← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 68

Sashe 61

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Reemah a free ta samu ta wuwwuce gate ɗin gidan dake babu masu dakatarwa yau ranar kowa da kowa ne, tana fita waje ta tarar ƙofar gidan a cike tam da mutane duk maza, abokan Angwaye ne da waɗanda suka zo daga ƙasar waje da kuma waɗanda suke garurruwa gasu nan kaca-kaca, ƴan mata kuwa ba'a magana wasu suna tare da samari su, wasu a wurin bikin suka haɗu har suka fara soyayya, Reemah ido kawai ta bisu da shi, wasu ne suka lura da ita dake Amarya a duk inda take saita fita daban, nan suka fara nuna ta suna faɗin "laa wancan ba ɗaya daga cikin Amare bane?..."

Wata daga cikin dangi ta ce "Reemah ce fa Amarya meta fito yi kuma?..."
Acan gefe guda kuma Razhdeen da Roshan da wasu abokansu su biyar suna tsaye a jikin wata ƙatuwar mota baƙa ƙirin mai bala'in tsada alamun shigar ta zasu yi suna son zuwa wani wuri...

Reemah baza idanu take tana son ganin yanda zata ga Roshan, ji tayi an dafa kafaÉ—arta tana juyawa taga wata Æ´ar uwarsu ce Fa'iziyyah,
Fa'iziyyah ta ce "Reemah kina da hankali kuwa kika fito waje?..."

Reemah cikin haɗe gira ta ce "ban gànshi ba, ina zan same shi?..."

"Wa kike nema?..." a cewar Fa'iziyya.

Reemah ta ce "Mijina nake nema ban gan shi ba..."

Dariya yarinyar tayi domin ba ƙaramin dariya ta bata ba jin abinda ta ce, nuna shi tayi da yatsa tana faɗin "wancan ba shi bane? naga suna shirin shiga mota..."

Dasauri Reemah ta kalli wurin da ta nuna, cikin farin ciki tana washe baki ta ce "yawwa shine wallahi..."
nan ta tafi da gudu tana ƙiran sunan sa "Yaya Roshan! Yaya Roshan!! Yaya Roshan!!!..."

Duk waiwayowa akayi ana kallon ta jin yanda ake ƙiran sunan Roshan,
Shima Roshan juyawa ya yi yana kallon ta, wani daga cikin abokan sa ya ce "wancan kamar Amaryar ka..."

Wani daga cikin su ne ya ce "buro uba shiyasa bazan taɓa Auran yarinya ba wallahi, domin yarinta zata rinƙa nuna mun har na bugeta..."

Razhdeen murmushi ya yi tare da kawar da kansa gefe...

Tana isowa ta rungume shi tana faÉ—in "wallahi har naji daÉ—i a raina ganinka da na yi..."

Idon kowa akan su,
Roshan ya É—ago ta tare da faÉ—in "akwai abinda ya faru ne Shalele?..."

tana turo baki ta ce "naga tin jiya ban ganka ba, kuma idan nayi kwana biyu ban ganka ba bazan iya cin abinci ba da bacci..."

Roshan ya ce "to ai ba ke kaÉ—ai bace Amarya su da basu ga mijinsu ba ai basu damu ba..."

Reemah ta ce "to kuma ai ba za'a haɗa soyayya ta da nasu ba, ni nafi su shiga shauƙin soyayya..."

Roshan ya ce "okay to yanzun kin ganni ko, ma za koma gida..."

Kamar zata yi kuka ta ce "to to ina zaka je naga zaku shiga mota?..."

Roshan kallon mutanen wurin yayi yaga duk idanunsu akan sa suke ya ce "kinga Shalele baki ga ina tare da abokaina bane? tare zan fita da su..."

Ta ce "Yaya Roshan zan bi ku..."
yayi saurin katse ta da cewa "ina? a'a bazai yu ba, ya kamata ki san cewa Amarya tana da kunya, yanzu a idon mutane zan É—auke ki a mota mu fita? ki koma gida..."

Reemah ta ce "Ni wallahi sai na bika duk yanda zaku je, haka kawai sai kana yin nisa da ni..."

Wani daga cikin Abokinsa ne ya dafa kafaɗarsa ya ce "kaga mijin yarinya wata ƙil tafiyar nan bada kai zamu yi ta ba, kaje ka zauna da Amaryar ka domin bazamu ɗauke ta mu tafi da ita ta hana mu rawan gaban hantsi ba, ƴan sirrikan da muke so mu ɗan tattauna akai bazai yu muyi ta a gabanta ba..."

Wani soja a cikin su Abokin sa daga ƙasar italia ne ya buɗi baki ya ce "wallahi bazai zauna ba tare zamu tafi kuma babu yanda zamu tafi da ita, shirmen banza kawai su duk Amaren mutuwa suka yi ne da basu ga mazajen su ba, get out my friend..."

Reemah É—agowa tayi tana hararar sa tare da turo baki ta ce "eh a bar mun kaya na ko kuma mu tafi tare ehen...."

Sojan ya ce "Ke get out for here before I finish you..."
Roshan dafa kafaɗar ta yayi tare da faɗin "Shalele ki kwantar da hankalin ki kinji, ina dawowa zan zo mu yi hira kiyi haƙuri ki koma gida, kinga idan mun tafi tare wannan sojan zai takura mun ke kin ga yanada zafi sosai..."

Reemah baki a É—ane ta ce "to shikenam..."
Roshan ya ƙira wasu ƴan mata biyu daga cikin ƴan uwansa ya sanar musu akan su raka Reemah cikin gida...

Reemah da wasu Æ´an mata sun sakata a tsakiya har sun fara tafiya Reemah ta tsaya sannan ta juyo, su kuma su Roshan suna shirin shiga mota suka ji Reemah ta ce "Kai Sojan nan...."

Duk juyowa suka yi su ma hatta Razhdeen, Sojan yana kallon yanda take cikin fushi ta ɗago ta hannayenta biyu ta danƙwale shi cikin tsoro kuwa ta juya da gudu ta nufi gida, anan tabar ƴan matan da aka haɗa ta da su...

Sojan buÉ—e baki yayi cike da mamaki ya ce "whatt! Ni yarinyar nan zata dankwala ?..."

Roshan ya riƙo hannunsa yana bashi haƙuri, sauran Abokan kuwa dariya duk suka fara yi domin Reemah ba ƙaramin dariya ta basu ba, cike da mamaki kuma wai a haka Amarya ce wacce aka ɗaura Auren ta yau, da haka suka shige mota cikin lokaci ƙanƙani suka bar wurin....

Reemah tana surutai da masifa da haka ta shige falo wanda yake cike da mutane, Aunty A'isha tana ganinta tayo kanta tare da jan hannunta suka shige wani ɗaki wanda anan Baiwar ALLAH take an gama shiryata cikin wedding gown fari tass har jan ƙasi yake, an gyara mata gashi ta gaban goshin nan gashi ne a kwance luf-luf yanda akayi wani irin design, ta sha makeUp bana wasa ba,
Wasu ne Æ´an mata biyu suke tsara mata kwalliya, Aunty A'isha tana shigo da Reemah ta zaunar da ita akan kujerar mirror tana faÉ—in "ina kika shiga ne haka ake neman ki za'a gyara ku, wa ya gaya miki Amarya tana yawo ne..."

Reemah ta ce "Mama dan naje wurin Yaya Roshan shine wani soja zai mun rashin kunya ni kuwa na tanƙware shi na gudo abuna..."

Aunty A'isha ta ce "ai da sai ki tsaya tinda rashin kunya zai yi miki, ban da hauka me zai kai ki wurin Roshan kuma..."

Reemah buÉ—an baki tayi zata yi magana Aunty A'isha tayi saurin katse ta da cewa "yi mun shuru ki tsaya a gyara mun ke, kin san akwai walimar da za'ayi a can hall..."

Reemah ta ce "Mama ba party za'ayi ba?..."

Aunty A'isha ta ce "Aunty Yolash ta ce bata buƙatar yin party tinda bikin har da ita a ciki, walima duk za'a haɗu ayi..."

Reemah tana turo baki ta ce "naso ayi party wallahi yanda za'a ƙira mana mawaƙa mu ma kamar yanda akayi a bikin su Aunty Ummy da Pinky da Rukky, amma a bikina kamar bikin mutuwa...."

Aunty A'isha ta ce "to wa ya sani ne ko ke zaki mutu..."
ta ƙarasa maganar tana mata dariya...

Reemah ta ce "nikam bazan mutu yanzu ba, yaushe ma nayi Auren..."

Ta cikin madubi Reemah ta hango Amreesh a zaune a bakin gado an gama tsarata kamar sarauniyar ƙasar india, a ruɗe ta ce "kai kai kaiiii Aunty Baiwar ALLAH so kike yau ki rikirkita Uncle Deen? innalillahi daman haka kike da wannan kyau? wallahi ba ƙaramin kyau kika sha ba..."

Baiwar Allah tana zaune sai zuba murmushi take tana jinta...

Aunty A'isha ce ta ce "haba ki tsaya a miki kwalliyar nan duk kin ishi mutane da surutu..."

Reemah ta kuma cewa "ai kuwa dole ayi dinner party wannan kwalliya haka..."

Aunty A'isha ta ce "yaushe aka gama magance matsalolin Aljanu shine zaki wani cewa dole ayi party, sai mu gani ai..."

Wata budurwa ce ta shigo tare da ce musu "kowa fa ya shishshirya Amare ake jira, kar lokaci ya ƙure..."

Aunty A'isha ta ce "ai wannan rigimammiyar ce duk ta ɓata mana lokaci wallahi..."

Aunty A'isha tana tsaye aka gama gyara Reemah itama aka sanya mata wedding gown irin na Amreesh, duk kwalliyar ko wacce ya yi mata kyau sosai, sai dai dake Baiwar ALLAH tafi Ƴar Amana hasken fata sosai duk da itama fara ce ƴar Amana....

Kowa ya shirya tsab har masu jego suma anyi bikin suna an raÉ—a wa kowa sunan jariri,
Ummy ta sanya wa uwar mijinta mai suna wato Maimuna, sai kuma Pinky ita kuma a uwar mijinta tayi wa mai suna sannan matar mahaifinta wato Ammy, Ummu Salamah...

Motar Amare ne suka fara tashi wanda ya kasance Amreesh da Reemah ne a ciki sai wani mota daban wanda aka ɗauki Aunty Yolash a ciki tana sanye da wata danƙareriyar gizner yasha aikin wuta da ƙaton gyalenta kalar gizner ba ƙaramin kyau tayi ba itama, anan kowa da kowa suka watse aka bar gida empty babu kowa sai security da sojoji...

★★★★★★

Cikin wani ƙaton hall wanda tarin dubban al'umma ne suke zazzaune kowa da robar lemo da farror a gaban sa da kuma naman ƙatuwar dabba da aka yanka kowa da nashi a ƙaton faranti wanda naman yasha gashi, wurin ba'a shiga sai da card da sunan mutum a rubuce da photonsa, in kazo wuce wa sai sojojin wurin sun duba card idan sun tabbatar kaine sai ka wuce,
A ta saman hall wani dogon kujera ne wanda ya sha kwalliya sai sheƙin haske kujerar take, ga wani table mai bada haske kala-kala a jiki wanda lemuka ne akai, a kujerar Amreesh ce da mijinta Razhdeen sai kuma a gefe guda Roshan da Amaryarsa Reemah suke zazzaune,
Aunty Yolash kuma ƙin fitowa tayi tana cikin mutane a zaune, a cewar ta bazata haɗa kanta da yara ba, ita yanzu ta girma Aure kawai aka ɗaura mata amma inda ita kaɗai ce walimar ma bazata yi ba....
Chapter 61 · 0% Book details