Sashe 34
My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Reemah da hanzarin ta ta miƙe tana faɗin "Ni dai sai naje na gaya mata..."
Aunty Yolash ce tayi saurin riƙo hannun ta tare da faɗin "ke wallahi bazata taɓa yadda ba, ai da dabara za'a sanar mata, kada kowa ya kuskura ya sanar mata..."
Reemah ta ce "to shikenam bazan gaya ba amma ina son zuwa wurin ta..."
Aunty Yolash ta ce "to je ki..."
Reemah fita tayi da gudu cikin farin ciki...
Ramlat itama tana cikin farin ciki lokaci guda ta haÉ—e rai domin a yanzu Reemah ce zata zamo abokiyar kishinta domin Roshan ya sanar mata cewa yana sonta...
Haka suka cigaba da hirar su a É—akin...
Reemah kuwa haka tazo ta wuce matan gidan a falo da gudu su biyar matan mai martaba da matan Abbah sai Madam Parveen, kai tsaye ta wuce room É—in Baiwar ALLAH,
tana shiga ta tarar da ita kwance akan gado ta kifar da kanta akan gado ba komai take ba sai kuka, domin tin daga lokacin da Roshan ya sanar mata magana da kuma munanan kalaman da Ramlat ta gaya mata yasa take kuka har zuwa lokacin nan,
Reemah ce tayo kanta tare da hawa saman gado itama ta kwanta tare da rungumar bayanta..
Baiwar ALLAH ɗagowa tayi ta sauƙe idonta akan Reemah, ganin ta yasa tayi saurin tashi zaune tana faɗin "Ƴar Amana yau ke ce a yanda nake?..."
Ƴar Amana ganin hawaye akan fuskar ta yasa tasa hannu tana share mata hawaye itama kukan ne yake shirin kuɓuto mata da sauri tasa hannu ta rungume ta sosai,
Baiwar ALLAH cike da mamaki da kuma farin ciki itama bata san lokacin da ta rungumeta ba..
sun É—au tsawon lokaci a haka kafin daga bisani suka É—ago suna kallon juna,
Ƴar Amana tana kuka ta ce "Aunty Baiwar Allah dan ALLAH kiyi haƙuri ki gafarce ni, na aikata miki kuskure saboda son zuciya ta, sannan nayi miki butulci na manta alkhairin da kika mun, tin ina jaririya ta ake baki raino na komai ke kike mun, kin sabar wa kanki wahala saboda Ni, idan bani da lafiya kwana kike bakiyi bacci ba duk ata dalili na, idan na gusa a kusa da ke hankalin ki baya kwanciya har sai kin jawo ni a kusa dake, amma yau ni ce duk na manta wannan saboda son zuciya ta, banyi adalci ba Aunty Baiwar Allah ina matuƙar ƙaunar ki ina sonki ...."
ta ƙarasa maganar tare da fashe wa da matsanancin kuka,
Baiwar ALLAH ce itama ta rungume ta tana kuka tare da faÉ—in "duk me ya kawo waÉ—annan maganganun, nifa nayi miji ne saboda Allah, banaso kina tayar da hankalin ki akan wannan, duk abinda zan yi a rayuwa ina yinshi ne da zuciya É—aya kuma inayin komai don Allah da kuma ladan da zan samu a wurin sa, saboda ki kwantar da hankalin komai ya wuce, duk abinda ya wuce ya wuce kenam ko a wurin Allah,
a rayuwa duk abinda nayi miki da wanda zan yi muku duk bai kai wanda iyayenki suka yi miki ba saboda su sukayi silar kawo ki duniya, ni kuma a duniyar muka haÉ—u, dan Allah kin san bana son ganin hawayen ki ba..."
Reemah ɗagowa tayi tana kuka ta ce "na faɗa miki munanan kalamai na ɓatanci, sannan na kushe miki jaririn dake cikin cikin ki, alhalin ke ma mahaifiya ce a wuri na, shin kin yafe mun? ...."
Baiwar ALLAH murmushi tayi sannan ta ce "ni babu abinda kika yi mun, saboda haka ki kwantar da hankalin ki na yafe miki duniya da lahira, ai dai nasan duk kishi ne, kishi kuma kumallon mata, nima ai inada kishi bakida yanda nake kishi akan Yaya Roshan ba..."
Dariya Reemah tayi tana girgiza kai ta ce "Aunty Baiwar ALLAH kenam zuciyar ki ta kusan hutawa kema, kin kusan samun muradin ki na gaskiya..."
Baiwar ALLAH cikin rashin fahimta take bin Ƴar Amana da kallo tana sakin murmushi...
A wannan lokacin Baiwar ALLAH da Ƴar Amana wuni sukayi a ɗaki suna shan hirar su, wanda tsawon shekaru basu haɗu sun zauna kamar yau ba...
Har zuwa yamma Baiwar Allah da Ƴar Amana suna tare, tare suka yi sallah sannan suka ci abinci, Baiwar Allah gaba ɗaya ji tayi kamar an yaye mata damuwar ta gaba ɗaya domin a wannan ranar Ƴar Amana ba ƙaramin ɗebe mata kewa tayi ba, suna cikin hirar su sai ga Ƴar tinny ta shigo da gudu tana faɗin "Aunty Daughter wai kuzo Amarya Aunty Pinky zata tafi ƙasar Saudiyya gidan mijinta ...."
Ƴar Amana ta ce "a yau ne daman?..."
Ƴar tinny ta ce "ai ita kaɗai ce zata tafi a yau har da mijinta Barrister Arash..."
Baiwar Allah riƙo hannun Ƴar Amana tayi tana faɗin "tashi muje..."
Pinky an shirya ta tsab cikin wedding gown har jan ƙasi yake, an yafa mata gyalen net mai irin rigar jikinta ba ƙaramin kyau tayi ba,
Ga masu rakiyar Amarya suma sun sha fashion motoci ne a jere sun kai ashirin duk zasu nufi airport daga nan su shiga jirgi, kowa ya shirya har da su Ummy da Rukky suma dake tafiyar su ba yau bane, su ma har da su zasu je ƙasar Saudiyya ganin ɗakin ƴar uwarsu, ga Minal da Ramlat da Aunty Yolash da matan gidan kab har da baƙin da suka zo biki,
Baiwar ALLAH da Ƴar Amana sakin baki sukayi suna kallon kowa da kowa domin su ba'a sanar musu cewa za'a tafi a yau ba shiyasa basu shirya ba,
Especially Ƴar Amana da ta kasance daga ita sai wando zuwa gwiwa da T-shirt turo baki tayi ganin kowa yana ta shiga mota ga wankan da suka sha ba ƙarya,
Ƴar Amana ganin Mahaifiyar itama tana shirin shiga mota yasa ta ruga da gudu taje wurinta ta riƙe ta tana faɗin "Mama! Mama tafiya zakiyi ki barni..."
Aunty A'isha buɗe baki tayi tana kallon ta daga sama har ƙasa ta ce "me zan gani haka? me ya hanani shiryawa kina ganin kowa yana ta shiri..."
Reemah ta ce "to ni ban sani ba, naga cewa akayi gobe ne za'a rakasu, tinda safe nake É—akin Aunty Baiwar ALLAH kuma wallahi sai naje..."
Ta ƙarasa maganar tana kukan shagwaɓa haɗi da bubbuga ƙafarta tana jumping,
Aunty A'isha ta ce "cab É—in ai kuwa baki isa ki bini a haka ba kamar wata Æ´ar inyamura..."
"wallahi sai na biku, kuma naga kafin na shirya tafiya zaku yi ku barni, kuma! kuma ban taɓa zuwa ƙasar Saudiyya ba...."
Aunty A'isha ta ce "to dole ne sai kinje? ki bari wata rana Abul É—in ki zai kai ki..."
Aunty Maimuna ce tazo gaban Reemah da doguwar rigar Abaya a hannunta yanda taje ta ɗauko mata, ta zura mata tare da yafa mata gyalen Abayar, dake ƙananun kaya ne a jikin ta sai kayan cikin bai nuna ta ba,
Aunty Maimuna ta riƙo hannunta tare da faɗin "zo mu shiga cikin motar, ina za'a tafi a barki Shalele..."
Ƴar Amana juyawa tayi tana kallon Baiwar Allah wacce take tsaye daga nesa tana mata dariya ganin irin shagwaɓar da take zubawa,
Ƴar Amana ta ce "Aunty! Aunty!! ga can Aunty Baiwar Allah itama zata bimu fa..."
Aunty Maimuna ta ce "to shiga ciki bari naje na mata magana..."
Kai tsaye ta nufi wurin ta, tana zuwa ta same ta tare da faÉ—in "ya kike tsaye ne kizo mu tafi mana..."
Baiwar ALLAH ta ce "gaskiya bazan iya zuwa ba saboda bana jin daÉ—in jikina sannan bana son hayaniya..."
Aunty Maimuna ta ce "to shikenam komai É—an lafiya ne, ya kamata kije ki kwanta ki huta ko?...."
Baiwar ALLAH ta amsa mata tare da sakin murmushi...
Ƴar Amana ganin Baiwar ALLAH taƙi zuwa yasa ta fito daga cikin mota tazo yanda take tana faɗin "Aunty Baiwar Allah dan Allah kizo mu tafi kowa fa na gidan tafiya zasu yi..."
Baiwar ALLAH ta ce "kinga saboda cikina banason shiga cikin jama'a, nasan za'a iya mauje mun ciki sannan kuma idan hayaniya tayi mun yawa kaina ciwo yake, kawai ku tafi..."
Ƴar Amana ta ce "to shikenam nima na fasa zuwa zan taya ki zama, kinga ba kowa a gidan fa..."
Baiwar ALLAH ta ce "kinga kije kawai bacci nake son yi, akwai maganin da ake sha, inason zama ni kaÉ—ai ne..."
Ƴar Amana ta ce "shikenam Auntyna ki kula mun da kan ki..." ta rungume ta tare da sumbatar ta akan goshi ta tafi,
murmushi Baiwar Allah tayi tana farin cikin kasancewar ta da Ƴar Amanar ta...
tana tsaye har duk motocin suka tafi, motar Amarya da Æ´an uwanta kuwa tin tinin suka tafi, yanzu babu mota ko É—aya a gidan kowa ya tafi sai iya ita kaÉ—ai,
Madam Parveen da Aunty Yolash sunyi tunanin Baiwar Allah da Ƴar Amana a mota ɗaya zasu tafi domin basu yi tunanin bazata je ba, da bazasu barta ita kaɗai ba tinda ba yau zasu dawo ba sai gobe....
Baiwar ALLAH tana tsaye ita kaɗai ta shiga nazarin duniya, can taji cikinta ya yi wani irin murɗewa alamun jaririn ne yake juyawa, da sauri ta kama cikinta tare da sakin ƙara dai-dai lokacin da Roshan ya buɗe gate ɗin compound ya shugo, idonsa ne ya sauƙa akan ta tana shirin kaiwa ƙasi tana riƙe da ciki sai ihu take ta kurmawa...
Da sauri ya nufi yanda take yayi saurin riƙo ta kafin taje ƙasi ya mannata a jikinsa yana faɗin "Sorry! Sorry!! Sorry!!! Okay..."
hannunsa yakai kan tumbin cikinta yaji cikin ne yake motsi ya ce "Sorry! jaririn ne yake juyi alamun yana cikin ƙoshin lafiya, muje ciki ko ki huta..."
Haka ya rirriƙe ta yana tafiya da ita a hankali, ganin tafiyar zai ɓata masa lokaci yasa ya ɗauke ta yayi mata ɗaukar luɗa ya nufi ciki da ita........
Typing âœï¸ Asmeetah writer.
*MY ENEMY*
*TAKUN ƘARSHE*
*BOOK 3*
51 to 55