← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 68

Sashe 55

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƴar Amana da sauri ta miƙe tsaye daga zaune tana ƙoƙarin barin falon bata ankara ba taji sauƙar ruwan nan akan ta, faɗuwa ƙasi tayi tana ihu tare da burburwa domin ji take kamar ana watsa mata ruwan asir a jiki tsabar zafi da ƙuna, a wannan lokacin Roshan ma baya jinta bare ganinta, daƙer shima ya zauna bayan ya daina jin sautin kukan ta,
haka take ja daƙer tana matsawa dab da Roshan domin bazata iya tashi ba, tana zuwa dab da Roshan ta ɗora hannunta akan ƙafar sa tana faɗin "ka taimake ni, ka taimake ni! ka taimake ni..."

Roshan wani irin shocking yaji ya bi jikinsa a zabure ya ƙanƙame Razhdeen wanda shine a kusa da shi sai Abbah dake ɗayan ɓangaren sa duk sun saka shi a tsakiya saboda kar ya tafi,

Ruwan nan haka yake sauƙa akan ta fatar jikinta har yayi jawur, inda asalin aljana ce shigewa jikin wani zata yi a cikinsu tayi magana amma Ƴar Amana bazata iya shiga jikin kowa ba sai dai aita gana mata azaba da wannan ruwan, ganin tana shirin shiɗewa shi kuma Roshan jikinsa ne yake ƙakkarwa kamar wanda aka jona masa shocking sai da Abbah da Razhdeen suna rirriƙe shi, a tunanin kowa aljana ce ta shige jikinsa, duk wannan abunda yake hannun Ƴar Amana ce akan ƙafarsa azabar da take ji shima haka yake jin hakan,
Ƴar Amana tinin ta sume a wurin tana kwance sai ga wani haske kamar walƙiya an ɗauke ta sai kuma aka turo wata aljanar da zata maye gurbin Ƴar Amana a wannan halin domin an ɗana tarkon da aljana bazata iya kuɓuta ba, Aljanar tana bayyana ta shige jikin Roshan amma sai dai aljanar da aka turo kurmiya ce bazata iya yin magana ba sai dai aita gana mata azaba domin turo mai baki zai sa taji azaba ta faɗi wata gaskiyar da ake ɓoyewa,
Roshan jin an shige shi yasa shi sakin dogon numfashi haka ƙirjinsa yake sama da ƙasa, ɗauke Ƴar Amana yasa ya daina jin shocking, yanzu kuwa baya cikin hayyacinsa gaba ɗaya........

*ASSALAMU ALAIKUM*
*BARKAN KU MASOYA DAN ALLAH INA MAI ƘARA BAKU HAƘURI AKAN JINKIRIN UPDATE, AKWAI AIKIN DA NAKE ZUWA TIN SAFE BANA DAWOWA SAI YAMMA KUSAN MANGARIBA, IDAN NA DAWO KUMA BA LOKACI NAN MA A GAJIYE GA BACCI SHIYASA BANA SAMUN YIN TYPING, KUYI HAƘURI YAU DAI BA AIKI PAGE BIYU ZANYI MUKU NAGODE.....*

Typing ✍️ Asmeetah writer

*MY ENEMY*

*TAKUN ƘARSHE*

*BOOK 3*

86 to 90

Ba irin maganin da ba'ayi ba akan Aljanar tayi magana amma sam ko gyaran murya bata yi ba, Roshan gaba ɗaya ya bi ya ƙaƙƙafe ko motsi baya iya yi, anan Malamin ya fahimci Aljanar kurmiya ce, a lokacin sai ya fara ƙoƙarin cire ta daga jikinsa, cikin ƙanƙanin lokaci aljanar ta gudu domin ba ƙaramin azaba take sha ba, tana fita Roshan ya dawo hayyacinsa daga nan sai ya wuce da yin bacci,

Abbah ya ce "ina Reemah take kuma?..."

Malamin yayi murmushi tare da girgiza kai ya ce "ai ba zasu barta a yanda za'a ganota ba, sun É—auke ta..

Abbah dafe goshin sa yayi yana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, wannan wani irin masifa ce da ƙalubale, Allah ka kawo mana ƙarshen wannan al'amarin..."

Malam ya ce "Insha Allahu zata bayyana amma sai mun dage da roƙon Allah, babu abinda yafi ƙarfin Allah, shi kuma Roshan a halin yanzu yana buƙatar hutawa zan baku maganinnuwan da zai rinƙa amfani da su da kuma turare Insha Allahu zasu yi nesa da shi..."

Abbah ya ce "ga shi Roshan baya son magani da ya shafi na hayaƙi ko jiƙo ko rubutu ban san ya zamu kaya ba..."

Malam ya ce "indai kuna son samun lafiyar sa haka zaku daure ku saka shi dole yayi amfani da su..."
Abbah ya ce "shikenam ba damuwa Allah yasa a dace..."
Malam ya amsa masa da Amin sannan ya ba shi maganin daga bisani ya yi tafiyar sa...

Roshan kuwa gyara masa kwanciya akayi aka miƙar da shi akan doguwar kujera tare da lulluɓe shi da mayafi, anan aka bar shi a falo yake ta shan baccin sa,
Duk mutanen gidan daga manyan har yaran gidan babu mai farin ciki kowa fuskarsa É—auke da damuwa,
Ammy ce ta ɗauko kasko ta haɗa hayaƙin da malam ya basu taje tana karawa a jikin Roshan, haka ta bi ko ina lungu da saƙo tana bi da hayaƙi har ɗakin Roshan ta shiga ko wani ɗaki babu yanda bata shiga ba...

A cikin kwana biyun nan Roshan bai ƙara jin motsin Ƴar Amana ba, ya koma normal yanda yake, magani kuwa Abbah daƙer yake saka shi a gaba ya sha da hayaƙi da turare, ganin yanzu Roshan baya wasu abubuwa kamar mahaukaci yasa hankalin kowa kwanciya, ana tunanin yanzu ya samu sauƙi, daman Ƴar Amana ce take rikita shi yanzu kuwa bata nan, dalilin da yasa bata zuwa masa shine itama tana can tana jinya, maganin da aka wawwatsa mata ne yasa ta fita hayyacinta, tinda ta suma bata ƙara farfaɗowa ba tana hannun aljanun ta, yanzu tsawon satin guda,
Kullum Roshan a cikin tsammanin ganinta yake domin ya damu sosai da rashin ganin spirit É—inta...

Bayan sati biyu Roshan ne ya tashi da safe yayi wanka ya shirya tsab cikin blue jeans da white T-shirt mai dogon hannu, ya sanya cover shoe ɗinsa mai white colour ya feffeshe jikinsa da turaruka kala-kala, ya gyara sumar kansa sai sheƙi yake sannan ya ɗauki agogonsa mai bala'in tsada ya ɗaura a hannunsa ya buɗe gidan glass ya ciro white glass ya sanya akan dara-daran idanuwansa ba ƙaramin kyau yayi ba,
Ta bayan sa kuwa Ƴar Amana ce take tsaye ta zuba masa ido ga sumar kanta a baje har gadon baya, sai dai a wannan lokacin bata fito masa a yanda zai ganta ba, ta miƙe itama daga jinyar da ta sha, tana tashi babu wanda ta fara sawa a rai sai Roshan hakan yasa ta bayyana domin taga kyakkyawar siffar shi...

Murmushi tayi sannan ta ce "Yaya Roshan kayi kyau sosai, bana son Æ´an mata su gane mun kai dole zan zana maka alamar da zai nuna cewa kai mijin wata ce..."
Yana tsaye a gaban mirror ta zo dab da shi ta bayansa da baƙin maker a hannunta ta rubuta masa (MIJIN ALJANA) ga rigar asalin fari ne sai rubutun ya fito sosai wanda ko daga nesa za'a iya karantawa,
Dai-dai lokacin da ya kammala shirin sa ya É—auki jakar sa na zuwa wurin aiki hospital ya fice daga cikin É—akin, itama bin bayansa tayi suka fita a tare,
Yana sauƙa falo ya tarar da kowa da kowa sun hallaru akan dinning daman shi kaɗai ake jira, da murmushi ya isa wurin yana faɗin "good morning to you all..."
duk suka amsa masa,
Abbah ne baya nan yana can falonsa da baƙi,
Madam Parveen da Aunty A'isha kuwa su sun daɗe da komawa sai da Abbah ya roƙi Aunty A'isha akan kada ta sanar wa mai martaba halin da ake ciki na ɓatan Reemah,

Roshan zama yayi shima suka fara breakfast, bayan ya ɗan taɓa abincin ya tashi yana goge bakinsa domin sauri yake zai fita, sallama yayi musu ya juya zai tafi,
Ummy ce ta fara ganin rubutun bayan sa ta ce "innalillahi Yaya Roshan haka kuma..."

Duk sauran juyawa suka yi suna kallon sa, lokacin shi kuma ya waiwayo yana faÉ—in "kinga sauri nake sai na dawo..."
ya ƙara juyawa anan ne Kowa yaga rubutan, duk zaro ido suka yi suna kallon sa,
Razhdeen ya ce "Twins....."

Roshan É—aga musu hannu yayi ba tare da ya juyo ba ya ce "duk maganar da zaku yi ku ajiye sai na dawo..."
daga nan ya buɗe ƙofar falo yayi ficewar sa.

Baiwar Allah ta ce "ai da an sanar masa kafin ya fita..."

Razhdeen ya ce "me za'a sanar masa bayan shi ya rubuta kayansa..."

Minal ta ce "kuma sai ya rubuta mijin Aljana?..."

Hajiya Kilishi ta ce "to ba masoyiyar sa yana ganinta a mazannin aljana ba shiyasa ya rubuta hakan..."
Rukky ta ce "ai kuwa zai sha dariya kam a wurin mutane..."
Pinky ta ce "ko kuma su yi ta guduwa masa ba..."

Haka duk suka gama tsegumin su, daga baya shima Razhdeen ya tashi ba tare da ya sake furta komai ba..

Roshan yana fita harabar gidan zai buɗe motar sa sai ga su Abbah sun fito shi da wasu baƙinsa su biyu manyan mutane,
Ɗaya daga cikin baƙin ne ya karanta rubutun bayan rigar Roshan ya ce "Roshan kuwa yana da hankali?..."

Abbah ne ya kalli wurin da yake yana tambayar "me ya faru ne?..."

Mutumin ya ce "baka ga abun da yasa aka rubuta masa a bayan rigar sa ba ne?..."
Sai yanzu Abbah ya karanta cike da mamaki yake binsa da kallo ba bakin magana har Roshan ya shige motarsa ya fice a É—ari daman already an buÉ—e masa gate...

Bayan isar sa hospital yana sauƙa a harabar hospital wasu Nurse su biyu suka gaishe shi ɗaya daga ciki kuma tsananin masifar son sa take, zai wuce ta sha gabansa ita kuma ɗayar ta ɗan koma gefe anan taga rubutun bayan sa, zaro ido tayi tare da toshe bakinta da hannayen ta biyu,
Ita kuma wacce ta sha gabansa Salma tsayawa tayi tana facing É—insa,

Ya ce "lafiya kuwa?..."

Ta ce "haba Roshan meyasa kake son wahalar mun da zuciya, tin yaushe nake bin ka da soyayyata amma baka sauraro na, wannan ai wulaƙanci ne..."

Roshan sauƙe numfashi ya yi sannan ya ce "bana son wulaƙanta mutum hakan yasa bana sauraronki amma tinda ban ma kulaki ba kince ina wulaƙanta ki yanzu abinda nake so da ke ki fita sabgata, bana son raini..."

Ta ce "wallahi Roshan ko yankan jikina kake da wuƙa bazan daina bibiyanka ba, ina sonka kuma banga wanda ya isa ya rabani da kai..."

Ƴar Amana sarkin kishi tana gefe guda ta kama kunkumi idonta akan Salma dake duk yanda Roshan zai je tana biye da shi,
Roshan ya ce "ban hanya na wuce..."
Ta ce "wallahi ba inda zan matsa naje har sai ka karɓi soyayya ta..."
Chapter 55 · 0% Book details