← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 68

Sashe 59

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Razhdeen kallon Baiwar ALLAH yayi sannan ya zamar mata da gyalen jikinta dake yanada tsayi ya rabe shi gida biyu ya ɗaure sannan ya cire rigar jikinsa ya yage gida biyu ya haɗa duk ya ɗaɗɗaure duk da hakan igiyar bai isa faɗin ramin ba, ya rasa yanda zaiyi babu wata mafita haka ya cire rigar Baiwar ALLAH ya barta daga ita sai dogon wandonta da shumi (best ) dake kayan irin na larabawa ne rigar dogo ne har ƙasi sai ƙaton wando a baje,
Baiwar Allah ba ƙaramin kunya ta shiga ba ganin yanda Razhdeen ya cire mata riga a gaban Abbah,
Haka Razhdeen yasa hannu ya yage rigar kashi biyu ya haÉ—a ya É—aure, sai a lokacin tsayin igiyar ya kai.
Abbah ya ce "wai duk mai zaka yi da wannan igiyar?..."

Razhdeen ɗaukan dutsi yayi ya ɗaure da igiyar sannan ya ce wa sojojinsa "ga nan igiya zan wurgo muku ku riƙe sosai..."

Haka ya wurga musu suka riƙe shima ya riƙe igiyar daga ɓangaren sa ya kalli Abbah sannan ya ce "Dad ka zauna a bakin ramin saika riƙe igiyar ka wuce da haka..."

Abbah buɗe baki yayi yana kallon Razhdeen ya ce "amma ban taɓa sanin baka sona ba sai yau Razhdeen, taya zan riƙe igiyar nan gangan jikina a cikin rami igiya ba ƙarfi ba wanda zai iya tsinkewa..."

Razhdeen ya ce "oh my God! Dad I know what am doing, zaka wuce da yardar Allah..."

Abbah ya ce "shikenam to, idan na faÉ—a na mutu na yafe maka..."
Haka Abbah ya zauna a bakin ramin ya riƙe igiyar yayi ciki, su kuwa suna riƙe da igiyar sosai,
Daga ɓangaren Sojojin su biyu suke riƙe da igiyar, sai kuma Razhdeen wanda ya tattaro ƙarfinsa ya riƙe shima, haka Abbah yake bin igiyar yake tafe a hankali, haka yake cilla hannayensa yake kama igiyar har sai da yazo tsakiya igiyar ta fara shirin tsinkewa,
A ruÉ—e Razhdeen ya ce "Abbah too fast, kana sauri Please igiyar ta kusan yankewa..."

Muryar Abbah ne ya fara rawa yana faÉ—in "ai daman na gaya maka, so kake dai kawai na mutu, ban san me na tare maka a duniya ba..."

Nan da nan Abbah ya ƙara sauri yana isa ya riƙe bakin rami dai-dai lokacin da igiyar ta yanke, da sauri Sojoji suka riƙo hannunsa, su biyu suka jawo shi sama anan Abbah ya samu ya kuɓuce...

Razhdeen sauƙe nannauyar numfashi yayi yana hamdala,
Baiwar Allah tana hawaye ta ce "to ni É—in ya zakayi da ni? wallahi bazan iya yin irin yanda Abbah yayi ba ina kallo igiyar ta yanke, kuma bazan iya yin tsalle ba..."

Razhdeen riƙo ta ya yi cikin ɗaga murya yake sanar wa sojojinsa cewa "Guys get ready..."

Duk suka kasance cikin shiri domin sun fahimci mai yake nufi,
riƙe hannunta ya yi duk biyun ya ɗaga ta sama nan ya fara hajijiya da ita,
ba abinda take sai ihu, sai da ya yi nisa a hajijiyan da yake da ita tukun yayi wurgi da ita, bata faɗa a hannun kowa ba sai a hannun sojojin da sukayi shirin karɓar ta, ita kuwa nan da nan har ta sume a wurin,
daga baya shima Razhdeen ya tsallako,
É—aukanta yayi ya sake goyata a baya suka yi gaba,
sai da suka ɗan yi tafiya kaɗan kafin ta samu farfaɗo wa, ganinta a bayan Razhdeen yasa ta yin hamdala domin a tunanin ta ta sheƙa ne...

Shiga cikin wani kogo suka ƙara yi anan suka tarar da wani rami wanda dole sai ka shiga ciki, nan ne hanyar wuce wa, wurin tsantsi gareshi kamar lilo, idan zaka shiga sai ka zauna tsantsin wurin ya zamar da kai cikin ramin,
Abbah ya ce "wai wannan wani irin tashin hankali muke fuskanta ne? ina Roshan yake son zuwa ne kodai shima ya zama Aljani ne kam, kar muje mu kai kan mu wurin da zamu hallaka..."

Razhdeen ya ce "Dad kawai mu je..."
Sojan farko ne ya fara zama sai yayi sululu ya wuce cikin ramin, haka sojan na biyun yayi, sai Abbah bayan ya shiga sai da Razhdeen ya ɗaure bakin Baiwar ALLAH da mayafin ta da ya tafo da shi, haka ya ɗaure mata baki gamm gudun kar tayi ihu sannan ya zaunar da ita ya tura ta ciki, haka take zazzaro ido waje tana son yin ihu amma ta kasa har sai da ta je ƙarshe, shima ya biyo bayanta,
duk faɗawa suka yi cikin wani dusan ƙanƙara da hanzari suke miƙe duk suka nemi wuri suka ɓuya a cikin lawani,
Abbah da sojoji biyu suna ɓangare guda cikin lawali, Razhdeen da Baiwar ALLAH suma su biyu a gefe guda, ta gaba kaɗan kuma Roshan ne yake tsaye a bakin ruwa wanda baka iya hango ƙarshen sa,
duk bai san ana biye da shi a baya ba amma Aljanin da yake bashi hanya yasan da zuwan su sai dai bai tanka musu ba saboda shi É—an aike ne, rakiya ne aikinsa saboda haka ne yasa bai dakatar da su ba..

Abbah a cikin ransa ya ce "mai wannan yaron yake anan kuma?..."

Kowa da saƙe-saƙen da yake a ransa, duk basa son Roshan yasan da zuwan su har sai sun ga me zai aiwatar...

Roshan cikin É—aga murya ya ce "gani nazo gare ku, ku kawo mun Reemah ina nan jiran ku,
Reemah ki fito ga Yayan ki Roshan yazo gare ki..."

Duk su Abbah suna jin abinda yake faɗi suna laɓe, Baiwar ALLAH itama idonta akan Roshan bayan ta since ɗaurin bakinta,
duk idonsu akan sa cikin ƙanƙanin lokaci suka ga Ƴar Amana ta bayyana a bakin ruwa tana zaune,
Roshan da gudu ya isa wurin ta yana ƙiran sunanta, yana zuwa ya rungume ta sosai, itama rungumar sa tayi tana kuka..

Baiwar Allah cikin tsoro da fargaba ta buÉ—e baki zata kurma ihu Razhdeen ya yi saurin toshe mata baki da hannunsa,
Abbah shima abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba,
Ƴar Amana miƙewa tayi tsaye cikin nuna farin ciki take faɗin "Yaya Roshan na dawo, na dawo Yaya Roshan bazan sake barinka ba, yanzu na zama cikakkiyar mutum kamar kowa..."

Cikin farin ciki Roshan bai ma san me zai ce ba haka ya ƙara rungumar ta yana shashshafa mata sumar kanta...

Baiwar Allah tana tsugune ta fara jin motsi ta wurin ƙafar ta, idonta ta sauƙar akan wani ƙaton maciji a nannaɗe, a ruɗe ta miƙe bata san lokacin da tayi tsalle ta fita da gudu tana sakin ihu mai ƙarar gaske, a firgice tayi kan su Roshan da ihu..

Ba shiri Roshan da Ƴar Amana suka rabe da juna duk suka kallo wurin da ake ihun, ganin Baiwar Allah ta nufe su yasa Roshan ƙarasa wa wurinta yana faɗin "Ammata meya kawo ki wurin nan?..."

Ita kuwa ba abinda take faɗi sai "Maciji! Maciji!! Maciji ne wallahi!!! Yaya Roshan Maciji na gani wani ƙato acan wurin..."

Roshan riƙe ta yayi yana faɗin "kinga ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai miki, amma taya kika zo nan?..."

Jikinta na kakkarwa ta ce "ni da Abbah da Habeey da sojoji biyu muka zo..."

Cike da mamaki Roshan ya ce "suna ina su É—in?..."
ta nuna wurin da suke da yatsa ta ce "suna can cikin lawali sun ɓuya..."

Roshan ya ce "okay it's okay..."
Ƴar Amana nufan wurin Baiwar ALLAH tayi tana faɗin "Aunty Baiwar ALLAH nah..."
suna kuka suka rungumi juna...

Razhdeen ganin Baiwar ALLAH ta riga da ta tona musu asiri yasa shi miƙewa ya kalli wurin da su Abbah suke ya ce "Dad muje wurinsu kawai..."
duk tashi suka yi suka nufi wurin su..

Roshan yana ganinsu yasau murmushi haÉ—e da girgiza kai,
Abbah yana zuwa ya tsaya a gaban Roshan ya ce "kai kace kazo É—aukan Amaryar ka ne shine ba gayya?..."

Razhdeen shima murmushi ya yi ba tare da ya furta komai ba,
Ƴar Amana rungumar Abbah tayi tana faɗin "Abbah nahh..."

Abbah cikin farin ciki ya ce "Shalele nah nayi kewar ki sosai..."
haka suka gama koke-koken su daga bisani suka ga wani hayaƙi kamar guguwa ya fito musu,
haka guguwar nan ta haɗa kayuwansu ta fara hajijiya da su gaba ɗayan su, daga Abbah har Razhdeen da Roshan da Baiwar ALLAH da Ƴar Amana da kuma sojoji su biyu duk a cikin guguwar, da ƙarfin gaske guguwar nan ta ɗaga su sama tana hajijiya da su,
Baiwar Allah ita kaɗai ce mai ihu a cikin su, domin ita Ƴar Amana dake tasan da abun bata wani tayar da hankalin ta ba, su kuma mazan dake jarumai ne babu wanda yayi ihu amma sun yi mungun tsorita, lokacin guda guguwar ta ɓace da su ɓattt...

A babban falo duk matan gidan sun hallaru ko wacce tana riƙe da Alkur'ani a hannunta duk suna sanye da hijab,
Ammy da Hajiya Kilishi suna kujera ɗaya suna karatu, minal kuma a one seater itama da Kur'ani a hannunta, Ummy da Pinky da Rukky su ma suna zaune a Three seater suna karatu, Ƴar tinny itama tana zaune a gefe guda har da ita ake karatun,
kowa ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba na rashin ganin su Abbah wuni guda gashi har ana shirin ƙiran sallar mangariba...
Afaf da Ra'ees kuma suna can bedroom suna shan baccin su...

Tafiya ba sallama babu wanda yasan da tafiyar su, Baiwar ALLAH suna tunanin ko tana tare da su Abbah, ga Roshan da Razhdeen suma basa nan...

Suna cikin karatun su bayan sun yi Addu'o'i kwatsam suka ga mutane daga sama an ciccillo su, duk dokuwa suka yi a tsakiyar falo,
Ai kuwa haka kowa ya ajiye littafinsa duk suka bar falon da gudu suna ihun neman agaji, sunyi tunanin Aljanu ne, iya Ammy kawai suka bari a zaune ta rufe ido sai jero Addu'o'i take,
Hajiya Kilishi kam ba'a san lokacin tashin ta ba nan itama ta fece ɗaƙin da duk yaran gidan suka shige,
A ɗaki ɗaya duk suka hallaru suna sauƙe numfashi, Hajiya Kilishi da yaranta gaba ɗaya haka zuciyar su take ta bugawa da ƙarfi-ƙarfi tsabar tsoro...
Chapter 59 · 0% Book details