← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 68

Sashe 38

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baiwar Allah miƙe wa tayi tsaye ta nufi yanda Ramlat take tsaye, tana zuwa ta goya hannayenta akan ƙirji idonta akan ta tasau murmushi sannan ta ce "gwara su saboda tin a baya kafin su musulunta sunada kyawawan ɗabi'u da kuma kyakkyawan zuciya da kuma hali, ko kaɗan basu da abun kushe wa sai dai ace su ɗin Christal ne, kuma yanzu Alhamdulillah ko a yanzu suka koma ga Ubangijinsu Aljanna direct insha Allahu, basu ajiye abun gori ba kuma kyakkyawan niyansu da ayyukansu yana kan binsu har yanzu har ƙarshen rayuwar su,
Amma ke fa? abun gori da magana yana ƙarƙashin ki tinda yanzu haka cikin Umanki wanda ku ka sha nono ɗaya tana can gidan prison hauka tuƙuru take ga kuma jarabta daga Ubangiji tana fama da yankekken ƙafa ɗaya duk tsutsotsi sun cinye naman ƙafar, bin bokayen ta da zalunci da girman kai duk baiyi mata amfani ba sai abun gori da ta bar miki, itace shirka bijirewa Ubangiji sannan ita ce sawa ayi kisan kai tirr in banda tsautsayi da ƙaddara ba mai zai sa a haɗa jini daku......."

Baiwar ALLAH bata ƙarasa maganar ba taji an ɗauke ta da wani irin gigitaccen mari, ɗagowa tayi tana kallon Ramlat hannu akan fuska tana binta da kallo...
ai kafin Baiwar Allah ta furta wani abu taji Ƴar Amana itama ta ɗauke Ramlat da mari, kafin Ramlat ta ɗago haka Ƴar Amana ta ƙara zabga mata a ɗayan ɓangaren,
A ruɗe Ramlat ta ce "ni kika mara Reemah? to wallahi bazan ƙyale ki ba..."
haka Ramlat ta rarumi glass bottle akan table ta doka akan goshin Reemah...

Ƴar Amana ƙara tasau tare da dafe goshin kafin kace mai jini har ya wanke mata fuska,
Ramlat ganin haka yasa ta zaro ido waje baki a sake gaba ɗaya ta gama tsorita tsabar ɓacin rai bata san ta doka mata ƙwalba akai ba.

Baiwar ALLAH gaba ɗaya hankalinta ya gama tashi haka zuciyarta take harbawa da ƙarfi-ƙarfi, tsabar a kiɗime take ko motsi ta kasa yi sai ƙafar ta da yake ta kakkarwa idonta akan Reemah wacce jini ya gama wanke mata fuska..

Ramlat ce tayo kan Reemah tare da furta "wayyo Allah nashiga uku Reemah dan ALLAH kiyi haƙuri, wallahi ban san lokacin da na aikata miki haka ba...."
tana kuka hannunta na kakkarwa ta riƙe hannun Reemah cikin damuwa..

Tsabar raɗaɗi da juyawar ƙwaƙwalwa Ƴar Amana bata san lokacin da tayi kukan kura ta hankaɗa Ramlat baya da iya ƙarfin ta, Ramlat faɗawa tayi kan table sannan ta faɗa ƙasi tana riƙe da cikin ta domin ba ƙaramin buguwa tayi a cikin ba...

Itama Ƴar Amana ganin kanta yana ta juyawa tana ganin abubuwa suna komawa bibbiyu bata san lokacin da ta kai ƙasi ba, Baiwar ALLAH ganin haka yasa ta nufi yanda take da gudu itama tayi tuntuɓe da ƙafar Ramlat wacce take kwance sai faman shure-shure take, Baiwar ALLAH sai da ta ɗagu sama kafin ta doku a ƙasi itama, dokuwar da tayi sai akan ƙaton tumbin cikin ta, a ruɗe tasau wani irin gigitaccen ihu na fitar hayyaci lokaci guda ta sume a wurin...

Wannan ihun Baiwar Allah sai da ta ratsa kunnen kowa na gidan,
Roshan dake cikin motarsa a wurin parking gama wayarsa kenam da Razhdeen yana shirin tayar da mota yaji wannan ihun, ai ba shiri ya fito a cikin motar ya nufi cikin gidan,
shima Abbah da saurin sa ya baro falon sa ya koma ciki, duk matan gidan Hajiya Kilishi da Ammy su ma ko wacce sauƙowa tayi daga part ɗinta duk suka nufi ɗakin su dake daga nan muryar ta fito, Abbah da Roshan su ma a tare suka wuce ɗakin.

Ƴan aikin gidan kuwa dattijan mata su biyu sukam a falo suka tsaya sai faman lelleƙawa suke, ɗaya ta fito daga kitchen ɗaya kuma dama a falon take tana goge-gogen kujeru da dinning...

Su Abbah suna shiga suka tarar da abun mamaki duk tsayawa sukayi suna binsu da kallo É—aya bayan É—aya kuma duk babu mai motsi a cikin su,
Reemah tana kwance itama ta suma ga jini yanda yake ta gangaro mata akan goshi har da ƙananun ƙwalba akan goshin yanda suka sossoke ta dake ƙwalbar akan ta ya fashe....

Ramlat itama tana kwance ba motsi ga yanda jini yake bin ƙafarta duk ta wanke sket ɗinta da jini...

Sai Baiwar ALLAH ita kam tafi kowa jikkata domin yanda ta kife da cikinta bata ƙara motsawa ba...

Abbah bakin sa ne yake ta motsi yana furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un! Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, me zan gani haka..."

Ammy girgiza kai take tare da faɗin "wannan da duk kan alamu faɗa sukayi domin gashi har da fashewar ƙwalba kuma a Reemah aka ƙwaɗawa tinda ga duk goshinta yankuwan ƙwalbar ne..."

Hajiya Kilishi ta kalli Ramlat ta ce "Blinding kuma Ramlat? kuma tana da ciki fa?..."

Roshan tsabar yanda jikinsa yake ɓari bai tsaya furta komai ba haka ya nufi Baiwar ALLAH da hanzarinsa yaje ya ɗago ta domin ita ta ta matsalar babba ce ga kuma a yanda take, especially abun da ke cikinta zai iya raunana sosai, ɗaukar luɗa yayi mata ya fice da ita a gaggauce kai tsaye wurin parking motoci ya nufa,
Ramlat itama Hajiya Kilishi da Ammy ne suka É—ago ta tare da fitowa da ita suka nufi da ita wurin motoci, kafin su kai Ramlat kuwa tin tinin Roshan ya ja mota ya tafi da Baiwar ALLAH hospital,
Ana saka Ramlat sai Ammy ta shiga Security yaja suka tafi...

Sai ga Reemah itama an fito da ita Ƴan aiki su biyu ne suma suka ɗauko ta, itama shigar ta cikin motar akayi Hajiya Kilishi ta shiga Security nan ya tafi da su, daga baya shima Abbah ya shiga mota Sojansa ya ja shi suka nufi hospital, sai ƴan aiki aka bari a gidan da kuma sojojin dake bakin gate....

A wannan ranar wuni suka yi a hospital har dare,
Reemah dai ta riga su farfaɗowa duk an ɗaure mata kai da bandeji bayan an ciccire mata ƙananun ƙwalbar da ya shige ta, amma ba ƙaramin ciwo kanta ke mata ba domin anyi mata bugu na gaske ne, duk da ta farfaɗo amma bata gama dawowa hayyacinta ba, bata iya furta komai sai kuka...

Itama Ramlat da misalin ƙarfe 10 na dare ta farfaɗo bayan anyi mata wankin ciki domin buguwar da tayi ya janyo mata yin ɓari domin har cikin ya fara juyewa zuwa mutum almost 4 to 5 months, Ramlat jin babu labarin cikin ta yasa ta shiga damuwa sosai haka take kuka ba ƙaƙautawa..

Hajiya Kilishi da Ammy ne suke tare da ita a ɗakin sai faman rarrashin ta suke suna bata haƙuri, Roshan ne ya shigo shima idonsa akan ta cikin ɓacin rai ya tsaya a bakin gadon yana faɗin "duk me ya janyo haka? abun nakun har ya kai haka? a cikin kuna maganganun ku ta fatar baki yanzu har ta kai sai kun taɓa jikin juna? ku karnuka ne?..."

Ammy ce ta kalli Roshan ta ce "kaga Roshan ka sassauta haka ka dubi halin da take ciki..."

hura iskar bakinsa yayi yana jinjina kai ya ce "shikenam ai, kin yi losses kin rasa abunda ke cikin ki kin huta tinda bakida haƙuri da juriya, itama Ammata gata can har yanzu bata farfaɗo ba tana nan rai a hannun Allah, tana cikin watan haihuwar ta wannan al'amarin ya afku yanzu dole Operation za'a mata yanzu, fatana Allah yasa jaririn yana cikin ƙoshin lafiya...."

Yana kaiwa nan ya fice, Ramlat sabunta kukan ta tayi tana faÉ—in "wayyo Allah na shikenam na rasa cikina, innalillahi wa inna'ilaihi raju'un wayyo ciki naaa...."

Baiwar ALLAH tana can duk wani gwaje-gwaje da ya kamata ayi mata anyi yanzu sauran operation..

Abbah kuwa shine a wurin Reemah sai lallamin ta yake akan taci abinci amma taƙi, ga kayan fruits a ɗore kan table ko kaɗan ta ƙi sai hawaye,
Roshan ne ya shigo ya zauna a gefen kujerar da Abbah yake yana faÉ—in "har yanzu ta kasa cin komai?..."

Abbah kamar zai yi hawaye ya ce "ina tsoron kar ƙwaƙwalwar ta ya taɓu fa..."
Girgiza kai Roshan yayi sannan ya ce "bai shafi ƙwaƙwalwa ba domin duk wani gwajin kai anyi mata, har photon ƙwaƙwalwar aka ɗau tare da tsawaita bincike amma matsalar a iya wajen kai ya tsaya, amma dole zata fiskanci matsanancin ciwon kai da hajijiya haka..."

Abbah ya ce "to amma taƙi yin magana da cin abinci gaba ɗaya..."

Roshan idonsa akan Reemah ya ce "Shalele Ƙanwata zaki sha milk?..."
ya kai hannun sa kan flask na ruwan tea ya haÉ—a mata shayi mai kauri ya zauna a kusa da ita a bakin gado, ya É—ebi madarar a spoon zai kai saitin bakinta cikin kulawa,
wani irin kallo ta watsa masa tare da sa hannu ta buge kofin cikin ɓacin rai, kofin madarar ce ta kife a ƙasin tiles.
É—ago wa yayi yana kallon ta ya ce "why?..."

Harararsa tayi tare da faÉ—in "babu ruwanka da ni...."

Abbah murmushi yayi jin tayi magana, domin ya tsorita sosai ganin tinda ta farfaÉ—o bata yi magana ba har wannan lokacin sai yanzu, Roshan kallon ta yake cike da mamaki ya ce "me kuma nayi? ai kune ku ka yi babban laifi tinda ku ka so kashe kan ku..."

Reemah ƙoƙarin tashi take zata sauƙa daga kan gadon,
Abbah ya ce "ina zaki je Shalele?..."

Ta ce "ina Aunty Baiwar ALLAH ban ganta ba tin É—azu...."

Abbah ya ce "itama tana kwance ba lafiya..."

A ruÉ—e ta ce "Meya sameta Abbah?..."
Abbah kallon Roshan yayi cike da mamaki, ya ce "ba faÉ—a ku ka yi a É—aki ku uku ba? ai gaba É—ayanku sai da aka kawo ku asibiti..."

Roshan yana kallon ta ya ce "me ya faru daku har ku ka ji rauni a kayuwanku haka?..."
Chapter 38 · 0% Book details