← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 68

Sashe 23

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Roshan kuwa kawar da kansa gefe yayi yana zubda hawaye...

Ƴar Amana cikin rashin fahimta take bin su da kallo domin a tunanin ta cikin Roshan gare ta saboda taji ana batun rabuwar Aure a tsakanin su..

Abbah idonsa ya sauƙe kan Roshan yana faɗin "shin cikin ka....."

kafin Abbah ya ƙarasa maganar A firgice cikin ɗaga murya Roshan ya ce "Not my own...."

Kowa zaro ido waje yayi jin abinda Roshan ya faÉ—a,
Aunty Yolash tana kallon Roshan ta ce "to idan ba naka ba kana nufin kace na Razhdeen ne don saboda abinda ya shiga tsakanin su? kai daka zauna da ita na tsawon shekara biyu baka karɓa ba sai wanda ya kasance da ita sau ɗaya?...."

Cikin ɓacin rai Roshan ya watsa mata wani irin kallo wanda idanuwansa suka yi jawur ga hawaye kwance akan idon.....

Sai da Aunty Yolash ta tsorata da irin kallon da Roshan yake mata, tinda take bata taɓa ganin ɓacin rai a fuskar Roshan irin na yau ba...

Ƴar Amana jin cikin yanada alaƙa da Razhdeen yasa zuciyar ta bugawa da ƙarfin gaske, lokaci guda numfashi ya ɗage sai luuu ta faɗa kan Mamanta dake itace a kusa da ita......

Typing ✍️

*MY ENEMY*

*TAKUN ƘARSHE*

*BOOK 3*

36 to 40

_______________★★★

Cike da takaici Roshan ya tashi yabar falon gaba É—aya,
Abbah gaba É—aya ya rasa ya zai yi da wannan al'amarin gashi cikin dake jikin Baiwar ALLAH ba'a tabbatar cewa na Roshan ne ko na Razhdeen,
Abbah juyo wa yayi yana kallon Baiwar ALLAH cikin kwantar da murya ya ce "Daughter gaya mun gaskiya wannan cikin na waye a cikin su, kina ji a gabanki Roshan yace ba nashi bane..."

Baiwar ALLAH kuka ne ya kuɓuto mata itama da gudu ta bar falon ta shige ɗakin ta tana kuka,

Ita kuwa Ƴar Amana tana kwance akan cinyar Mamanta wanda ba'a san dalilin sumar ta ba, Ummy ce ta ɗauko water bottle Mai sanyi ta kawo aka feffeshe mata fuska da ruwan, a zabure ta farfaɗo tana faɗin "dan Allah kar ku raba ni da shi ina sonsa sosai, ina sonsa sosai kar ku rabani da shi, bana so ya auri wata bayan Ni...."

Aunty A'isha zaro ido tayi tana binta da kallo cike da mamaki,
Shima Mai martaba abun mamaki ya bashi taya Reemah ta fara soyayya tin yanzu? ...
hannun ta ya riƙo tare da faɗin "Shalele nah, ki kwantar da hankalinki kinji za'a baki wanda kike so..."
Sai a lokacin ta dawo hayyacin ta, haka take bin kowa da kallo lokaci guda ta fashe da kuka itama, Aunty A'isha ce ta rungume ta a jikin ta tare da rarrashin ta...

Abbah ne ya ce "shin ita É—in wa take so ne?..."
kowa karkaÉ—a kai yayi alamar basu sani ba, sai Maimuna da ta buÉ—e baki ta ce "waye in banda Razhdeen..."

kowa tsumu yayi yana jinjina zancen,
Aunty Yolash ce ta furta "cab ana wata ga wata, chakwakiya kenam, to yanzun mai ya kamata ayi?..."

Mai martaba wanda idonsa akan Reemah ya ce "dan Allah ina so abar komai yanzu sai Razhdeen ya samu lafiya, duk wani maganar soyayya ko Aure a barshi ba yanzu ba, idan ya samu lafiya sosai in yaso sai ayi komai domin yanzu samun lafiyar sa shine abu mai muhimmanci a yanzu...."

Abbah ya ce "shikenam yanzu abinda ya kamata ayi shine Daughter zata cigaba da zama da mu anan gidan har Allah yasa ta haihu..."

Aunty Yolash ta ce "to amma ita Daughter bata son Razhdeen kuma ga cikinsa a jikin ta sannan kuma ga Reemah ita da take matuƙar son sa shin ya za'a ayi kenam...."

Mai martaba ya ce "duk wannan maganar a bar shi sai Razhdeen ya samu sauƙi sannan itama idan ta haihu duk za'a warware matsalar..."

Chief yana tsaye ya goya hannayensa biyu akan ƙirji kansa na kallon ƙasi, ƙwaƙwalwarsa ce take ta faman jujjuyawa ga Matarsa ta musulunta ba tare da sanin sa ba ga kuma alƙawarin da yaso cikawa na haɗa Ɗiyarsa da Razhdeen kuma yanzu yaji wani batu da ban akan cewa Ƴar uwar sa tana son sa again, abun da ya ɗauka shine bazasu taɓa faranta wa ƴarsa sannan su baƙanta wa nasu ba....

Abbah ne ya katsar da Chief daga dogon tunanin da ya zurfafa, yana faÉ—in "naga kayi shiru Allah yasa dai lafiya..."

Girgiza kai Chief yayi sannan ya ce "kawai ku aura mata Razhdeen É—in tinda tana son sa kuma É—an uwanta ne, ita kuma Daughter zan tafi da ita..."

Abbah ya ce "to alƙawarin fa...?"

Chief a taƙaice ya ce "na janye, ina so a faranta wa wancan, kuma nasan Daughter ta nuna bata son Auran Razhdeen bana so a samu matsala ne..."

Abbah ya ce "amma kuma cikin sa ne fa a jikin ta ..."
Chief ya ce "zata haifa masa kayansa Insha Allah..."

Aunty Yolash ta ce "to in kuma Roshan take so ba sai a maida musu Auren ba, bayan ta haihu..."

Chief girgiza kai yayi yana murmushi ya ce "Bama Auran mata biyu sannan ƴaƴan mu bama Aura musu masu mata, haka ƙa'idar mu take..."

Mai martaba ya ce "Insha Allahu dole za'a haÉ—a Auren Razhdeen da Amreesh saboda mai haÉ—awa ya rigada ya haÉ—a tinda akwai juna biyu a tsakani, ita Reemah zamu san yanda za'ayi da ita. ..."

Abbah cike da damuwa ya ce "Insha Allahu Razhdeen zai miƙe ya koma kamar kowa za'a magance matsalar nan, zai kuma zaɓa idan Amreesh ne za'ayi Auren idan kuma Reemah ne nan ma zai zaɓa, idan kuma duk biyun ya zaɓa sai dai ya rasa su gaba ɗaya...."

Chief kallon yanda Madam Parveen take a zaune ya yi sannan ya ce "tashi mu tafi..."

Kallon sa tayi sannan ta ce "kasan zaman mu bazai yu ba, ina musulma kai kana Christal...."

Cikin fushi Chief ya darara mata tsawa tare da faÉ—in "you are not a Muslum..."

Itama miƙe wa tayi tsaye suna facing juna ta ce "i'm a muslum..."

Chief ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba yana nuna ta da yatsa ya ce "okay don't worry, but you better stay away from me..."

Yana gamawa ya juya kan Rakesh yana faÉ—in "tashi mu tafi..."
Rakesh motsi-motsi ya fara yi kamar wanda baya son tashi idonsa akan Mommyn su...

Chief ya ce "tashi mana ina maka magana..."
Rakesh gira a haÉ—e ya ce "sorry Dad me too i want to be a musulum..."

Chief zaro dara-daran idanuwansa yayi yana kallon sa ya ce "whattt?..."

Rakesh ya ce "Sorry Dad, my brother Mohandas ya musulunta still My mother itama ta musulunta sannan ga my younger sister she's a muslum why bazan zama musulmi ba...."

Chief cikin ɓacin rai ya daka masa tsawa tare da faɗin "shut up very stupid, okay kaima ka cigaba da zama a wurin su, bana son ganin kowa a cikin ku yaje yanda nake...."

yana kaiwa nan yayi ficewar sa,
Madam Parveen ce ta fashe da kuka tsabar takaici kuma gashi tana son mijinta,
Aunty Yolash ganin yanda take ta kuka yasa ta taso ta je yanda take tare da rungumar ta suka zauna tana rarrashinta..

Mohandas da Rakesh suma gaba É—ayan su babu wanda yaji daÉ—in abinda ya faru amma sai dai dole daman zasu fuskanci kalubale...

Abbah zama yayi yana kallonsu cike da tausayawa ya ce " kuyi haƙuri zai dawo gare ku Insha Allahu, zaku cigaba da zama anan gidan, kafin Allah yasa komai ya daidai ta...."

Suna cikin wannan halin sai ga wani soja ya shigo da sallama a bakinsa yana riƙe da hannun wani saurayi fari tass suka shigo tare,
Maimuna tana ganin Ashmar ta tashi da gudu ta nufo yanda yake tare da rungumar sa tana kuka tana faÉ—in "Yarima na ya dawo gareni, Allah na gode maka..."
tana shafa fuskarsa cikin kuka take faɗin "Ashmar ina ka shiga ne haka? ka tafi ka barni cikin ƙunci da tashin hankali, meyasa ka jefa rayuwarka cikin hatsari?...."

Shima kukan yake ya rungumi Mamansa sosai....

Ƙarasa shigowa ciki suka yi, Mai martaba ganin Ashmar bai san lokacin da ya fara washe baki ba cike da farin ciki shima ya tashi yaje ya rungume shi yana faɗin "yanzu shima yaro nane? Ikon Allah kenam Allah nagode maka, ashe zubar hawaye na bai zube a banza ba, addu'a ta bai faɗi ƙasi banza ba, zubar hawaye na alkhairi ne, ga Yarima da Reemah Allah ka bar mun su..."

Kowa cike da farin ciki yake binsu da kallo, Maimuna da Yarima duk zama suka yi cikin rashin fahimta Ashmar yake bin kowa da kallo, idonsa ne ya sauƙa akan Ƴar Amana, a ruɗe ya buɗe ido yana kallon ta...

Ita kuwa Ƴar Amana har zuwa wannan lokacin bata daina kuka ba tana kwance kan cinyar Mahaifiyar ta, kallon Ashmar tayi jin ana faɗin ɗan uwanta ne, ganin yanda yake ta kallon ta ne yasa abun ya ɗaure mata kai ga baƙin cikin abinda ya faru tsakanin Razhdeen da Baiwar ALLAH,
Ita bata san shi ba dake lokacin koda yaushe fuskar sa a rufe take...

Madam Parveen hankalin ta ne ya kasa kwanciya ganin a halin da Baiwar ALLAH ta bar wurin, itama tashi tayi tare da barin falon ta koma cikin ɗaki, anan ta tarar da Baiwar ALLAH kwance akan gado sai sharar kuka take ba ƙaƙƙautawa, baƙin cikin ta shine cikin dake jikin ta kuma na Razhdeen...

Madam Parveen zama tayi a bakin gado ta riƙo hannun Baiwar ALLAH tare da ɗagota tana share mata hawaye, tana faɗin "Amreesh! kukan me kike yi?..."

Cikin kuka Baiwar ALLAH take faÉ—in "haba Mommy dole nayi kuka, ji nake kamar na kashe kaina wallahi, ciki ne fa dani? cikin Razhdeen shin meye sunan cikin dake jikina? cikin shege kenam fa, da igiyar Aure a kaina na aikata alfasha kuma har da ciki, me zance wa Ubangiji na idan naje gabansa...."

Madam Parveen girgiza kai tayi ta ce "kina gani fa ba'a son ranki kika aikata ba, bakida laifi kuma haka shima Razhdeen bashi da laifi akan wannan al'amarin..."

Baiwar Allah tana kuka ta ce "taya zaki ce bashida laifi alhalin shi ya jefa ni cikin hargutsi..."
Chapter 23 · 0% Book details