← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 68

Sashe 43

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai Madam Parveen da ta tada hankalin ta sai da suka fice daga gidan tukun hankalin ta ya fara kwanciya,
Duk airport suka nufa Madam Parveen da Chief a mota É—aya, sai Mohandas da Minal a mota É—aya, Rakesh da Rukky a mota É—aya duk suka tafi don ko Æ´an rakiya basu nema ba...

Abbah ne ya taso yazo gaban Reemah shima ya É—ora hannun sa akan goshin ta, girgiza kai yayi sannan ya kalli Roshan ya ce "Roshan zo ka kaita room É—inta jikinta ya É—au zafi..." bayan sun tottofa mata Addu'o'i...

Mai martaba ne ya ƙira Ummy yana faɗin "Uwar masu gida zo ki karɓi yarinyar nan..."

Ummy jin haka yasa ta zille ta bar falo babu wanda ya sani sai gani akayi bata nan....

Roshan wuce wa yayi da Reemah cikin ɗaki, idonsa akan ta domin bai taɓa tunanin tana cikin wannan matsalar ba..

Abbah ya ce "to ke Auntyn yara zo ki karɓe ta tinda uwar masu gida bata nan..."

Aunty Yolash sai da taji wani rass, kallon jaririyar tayi tare da haɗiyar yawu tana murmushin yaƙe ta ce "ai matsala tayi baƙin jini a wurin bil'adama, kar kana zaune kaji an yaƙe maka wuya..."

tana kaiwa nan bata jira an furta komai ba tayi saurin barin falon itama...
Hajiya Kilishi ganin ta haɗa ido da Abbah yasa ta faɗin "laaa! nabar girki akan wuta, nasan yanzu ya ƙone wayyo..."
itama da gudu tabar falon ta nufi kitchen, tayi hakane saboda tasan ita za'ace ta É—auki yarinyar...

Ammy murmushi tayi ta je tasa hannu ta karɓi Afaf daga hannun Mai martaba..

Mai martaba ne ya ce "to ku ƙira mun Uwar masu gida tazo mu ma zamu koma tinda an gama komai..."

Aunty Maimuna ta ce "to ita Reemah fa?..."

Mai martaba ya ce "indai zamu tafi da Reemah to dole tare da jaririyar zamu tafi..."

Abbah ya yi murmushi sannan ya ce "Ku bar mun Reemah kawai zata cigaba da zama anan..."

Mai martaba ya jinjina kai anan suka yi sallama suma suka tafi, Ummy duk son da take wa Afaf da ta zo tafiya bata bari ta kalle ta ba ma haka su ma suka tafi..."

Ramlat ai tin lokacin da Roshan ya shiga da Reemah ciki babu wanda yasan lokacin da ta fice daga falon, cikin tsoro da fargaba ta nufi part ɗin ta, tana zuwa ta shige bedroom tasa key, wani irin nannauyar numfashi take fitar wa tana hasasho yanayin da ta ga Reemah, haka jikinta yake ɓari tana kakkarwa...

★★★★★

Chief da iyalan sa suna koma wa ƙasar U.S kowa ya ɗauki matar sa ya tafi da ita gidansa,
Chief da Madam Parveen ne kawai suka sauƙa a wantalelen gidan su, sojoji ne guda uku suka nufi yanda motar su take, bayan sun yi musu Barka da dawowa anan suka sanar cewa sunyi baƙuwa amma basu barta ta shigo ba...".

Madam Parveen ta ce. "aina take?..."

Suka ce "tana É—akin visitors room yau kwana biyar da zuwan ta..."

Chief ne ya bada umarnin a kawo ta, kafin nan suka wuce ciki,
Madam Parveen tana shiga falon su ta jefar da handbag ɗinta akan sopa ta zauna tare da ɗora hannayenta biyu akanta sai zubda ƙwallah take cikin damuwa da tashin hankali...

Chief ne ya zauna kusa da ita ya É—ora hannunsa akan kafaÉ—a tare da rungumar ta yana rarrashinta cikin kulawa.
suna cikin wannan halin suka ji ana knocking, bada umarnin shugowa akayi wani soja ne ya shigo tare da faÉ—in "Sir gata nan..." duk da yaren turanci suke magana domin in har suka zo gida basa Hausa kwata-kwata.

Madam Parveen saboda tsananin damuwa ko ɗagowa bata yi sai Chief ne ya ɗago, idonsa ne ya sauƙa akan Baiwar ALLAH wacce ta shigo tana sanye da manyan kaya ta ɗage niƙab ɗinta sama,
A zabure Chief ya miƙe tsaye tare da faɗin "Daughter...."

Madam Parveen jin haka yasa itama ta zabura ta tashi tsaye tana kallon bakin ƙofa, buɗe baki tayi a ruɗe ta ce "Amreesh?.."
Da gudu ta nufi bakin ƙofa tana zuwa ta rungume ta sosai, itama Baiwar ALLAH rungumar mahaifiyar ta tayi tana kuka..

Sai da suka gama koke-koken su tukun suka ƙaraso ciki, Madam Parveen ce ta zaunar da ita tana hawaye ta ce "Amreesh ina kika shiga ne, kin bar mana Baby Aljanu sun mallake ta..."

Baiwar Allah tana kuka tasa hannu tana goge hawayen Mommynta murya na kakkarwa ta ce "Mom kuyi haƙuri, ba'a son raina bane, hankali na bazai taɓa kwanciya ba idan ina tare da Babyna, gwara na nisanta kaina da ita ko zan samu sassauci, kullum ina cikin damuwa da tashin hankali, Mom na bar musu ita..."

Madam Parveen rungumar ta tayi tana faɗin "it's okay my Daughter, stop crying okay, zaki cigaba da zama a wurin iyayen ki kema, ki bar musu yarinyar Insha Allahu zata kasance cikin ƙoshin lafiya..."

Chief shima murmushi yayi tare da faɗin "Daughter taya kika zo nan ƙasar ke kaɗai?..."

Baiwar Allah tashi tayi taje ta zauna a kusa da Daddynta ta rungume shi tana dariya ta ce "Dad inda kuɗina ina ne bazan je ba, idan na sauƙa a ƙasar nan gidan ka ba ɓoyayye bane domin kai ɗin ba ƙaramin mutum bane..."

Murmushi ya yi ya ce "Ma sha ALLAH, yanzu dai bari na ƙira can Nigeria na sanar musu cewa My Daughter tana tare da mu..."

Baiwar Allah kamar zata yi kuka ta ce "Dad kada ka sanar musu domin ni bazan koma ba kuma bana so a kawo mun Baby..."

Chief ya ce "zan sanar musu saboda hankalin su zaifi kwanciya..."

Chief sanar musu yayi, Abbah ba ƙaramin farin ciki yayi ba, sai da ya nemi haɗa su da Baiwar ALLAH,
Daƙer Baiwar ALLAH ta karɓa cikin jin kunya ta ce "ina wuni Abbah..."

Cikin nuna farin ciki ya ce "Daughter kin tsoratar damu sosai, fatan kina lafiya..."

Ta amsa masa, Abbah ya ce "kar ki damu zamu kula miki da yarinyar ki..."

Baiwar Allah miƙawa Chief tayi wayar ta juya kan Mommynta tare da kifar da kanta akan ƙirjinta tana kuka...

Da haka wannan rububin ya wuce yanzu Baiwar Allah itama ta koma gida...

★★★

Reemah kuwa ta samu Jaririya a bononza kullum ita take rainonta, sai kuma Roshan da yake karɓar ta,
Ramlat kuwa duk inda Afaf take bata zama a wurin, idan Roshan ya tafi da ita part É—insa to kuwa Ramlat zata baro part É—in...

★ One Year ★

Wasu zura-zuran motocin sojoji ne kusan guda hamsin suka baro airport kai tsaye gidan General suka nufa,
A ƙofar gidan General kuma wasu sojoji ne da baƙin fuskoki duk suke tsatstsaye aciki har da Roshan da Abbah da wasu mutane daban, ƙofar gidan da ciki duk a cike suna jiran taryar babban baƙo wato Razhdeen wanda sai wannan lokacin Allah ya bashi damar dawowa tsawon shekara......

Typing ✍️ Asmeetah writer

*MY ENEMY*

*TAKUN ƘARSHE*

*BOOK 3*

66 to 70

Wasu zura-zuran motocin ne suka yi parking a wajen gidan General, sojoji ne suka firfito daga bisani wani soja ya buɗe murfin wani zureren mota dake tsakiyar motoci, wanda yake ciki ne ya zuro da ƙafarsa wanda yake sanye da ƙaton takalmi irin na sojoji, sai da ya ɗan juma tukun ya fito gaba ɗaya yasa sanye da baƙin glass akan dara-daran idanuwansa, ga yayi wani irin fari na hutu wanda rana baya taɓa shi, sumar kansa ya koma yanda yake kamar ba'a taɓa aske shi ba har ya wuce kafaɗarsa, ga sajen nan ya kwanto luf akan kyakkyawan fuskar sa wanda yake ta shining, lips ɗinsa yanda kasan ya shafa lip glow sai sheƙi yake tayi ga ya ci red sosai, ba ƙaramin kyau Razhdeen ya yi ba, yana sanye da wandon sojoji na ƙasar U.S da baƙar riga mai high neck da dogon hannu sai kuma sweater da ya ɗora akai.
Yana tsaye a jikin motar da ya fito yana bin kowa da kallo, idonsa ne ya sauƙa akan Roshan wanda ya nufo shi da murmushi akan fuskar sa, yana zuwa suka rungumi juna sosai cike da kewar juna,
Roshan ɗago wa yayi da fararen haƙwaransa ya ce "My Man your welcome..."

Razhdeen shima cike da murnar ganin twins É—insa ya ce "thanks my twins..."

Suna cikin ganawa da juna sai ga Abbah ya zo wurin yana faÉ—in "Deen saboda ka haÉ—u da twins shine ka manta da Dad?..."

Murmushi ya yi sannan ya rungumi Abbah tare da faÉ—in "i missed you my Dad..."

Abbah shima rungumar sa yayi yana bubbugan bayansa ya ce "me too my Son, ku ƙarasa shiga gidan..."

Razhdeen da Roshan a tare suka shiga mota aka shigar da su cikin gidan....

A babban falo Hajiya Kilishi da Ammy ne zaune a kujera sun sha fashion shigar gizner doguwar riga iri ɗaya, ga Ramlat itama ta sha danƙareren less mai ɗinkin bu ba ga cikin ya girma haihuwa yau ko gobe, tasha ɗaurin ɗankwali da yafin gyalen ta fari akan kafaɗa tana zaune da su Hajiya Kilishi,
Ta ko ina an gyara tsab-tsab an canza kayan furnitures na ɗakuna saboda dawowar Razhdeen, ga girke-girke na musamman da akayi duk aka jejjera akan dinning, dake Abokan Razhdeen sojoji su ma sun zo, da waɗanda suka yo rakiyarsa, gidan ya cika da manyan baƙi sojoji...

Roshan da Razhdeen ne suka shigo falo da sallama a bakin su, duk waɗanda suke falon miƙe wa tsaye sukayi cike da farin cikin ganin Razhdeen, kowa masa sannu da dawowa yake da taya shi murnar samun lafiya, zama suka yi duk wanda ya gaishe shi cikin fara'a yake amsawa, gaba ɗaya Razhdeen ya sauya kamar ba Uncle Deen ba, yau shine yake murmushi abun ya bawa kowa mamaki ganin Razhdeen sai zabga murmushi yake ga ya ƙara kyau kamar asalin Balarabe, kowa bai san lokacin da ya tsinci kansa cikin farin ciki ba ganin yanda shima yake cikin farin ciki....
Chapter 43 · 0% Book details