Sashe 21
My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maimuna ce ta fara kora bayani kamar haka,
"nasan dai kun san ni ce masoyiyar Mai martaba tin farko, kuma ni ce yayi burin Aura, ita kuma Maamie ƙawata ce sosai, tare muka tashi tin yarinta, sai dai kuma ita Allah ya yo ta a gidan talakawa, kullum tana cikin damuwa da tashin hankali musamman lokacin da taji labarin Aurena, na ɗauka saboda zanyi Aure ne yasa ta kasa kwantar da hankalin ta, hakan yasa na nemi alfarma a wurin Mai martaba cewa inaso ya haɗa mu ya Aura ni da Maamie, a lokacin ya nuna mun rashin yardar sa, amma na dage akan saiya Aure ta saboda zata fi samun kulawa da nutsuwa, nayi tunanin Maamie mutumiyar kirki ce ashe mai fuska biyu ce,
Bayan mai martaba ya Aure mu a lokacin na ɗauki Maamie tamkar ƴar uwata, na ɗauke ta da zuciya ɗaya, ashe Maamie ƙulle-ƙulle take akan ta fitar dani daga gidan Mai martaba,
Duk wani sirri na sai na gaya wa Maamie, duk abunda ya faru dani sai na sanar mata, duk hirar da mukayi da mai martaba indai akan abinda ya shafi rayuwar mu ne gaba É—aya saina sanar mata,
A lokacin da na samu juna biyu kafin na sanar wa mai martaba sai da na fara sanar wa Maamie, ta nuna farin cikinta matuƙa a fuska amma a cikin zuciyar ta tamkar ana hura wuta ne, duk ban gano hakan ba, na sanar mata cewa inada ciki amma ina jiran Mai martaba ya dawo shima saina sanar masa,
Maamie ta ce mun kada na sanar masa yanzu na bari nayi masa bazata, sai dai yaga cikin ya fito, na amsa mata da hakan, bance masa inada ciki ba,
Maamie daga lokacin ta ɗaura ɗamarar yaƙinta akaina,
wata rana na shiga bathroom yin wanka ashe Maamie ta ƙira wani mutumi gidan suna jiran na shiga wanka ta turo mutumin, mutumin ya shigo ɗakin da nake tare da cire rigar jikinsa ya hau saman gado na ya kwanta dai-dai lokacin da Mai martaba ya dawo cikin masarauta,
kuma dake a ranar kwanan ɗaki nane anan ya tarar da mutumin yana kwance yana daddanna wayar sa, jin hayaniya yasa nayi saurin fitowa daga cikin toilet, abunda na tarar ne ya tayar mun da hankali, daga lokacin mai martaba yasa aka kama mutumin, ni kuma bai ƙara saurarona ba, ya ƙaurace mun, ya ɗauki tsanar duniya ya ɗora mun, duk ban kawo a raina cewa tarkon Maamie bane, ita kuma Maamie bata daina bani kulawa ba na makirci, kullum tana ɗakin da nake tana shan ciki na, a lokacin da nake baƙin cikin mijina ya ƙaurace mun ita kuma a lokacin kamar anyi ma ta bushara da gidan Aljanna ne,
Bayan kwana biyu akwai ƙasar da Mai martaba ya tafi kuma sai yayi kwana biyu kafin ya dawo,
cikin dare ina kwance na fara jin bugun ƙofar ɗakin da nake, ina buɗe wa naji an shaƙo wuyana tare da ɗaure baki na da wani ƙyalle akayi waje da ni, inaji ina gani ba halin yin ihu haka aka sakani a cikin mota aka fita dani,
ba'a sauƙe ni a ko ina ba sai a cikin daji, haka na buɗe ido na ganni a cikin wannan halin, baki na kuma yana ɗaure da ƙyalle sai ido da nake bin wurin da kallo ga hasken mota da ya haska wurin sakamakon duhun dake wajen,
Idanu nane suka fara sauƙa akan Maamie wacce ta tsaya mun a gaba, sai kuma wannan mutumin wato Ghali,
nayi mamaki sosai domin ban taɓa tunanin Maamie zata iya aikata mun wannan ta'addanci ba sai ranar, tafi so ta zauna ita kaɗai a gidan Mai martaba duk da ni na sa aka aure ta, sannan babban baƙin cikinta shine cikin dake jikina har na tsawon wata huɗu, ina ji ina gani ga ƙaton ramin da aka tona kafin zuwa na yanda za'a bisine ni da raina,
Ina ɗaɗɗaure da igiya hannu da ƙafa suka hankaɗani ciki tare da zuba mun ƙasa, Maamie tana tsaye Ghali ya gama rufe ni da ƙasa saida suka shafe ni da ƙasa kafin Maamie taje ta shiga mota ita da Ghali suka tafi,
daga lokacin ban ƙara sanin a inda nake ba,
ashe daga baya Ghali ya dawo ya buɗe ni ba tare da sanin Maamie ba, yasa aka fitar dani daga ƙasar Jidder gaba ɗaya,
Bayan farfaɗowa ta Ghali na gani shi yake zuwa dubani a yanda ya killace ni, ya sanar mun halin da ake ciki sannan ya cigaba da bani kulawa, ita kuwa Maamie a tunanin ta an rufe shafi na, a ƙasar da na cigaba da zama shine ƙasar Iran, anan har cikina ya tsufa na haifi jaririn ɗana, amma kuma duk wasu bayanai na masarautar Jidder ina sani, nasan duk halin da ake ciki a masarauta, har yaro na ya girma a lokacin da naji labarin Mai martaba ya ƙara Aure ba ƙaramin tausayawa Amaryar sa nayi ba, dan ma ƴar sarkin ƙasar Niger ce su ma sunada ƙarfi amma duk da hakan bai hana Maamie ƙuntata mata ba, duk biye-biyen bokayenta na sani, tayi yunƙurin hana Indo ɗaukar ciki amma sai dai bokan bashida ikon aiwatar da aikinsa akan Indo saboda itama iyayenta basu barta haka ba, amma su ba ta hanyar bin boka ba, har Allah yasa Indo ta haihu a lokacin naji labarin an cire mata mahaifa kuma nasan makircin Maamie ne, a lokacin da tasa aje a bisine jaririya Ghali bai bi maganar ta ba haka ya wuce Nigeria da ita ya kaita gidan marayu, duk halin da Reemah ta shiga duk akan idon mu ne, da lokacin da Razhdeen ya tsince ta, sai dai kuma ni kafin zuwa wannan lokacin na rasa yarona, ba mutuwa yayi ba ɓata yayi ban sani ba shin sace shi akayi ko kuma mutuwa yayi Allahu a'alamu, Ni dai na barshi ne akan zai je ƙasar jidder can masarauta, akan zai bayyana cewa shi ɗan mai martaba ne sannan zai sanar cewa ina nan da raina, bayan ya tafi nake jin labarin anyi kidnaping ɗin su, nayi shige da fice amma har yanzu banji labarin sa ba, da haka har na haƙura da Yareema Ashmar mai shekara 28....."
Maimuna fashewa tayi da matsanancin kuka bayan ta gama bada labarin abinda ya faru da ita..
Ghali dake zaune shine shaidar hakan domin shi yake kai mata wasu bayanai na cikin masarauta, fuska biyu yayi yana ɓangaren Maamie sannan yana ɓangaren Maimuna amma ita Maamie yana zaune ne da ita saboda duk abubuwan da zata aikata na sirri zai ɗauka yakai wa Maimuna....
Mai martaba yana zaune yayi tsumu da shi ga yanda hawaye yake ta zuba daga cikin ƙwayar idanuwansa,
Aunty A'isha da gudu ta zo yanda Ƴar Amana take a kwance saman cinyar Baiwar ALLAH ta ɗago da ita tare da rungumar ta jikinta sosai tare da fashewa da matsanancin kuka tana girgiza ta tare da faɗin "Reemah ta ta dawo gare Ni, Allah na gode maka, wayyo Allah Reemah ta, Allah na gode maka daka bayyanar mun da Reemah...."
Abbah rasa abun cewa yayi sai jinjina kai yake tayi domin wannan al'amarin babba ne,
Duk mutanen falon babu wanda bai tausaya wa Maimuna da Reemah ba, ita wannan an rabata da mijinta ita kuma Reemah an rabata da iyayenta...
Mai martaba yana kuka ya ce "Maimuna meyasa baki dawo gare ni ba?..."
Maimuna itama kukan take ta ce "Yaro na yaso ya bayyanar da ni Allah bai so ba, ni kuma ina fargaban bayyana kaina saboda Maamie zata iya É—ana mun wani tarko kuma du, ina tsoron Allah ina tsoron Maamie, matar da zata iya kashe mutum ai babu sauran imani a tattare da ita...."
Maamie wani irin tsalle ta daka tare da miƙewa tsaye tana jumping tare da faɗin "hEheeee Ahayyeeee nanayeeee Anayi muna jin daɗi ana bariii muna jin haushi, duk saina kashe ku wallahi tallahi, na rantse da Allah sai na kashe ku gaba ɗayan ku...."
Pinky da Rukky a zabure suka tashi cikin tsoro suka nufi yanda Hajiya Kilishi take a zaune duk suka rurrungume ta, itama Hajiya Kilishi rungumar su tayi sosai jin yanda take ta rantsuwa zata kashe su, kowa tsoro ne ya bayyana akan fuskar sa banda mazan wajen,
Uwar masu gida itama da gudu taje da rungumi Aunty Yolash sosai jikinta har wani kakkarwa yake,
Madam Parveen itama a zabure tazo ta jawo Baiwar ALLAH a jiki
ta rungumeta tana faɗin "dan Allah dan Annabi ku bata haƙuri kar ta kashe mu..."
Ammy rufe idonta tayi tana jero Addu'o'i..
Roshan cikin fushi da takaici yake bin Maamie da kallo domin abubuwan da ta aikata ko wanda bashida addini iya kaci...
Razhdeen yana zaune duk yana jin abubuwan da yake faruwa amma ba halin motsawa...
Maamie tana cikin haukar ta Mai martaba ya zuciyo ya tashi a fusace ya zabga mata wani irin gigitaccen mari har sai da ta kife akan kujera,
haka yasa hannu ya shaƙe mata wuya yana faɗin "kafin ki kashe su ni zan fara aika ki lahira, na tsane ki wallahi...."
Abbah da Chief Suraj ne suka taso su na ƙoƙarin janye Mai martaba,
Ramlat itama duk ta wanke fuskar ta da hawaye, gaba É—aya jikinta yayi sanyi kanta a sunkuye, duk haukar da Mamie take yi bata É—ago ba balle ta kalli yanda take, duk wannan zaluncin da Mamie ta aikata Ramlat bata san da labarin ba....
Abbah ne ya ƙira waya, ba jumawa sojojin sa suka shigo su uku ƙarfafa, aka sanar musu cewa a tafi da Mamie a kaita kotu, duk abunda kotu ta yanke mata shikenam duk da bata cikin hankalin ta yanzu.....
Sannan Abbah ya ce wa ɗaya daga cikin sojoji cewa ya tafi da su Pinky can headquarters a je fa su ɗakin duhu tare da gana musu azabar da sai sun kusan mutuwa, Abbah ya lissafo irin hukuncin da za'a rinƙa gana musu, sannan a tsayar da su, su kwana a tsaye, da zaran sun zauna a jona musu shocking a jiki, kullum aita gana musu azaba ba ƙaƙƙautawa sannan abinci sau ɗaya za'a basu su ci sai kuma washe gari har sai sun gane kuran su....