Sashe 65
My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kafin Baiwar ALLAH ta buÉ—e baki tayi magana har yasa hannu ya yi mata É—aukan luÉ—a suka nufi ciki tare da ce mata "idan baki iya turanci ba just tell me I'll find away for you..."
Bugan ƙirjinsa tayi ta ce "lallai ma Habeey baka san da turanci aka haifeni ba..."
Sauran ma'aikatan gidan suma ko wacce hanyar ta tayi suka koma kan aikinsu, wacce take ɗauke da Afaf kuma bin bayan su Razhdeen tayi, suna shiga Baiwar ALLAH ta fara kallace-kallace a falo tareda faɗin "wow 😲..."
sai a lokacin ya sauƙe ta, ji tayi zata lotse cikin ƙasi tayi saurin rungume shi tana ihu, riƙe ta yayi sosai yana faɗin "Please cold down, ki lura da kyau tudun carpet ne..."
Baiwar Allah sauƙe numfashi take cikin tsoro da fargaba ta ce "ayyo carpet ne daman, wayyo Allah na ɗauka burmawa ƙasi zanyi ai..."
Riƙo hannunta yayi ganin yanda take ta bin falon da kallo, buɗe wata ƙofa suka yi nan ma wani falon ne yana ɗauke da wasu arnakun kujeru masu lion designer, anan ne suka haura upstairs, sai da suka haura upstairs hawa bakwai kuma a ko wani upstairs guda ɗaya akwai ɗakuna a ƙalla sunyi biyu, a upstairs na bakwai suka tsaya, wani wantalelen ɗaki suka shiga wanda yake ɗauke da wata shegen gado mai designer ɗawisu, sai kujeru ata gefe da gefen gadon sai wata glass table a ta tsakiyar ɗakin, ga wata ƙatuwar plasman tana gaban gadon a manne a jikin bango, da wasu flawowi a gefe da gefen plasman, ta ɗan gefe guda kuma frig ne ɗan ƙwaƙwas gwanin sha'awa shi ba ƙato ba sannan ba ƙarami ba, sai wani ɗan matakalan beni ata gefe wanda bai wuce taku biyar ba wani curtain ne mai yanka-yanka kamar taliya kana ratsa wa sai wani ɗan dinning table wanda na iya mutum biyu ne,
Baiwar Allah baki ya kasa rufuwa tsabar tsaruwan ɗakin, ji tayi an riƙo hannunta Razhdeen yana janta suka buɗe wani ƙofa again a cikin bed room ɗin wani babban ɗaki ne kuma a cikin bedroom amma na kayayyakin sakawa ne,
Wasu arnakun kayayyaki ne a shirye yanda aka lallanƙaya su, layi guda duk Abayoyi ne kala-kala, layi na biyu kuma ƙananun kaya ne na kanti wanduna da rigunan su da kuma skirt kala-kala da su mini skirts da T-shirt, ga kuma ɓangaren Lace-lace da su swizlace, da layin gizner kala-kala, ga ɓangaren Atamfofi ba'a magana, kayayyaki ne a jejjere kuma duk na mata kamar shagon kayayyakin mata,
yana riƙe da hannunta suka wuce can ciki wuri ne wanda a jikin bango drowowi ne daga sama har ƙasa duk wanda ta buɗe jerin takalma ne, drower thorns daban, plate-plate ma daban haka masu tudu ma daban, ga drower sarƙoƙi da ɗankunnaye da warwaraye, sai drower mayukan shafe-shafe kala-kala, duk wani kayan makeup akwai drower sa, zuwa gaba kaɗan wardrobe ne a jikin bango ƙato ga tsayi da faɗi a ciki kuwa wasu Akwatuna ne manya-manya a jere kala-kala sai wanda ka zaɓa, ga ɓangaren jakakkuna manya da ƙananu, ɗakin nan dai gaba ɗaya kayayyakin Amreesh ne,
Bayan ya gama nunnuna mata ne suka fita,
Bayan sun koma asalin bedroom ne ya kuma nuna mata bathroom tana fitowa daga wanka kawai zata shige É—akin kayan sakawar ta...
Kallonsa tayi ta ce "amma kuma banga naka kayayyakin ba..."
Murmushi ya yi sannan ya ce "wannan ai room É—inki ne, me zai kawo kayana nam..."
Cikin farin ciki ta ce "duk waÉ—annan kayayyakin wai duk nawa ne? shiyasa ka hanani É—auko kayana ko É—aya a gida, na jikina ma sabon sakawa ne shiyasa ka barni na tafo da shi...."
Razhdeen ya ce "sabon Aure kika yi kina buƙatar sabon komai a rayuwar ki, don haka ki bar maganar wasu kayan ki a gida, ga waɗannan idan sunyi kaɗan zan sa a ƙaro miki wasu sabbin kayan, ko idan babu kalar kayan da kike so now kiyi magana a kawo miki su...."
Toshe bakinta tayi da hannayenta biyu tana zaro ido ta ce "kaiiii Habeey ina zan kai kayayyaki haka, a cikin waɗannan ma inaga har na mutum bazan saka wasu ba tsabar yawan su, tsabar yawan su a cikin ina ƙirgawa har na daina, kuma a ƙirgen nawan nakai ɗari da tamanin da wani abu hakan ma da yawa ban ƙirga ba, gaskiya zan ƙira mommy a waya na sanar mata cewa Akwatunana na gida a kyautar da su...."
Dariya Razhdeen ya yi tare da faɗin "sai dai a aika wa yaran ƴan Nigeria su zasu fi buƙatar kayan, amma nan kam babu wanda zai saurari kayayyakin ki..."
Baiwar Allah rungumar sa tayi tana masa godiya...
Ya ce "bana buƙatar hakan, muje na nuna miki part ɗina..."
suna fita a tare kai tsaye room É—insa suka shiga wanda ba rata a tsakanin su duk a upstairs na bakwai suke,
Baiwar Allah tana shiga room É—in Razhdeen taji kamar ba'a duniya take ba,
Idan nace zan tsaya tsara muku yanda ɗakin yake zamu ɓata lokaci ne sosai amma ya ninka room ɗin Amreesh tsaruwa da haɗuwa da girma sosai, shima har da ɗakin kayayyakin sa kamar yanda na Amreesh yake...
Suna fita suka sauƙa down upstairs wanda anan room ɗin Afaf yake na biyun ƙarshen beni kenam, shiga suka yi ɗakin Afaf ɗan ƙwaƙwas gwanin burgewa da gadon ta itama har da plasman da frig ɗinta ɗan ƙarami, ta ɓangare guda kuma computer ne a ajiye akan table wanda yake cike da Game's da videos na karatu, ga kuma abubuwan wasan yara a ɗakin har da su mota wanda zata iya shiga ita kanta da keke da dokuna, ga bathroom ɗinta itama da ɗakin kayayyakin ta a jere a cikin wardrobe su takalma da kayan kwalliyar ta a baje akan mirror, daga nan suka fice a ɗakin Baiwar Allah ba abinda take sai jinjina kai ganin ƴar yarinya ƙarama ma ba'a barta a baya ba, kayayyakinta kamar na hauka...
Suna fita daga É—akin Afaf ya nuna mata wani É—aki yana faÉ—in "muje can..."
Baiwar Allah kawai binsa take domin idan bata yi a hankali ba zata iya ɓata a cikin gidan nan, suna shiga wani ɗaki suka tarar da wasu irin kayayyaki na yara maza da mata wanda bazasu ƙirgu ba,
Baiwar Allah buÉ—e baki tayi cike da mamaki ta ce "waÉ—annan kayayyakin yara fa?..."
Murmushi ya yi sannan ya ce "kayayyakin yaran da zasu zo nan gaba, kuma nasan suna nan tafe da yardar Allah...."
Baiwar Allah dariya tayi tare da bugan ƙirjinsa ta cigaba da bin ko ina da kallo har da gadon wasan su da abubuwan wasan yara, kayan kanti da takalma da kayayyakin sanyi sweaters ba'a magana, waɗannan kayan ko ƴaƴa ɗari za'a haifa a gaba iyakaci kenam,
Haka Razhdeen ya nunnuna mata ko ina na gidan daga bisani suka koma public falor zasu yi lunch, akan dinning wasu irin kayayyakin abinci ne aka tanadar musu, dake dinning ɗin babbane dogo kayan abinci sun fi kala goma a ciki har da su ferfesun kaji dana kifi da eggs soups and meat da vegetable soups haɗi da tuwon shinkafa da na semo, sai shinkafa da jar miya da nama baje-baje a ciki 😋😋, sai ɓangaren kayan fruits komai da komai akwai ba sai na lissafo su ba domin wasu abubuwan ban san sunayen su ba....
Bayan sun kammala lunch Razhdeen ne ya ƙira ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ta zo, sanar mata ya yi akan ta ɗauki Afaf ta kaita room ɗinta tayi mata wanka sannan ta shiryata cikin sleeping dress sai ta sakata yin bacci...
Ƴar aikin ce ta amsa masa tare da ɗaukan Afaf ta nufi da ita upstairs yanda room ɗinta yake, bayan ta je ta kammala mata abubuwa har sai da Afaf tayi bacci tukun ta fito, dai-dai lokacin da su ma suka tashi suna ɗan taku a hankali suna hira cikin so da ƙauna suka haura upstairs, wasu ma'aikata su biyu suka zo suna kwashe abubuwan da aka bari a dinning nan danan suka gyara wurin fess, sauran kayan abincin kuma ƙarshen ta zubar wa za'ayi ko a bawa karnuka domin ya gama amfani, wani kular kam ma ba'a buɗe shi ba balle aga wani irin girki ne a ciki...
Baiwar Allah kafin ta ƙarasa haura upstairs sai da ta shiga room ɗin Afaf ita da Razhdeen suka tarar da ita tana shan baccin ta, Baiwar ALLAH haurawa tayi ta tottofa mata Addu'o'i kafin ta kashe hasken ɗakin ta kunna green lamp ɗakin ya ɗan bada hasken colour, daga nan suka fice a ɗakin.
Razhdeen room É—insa ya nufa shima.
itama Baiwar Allah ta shiga room ɗinta, tana shiga ta zauna a bakin gado tare da yin tagumi tana tunanin kenam shikenam sai da safe ko zamu ƙara haɗuwa, a cikin ranta take faɗin "wannan wani irin Aure ne..."
bayan wasu mintuna taga Razhdeen ya shigo shima ya rufe É—akin,
miƙewa tayi tsaye tare da haɗe gira ta ce "miyasa ka dawo ka koma room ɗinka mana..."
Murmushi ya yi sannan ya ce "bakya son muyi sallah mu godewa Ubangiji da ya nuna mana wannan ranar?..."
Kama goshi tayi ta ce "Oh na manta mijina..."
Jinjina kai ya yi ya ce "okay je ki yo alwala..."
Ba musu ta shiga bathroom tayo alwala ta fito, ta samu har ya shimfiÉ—a musu sallaya, already shi ya yi alwalarsa a can room É—insa,
tsayar da Sallah suka yi suka yi raka'a biyu na godewa Allah da ya nuna musu rana kamar ta yau mai tarin albarka..
Bayan sun kammala ne Baiwar ALLAH ta miƙe tare da cire hijab ɗinta tana faɗin "tam Habeey tashi ka koma room ɗinka..."