← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 68

Sashe 64

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan wata biyu.
A yau Abbah ya buƙaci akai Amare gidan mijinsu, har ilah yau babu wargi a jikin Abbah da Mai martaba especially Abbah,
ba Amare ba hatta masu wankan jego Abbah ya sanar cewa kowa ta koma É—akin mijinta,
Dake ba wani isheshshen lafiya Abbah yake da shi ba ko rakiyar Amare ba'ayi ba, ko wacce daga gidan Abbah sai É—akin mijinta,
A yau Mai martaba ne ya fara tattaran iyalansa zasu koma ƙasar Jiddah,
Aunty Maimuna da Aunty A'isha da Ummy tare da jaririyar ta sai mijinta Yarima Ashmar, duk tafiya sukayi bayan Mai martaba ya gama yiwa Reemah da mijinta nasiha da fatan alkhairi mai ɗorewa har ƙarshen rayuwar Aurensu da fatan samun zuriya masu albarka....

Washe gari itama Pinky da Æ´ar jaririyar ta ta tafi tare da mijinta Arash wanda tin Aure har rasuwar Aunty Yolash yake nam bai koma ba sai yanzu zai tafi da Matar sa....

A washe gari Chief Suraj Mahendra Marka shima ya hallara kan iyalansa gaba ɗaya zasu tafi wanda duk ƙasa ɗaya zasu zauna, yana tare da matarsa Madam Parveen, Mohandas da matar sa Minal da yara biyu, sai Rakesh da matar sa Rukky, shima Razhdeen ya shirya tsab da Amaryar sa Amreesh wanda zasu cigaba da zama a ƙasar U.S sakamakon komawar Razhdeen wurin aikin sojan sa wanda ya ɗauki lokuta da dama bai je ba, itama Afaf wato Biju Mama ƙin zama tayi a wurin kowa wai ita zata bi Mamanta, haka kuwa aka ɗauke ta ba'a son ran Reemah ba domin a tunaninta za'a bar mata Biju Mama, Baiwar ALLAH bata karɓi Biju Mama ba sai da Reemah ta ce ta haƙura da ita kafin Baiwar Allah ta ɗauke ta dake Biju Mama tana da matuƙar wayo tin yanzu ta gane mahaifiyar ta, suma duk airport suka nufa sai ƙasar Australia 🌏....

Yanzu wanda ya rage shine Roshan da Amaryarsa Reemah wanda shima sun shirya tsab zasu koma ƙasar Egyph wanda anan babban hospital ɗin Roshan yake, ya zuba ma'aikata a asibiti sai haɓaka yake yana ƙaurin suna duk da baya can da zama, amma ana kula masa da harƙoƙinsa, yanzu ya kammala aikin da yake gudanarwa anan ƙasar Nigeria, zai koma ainihin yanda yake da aikinsa wanda zai tafi ne tare da matar sa da kuma yaron sa Ra'ees...

A lokacin da zasu tafi Ammy ta buƙaci a bar Ra'ees ya ɗan ƙara wayo kafin a kai shi saboda su samu damar cin Amarcinsu, Roshan har ya yadda da hakan amma ita Reemah sai ta nuna cewa bata yadda ba, tana son zama da yaro, a cewar ta tana son Ra'ees ya tashi yana kallon ta a mazannin mahaifiyarsa...

Babu yanda aka iya haka aka bar mata shi, Ammy ce tayi musu rakiya har ƙasar Egyph wanda sune kawai suka samu ƴar rakiya, ita kuma Hajiya Kilishi ta zauna tana kula da Abbah,
Ammy sai da tayi kwana biyu tare da su kafin ta dawo Nigeria, gida yanzu babu kowa sai gidan yayi shiru ba daɗi, iya Ƴar tinny ce kawai yarinyar gida sai mata biyu Hajiya Kilishi da Ammy sai masu aiki...
A wannan lokacin ne Abbah yayi ritaya a wurin aikin soja, saboda yanzu gani yake duniyar babu daɗi, jikinsa ba ƙwari yanzu kuma duk mutuwar Aunty Yolash ne ya saka shi cikin wannan halin, hakan yasa ya ajiye aikinsa....

A can ƙasar U.S sai da Baiwar ALLAH tayi kwana biyu a gidan su kafin aka kaita gidan mijinta dake ko wacce gidanta daban,
Razhdeen shi da kansa ya É—auki Amreesh da É—iyarsa Afaf ya kai su gidansa wanda ya tanadar musu, dake a wurin su ba'a rakiyar Amarya, miji da kansa yake É—aukar Amaryarsa daga baya kuma aje a duba gidan ta,
wani zureren mota ne black colour wanda a ciki wani jibgegen soja ne bature yake driving, ta baya kuma Razhdeen ne sai Amreesh dake gefensa, Afaf kuma akan cinyarsa, suka miƙe hanyar new York road yanda gidan Razhdeen yake, tafiya suke babu wanda yayi magana a cikin su sai Afaf wacce take wasa da ƴar tsanar ta, Razhdeen juyowa ya yi yana kallon ta a yayinda ita kuma kanta yake kallon ƙasi tana wasa da yatsun hannunta, a hankali ya ɗago da hannunsa ya ɗora akan nata hannun ya riƙo mata su, ɗagowa tayi tana kallon sa jiki ba ƙwari, fuska a sake ya ce "meya faru ne?..."

Girgiza kai tayi ta ce "babu komai..."
Ya ce "Please bana son ganin ki a cikin wannan yanayin, nifa mijinki ne duk abinda yake damun ki ki sanar mun, nayi miki alƙawari duk abinda ke damunki zan magance miki shi..."

cikin damuwa ta ce "ba komai ne yake damuna ba, haka kawai Aunty Yolash take mun gizo, na damu sosai da rashin ta..."

Sauƙe numfashi Razhdeen ya yi sannan ya ce "she already passed away almost 2 months now, yakamata ace rashin ta yabi jikin ki yanzu, ki daina damun kan ki saboda a rayuwar nan duk mai rai mamaci ne, shin kin manta mutuwar Ramlat matar twins? ita fa barin jariri tayi gashi yanzu sai dai labari, everything has passed, shi mutuwa ba yaro ba babba idan lokaci yayi sai tafiya sannan baya sallama, Please bana son ki rinƙa shiga damuwa..."

Jinjina kai tayi sannan ta ce "shikenam Insha Allahu zan daina damun kaina akai, tinda dole ne mutuwar nan kuma tana kan mu da iyayen mu gaba É—aya, waÉ—anda suka riga mu gidan gaskiya zan cigaba da musu addu'a..."

Ya ce "ina so kimun alƙawari ɗaya..."
Ta ce "ina jinka mijina, ko wani irin alƙawari zan yi maka indai bai saɓawa Ubangiji ba..."

Jinjina kai ya yi sannan ya ce "bana so ki ƙara saka wani abu a ranki, duk abinda yake damunki a ranki ki sanar mu domin yanzu nine abokin shawarin ki, idan naga wani unreachable a tattare dake zamu samu matsala ne..."

Murmushi tayi tare da kwanta mishi akan ƙirji hannunta a cikin sumar kansa tana bin tsayin gashin tana ja tare da yin wasa da shi ta ce "nayi maka Alƙawarin babu wani matsalar da zaka same ni da shi, nayi alƙawarin zan cigaba da faranta maka rai har ƙarshen rayuwa ta mijina Daddyn Afaf..."

Shima murmushi ya yi tare da sumbatar ta akan tsakiyar kanta dake kanta akan ƙirjinsa yake, haka ya haɗe su ya rungume su daga uwar har ƴar tasun da haka suka isa gidan,
Baiwar Allah gani tayi motar ta karya kwana ta nufi yanda aka buɗe wani ƙaton gate mai design kalar ruwan zuwa, a zabure ta tashi tana kallace-kallace ganin girman gidan da suka shiga, a ruɗe ta kalli Razhdeen ta ce "Habey wani irin gidane ka kawo mu?..."

Murmushi kawai yayi ba tare da ya furta komai ba,
Baiwar Allah wasu ɗirka-ɗirkan manya-manyan sojoji ta fara gani a jere suna tsaye samƙam da manya-manyan bindigu a hannayen su sunyi guda ashirin, goma fararen fata wato baturaye goma kuma baƙaƙen fata,
motar ce tayi parking a wurin ma'ajiyin motoci wanda yawan motocin wurin sun kai arba'in ko wacce ta kalar design ɗinta, fitowa suka yi haka idanuwanta suke jujjuyawa tana bin ko ina da kallo, haɗiyar yawu kawai take domin marubuciyar ma ƙwakkwalwar ta bazai iya zayyano mata yanda tsarin gidan yake ba, tsayin gidan ba'a magana domin upstairs ne hawa-hawa a gidan,
Baiwar Allah tana cikin kallace-kallace kwatsam taji kukan karnuka ata gaban su dasauri hankalinta ya dawo jikinta a tsorace ta rungumi Razhdeen tana furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un..."
ganin karnukan turawa ne masu buzuzun gashi yasa ta dawo hayyacinta domin a can gidan mahaifinta Chief akwai irin su, amma tsarin gidan ne har ya ci uban gidan Chief tsaruwa da girma da kuma tsayi,
a hankali ta juyo tana kallon Razhdeen murya ciki-ciki ta furta "Habeey kana nufin duk girman gidan nan a ciki zamu zauna? ni kaÉ—ai? wai?..."

Murmushi ya yi yana É—auke da Afaf akan kafaÉ—arsa ya ce "É—aya daga cikin gidaje na..."

Zaro ido tayi tana faɗin "kana nufin kace kanada wasu gidaje anan ƙasar bayan wannan?..."

Jinjina mata kai yayi sannan ya ce "iya gidaje kawai kika lissafo, banda wasu kadarori daban-daban, kedai zaki san komai a hankali domin idan na tsaya lissafa miki zaki kusan zaucewa, muje daga ciki..."

Ya ƙarasa maganar yana nuna mata hanya dai-dai lokacin da wasu mata turawa masu blue eyes su 6 suka iso wurin da suke a tsaye, duk durƙufar da kai ƙasin gwiwa sukayi suna kwasar gaisuwa, ɗaya daga ciki tasa hannu ta karɓi Afaf a hannun Razhdeen,
Baiwar Allah binsu tayi da kallo cike da mamaki ta ce "waÉ—annan matan fa daga ina?..."

Duk suna sanye da farar doguwar riga zuwa gwiwa iri ɗaya , uniform ne na aikatau kalar na ƴan ƙasar kenam,
Razhdeen ya ce "waɗannan sune ƴan aikin ki waɗanda zasu na miki hidima, gyare-gyare da su wanki, girki ko meye idan kina so zasu yi miki, domin gidan nan bazaki iya gudanar da aikin gida ba, sannan zasu taya ki zaman gida idan bana nan, aikin da nake babu lokaci tin safe idan na fita bana dawowa sai yamma, kina buƙatar waɗanda zasu na ɗebe miki kewa, sannan zasu na miki rainon Afaf...."

Jinjina kai Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "amma a gidan suke da zama ko kuma zuwa zasu na yi kullum?..."

Razhdeen ya ce "a gidan suke sai dai idan suka É—an daÉ—e zasu na kaiwa ziyara a iyayensu, É—akunan wajen nan shine wurin kwanan su..."

Sai ta waiwaya tana ganin É—akunan kafin a shiga falon gidan, ta wajen ma sai ka haura upstairs mai hawa ta uku kafin ka iske É—akunan su...

Hura iskar bakinta tayi daga bisani ta ce "shikenam Allah yasa na iya zama da su..."

Razhdeen ya ce "bangane ba? su É—in sunada aibu ne? sunada daÉ—in zama da mutane sosai..."

Baiwar Allah ta ce "to ai naga ba ƙabilan mu ɗaya ba, naga wasu chinoni ne a ciki wasu kuma turawa, amma basu iya Hausa ba ko?..."

Dariya Razhdeen ya yi sannan ya ce "Anan kuma wa ya san miki Hausa? ko can gidan Chief kinga suna hausa ne? to yanzu ma da suke sauraron mu kallon baibai suke mana domin jin yaren suke kamar yaren jinn..."
Chapter 64 · 0% Book details