso ban san da wani ido zata rinƙa kallo na ba, nasan itama zatana mun kallon mazinaciya kamar yanda kowa yake mun kallon haka, kuma nasan bazan iya juran ganin ana goranta mun yarinya kamar yanda ake goranta mun ba, ga shi na haifa muku dan Allah kuyi haƙuri ku riƙe mun ƴata kamar yanda ku ka riƙe ni da amana, Nagode sosai da irin kulawar da ku ka ban,
Yaya Roshan ina matuƙar ƙaunar ka amma a yanzu dole zan cire sonka a cikin zuciyata domin kai ɗin ba nawa bane, kuma nima ba naka ba ne domin ban cancanci ka zauna dani a matsayin matarka ba, amma ina so ka ɗauki ɗiyata tamkar ɗiyarka, sannan magana ta ƙarshe inason sanar maka cewa ƴar uwata Reemah tana matuƙar ƙaunar ka dan Allah kayi mata halacci, ita ɗin yarinya ce ƙarama bana so ta kamu da ciwon soyayya, kamar yanda kayi niyar zama da mata biyu wato Ni da Ramlat inaso yanzu Reemah ta maye gurbi na dan ALLAH Yaya Roshan,
Sannan idan Razhdeen ya dawo ku sanar masa cewa ga ɗiyarsa nan na haifa masa, sannan na yafe masa amma banaso na ƙara yin ido huɗu da shi, idan kuwa hakan ta faru to bazan yafe masa ba domin zai fame mun ciwon dake cikin zuciyata,
Kada kowa ya neme Ni domin babu wanda zai same ni, hatta iyayena su ma ba zasu san a yanda nake ba,
Alfarma ta ƙarshe da za'a mun shine idan yarinyata ta girma ku sanar mata cewa Mamanta ta mutu,
Kowa da kowa ya gafarce Ni, Bissalam!...."
Cikin tashin hankali Abbah ya doku akan kujera yana firfito da ido waje, tare da faÉ—in "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, me zan ce wa iyayenta? gashi yau suna kan hanyar su ta zuwa...."
Mai martaba ba abinda yake faÉ—i illa "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un...."
A ruɗe Reemah ta miƙe tsaye tana zubda ƙwallah,
Aunty Yolash cikin tashin hankali ta ce "nashiga uku na shigo cikin farin ciki ashe zan tarar da labari marar daÉ—in ji..."
Kowa babu wanda bai ji daÉ—in wannan lamarin ba..
A ruÉ—e Roshan ya yi waje da hanzarin sa.....
Typing âœï¸ Asmeetah writer
*MY ENEMY*
*TAKUN ƘARSHE*
*BOOK 3*
61 to 65
Fitar Roshan motarsa ya shiga ba shiri ya ja motar da gudu wanda shima kansa bai san ina ya nufa ba, baza idanuwa kawai yake ko zai ga Baiwar Allah amma duk layin da ya bi baya dace, ya yi tambayar amma babu wanda ya ce ya ganta har photonta yake nuna wa amma babu labari, Roshan har ana ƙiran sallar mangariba amma bai koma ba, ta ko ina bi yake lungu da sa ƙo amma Baiwar Allah shiru babu labarin ta, bai tashi komawa hospital ba sai ƙarfe 10 na dare...
Abbah gaba ɗaya ba ƙaramin shiga damuwa yayi ba, kowa na waran babu wanda bai jijjiga ba, ga jaririya a hannun Ammy tana bata madara, dake bata wani saba da shan nono ba kullum madara mai kyau ake bata, domin tin da aka haife ta sau ɗaya tasha nonon mahaifiyar ta..
A wannan daren Abbah ya sanar cewa su wuce gida,
Gaba É—ayan su gida suka koma har Ramlat,
a wannan ranar kowa kwanan baƙin ciki ya yi...
★★★★★
Ita kuwa Baiwar ALLAH gidan marayun da suka zauna ta koma, taje a mazannin ta kai musu ziyara ne, cikin sa'a ta samu mutuminyar ta wato Aunty Habiba, akwai da ta sani sosai waɗanda ta barsu har yanzu suna nan da kuma sabbin fuskoki waɗanda suka je daga baya, waɗanda suka san Baiwar ALLAH sunyi matuƙar farin ciki sosai da ganinta,
Akwai wata ƙawarta a ɗakinta ta sauƙa, sun yi mata tarya ta musamman, sannan Baiwar Allah tayi musu dubun alkhairi domin tana da maƙudan kuɗaɗen da bata san yawan su ba a cikin account ɗinta, saboda kuɗin da take da su account ɗinta sunyi biyar kuma ko wanne da lodin kuɗi a ciki, iyayen ta kullum a cikin turo mata kuɗi suke, mahaifinta kullum yana kan turo mata, sannan mahaifiyar ta itama tana kan turo mata ga Yayunta su ma koda yaushe idonsu akanta yake, shima Abbah sai dai taga ya tura mata kuɗi duk da bata rasa komai a gidan ba, ita kuma ba komai take siya ba, ko kaɗan bata iya kashe kuɗi ba, da ta tashi zuwa gidan marayu sai da taje super market tayo siyayyan kayayyaki da takalma kala-kala komai-komai sannan ta loda su a cikin motar haya kai tsaye sai gidan marayu, sannan da ta je ta raba musu kuɗaɗe masu yawan gaske,
Suna zaune a É—aki duk waÉ—anda suka santa suna É—akin duk zagaye ta,
Baiwar Allah ƙaresu da kallo tayi daga bisani ta ce "ya na ganku bakuda yawa ne duk ina sauran ƙawayen namun? sai sabbin fuskoki nake gani..."
wata daga ciki ta ce "wallahi duk basa nan muma Allah ne yasa zaki tarar da mu, wasu sun haÉ—u da iyayensu, wasu kuma masu kuÉ—i ne suka É—auke su a mazannin Æ´an aiki, wasu kuma sun yi Aure, yanzu gamu nan bamu fi mu goma ba..."
Baiwar Allah ta ce "Allah sarki rayuwa kenam, kamar baza'a kawo wannan lokacin ba, kuma Allah ya fidda ku, zan so ku haÉ—u da iyayen ku..."
Wata daga ciki ta ce "yo mu kam ina zamu ga iyayen mu bayan an tabbatar cewa sun rasu, dangin su kuma duk babu masu ƙarfi suka ce kawai na cigaba da zama anan har Allah yasa mijin Aure ya fito mun, kinsan fa wasu mazan har nan ake zuwa neman matan Aure saboda sun fi son su ciyar da marayu..."
Baiwar Allah ta ce "Allah sarki..."
ta kalli Aunty Habiba sannan ta ce "Aunty Habiba meyasa bakiyi Aure ba keÉ—in? kuma sannan duk ina sauran shuwagabannin matan gidan waÉ—anda na sani?...."
Dogon numfashi Aunty Habiba ta ja tana murmushi ta ce "Baiwar ALLAH kenam, kinga sauran ni kaÉ—ai na rage ko? wallahi dalilin da ya hanani tafiya shine saboda waÉ—annan yaran da na saba da su tin shekara da shekaru bazan iya tafiya na barsu ba, iya su goma yanzu suka rage da zaran ko wacce ta samu mafita Nima zan kama gabana..."
Baiwar Allah har da hawayen ta tace "Aunty Habiba Allah ya saka miki da gidan Aljanna, su suma Allah ya kawo musu É—auki ta hanya mafi alkhairi..."
cikin haɗin baki suka ce "ya labarin Ƴar Amana ne?..."
Murmushi Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "Ƴar Amana tana nan cikin ƙashin lafiya itama ta haɗu da iyayenta, ita ɗin Ƴar sarkin ƙasar Jidder ce kuma sannan bakinta ya buɗu yanzu tana magana sosai..."
Gaba É—aya basu san lokacin da suka saki ihun farin ciki ba, murna kamar bazasu mutu ba, Aunty Habiba hamdala ta soma yi tana godewa Allah,
duk babu wanda bai kasance cikin farin ciki ba..
Wata daga ciki ta ce "Amma Baiwar ALLAH meye asalin sunan Ƴar Amana?..."
Baiwar Allah ta ce "Reemah..."
Duk É—insu fatan alkhairi suka yi musu da taya su murna...
Aunty Habiba ta ce "to ke É—in baki sanar mana labarin yanda ta kasance miki ba, Allah yasa kema kin haÉ—u da iyayen nakin..."
Murmushi Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "na haɗu da iyayena amma sai dai su ɗin ba'a nan Nigeria suke ba, suna can ƙasar Australia, Mahaifina shine shugaban sojoji na ƙasar, inada Yayuna guda biyu suma duk sojoji ne, asalin sunana Amreesher..."
Duk haÉ—a baki suka yi suka ce "wonderful, labarin ki kamar a Film, film É—in ma kamar irin indian film, gaskiya kinyi babban dace a rayuwa Baiwar ALLAH, Addu'ar ki bata faÉ—i a banza ba, ke Æ´ar gata ce sosai kuma sannan ke ba abun rainawa bane..."