← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 68

Sashe 10

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummy itama a wannan ranar ba ƙaramin shiga damuwa tayi ba ganin halin da Uncle Deen da Baiwar ALLAH suka fa ɗa, kowa sai tambayarta yake meke faruwa amma ta kasa sanar wa kowa, hatta mahaifiyar ta ma ƙin gaya mata tayi,
A lokacin da mutanen gidan suka ji labarin hatsarin Razhdeen kowa gagara zama yayi haka duk suka nufi hospital, koda suka je ba'a barsu sun gànshi ba saboda a halin da yake ciki baza'a so wani ɗan uwansa ya gànshi ba, hatta likitocin tsammanta masa mutuwa suke...

Duk suna asibiti babu wanda aka bari a gida,
Rukky fashewa tayi da kuka tana bugan Pinky tare da faÉ—in "kinga duk mu muka jawo, sai da nace kada muyi wannan aikin amma kika dage gashi nan yanzu É—an uwan mu zai mutu ata sanadiyar mu...."

Pinky ta ce "dallah wa ya gaya miki saboda mu yayi hatsarin? Allah ne ya aiko kuma babu wanda ya isa ya tsallake ƙaddarar sa..."

Rukky ƙasa-ƙasa take da murya ta ce "kinsan fa Yaya Roshan ya kamasu, nasan saboda damuwar nan ne yasa Uncle Deen hatsari kuma in ba sa'a ba bazai tashi ba..."

Pinky ta ce "shikenam idan ya mutu Baiwar Allah babu wanda zata samu a cikin su, tinda nasan Roshan bazai ƙara kusantar yanda take ba, shi kuma Uncle Deen yabar duniya..."

Rukky ta sauƙe numfashi tare da faɗin "ke fa bakida imani wallahi, Ni banga ribar hakan ba, wallahi zan daina biye miki muna aikata ɓarna, yanzu sai alhakin su ya kama mu...."

Pinky tsuka taja sannan ta wuce tabar Rukky a wurin...

Su Mommy da Ammy dasu Aunty Yolash basu bar asibiti ba har dare misalin ƙarfe 9 amma basu samu ganin Razhdeen ba, a wannan lokacin ne Abbah ya zo hospital da motar sojojin sa ƴan rakiya, a ruɗe Abbah ya shigo yana faɗin "aina aka kwantar da Razhdeen?..."

Aunty Yolash ta ce "yana emergency room har yanzu basu bar kowa ya gànshi ba..."

Abbah a firgice ya nufi hanyar É—akin da aka kwantar da Razhdeen cikin sa'a sai ga Doctor ya fito daga room É—in,
Abbah ne ya tsayar da shi tare da tambayar sa Razhdeen.

Doctor girgiza kai yayi sannan ya ce "a gaskiya har zuwa yanzu bamu iya ceto shi ba..."

A ruÉ—e Abbah ya katse shi da cewa "ban gane baku ceto shi ba, shin me kuke nufi, dan Allah kada ku sanar mun yarona ya mutu..."
Abbah ya ƙarasa maganar yana kuka..

Doctor rarrashinsa yake yana faɗin "har yanzu da sauran bugun zuciyar sa amma gaskiya bazai wuce wasu sa'o'i ba indai ba'a tare shi da wuri ba, kuma kamar ƙwaƙwalwarsa ta ɗan taɓu, koda ya farfaɗo ma dole sai ya ɗau dogon zango kafin ya iya dawo hayyacin sa...."

Abbah a firgice ya ce "to me kuke jira da bazaku fara masa abinda ya dace ba?..."

Doctor ganin yanda Abbah ya ruɗe ne yasa shi cewa "ka kwantar da hankalin ka Chief Insha Allahu zai tashi, akwai abinda bamuda shi a wannan hospital kuma dole sai da shi zamu iya ceto rayuwar sa, abun babu a Nigeria gaba ɗaya amma mun aika can ƙasar misrah zuwa nan da wasu mintuna jirgin zai iso..."

Abbah yana zubda ƙwallah tinda har aka fara masa wannan lissafe-lissafen yasan ba ƙaramin ciwo bane,
Ya ce "Doctor please idan kunsan bazaku iya dawo mun da yarona cikin hayyacinsa ba tin wuri ku sanar mun na fita dashi ƙasar waje..."

Doctor ya ce "musamman muka aika can ƙasar waje akan muna buƙatar ƙwararru likitocin da zasu taya mu duba shi, suna nan tafe..."

Abbah ya ce "yanzun yana ina?..."

Doctor ya ce "amma sai dai ba'a barin kowa ya gànshi..."

A fusace Abbah ya ce "idan kun hana kowa ganinsa ni baku isa ku hanani ganin É—an cikina ba..."
Doctor ya ce "hakane mu shiga kawai..."

A tare suka shiga room É—in da aka kwantar da Razhdeen,
Abbah yana ido huɗu da shi zuciyar sa tayi wani kyakkyawan bugawa da ƙarfin gaske ganin halin da Razhdeen yake ciki...

A ruɗe Abbah ya ƙarasa wurinsa yana ambaton sunan sa,
Razhdeen an É—aÉ—É—aure gaba É—aya kansa da bande ji, har da fuskar sa, gaba É—aya dai duk jikinsa an zagaye da bandeji domin ko ina na jikinsa yaji ciwo, an sanya masa oxygen sai bugun zuciyar da yake É—an harbawa da kaÉ—an-kaÉ—an domin duk bugun zuciyar sa ana gani ta cikin computer dake manne a jikin bango, da zarar bugun zuciyar ta tsaya shikenam computer zai daina aiki shima,
Kuma dole sai anyi masa aiki a ƙwaƙwalwarsa wannan gashin kan nashin ana buƙatar Aske shi gaba ɗaya...
Abbah ne ya kifa kansa a bakin gadon sai sharar kuka yake, yana cikin wannan halin sai ga su Aunty Yolash sun shigo da sauran Æ´an gidan,
Duk wanda yaga Razhdeen sai ya zubar masa da hawaye, hatta suma Pinky da Rukky fashewa sukayi da kuka, basu yi tinanin hatsarin har ta kai haka ba, Ummy uwar masu gida zuwa tayi ta rungumi Abbah tare da fashewa da kuka tana faÉ—in "Abbah dan Allah kar Uncle Deen ya mutu, shikenam ya mutu ko? meyasa zai tafi ya bar mu muna sonsa sosai..."

Daƙer Abbah yake rarrashin Ummy domin muryar ta tafi fitowa, daƙer Abbah ya kora su gida, duk shiga mota sukayi akayi driving ɗinsu zuwa gida, iya Abbah ne kawai ya rage a hospital...

Can misalin ƙarfe 10 na dare likitoci ne ƴan ƙasar waje sunfi biyar duk akan Razhdeen ga na cikin hospital ɗin,
Abbah yana daga waje zaman jiran su, kwatsam Roshan ya faɗo masa a rai, kuma Doctor ya sanar masa cewa tinda aka kawo Razhdeen bai ga Roshan yazo ba, sai abun ya bawa Abbah mamaki, zaro wayarsa yayi yana ƙiran wayan Roshan amma ba'a picking, ya ƙiƙƙira security gidan yana tambayar su Roshan amma kowa sanar masa yake da ba'a san yanda yake ba...

Abbah ganin tambayar bazai kai shi ba yasa yayi tracking number sa a wurin da wayar ta nuna masa Roshan yana wajen abun ba ƙaramin ɗaure masa kai yayi ba, domin alamun a jeji yake...

Abbah ƙiran wasu sojojinsa yayi ya sanar musu cewa suyi tracking number Roshan suje su same shi a yanda yake a cikin daren nan...

Sojojin amsa masa suka yi a lokacin suka nufi hanya suna bin yanda wayan sa yake ta hanyar tracking...

★★★★★★

Baiwar ALLAH kuwa farfaɗowar ta ke da wuya haka ta tashi da matsanancin ciwon kai da zazzaɓi tsabar kukan da tasha ga damuwa, haka jikinta yake kakkarwa gaba ɗaya ta zamo wata kala kamar ba Baiwar ALLAH ba, duk ta rarrame lokaci guda, daƙer ta tashi tana ɗingishi ta shige toilet tayi wanka sannan ta ɗauro alwala ta fito tana jan ƙafa jiki duk ba ƙwari, saka kayanta tayi doguwar riga marar kauri sannan ta zura hijab tare da shimfiɗa sallaya ta tsaida sallah, duk sallar da ya wuce ta sai da tayi su a ranar yau, sannan ta haɗa da lafula sujjadar ƙarshe da tayi ta juma bata ɗago ba tana jero Addu'o'i tare da neman gafarar Ubangiji, haka take kuka tana addu'a, har zuwa yanzu hawayen ta maimakon kaga ruwa sai jini, ta juma sosai kafin ta ɗago fuskar nan yayi jagab da hawayen jini,
tashi tayi tana mai ƙara fashewa da kuka domin idan ta tuno da abinda ya faru yau sai taji kamar ta kashe kanta domin zaman duniyan ya ishe ta haka, zamar da hijab ɗinta tayi tare da durƙusa da gwiwowinta tana ambatar sunan Razhdeen tare da faɗin "meyasa zaka yi mun haka Razhdeen, ka cutar da rayuwa ta Razhdeen bazan yafe maka ba duniya da lahira, na tsane ka bana ƙaunar ganin fuskar ka wallahi, kaji daɗi ka rabani da mijina, ina son Roshan har cikin zuciyata amma lokaci guda an rabani da shi, da wani ido zan kalli Roshan? da wani ido zan kalli Abbah, da wani ido zan kalli sauran mutanen gidan wayyo Allah nah, na shiga uku Ya Allah ka ɗauki rayuwa ta cikin gaggawa, innalillahi wa inna'ilaihi raju'un zina! zina!! zina!!!,
yau ni ce wai na aikata zina? da igiyar Aure nah 😭...."

Haka take ta wannan surutan tana kuka gaba ɗaya ta jiƙe gaban rigar ta da kukan jini,
haka ta tashi ta nufi wurin mirror haka ta tsaya tana kallon kanta, ganin yanda jini yake tsiyayo wa daga cikin ƙwayar idanuwanta yasa ta daki jikin madubin da hannunta, haka take dukan madubin da hannayenta biyu tana ihu kamar ranta zai fita,
Gaba É—aya duk ta dagargaje madubin da hannunta ga hannun yanda yake jini tsabar yayyankewar da tayi...

Aunty Yolash ce ta shigo falon tana sallama jin shiru sai ihun da take taji a cikin ɗakin Baiwar Allah yasa ta nufi ɗakin da sauri, tana buɗe wa taga yanda Baiwar ALLAH take ta ruso da kayayyakin ta ƙasi, haka ta jawo wardrobe ya doku a ƙasi duk ta fiffirgice ɗakin ta faffasa abun fashe wa still tana ihu bata dakata ba.....

Aunty Yolash ganin aika aikan da Baiwar Allah take ne yasa ta nufi ciki da gudu ta rirriƙe ta tana faɗin "lafiyar ki ƙalau kuwa Daughter? kin haukace ne? ki duba kiga yanda kika ji wa kanki ciwo a hannu...."

Baiwar ALLAH girgiza kai take tana kuka na fitar hayyaci,
Aunty Yolash ganin yanda take kukan jini yasa ta sakin baki tare da zaro ido waje tana faÉ—in "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Daughter me zan gani haka, kukan jini fa kike wayyo Allah...."

Haka Aunty Yolash ta rungume ta sosai a jikinta tana rarrashinta...

★★★★★★

Roshan kuwa an same shi a wurin da yake a kwance ko motsi baya yi, ruwan sama ya gama jibgar sa ga zuciyar sa yanda yake kawo masa hari, sojojin nan haka suka ɗauke shi ba yanda yake kai tsaye hospital suka kai shi domin a halin da yake ba buƙatar kai shi gida domin bakinsa haka take fitar da jini...

Hospital ɗin da su Razhdeen suke nan aka kaishi shima, a wannan daren Abbah yana ganin sojojin sa ɗauke da Roshan yasa zuciyar sa bugawa da ƙarfi, a firgice ya miƙe tsaye yana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un me yake faruwa dani ne kam? Roshan again?...."
Chapter 10 · 0% Book details