← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 68

Sashe 32

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Roshan maida kallon sa yayi kan Ramlat sannan ya ce "ina so ki sa ni cewa ita É—in Æ´ar uwata ce jinin jikina, ba ko wani irin furuci zan juri ji ana gaya mata ba, kina jifan ta da munanan kalamai saboda sakarci irin naki kuma a gabana, to zan Aure ta sai kuma naga mai zakiyi, sannan ke baki isa ki bani umarni ba, ki tsaya a iya matsayin ki idan kuma ba haka ba zamu fiskanci rashin jituwa a tsakanin mu..."

Sannan ya juya da kallonsa kan Baiwar Allah ya cigaba da cewa "ke kuma last warning da zan yi miki na ƙarshe shine kada ki sake nuna cewa ni mijinki ne, ki tsaya a yanda kike yanzu rabuwa ne na kuma rabu da ke har abada, bana jin haushin ki yanzu akan komai domin na tsawaita bincike na gano cewa bakida laifi sannan ƙaddara ce ta kuma riga fata, a baya na so ki kamar raina zai fita haka nan kuma yanzu ma idan nace bana sonki nayi ƙarya, zama ne bazan iya cigaba da zama da ke ba saboda inada matuƙar kishi na gaske, sannan kuma tin kafin ki kai haka aka kyautar da ke saboda haka na haƙura na barwa twins ɗina..."

Jin ƙarshen maganar sa yasa tayi saurin kallon yanda yake zuciyar ta na bugun uku-uku domin a rayuwarta ta tsani a yi mata maganar Razhdeen,
kuka ne ya kuɓuto mata ta juya da sauri tana kuka, shi kuwa binta yayi da kallo zuciyar sa na harbawa domin har yanzu yana jinta a ransa..

Ramlat itama tana kuka ta koma cikin room É—inta,
Roshan goya hannayensa yayi akan ƙirji yana hura iskar bakin sa, daga bisani ya girgiza kai shima ya nufi hanyar waje zai nufi part ɗin su Abbah...

Reemah lokacin da ta koma part É—insu bata tarar da kowa a falo ba kai tsaye room É—insu ta haura da gudu, tana shiga ta tarar da Ummy tana zaune akan kujerar mirror tana makeup, Reemah tsaya kallon ta tayi tare da faÉ—in "Amarya wai shin ba yau zaku tafi gidajen mijinku ba ne?..."

Ta cikin mirror Ummy take kallon Reemah sannan ta ce "wato har an gaji da ganin mu kenam, abun har da kora..."

Reemah ta ce "ey ai tambaya nayi, ba yau bane?..."

Ummy ta ce "ai dake zamu tafi idan lokacin tafiyar yayi..."
Reemah turo lips É—inta tayi sannan ta ce "sai dai na iso ku daga baya..."

Ummy ta ce "Oh ashe dai kin ce sai kin jira dawowar Uncle Deen koh?..."

Kallon gefe tayi tana tunanin wani abu daga bisani ta nufi yanda Ummy take zaune tana fuskantar mirror taje ta dafa kafaÉ—ar ta tana murmushi ta ce "kin san meye?..."

Ummy tana kallonta ta cikin madubi ta ce "me ya faru?..."

Reemah tana rungume da ita tana tsaye ta ce "Aunty Ummy Allah ya ga zuciya ta ina son Uncle Deen, amma sakamakon abinda ya faru a tsakanin sa da Aunty Baiwar Allah yasa gaba É—aya bana jinsa a raina, amma yanzu na samu wanda zai maye mun gurbinsa a cikin zuciya ta..."

Ummy cike da mamaki ta juyo da kujerar ta tana kallon ta tace "wa kika samu amma?..."

Reemah tana kallon ta tace "Yayana Roshan..."
Ummy zaro ido waje tayi tana kallon ta cike da mamaki ta ce "whatt?..."

Reemah ta ce "yess shi da kansa ya ce yana sona, kuma naga ya iya kula da mace da kuma soyayya, ga yanada sauƙin kai sai kuma naji lokaci guda ya kwanta mun a rai, sannan kuma matar sa Ramlat sai na koya mata hankali kinji irin maganganun da ta gaya mun kuwa? har ni zata ce wa jahila marar tarbiyya da ilimi sannan wai ban je islamiyya ba, ai wallahi sai nayi maganinta...."

Ummy sauƙe numfashi tayi tana jinjina zancen ta ce "yanzun kin koma kan Yaya Roshan kenam, toh amma meye dalilin da yasa ta zage ki haka kuma naga Ramlat yanzu tayi sanyi ba kamar baya ba lokacin da Auntyn ta Maamie take zuga ta ba..."

Reemah ta ce "Hmmm! ƙyale ta kawai zan rama domin ni bana barin bashi..."

Ummy ta ce "wai ma tsaya shin aina kika kwana?..."
Reemah ta ce "naje taya su kwana ne..."
Ummy zaro ido tayi tare da faÉ—in "su waye wai?..."
Reemah ta ce "su Yaya Roshan mana, a É—aki É—aya na kwana da su hakan ma akan gado, ni da matar sa akan gado shi kuma Yaya Roshan yana kan kujerar É—akin..."

wani irin haɗiyar yawu Ummy tayi tare da faɗin "amma ban taɓa sanin cewa ke mahaukaciya ba ce sai yau, taya zaki je ɗakin ma'aurata ki ce zaki kwana ai kin takura musu kuma hakan ma bai dace ba sam..."

Reemah ta ce "hakan shine dai-dai domin na fahimci akwai ƙwari a cikin ƙwaƙwalwar Ramlat, kaɗan daga cikin aiki na kenam..."

Ummy ta ce "au kenam da biyu kika yi musu haka? ai dole ta zage ki domin kinyi mata abubuwan da ba ko wace mace bace zata yadda ayi mata ba, da farko a gabanta ya yi miki É—aukar luÉ—a ya shiga da ke wurin taron al'umma fa sannan kuma kije ki kwana a É—akin su na Aure?..."

Reemah gaba ɗaya fuskar ta ba annuri haka take kallon Ummy rai a ɓace ganin yanda take mata magana cikin fushi, zuciyowa tayi ta juya zata fice daga ɗakin sai taci karo da Mamanta Aunty A'isha,
Aunty A'isha tsaya wa tayi tana kallon ta cikin fushi daga bisani ta ce "ina ma kika ce kin kwana?..."

Reemah tana turo baki ta ce "na je na taya su Yaya Roshan kwana..."
kafin takai karshen maganar Aunty A'isha ta zabga mata mari har sai da ta faɗi ƙasin carpet, tana faɗin "kinje kin taya su kwana ke mahaukaciya ce? ai yau da safe daman Ramlat ta ƙira ni a waya tana kuka take sanar mun aika-aikan da kika yi musu, meyasa hakane?
na tsani mummunan hali a rayuwata, ni ba haka nake ba, dan Allah ki zama mai kyakkyawar hali wanda a duk yanda kika zauna za'a yabe ki"
tsuka taja tsabar takaici bata ƙarasa maganar ba ta fice..

Reemah tana zaune ƙasin carpet yanda ta faɗi tana dafe da fuskar ta ga yanda hawaye yake gangaro mata,
Ummy ce ta tsuguna tana rarrashin ta...

Sai da suka ɗau lokaci suna haka babu wanda ya motsa a cikin su daƙer Reemah haƙura tasa hannu tana sharar hawaye ta ce "yanzu laifi ne dan Yaya Roshan ya ce yana sona nima kuma ina son sa?...?"

Girgiza kai Ummy tayi sannan ta ce "ba laifi bane matsalar shine zuwa da kika yi ki ka taya su kwana..."

Reemah ta ce "shine kuma zata ƙira Mamana ta faɗa mata?..."

Ummy ta ce "kiyi haƙuri ki mance da komai..."

Reemah tana zubda ƙwallah ta ce "to wallahi saina Auri mijinta sai dai ta mutu, yanzu ma kuwa zan fara nuna masa asalin ƙauna..."

Suna cikin wannan yanayin sai ga Aunty Yolash da Minal da Pinky da Rukky da kuma Ramlat wacce bata juma da zuwa ba duk suka shigo, da sallama a bakin su..

Aunty Yolash ce ta gansu a haka ta ce "ha'a lafiya dai kam ko? meya faru da Shalele take kuka kuma?..."

Ummy ganin har da Ramlat aka shugo yasa ta cewa "babu komai wai an sanar mata cewa duk yau zamu tafi shine take kuka..."

Aunty Yolash ta ce "naga da ita duk za'a tafi.."

Ummy ta ce "sai fa ta jira Uncle Deen ya warke kafin..."

Aunty Yolash ta ce "toh pah! amma naji labarin yanzu Roshan take so ai kodai duk biyu zata Aura?..."

Reemah É—ago da dararan idanuwanta tayi waÉ—anda suka kaÉ—a sukayi jawur tana yiwa Ramlat wani irin kallo fuska ba annuri...
Itama Ramlat É—in ita take kallo tana wani yamutsa fuska domin duk halin da ake ciki ta sanar musu...

Aunty Yolash ce ta kuma cewa "Reemah meyasa hakane? kina fushi da Baiwar Allah saboda Razhdeen, yanzu kuma kin koma samun matsala da Ramlat saboda Roshan Anya kuwa akwai ƙamshin gaskiya a cikin lamarin nan?..."

Reemah ta ce "Razhdeen da Baiwar Allah amanata suka ci shiyasa..."

Aunty Yolash ta ce "oh kafin lokacin kin san sunada alaƙa ne? ko shi Razhdeen kin san yana tare da ita ne? kuma hakanan Baiwar Allah bata san kina tare da Razhdeen ba, babu maganar cin amana anan ke dai tsantsar kishi ne yake damun ki, hmmm! Razhdeen da Baiwar Allah lallai kam to ku zauna in baku wani labari naga har yanzu baku gane komai ba..."
Chapter 32 · 0% Book details