← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 68

Sashe 36

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai Razhdeen ya yi tare da goge hawayen fuskar sa ya ce "okay, Insha Allahu zan sassauta wa kaina..."

Roshan ya ce "good yanzu dai ka fara shirin yanda zaka mallaki mafarkin ka...."

Razhdeen jin ya ambaci mafarki sai kuma Ƴar Amana ta faɗo masa a rai, wani irin yawu ya haɗiya cikin sassanyar murya ya ce "where is Sarah?..."

Roshan ya ce "Sarah tana tana gaban iyayen ta cikin ƙoshin lafiya..."

Razhdeen murmushi ya sau ganin yanzu Sarah ta gana da iyayen ta, hankalin sa a kwance ya yi hamdala...

Roshan ne ya ce "my man bari na bar ka haka saboda ba wani lafiya gare ka ba, insha Allahu nima a cikin wannan satin zan zo duba ka..."

Razhdeen ya ce "kai baka gajiya da tafiya ko?..."

Roshan ya ce "ai in ban ganka ba hankali na kasa kwanciya yake, especially a halin da kake ciki dole zan rinƙa zuwa yanda kake..."

Razhdeen murmushi ya sau tare da faÉ—in "wish you the best my twins..."

Roshan ya amsa masa cikin kulawa da kewar juna a haka suka katsai wayar ba tare da sun so ba...

(Ikon ALLAH twins kenam, wato duk wanda ya shiga tsakaninsu shi ya ji kunya...."

Roshan yana gama wayar bacci ya É—auke shi domin yanzu ya daina sa wata damuwa a ransa, ya cire komai a ran sa amma banda soyayyar Baiwar ALLAH, shima a sannu a hankali zai cire ko ba du ka ba....

Cikin dare Baiwar ALLAH ce akan sallaya tayi sallar daren ta kafin da asuba, wani irin yunwa ne ya kawo mata ziyara haka take jin cikinta yana kaɗawa domin yanzu ba ita kaɗai ba ce, tashi tayi ba shiri ta fice daga ɗakin tana sanye da hijab ɗinta har ƙasi, tana fita falo ta tarar da Roshan a kwance kan doguwar kujerar falo sai sharar baccin sa yake, nufan yanda yake tayi har sai da taje gaban sa tukun ta durƙusa ƙasi yanda zata kalle shi da kyau,
yana facing ceiling ido a lumshe fuska É—auke da murmushi haka take kallonsa itama bata san lokacin da ta sau murmushin ba, a hankali ta furta "Yaya Roshan am so sorry but I really loved you, anya zan iya rayuwa da wani É—a namiji bayan kai? no no no bazan iya baa......"

"Zaki iya...."
zaro ido tayi waje tana kallon fuskar sa jin amsar da ya bata still idonsa a lumshe....

A ɗan ruɗe ta miƙe tsaye ba shiri ta bar wurin kai tsaye kitchen ta nufa,
tana shiga ta tsaya a gaban sink tare da kunna ruwan fanfo ta tsaya idonta akan ruwan amma hankalin ta ya bar jikin ta, dogon tunani ta zurfafa, tana cikin wannan tunanin ganin ruwan da idonta yake kai ya tsaya yasa ta dawo hayyacinta ta waiwaya tana kallon wanda ya kashe ruwan,
Roshan ne shima ya tsaya idonsa akan ta ya ce "mai kike son ci?...."

Girgiza kai tayi ta ce "babu komai..."
Ya ce "Nop! nasan yunwa ne ya fito da ke don haka ki gaya mun mai kike son ci ko sha na haÉ—a miki ki..."

Cikin sassanyar murya ta ce "madara nake son sha..."

Ya ce "ok koma É—aki zan kawo miki..."
ba mu su haka ta juya ta fice, shi kuwa bin bayanta yayi da kallo daga bisani ya maida idonsa kan flask zai haÉ—a mata...

tana zaune a bakin gado ya shigo hannunsa ɗauke da cup mai milk a ciki, miƙa mata yayi sannan ya ce "akwai abinda kike buƙata bayan wannan?..."

Girgiza kai tayi ba tare da ta furta komai ba,
shima juya wa yayi tare da faÉ—in "Asuba ta gari..."

A wannan lokacin babu wanda ya rintsa a cikin su har sallar asuba,
haka kuma suka kai rana a lokacin kuma mutanen gidan sun fara dawowa,
Baiwar ALLAH da Roshan a falo suke zaune ga table na abinci a gabanta yana bata abincin a baki ata gefe kuma magunguna ne da water bottle,
Yana cikin bata sai ga Ummy da Pinky da Ramlat da Minal tana É—auke da yaronta sun shigo a jere suna shan hirar su, ganin su yasa duk suka tsaya suna kallon ikon Allah,
Baiwar ALLAH ce ta motsa zata tashi ganin su zata musu sannu da dawowa ya yi saurin riƙo hannun ta tare da faɗin "wallahi sai kin cinye abincin nan ko zaki tashi..."

Babu yanda ta iya haka ta bi umarnin sa idan ya É—ebo abincin a spoon sai ta É—an buÉ—e bakin ya bata,
ƙarasa shugowa suka yi tare da faɗin "Yaya Roshan tsohuwar zuma ce ta motsa..."

Ramlat bin su kawai take da kallo ta gagara cewa komai, neman wuri tayi ta zauna kamar yanda sauran ma suka zauna idonta akan su...

Shi kuwa Roshan ko a jikinsa haka ya cigaba da feeding É—in ta.

Reemah ce itama ta shigo da zumuɗin ta tana son ganin Baiwar ALLAH domin tayi missed ɗin ta, tana shugowa baki ta buɗe zata yi sallama idonta ya sauƙa akan su Roshan, sallamar da bata ƙarisa ba kenam, cike da mamaki ta nufi yanda suke tana faɗin "Yaya Roshan ka ce daga jiya zuwa yau kun sha soyayyar ku har kun ƙoshi...."
ta ƙarasa maganar tana maida idonta kan Ramlat wacce ko ƙibta idon bata yi ganin yanda ko lura da ita bai yi ba balle yasan tana wurin...

Da haka har sauran matan gidan su ma duk suka shishshigo duk wacce ta shigo sai ta tofa albarkacin bakin ta especially Aunty Yolash da Ummy uwar masu gida su kam bakin su ya gagara rufuwa...

Bayan ya tura mata abincin haka ya ɗauki maganin gaba ɗaya ya ɓare su ya juyo yana kallon ta ya ce "Haaaa! buɗe bakin..."

Girgiza kai tayi tare da faÉ—in "Yaya Roshan na warke fa..."

wani irin kallo ya mata ya ce "ko sai na danne ki irin na jiya...."

Ummy wangale bakinta tayi tana faÉ—in "Ah! Ah!! Ah!!! Danne wa kuma..."

Aunty Yolash ta ce "to pah ikon Allah mai kuma ya faru jiya rai ?...."

Reemah zaro ido waje tayi tare da faÉ—in "an zo wurin..."

Ramlat takaici kamar ya hallaka ta bata san lokacin da ta ja dogon tsuka ta tashi tabar falon ba, tana fita waje ta fashe da kuka zuwa tayi ta zauna akan wani É—an dakalin flower sai sharar kuka take....

Can taji an dafa kafaÉ—arta da sauri ta É—ago tana kallon Roshan wanda fitowar sa kenam, zama yayi a gefen ta tare da faÉ—in "mai yasa kike kuka?..."

Ramlat kallon sa tayi tare da cewa "Baiwar ALLAH da ka nuna baka sonta yanzu me yasa kake bata abinci a baki? sannan a gabana kake furta cewa zaka danne ta irin na jiya shin me haka yake nufi?...."

Sauƙe numfashi Roshan ya yi sannan ya ce "ina son tambayar ki wani abu Please, shin kafin ki Aure ni wacece ta fara Aura na? sannan kafin na so ki wacece na fara so? kafin na zauna dake da wa na fara zaman Aure? ina so ki amsa mun tambaya ta..."

Ramlat shiru tayi ba tare da ta furta komai ba,
ganin tayi shiru yasa shi faÉ—in "ki bani amsa nace miki..."

Tana sharar hawaye ta ce "Ita..."

Ya ce "okay kin san dai in badan ta bani matsala ba da babu wanda zai sa na ƙara Aure, a burina da iya ita kaɗai na tsara rayuwata har ƙarshen rayuwata, domin ina yi mata son da babu macen da nayi mata irin sa hatta marigayiya Mariam, kin dai san labarin ta, to ina so ki fitar da idonki akan ta idan har kina son zaman lafiyar ki, abinda kike yayi yawa Ramlat, ba ta hanyar nan zaki mori mutum ba, bana son damuwa Please...."

Yana kammalawa ya tashi yayi tafiyar sa...

Ita kuwa sabunta kukan ta tayi ita kaÉ—ai a wurin...

A washe gari da safe an shirya tsab za'a raka Amaryar Rakesh wato Rukky can ƙasar U.S itama Minal yau zasu koma can itama da Madam Parveen duk zasu tafi gaba ɗaya,
Ummy kuwa ita sai gobe zasu tafi da su Mai martaba,
A wannan ranar kam har da Baiwar ALLAH za'ayi rakiyar saboda zata je ta ga gidan Mahaifinta amma idan aka tashi dawowa da ita za'a dawo...

Ramlat kuwa ƙin binsu tayi saboda family su Baiwar ALLAH ne, haka ta zauna daga ita sai mijinta..

Bayan isar su ƙasar U.S daga lokacin wasu suka fara santin ƙasar domin ƙasar yayi a rayuwa har su ka je gidan Chief domin anan zasu fara sauƙa kafin akai Amarya gidan ta dake cikin country itama,
Innalillahi ai kana shiga gidan Chief zaka fara zauce wa domin sai ka gagara tantance wa shin a duniya kake ko a lahira, lahirar ma a aljanna, domin wannan gidan shi ake ƙira da aljannar duniya domin kaf Nigeria babu mai irin gidan nan, gidan ba ƙaramin tsaruwa yayi ba, mutum sai ya ɓata a cikin gidan,
Kowa tsaya kalle-kalle yake, sai da suka gama hutawar su kafin daga baya wasu zafafan motoci sun kai hamsin suka zo É—aukar Amarya za'a kai ta can É—akin ta, daga nan aka raka Minal itama É—akin mijinta,
washe gari da safe kuma yan Nigeria zasu koma, anan ne aka fara shan fama da Baiwar ALLAH wai ita bazata koma ba, kuma dalilin da yasa bata son komawa saboda Mommynta itama ta dawo kenam bazata koma ba, sai kuka take ta sha ita bazata tafi ba tare da Mommynta ba, daƙer daƙer sai da Daddynta ya rarrashe ta yana sanar mata cewa "da zarar ta haihu zai ɗauko ta..." sai da aka lallame ta tukun ta yadda suka koma Nigeria...
Chapter 36 · 0% Book details