← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 68

Sashe 1

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Typing ✍️

*MY ENEMY*

*TAKUN ƘARSHE*

*BOOK 3*

1 to 5

______________A fusace ya tashi ya nufi bakin ƙofa jin yanda ake ta buga ƙofar ba ƙaƙƙautawa.
Baiwar ALLAH da ƙarfi ta tura ƙofa dai-dai lokacin da aka buɗe sai kawai tayi ciki bata ankara ba, ta faɗa kan Razhdeen gaba ɗaya suka je ƙasin carpet tana saman kan sa, da sauri ta ɗago tana kallonsa a yayin da shima idonsa yake kanta haka suke kallon juna ba bu mai ƙarfin motsa wa, sai da suka ɗau seconni kafin ta firgita a ruɗe ta tashi daga kansa cike da jin takaici...

Wani abun mamaki kuma su Pinky sun biyo bayan Baiwar Allah ganin ta fita, suma suka sa security ya kawo su da mota amma daga wajen gate suka tsaya suka shigo gidan da ƙafa, suna tsaye a bakin ƙofar falon Razhdeen, faɗuwar da Baiwar ALLAH tayi akan Razhdeen akan idonsu dasauri pinky ta ciro wayar ta tare da musu video harda photo sannan ta ja hannun Rukky suka gudu ba tare da ganin me zai faru ba domin sun samu wani makamin sharri daga nan suka tafi a waje suka tarar da security da ya kawo su suka shiga mota cike da murna...

Pinky Rukky sun ci alwashin raba Auren Roshan da Baiwar Allah kuma sun san Razhdeen ba Auren ta zai yi, su burin su ta fita musu daga cikin Ahali kuma suna so tayi baƙin jini a wurin Abbah...

Razhdeen yana shirin tashi Baiwar Allah ta jefa masa ledar rigar gift akan ƙirjinsa ta cigaba da cewa "Razhdeen ka ke ko waye? to bari kaji na sanar maka Ni nafi ƙarfin ka wallahi, ni zaka yiwa sharri saboda ka raba ni da mijina? me nayi maka haka? meyasa kake son shiga mun rayuwa ne? kayi mun sharrin zina wanda tinda nake ban taɓa aikata wa ba saboda ka rabani da mijina, kana ta wani cewa hotel shin da wa zaka haɗu a hotel ɗin? to bari kaji daman wata ƙila can halin ka ne yawon zuwa hotel kana kaiwa ƴan mata can, to ni ba haka nake ba, ni ba mazinaciya bace kamar kai, Razhdeen ka fita daga shirgi na, ka nisanta kan ka daga gare ni, bana neman komai daga wurin ka saboda ka fita hanya ta,
I hate you wallahi..."

tana kammala wa ta juya zata tafi yayi saurin riƙo hannun ta tare da juyo da ita ya manno ta kan ƙirjinsa, dai-dai lokacin da Ƴar Amana ta shigo falon tana goye da jakar ta tayi shirin makaranta tsab, abun da ta tarar ne yasa ta ja da baya tana zazzaro ido waje ta tsaya a jikin labule tana rurrungume shi jikinta har rawa yake idonta akan su.

Razhdeen ne ya riƙo sumar kan Baiwar Allah suna fuskantar juna kamar zasu haɗe baki har numfashin su yana haɗuwa ya yi saurin kai ƙaramin bakinsa sai tin kunnen ta yana magana a hankali cikin sassanyar murya yake faɗin
"Duk ban fahimci mai kike nufi ba amma naji kin ƙirani da mazinaci, ki iya bakin ki domin wata rana zaki faɗi abun da zai sa na yanke miki harshe gaba ɗaya...."
Cikin ɓacin rai da mugunta ya damƙi gashin kanta da ƙarfi har sai da ta ɗan yi ƙara sannan ya kuma cewa "inda kin san yanda na tsane ki a raina da baki yi gigin zuwa yanda nake ba, ki kiyayi ranar da zan raba miki ƙafa gida biyu, i hate you too....."

Riƙe hannun sa tayi ta finciki kanta daga riƙon da yayi mata har sai da gyalenta ya za me, tana kuka ta tsuguna zata ɗauki gyalen sai ga sarƙar wuyanta shima ya faɗo bata lura da shi ba haka ta ɗago a fusa ce ta bugi ƙirjinsa tare da ture shi baya ta juya da gudu tana kuka da haka ta fice, shima ya daɗe yana tsaye yana kallon hanyar da ta bi sannan idonsa ya sauƙa akan sarƙar da yake a yashe, hannu ya kai ya ɗauko idonsa akan sarƙar yana jujjuya shi, yana tunanin aina ya taɓa ganin irin wannan sarƙar...

Ƴar Amana ce ta tako har yanda yake tsaye tana kuka, ganinta yasa ya dunƙule sarƙar a tafin hannunsa, Ƴar Amana bata ga fuskar Baiwar Allah ba dake ata bayanta take, itama Baiwar ALLAH da ta tashi baya waiwaya ba kai tsaye gaba tayi ta fice.

Ƴar Amana tsaya wa tayi a gaban Razhdeen fuska shaɓe-shaɓe da hawaye ganin ta acikin wannan halin ne yasa shi faɗin "Sarah what's wrong?..."

Ƴar Amana ɗaukar pillow kujera tayi ta fara kwaɗa masa tana kuka sai da ta gama dukan sa da pillow sannan ta wurgar ta juya da gudu ta koma room ɗin ta, tana shiga ta jefar da jakar goyon ta sannan ta ciccire uniform ɗinta, jin motsin mutum yana nufo room ɗinta ne yasa ta je ta rufe ƙofar ɗaki tareda saka sakata, tana jin yanda Razhdeen yake ta buga ƙofar yana ƙiran sunanta amma tayi kunnen uwar shegu, sai gajeren wandon ta da ta sanya wanda ya tsaya mata iya cinya sai best mai hannun breziyya ta haura saman gadonta ta mimmiƙe yau kam ba zuwa school tayi fushi da Uncle Deen ganinsa da wata, abinda yafi ƙona mata rai shine rungumarta da yayi kamar zasu haɗe kuma duk maganganun da Razhdeen ya faɗa wa Baiwar Allah a kunne babu wanda ya ji mai yake faɗa mata sai ita,

Razhdeen ganin bazata buÉ—e ba yasa shi koma wa part É—insa...

★★★★★★

Baiwar ALLAH bayan komawar ta gida tana shiga falo ta tarar da Roshan zaune daga shi sai Three quarter da singlety yana facing ɗin plasman, jin sallama yasa shi kallon bakin ƙofa yana binta da kallo,
jiki a sanyaye ta je har gabansa ta durƙusa ta gaishe shi zuciyar ta bugun uku-uku domin bata son yasan taje gidan Razhdeen,
Amsa wa yayi cikin murmushi tare da riƙo hannunta ya ɗagota ta faɗa jikinsa,
Ya ce "Ammata ina kike je ne da sassafen nan ko kammala breakfast bakiyi ba..."

tunani ta fara yi shin me zata ce masa gashi bata iya ƙarya ba, ganin bata da abun cewa ne yasa ta ɗagowa suna kallon juna tasau murmushi tare da faɗin "Kayi haƙuri my D..."

shima murmushi ya sake mata tare da sumbatar ta a kan lips ya ce "it's okay..."

tana kwance akan sa ya ce "tashi muje muyi breakfast..."

Tashi tayi ba musu suka nufi dinning ganin kuloli a jere kan dinning ta tsaya tana kallonsa gira a haÉ—e ta ce "kar fa kace kai ka haÉ—a breakfast?..."

Murmushi ya yi sannan ya ce "to wa kike tunanin zai yi?..."

tunawa tayi da lokacin da suka fara shiga kitchen tare da gishirin da ya zabga musu a abinci a fili ta ce "yau ma abinci bazai ci yu ba..."

Zaro ido ya yi ya ce "ban gane ba, kina nufin ki ce duk shiga kitchen É—in da nake yi har zuwa yanzu ban iya komai ba?..."

Baiwar Allah tayi gaba tare da faÉ—in "shikenam muje nayi testing..."

Murmushi yayi ya bi bayan ta, suka jeru a dinning shi da kansa ya zuba musu abincin, cukali É—aya Baiwar Allah tayi ta ce "wow my D na baka award..."

Yana caccakar indomie ya ce "Ni yanzu kyautar abu ɗaya zaki mun nasan kin mun kyautar da bazan taɓa manta wa ba har ƙarshen rayuwata..."

Baiwar Allah ta dakatar da yin breakfast ta ce "wani irin kyauta ne haka?..."

Wani irin kallo yake mata na so da ƙauna murya ciki-ciki ya ce "yaushe zaki kammala period ɗinki?..."

Baiwar Allah ta ce "Ohhhh shine kyautar daman?..."

Ya ce "Please Ammata am asking you, wallahi a duk sanda na kasance dake ji nake bani da kwanciyar hankali, gaba É—aya hankali na tashi yake, Ammata i need you..."

Kwashewa tayi da dariya ganin yanda ya zamo kalar tausayi, ta ce "haba D ka kwantar da hankalin ka remain 5 days..."

A ruÉ—e ya ce "whattt?..."
har sai da ta tsorata ta ce "meya faru Yaya Roshan?..."

Ya ce "naji kin ambaci 5 days, shin har kwana nawa kike yi ne?..."

Dukan ƙirjinsa tayi tana faɗin "har ka tsoratar da ni, 7 days nake nake yi, yau nayi 2 days remain 5...."

Jinjina kai ya yi sannan ya ce "jiya Abbah ya sanar mun cewa gobe na tafi ƙasar Jidder ganin Yarinyar..."

Baiwar ALLAH ta ce "daman baka santa ba ne?..."

Girgiza kai ya yi sannan ya ce "Ramlat ce wai zamu ƙara fahimtar juna ne..."

Lokaci guda Baiwar Allah taji wani bugun zuciya na tsananin kishi, hawaye ne yake shirin kuɓuto mata tayi saurin kawar da kanta gefe tana share wa..."

Roshan riƙo hannun ta yayi tare da faɗin "meya faru ne?..."

Juyowa tayi a wayance har da murmushin yaƙe ta ce "babu komai amm ya kamata ka fara shiri tin yanzu ko saboda nasan fitan sassafe zakayi..."

Tashi tana cewa "muje na taya ka shirya kayan..."

Riƙo hannunta yayi tare da zaunar da ita akan kujerar dinning ya ce "zauna mana tukun..."

Ta zauna tana fuskantar sa cikin zuciyar ta kuwa kamar ana hura wuta...

Idonsa akan ta ya ce "bazan tafi ba sai na jira kin mun kyautar da bazan taɓa manta wa ba..."

Baiwar Allah kamar zatayi kuka ta ce "zaka iya jira har kwana biyar baka tafi ba?..."

Ya ce "ke fa rayuwata ce, me zai hana na jira..."

Dasauri ta girgiza kai tare da faÉ—in "bazai yu ba saboda zuwa lokacin Auren ka yazo, kuma bazai yu ace har zuwa lokacin Aure baka je ka gano Amarya ba, hakan kuskure ne..."

Cije lips ɗinsa yayi na ƙasi har cikin zuciyarsa ba son Auren yake ba shima just saboda ba yanda ya iya ne...
Ya ambaci sunan ta a hankali "Ammata..."

ÆŠagowa tayi tana kallonsa bata san lokacin da hawaye yake shirin gangaro mata ba,
jawo ta yayi jikinsa ya riƙo gefe da gefen fuskarta suna fuskantar juna lokaci guda hawaye suka gangaro mata a duk ɓangare biyun, haka yasa harshensa yana lasar hawayen fuskar ta, tas sai da ya gama sannan yakai ɗan ƙaramin bakinsa kan nata ya fara sunbatar ta cikin salo da ƙware wa, cikin lokaci ƙanƙani ya cire mata damuwar da yake shirin wanzuwar mata,
Chapter 1 · 0% Book details