← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 68

Sashe 40

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk waiwaya wa sukayi suna kallon Aunty A'isha wacce ta shigo tana riƙe da hannun Ramlat suka ƙarasa shugowa sai Aunty Maimuna da Hajiya Kilishi da Ammy duk suka shigo,
Aunty A'isha zaunar da Ramlat tayi akan kujerar ɗakin sannan ta juyo kan Reemah tana faɗin "baki da hankali Reemah? ashe zaki iya yin sanadiyyar zubar da cikin mutum? kashe Ramlat zakiyi ne? to bari kiji kamar yanda kike a mazannin ƴanta wanda na haifa haka itama Ramlat a matsayin ƴar ciki na na ɗauke ta, ƴar uwa take a wurin ki tinda tin tana yarinya ƙarama take tare da Mahaifinki, shi ya raine ta, kafin ya saba da ke da ita ya fara sabawa tsawon shekara da shekaru, kin zubar mata da ciki meye ribar ki? daman ni wallahi ban so zaman ki anan ba saboda nasan bazaki bar su suyi zaman lafiya ba saboda tin kafin mu tafi kike nuna alamun haka...."

Reemah tana kuka ta ce "Mama wallahi....." bata ƙarasa ba taji Mamanta ta ɗauke ta da mari tare da kai mata duka..
Roshan ne ya jawo Reemah jikinsa yana faɗin "dan ALLAH banda duka, kuma itama taji rauni sosai kar aga laifin ta ita kaɗai, kuma babu yanda za'ayi da hankalinta ta ɓarar mata da ciki..."

Ramlat itama tana kuka ta ce "wallahi ita ta ture ni na faÉ—i cikina ya zube..."

Sai a lokacin Baiwar ALLAH tayi magana idonta akan Ramlat ta ce "kafin ta ture ki mai kika aikata mata?..."

Ramlat shiru tayi kanta a ƙasi sai zubda ƙwallah take..

Baiwar ALLAH ta ce "ya kamata a rinƙa yi wa juna adalci...." kaf abubuwan da suka faru duk Baiwar ALLAH ta zayyanar bata ɓoye komai ba da sanadiyyar raunanar kowa ...

Roshan wani irin kallon takaici ya wurga wa Ramlat yana faɗin "daga mari sai ɗaukan ƙwalba ki doka mata akai saboda rashin tunani, hakan nan idan wuƙa kika raruma zaki caka mata..."
Ya kalli sauran mutanen ya kuma cewa "to meye laifin Reemah anan? har ana cewa ita ta ɓarar da ciki tayaya? to idan hakane itama Ramlat ita ta jawo akayi wa Ammata Operation har ta jikkata sai da tayi kwana biyu kafin ta farfaɗo, idan a lokacin jaririyar cikin ta ta raunana fa? saboda haka bana so aga laifin kowa in ba na Ramlat ba, saboda ita ta kai kanta sannan bada arziƙi taje musu ba, har tana goranta wa Ammata cewa iyayenta Christal? wani irin hauka ne...."

Ramlat miƙe wa tayi tana kuka ta ce "Yaya Roshan daman ba Sona kake ba, baka taɓa goyan bayana ba sannan cikin jikina dana rasa baka nuna damuwar ka akai ba, ni kaɗai na damu da cikina amma kai sam babu ruwanka saboda ba Sona kake ba...."
Roshan cikin ɓacin rai ya ce "eh bana sonki kije, indai da haka zan zauna da ke ba zan taɓa sonki ba, idan kina so na damu dake to kema ki damu da waɗannan mutane biyun, Reemah da Ammata domin su ɗin masoyana ne, kuma wallahi tallahi indai aka ƙara sa hannu a jikin Reemah da suna duka ko mari ta sanadiyar ki to kisa a ranki cewa daga ranar na rabu da ke har abada...."

Ramlat ba abinda take sai kuka,
duk babu wanda ya ƙara furta komai a cikin su sai Reemah da tayi hanyar fita, Aunty Maimuna ce ta kalle ta ta ce "ina zaki je Shalele?..."

Reemah tana kuka ta ce "zan tafi ne..."
ta ce "ina kuma?..."

Reemah ta ce "zan koma inda na fito, zuwana cikin ahalin nan ya sanya wasu cikin ɓacin rai, kullum a cikin fushi ake da ni, idan ina nam babu kwanciyar hankali gwara kawai na tafi...."

Aunty Maimuna ta ce "Shalele mai kike faÉ—i hakane?..."

Baiwar ALLAH buÉ—e baki tayi tana kallon ta kamar zata yi kuka..

Aunty A'isha idanuwanta ne suka cicciko ta ce "Reemah ki dawo nace..."

Reemah girgiza kai tayi ta ce "Bakya sona ya za'ayi na zauna da ke, kin nuna mun kin fi son Ramlat akaina, na haƙura da iyayena gwara naje na zauna ni kaɗai nafi jin daɗi..."
tana kaiwa nan ta fice,
Aunty A'isha a ruɗe ta ƙwalla ƙiran sunanta,
Tare da bin bayanta da gudu, suma bin bayan ta suka yi har Roshan da Ramlat kowa fita yayi...

Baiwar ALLAH tana zaune ita kaɗai da jaririyar ta a jefe, a hankali ta ɗauki jaririyar tana kallon ta sosai ga hawaye yanda yake ta zuba mata a fili ta ce "Baby na ina matuƙar ƙaunar ki har cikin zuciyata, laifin Abbanki ne ya shafe ki, duk da nasan ban kyauta miki ba, nayi miki babban laifi, ta hanyar da ya dace na kawo ki duniya bata nan kika zo ba, nasan zaki ji haushi na, dan Allah ki yafe wa Mamanki, kar kiyi fushi da Mamanki kinji ko, ina so kiyi rayuwa cikin ƴanci, inasonki...."
ta sumbaci yarinyar akan goshi sannan ta sauƙar da ƙafar ta ƙasi ta miƙe daƙer taje ta kwantar da yarinyar akan gadonta na yara, sannan ta ɗauki wani littafi akan table da biro tayi dogon rubutu ta nannaɗe ta ajiye a cikin gadon jaririyar ta gefen ta, sai da ta shafa kan yarinyar kafin ta yafa gyalen ta ta fice daga ɗakin.....

Reemah kuwa tana kan gudu kwatsam ta ci karo da su Abbah da Mai martaba wanda isowarsa kenam,
Abbah ya ce "ha'a Shalele ina zaki je haka kike ta gudu..."
Mai martaba murmushi yayi tare da faɗin "My rigimata zo mana..." yasa hannu ya rungume ta cikin nuna farin ciki domin ba ƙaramin ƙaunar Reemah yake ba, yana matuƙar ji da ita har cikin zuciyarsa..

Sai ga sauran su ma sun fito da saurin su,
Aunty Maimuna ce ta ce "yawwa Allah mun gode maka daka kawo mana agaji..."

Abbah ne yake tambayar su cewa "me yake faruwa ne?.. "

Aunty Maimuna ce ta kora musu bayanin abinda ya faru,
Abbah ya ce "meyasa haka kuma? ya zaku sa yarinya a gaba ku ce ita ta zubar da ciki meye haka? faɗa suka yi a junan su kuma kowa ya raunana, ita Daughter ba Operation dole akayi mata ba? Ƙaddara ne da tsautsayi ya kuma afku sai a bar maganar haka..."

Mai martaba sam bai ji daÉ—in abinda Aunty A'isha tayi wa Reemah ba domin tasan dole yarinyar zata ga kamar ba'a sonta..
ɗagota yayi tare da faɗin "Shalelen Abul kiyi haƙuri kinji, idan kika tafi mutuwa zanyi, kina so Abul ɗinki ya mutu?..."

Da sauri Reemah ta girgiza kai, ɗagowa tayi tana kallon Mahaifinta sai anan Mai martaba yaga shatin hannun Aunty A'isha yanda ta mare ta bayan ɗaurin bandejin dake ɗaure akan goshin ta, shafa wurin yayi rai a matuƙar ɓace ya ɗago yana kallon Aunty A'isha ya ce "wani irin mari ne haka?..."

kallon Mai martaba tayi kamar zatayi kuka tazo yanda yake tasa hannu ta juyo da fuskar Reemah taga zanen shatin hannu, kallon ta tayi cikin tausayawa ta ce "My Reem kiyi haƙuri ki yafewa Mamanki, rai nane ya ɓaci sosai shiyasa, ba wai bana sonki bane bana so Ramlat tayi zaman kaɗaici ne kinga yanzu bayan mu bata da kowa, idan ban nuna na damu da ita ba zata ga kamar mun jefar da ita ne saboda mun same ki, don haka kiyi haƙuri kimun uzuri ..."

Reemah fashewa tayi da kuka haka Aunty A'isha tasa hannu ta rungume ta a jikin ta tana rarrashin ta, tare da faɗin "Insha Allahu bazan ƙara dukan ki ba, tare zamu koma dake bazan bar ki ba kar wani abu ya sake ɓullo wa...."

Ramlat kuwa tin kafin ta fito marar ta ya riƙe a wurin ta faɗi tana kame da cikin ta,
Roshan ne ya waiwaya jin kamar ƙaran kuka, ganin Ramlat a durƙushe yasa ya juya baya ya koma gareta, ɗagota yayi ya zaunar da ita akan kujerar wurin shima ya zauna a gefenta yana faɗin "meya faru ne?..."
tana kuka ta ce "ciki na ciwo..."
Ya ce "kin san da hakan kika fito? ai da sai ki zauna a ciki tinda kinsan kinada matsala..."

Kallon sa tayi tana kuka gaba É—aya ta zamo kalar tausayi,
Roshan a hankali ya ce "Ramlat ki daina kukan nan mana..."
Ta ce "kai ne baka Sona Yaya Roshan..."
Roshan ya ce "kiyi haƙuri rai nane yake a ɓace banaso kina haɗa ƴa da uwa, gashi a kan ki mahaifiyar ta tazo tana dukan ta alhalin itama tanada ciwo a jikinta ta sanadiyar faɗan ku, nace ki daina shiga damuwar su, kina kawar da kan ki akan su, duk abinda Reemah zata yi just leave her she's a younger girl, yarinta yana damunta shiyasa nake binta a hankali, please ki kwantar da hankalin ki, gashi yanzu kin mun losse Baby...."

Ramlat tana kuka ta kwantar da kanta akan ƙirjinsa,
shima rungumarta ya yi yana rarrashinta...

Suna cikin wannan halin sai ga su Abbah sun shigo, Mai martaba yana riƙe da hannun Reemah ga Aunty A'isha da Aunty Maimuna da kuma Hajiya Kilishi da Ammy da kuma Ummy duk ana suka tarar da Roshan da Ramlat,
Abbah ne ya ce "lafiya kuwa kuke zaune anan?..."
Roshan ya ce "wallahi jikin ne bai gama warwarewa ba..."

Reemah wani irin harara take wurga musu, zuciyarta wani tafarfasa yake yana harbawa...

Abbah ya ce "to ka kaita É—akin da aka kwantar da ita gwara ta kwanta ta huta...."

Roshan ya ce "tam shikenam..."
Mai martaba ne ya dubi Ramlat sannan ya ce "Ramlatu ya jikin nakin?..."

Sai yanzu Ramlat ta lura da Mai martaba cikin fara'a ta gaishe shi,
Amsawa yayi tare da jajanta mata rashin da tayi.

Roshan yana riƙe da ita ya wuce da ita room ɗin ta,
suma wuce wa suka yi É—akin mai haihuwa,
tin kafin su shige suke jin kukan jaririya, shiga suka yi da sallama a bakin su gani suka yi babu Baiwar ALLAH sai yarinyar dake cikin gadonta mai basket,
Abbah ne ya ce "ha'a ina kuma tayi tabar yarinya sai kuka take?..."
Chapter 40 · 0% Book details