← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 68

Sashe 25

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daƙer Mai martaba yasa aka fito da su Pinky da Rukky daga ɗakin horo domin a niyar Abbah sai sunyi wata biyar suna kulle, a sati biyu gaba ɗaya sun fita hayyacin su domin azabar da ake gana musu ko namiji iya kar abinda za'a masa kenam, sunyi baƙi sun rame kamar masu cutar HIV, especially Rukky tafi jikkata sosai domin ko baccin kirki ba'a barin su suyi sai kwanan tsaye ga shocking da ake kwana ana jona musu, abinci kuwa kamar yanda Abbah ya sanar sau ɗaya ne a rana idan aka basu da rana sai washe gari da rana hakan ma ba isar su yake ba, abun breakfast da abincin dare duk babu lissafin wannan domin zama da yunwa ma horo ne,
a cikin ɗakin horon nan sun suma yafi sau adadi, gaba ɗayan su sai da suka raina kansu, ba ƙaramin danasani suka yi ba, kullum kukan su shine abar su suje su nemi yafiyar Abbah amma anƙi barin su, shi kuma Abbah ba zuwa yanda suke yake yi ba sannan ya hana kowa yaje dubo su,
A yanzun ma dalilin fitowar su shine akwai sojan da ya samu Mai martaba akan maganar su yana faÉ—in cewa "yaran nan fa zasu iya mutuwa a kowane lokaci domin azabar da ake musu yayi yawa ba zasu iya jura ba, ga sauraye sannan ga rashin abinci idan sunyi rashin lafiya babu magani, yanzu haka duk suna kwance rai a hannun Allah babu wacce take iya motsi da kanta..."

Mai martaba hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba jin halin da yaran suke ciki, bai bi ta Abbah ba haka yasa aka ɗauko su a kafaɗa domin ba zasu iya tashi suyi tafiya ba, ko gida ba'a kai su ba haka aka miƙi hanyar hospital da su, daga baya gidan suke jin labarin halin da suke ciki, kowa ba ƙaramin tausaya musu akayi ba banda Abbah da yake ta masifa cewa "meyasa aka fitar da su?, ba rashin lafiya ba ko gawarsu aka tarar nafi son sai sunyi adadin kwanakin da na yanke musu..."

Mai martaba sam bai ji daɗin kalaman Abbah ba shima cewa yayi "haba ai rashin imanin zai yi yawa ai idan har aka barsu acikin wannan halin, ƙarewa ko kisan kai suka aikata dai-dai hukuncin da yakamata ayi musu kenam, waɗanda suke gidan prison ma sun fisu gata wani irin abu ne haka? to nidai na fitar da su..."

daga nan Abbah bai ƙara furta komai ba,
har sai da su Pinky suka yi kwana biyu akan gadon asibiti, sai yanzu suka dawo hayyacin su, mahaifiyar su ita take jinyar su babu yanda ta iya dole zata saurari Æ´aÆ´anta ko me suka aikata,
Bayan su samu sauƙi sallamar su aka yi, sun samu lafiya amma sai dai har yanzu akwai wannan ramar da fitar hayyaci, domin babu wanda bai tausaya musu ba...

Pinky da Rukky bayan sun koma gida sun je sun samu Abbah a falon sa suka durƙusa har ƙasi suka gaishe shi,
Abbah sama-sama ya amsa musu rai a ɓace, neman yafiyar sa suka fara yi suna kuka, sai da suka yi kukan su mai isar wa suna bawa Abbah haƙuri kafin Abbah ya ɗago yana bin su da kallo, daga baya ya ce "a wannan rayuwar da muke ciki wasu da kuɗin su sun nemi su sayi mutunci wa kansu amma sun kasa, saboda shi mutunci kamar madara ne idan ya zube ba halin kwashe wa, da yawa mutane suna son su zama mutanen kirki amma tin tinin sunayen su ya rigada ya ɓaci a ko ina babu yanda zasu yi su zama mutanen kirki a cikin al'umma, a zamanin yanzu idan baka linbanci damar ka ba har ya wuce to kuka ne ka rinƙa yinsa har ƙarshen rayuwar ka, yanzu zan baku misali da matar Uncle ɗin ku kuna gani a gaban ku abinda ya faru da ita, ta mayar da kanta mahaukaciya, su waɗanda ta shuka musu sharri gasu nan suna nam cikin kwanciyar hankali ita kuwa tana can sai yanda rabbani yayi da ita, a cikin satin nan muka ji labarin haukar da take yi muraran yasa ta fita daga prison da gudu garin haka mota ya buge ta, gashi tayi sanadiyar rasa ƙafarta ɗaya kuma haukar yanan a kanta, yanzu wannan al'amarin wa gari ya waya?
kuna yara ƙanana zaku ɓata future ɗin ku, yanzu duk namijin da yaji labarin abinda kuke aikata wa shin akwai wanda zai yi sha'awar auren ku ne? impossible wallahi, to ya kamata kuyi ƙoƙarin maida kanku mutanen kirki tin kafin lokaci ya ƙure muku, domin yanzu da sauran lokacin ku...."

Pinky da Rukky kuka suke sosai kamar ransu zai fita haka suke ta zuba godiya wa Abbah tare da yin nadamar abinda suka aikata, kuma sunyi alƙawarin bazasu sake aikata wani kuskure ba....

Abbah ya ce "Ɗan Adam dole ya aikata kuskure amma ba wanda za'ayi Allah wadar ba, don haka ku tashi kuje ni na yafe muku, ina so kuma kuje ku nemi yafiyar kowa na gidan domin ba ƙaramin ɓata musu rai ku ka yi ba musamman ita Daughter da kuma Roshan, shi Razhdeen baya nan an fitar da shi ƙasar waje..."

Suka amsa cikin girmamawa sannan suka yi wa Abbah sallama tare da fice wa...

Ƴar Amana yanzu gaba ɗaya haushin Baiwar ALLAH yasa ta daina zama a yanda take, duk hanyar da zata haɗa su bata bari su haɗu,
Baiwar ALLAH ta sha dakatar da ita akan ta tsaya suyi magana ta fahimtar juna amma Ƴar Amana taƙi sauraron ta, yanzu har ta kai idan Ƴar Amana tana zaune a falo Baiwar ALLAH ta shigo sai ta tashi tabar falon, a cikin ba'a fahimci komai ba har aka zo kowa ya fahimci halin da suke ciki...

Baiwar ALLAH shawara ɗaya ta yanke cewa da daddare zata je wurin makwancin Ƴar Amana ta tilasta mata akan meyasa take jin haushin ta yanzu, dake a ɗaki ɗaya suke kwana Ƴar Amana da Ummy domin jinin su yafi haɗuwa,
Baiwar ALLAH tura ƙofar ɗakin su tayi da sallama a bakin ta, tarar da su tayi su duk akan gado, ita Ummy tayi bacci, Ƴar Amana kuma sai buɗe litattafai take tana duba abubuwan da aka koyar da ita, jin sallama yasa ta ɗago tana bin Baiwar ALLAH da kallon daga bisani ta maida kanta kan littafin ta cigaba da dubawa,
Baiwar ALLAH zama tayi a bakin gado idonta akan Ƴar Amana, gaba ɗaya Baiwar ALLAH cikin jikinta ya fara nuna ta domin ba ƙaramin fari tayi ba daman gata fara ce tass sai yanzu kuma har ta ɗan haɗa da yellow-yellow kamar ba jini a jikin ta amma kuma ba rashin jini bane domin tana samun kulawa sosai, domin abincin ta ma daban ake girka mata na samu juna biyu wanda zai ƙara mata lafiya da ƙarfin jiki tare da jaririn jikinta...

motsi ta fara yi da lips ɗinta a hankali ta furta "Ƴar Amana..."

Ƴar Amana kuwa ko kallon ta batayi ba balle ta saurare ta,
Baiwar ALLAH ƙara ƙiran sunanta tayi anan ne Ƴar Amana ta ɗago da dirarrun idanuwanta waɗanda suka kaɗa sukayi ja lokaci guda domin idan ta ga Baiwar ALLAH gaba ɗaya zuciyar ta hargutsuwa yake...

Baiwar ALLAH ta ce "dan Allah ina so ki sanar mun me nayi miki ne haka? ko dai baki yi murnar haɗuwa da ni bane? dan Allah ki sanar mun ko meye kike so zan yi ƙoƙarin ganin na faranta miki...."

Ƴar Amana idonta ta sauƙar kan cikin Baiwar ALLAH tare da faɗin "bazaki taɓa dawo mun da farin ciki na ba har abada domin aikin gama ya rigada ya gama, lokaci ya wuce amma sai dai mallakar farin ciki na abu ne mai sauƙi a gareni, ke kuma in har ke zaki sanya ni farin ciki to kin yaudari kan ki ne domin bana jinki a raina...."

Baiwar ALLAH tana kuka ta ce "to ki gaya mun mana me nayi miki?...."

Ƴar Amana ta ce "meye ma bakiyi ba, kinga dan Allah tashi ki bar mana ɗaki bana buƙatar ganin ki..."

Baiwar ALLAH ta ce "Ƴar Amana ni ce bakya son gani?..."

A fusace Ƴar Amana ta watsar da litattafan da suke gaban ta a tsawa ce ta ce "ki tashi ki bar yanda nake please, kin lalata mun gobe na, mijin da nake sa ran zai zamo uban ƴaƴana kin zo kin dasa ɗan da bana sunnah ba a cikin rayuwar mu, ƴaƴan da zan haifa kin zo kin fara zuba musu gura gurbi a cikin su, taya bazan tsane ki ba? hakan ma kinada aure maimakon ki fara haifan tsabtataccen yaro amma sai kika fara zuba wa mahaifarki dattin zina wanda ta sanadiyar haka zaki haifo dattin jariri da sunan ɗa a gurin mijin da nake sa ran shi zai zamo madubin dubawa ta dana ƴaƴana....."

Baiwar ALLAH jin kalaman da Ƴar Amana take jifanta da shi ne yasa ta fusata ta zabga mata mari tana kuka,
miƙe wa tayi tana nuna ta da yatsa tare da faɗin "ki san irin maganganun da ya dace kina faɗa domin indai kika cigaba da jifan munanan kalamai akan abinda ke cikina zamu samu matsala sosai..."

Ummy wacce ta daɗe ta farkawa jin hayaniya itama ta tashi zaune idonta akan Baiwar Allah ta ce "to ba gaskiya bane? shin ta hanyar Aure kika samu cikin? ai ba ƙarya akayi miki ba tinda tin da kike da Roshan bai taɓa kusantar ki ba balle ki ɗaura mar sharrin cikin, ke da bakin ki kike sanar mun haka to kinga kuwa sai dai ki toshe kunnuwan ki, kuma kada ki sake sa hannu ki mari ƴar uwata akan ta faɗi gaskiya...."

Baiwar ALLAH tana kuka ta juya zata fi ce itama Ƴar Amana a cikin kuka ta furta "tirrrr...."

A wannan ranar Baiwar ALLAH kwana tayi bata rintsa ba sai kuka sai yanzu ta ƙara jin ta tsani cikin dake jikin ta, bata ƙaunar cikin ko kaɗan, kamar yanda ta tsanin uban cikin haka ta tsani cikin shima....
Chapter 25 · 0% Book details