Sashe 58
My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Roshan ya ce "bazan tafi na bar Reemah ba, ko ku bani ita mu tafi tare ko kuma nima ku barni anan tare da ita..."
Ji yayi ance "kar kayi mana gardama..."
Ƴar Amana cikin tsoro da fargaba ta ce "Yaya Roshan kaje kawai gobe zaka same ni a yanda zasu kai ka, insha Allahu zaka kasance dani har abada, kaje kawai..."
wani haske ne ya bayyana,
Roshan girgiza kai yake yana faÉ—in "ba yanda zan je na barki Shalele..."
Ƴar Amana ganin Roshan yana shirin fusata Aljanin yasa ta hankaɗa shi da ƙarfi bai ankara ba ya faɗa cikin hasken da ya kawo shi nan danan hasken ya ɓace da shi,
Roshan bai sauƙa a ko ina ba sai a saman katafaren gadonsa,
cikin tashin hankali yake ambatar sunan Reemah yana kuka,
ganin ya kasa samun sukuni ne yasa shi shige wa toilet ya ɗauro alwala ya fito ya tsaida sallah, har akayi sallar asuba yana kan sallaya, a cikin ɗakinsa yayi sallar asuba saboda gudun kar ɗan muƙullo ya bayyana ba tare da yana nan ba..."
Ƙarfe 6 na safe na yi dai-dai lokacin ɗan Aljanin ya bayyano, ɗan ƙarami da shi wanda gaba ɗayansa bai wuce tsayin jariri haihuwar yau ba sai ƙaton kai ga jikinsa yanda yake fitar da farfatsin haske,
a zabure Roshan ya miƙe tsaye yana sanye da jallabiyar sa ganin ɗan Aljanin ya bi ta ƙofa ya fice yasa Roshan ɗaukan key ɗin motarsa shima ya fice da hanzarin sa,
A falo ya tarar da Baiwar ALLAH ko tsaya mata magana bai yi ba haka ya wuce, cike da mamaki ta bi bayansa da kallo itama ta bi bayansa ta fice,
Roshan yana fita ya tarar da su Abbah shi da Razhdeen dawowar su daga masallaci kenam,
Abbah ganin Roshan ya ce "ina kuma zuwa Roshan? ban ganka a masallaci ba..."
Roshan idonsa akan Aljanin wanda shi kaÉ—ai yake iya kallonsa ya ce "Abbah zan fita..."
Abbah ya ce "ina kuma zaka je..."
Roshan ya ce "wani wuri bana buƙatar rakiyar kowa..."
daga nan ya shige motarsa daman gate a buÉ—e take,
Baiwar Allah itama fitowa tayi tana faÉ—in "Allah yasa dai lafiya..."
Abbah ya ce "dole zamu bi bayansa, sojoji biyu su rakamu muje..."
Kamar yanda ya ce hakan kuwa akayi,
Razhdeen ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "ki koma ciki zamu bi bayansa yanzu..."
Sojoji biyu a gaban mota ɗaya shine mai driving sai kuma Abbah da Razhdeen a bayan mota, kafin motar ta tashi Baiwar ALLAH ta lallaɓa ta buɗe bayan booth ta shige ta rufe, lokaci guda motar ta tashi a ɗari suka fice...
Roshan yana driving idonsa akan É—an Aljani wanda yake bin iska yana furawa shine a gaba da motar Roshan sai É—ikar gudu yake shima Roshan gudu yake da motarsa,
Suma su Abbah haka motar su take gudu har sai da suka hango motar Roshan, duk yanda yabi haka suma suke bi,
Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske kafin Roshan ya shige cikin daji da motar sa yanda Aljanin yabi kenam...
Daga Abbah har shi Razhdeen cike suke da mamaki kowa yana saƙe-saƙe a cikin ransa,
Abbah ya ce "Anya kuwa ba aljanu ne suke son É—auke shi ba shima?..."
Razhdeen ya ce "ina zai je?..."
Baiwar Allah wacce take cikin booth gaba É—aya ta gama gajiya...
Gani suka yi Roshan ya yi parking da motar sa ya fito da hanzarinsa ya shige cikin wani kogo,
yana shiga suma su Abbah suka fiffito suka shige kogon, Baiwar ALLAH itama fitowa tayi tana bin bayan su a hankali itama ta shiga cikin kogon, tafiya suke bana wasa ba a cikin kogon domin É—an uban zurfi gare shi,
sai da akayi tafiya mai nisa kafin aka fita daga cikin kogon, ana tafiya kaÉ—an kuma du aka sake iske wani kogon,
yanda Aljani yake bi haka Roshan yake bin bayansa, ta ɗan nesa da shi kuma su Abbah ne su huɗu, sojoji biyu da Razhdeen da bayansu kuma Baiwar ALLAH ce wacce ta gama jikkata domin ba ƙaramin gajiya tayi ba, tafiya kawai take...
suma ƙara shigewa wani kogon suka yi daƙer Roshan ya wuce wurin tsabar baƙaƙen tsuntsaye sun dubu da haka ya ratsa ta cikinsu ya wuce, su Abbah suma cikin fargaba suka wuce tsuntsayen,
Baiwar Allah tana zuwa wurin ganin sun wuce ta cikin su yasa itama ta kutsa ciki saida tazo tsakiyar su taga duk sun mamaye ta kuma suma hakane sai dai a ture su, ita kuwa tsoronsu ne ya hanata ture su haka ta fara rausa ihu tana faÉ—in "Wayyo Allah na nashiga uku kuzo ku taimake ni, na mutu na lalace..."
Su Razhdeen waÉ—anda basu gama yin nisa ba suka fara jin ihu, shi kuwa Roshan ya yi nisa bai ji ihun ba,
A kiÉ—ime Razhdeen ya ce "wannan kamar muryar Reesh..."
har zai juya wani sojan ya riƙe hannunsa yana faɗin "Oga nan wurin fa akwai tarin aljanu wata zata iya fito mana..."
Razhdeen zamar da hannunsa ya yi yana faÉ—in "dallah sake ni wani irin aljanu kuma, har ya juya zai koma sai ga Baiwar ALLAH ta fito daga cikin kogon da gudun gaske tana ihu haÉ—i da cewa "dan Allah ku jira ni Wayyo Abbah..."
Tana isowa ta rungumi Razhdeen tana sauƙe numfashi ga yanda duk tsuntsayen suka yakushe ta,
Razhdeen ya ce "meyasa kika biyo mu bayan nace ki zauna..."
Abbah girgiza kai kawai yayi ya ce "ku zo mu tafi kar ya mana nisa..."
Haka Razhdeen ya riƙe hannunta suka fara tafiya, sai da suka yi tafiya mai nisa kuma du suka tarar da wani ƙaton rami wanda cikinta ruwa ne yake ta ambaliya, gani suka yi Roshan har ya tsallaka da taimakon Aljani, sai dai akwai ɗan ƙaramin kada wanda girmansa bazai wuce girman katako ba,
Abbah ya jinjina kai ya ce "yanzu taya zamu fara wuce wannan wurin?..."
Razhdeen ya ce "zamu iya amma sai dai abi a hankali ta gefe da gefe..."
wani soja ne ya fara ɗora ƙafarsa akan icen jikinsa na rawa a hankali yake jan ƙafar sa,
Abbah kuwa ba abinda yake faÉ—i illa "kayi a hankali, a hankali, a hankali..."
da haka sojan ya wuce, shima É—ayan sojan kamar yanda wancan yayi haka ya wuce shima a tsorace,
Abbah shima haka ya taka matakalan a hankali yana jan ƙafa domin tsabar ƙarantar icen baka isa ka ɗaga ƙafarka ba, nan zaka ji hajijiya inba sa'a ba ka faɗa cikin ruwan, daƙer shima Abbah ya samu ya wuce..
Razhdeen kallon Baiwar ALLAH ya yi ya ce "sauran ke..."
Baiwar Allah tin kafin ta ɗora ƙafar ta jikinta ya fara ɓari yana kakkarwa kamar wacce ta faɗa cikin ruwan ƙanƙara, haka take faɗin "to, to, to, to mu je, a hankali, wayyooo..."
Razhdeen ɗorata yayi akan icen kafin ya sake ta, tana hawa da ta leƙa ƙasin ruwan nan ta fara jin hajijiya, tangal-tangal ta fara yi har ƙafar ta ya rabe da icen tayi cikin ramin zata faɗa cikin ikon Allah Razhdeen ya yi saurin riƙo hannunta, gangar jikinta duk yana cikin ramin iya hannunta kawai ya iya riƙe wa haka zuciyar sa yake bugawa da ƙarfin gaske,
Shima Abbah hankalin sa ba ƙaramin tashi yayi ba haka yake faɗin "Razhdeen ka riƙe ta sosai, kar fa ka sake ta, ka riƙe ta sosai..."
Ita kuwa ba abinda take ihu tana faÉ—in "Wayyo Allah na dan kar ka sake ni, wallahi bana so na mutu yanzu, hannuna zai yanke Habeey..."
kanta ta sunkuyar ƙasi tana kallon ruwan da yake ta ambaliya gani tayi wani ƙaton shark ya yi tsalle yayo sama bakinsa a wangale, wani irin ihu ta ƙara kurmawa tana faɗin "wallahi akwai shark 🦈 wallahi akwai shark 🦈 wallahi akwai shark 🦈 shikenam yau kam na hallaka..."
Haka shark waran su biyar suke yin tsalle su koma cikin ruwan,
Razhdeen kuwa haka ya ruƙe ta sosai ya barta so yake ta gama tsorata sai ya ciro ta,
Abbah kuwa cewa yake "Razhdeen kanada hankali kuwa, ka ciro ta mana ya ka barta a haka..."
Razhdeen sai da ya gama yinsa tukun ya ɗagota da hannu ɗaya, yana ciro ta sai da ya zabga mata wani kyakkyawan mari tare da faɗin "Banga amfanin biyo mu ba, gashi yanzu kin zamo mana ƙarfen ƙafa..."
Baiwar Allah fashewa tayi da kuka, bata ankara ba taji ya ɗaga ta sama tare da saɓata a baya, sai da ya goye ta kafin ya ɗora ƙafarsa akan icen ya fara tafiya a hankali yana jan ƙafa, Baiwar ALLAH wani irin ƙanƙamo tayi masa haka jikinta yake rawa da haka ya samu ya wuce da ita,
Bai sauƙe ta ba haka suka cigaba da tafiya, Roshan kuwa yayi musu nisa domin basa iya hango shi amma sai dai tafiyar hanya ɗaya ne babu wata hanyar da ta kauce, nan ma sai da suka ƙara yin tafiya mai nisan gaske kafin suka isko wani ƙaton rami kuma du amma bai kai wanda suka baro ba,
Abbah ya ce "wani tashin hankali kuma du..."
Wannan ramin zurfi gare shi baka iya hango tsayinsa sannan wannan babu wani icen da aka saka alamun sai kayi tsalle kafin ka tsallaka..
Razhdeen sauƙe Baiwar ALLAH yayi daga bayansa ya kwatanta musu yanda zasu yi su tsallaka, soja ɗaya ne yayi baya sosai kafin ya tafo da gudun gaske ya yi tsalle ya tsallaka,
haka É—ayan sojan ma yayi,
Razhdeen ya kalli Abbah sannan ya ce "Dad zaka iya kuwa?..."
Abbah ya ce "wai ina zan samu ƙarfin jikin da zan iya tsalle har na tsallaka wannan ramin?..."