← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 68

Sashe 57

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Roshan cikin rashin fahimta ya ce "kenam kuna nufin kuce Shalele ta koma aljana? kenam da gaske ne ni mijin Aljana ne indai haka ne, to kuwa sunan nan bazai taɓa goguwa ba ko ina zan iya shiga da sunan mijin Aljana indai bata bayyana ba..."
Roshan yana kaiwa nan ya haura upstairs, yana shiga room É—insa ya wurgar da rigar sa saman gado, juyawar da zai yi yaga anyi rubutu a jikin madubi da jini an rubuta "SAVE ME YAYA ROSHAN..."
Ƴar Amana ce ta rubuta haka a yayin da take tsaye sai zubda ƙwallah take domin tana gab da rasa Roshan indai ta zama Aljanan asali kuma sauran kwana ɗaya hakan ya faru domin manyan Aljanu sun haɗa Meeting akan ta, in har ta zama Aljana bazata taɓa dawowa mutum ba balle ta kasance a cikin ƴan uwanta...

Roshan gaban mirror ya je ya tsaya murya na kakkarwa ya furta "Shalele!
Dan ALLAH ki bayyana mun kan ki Shalele, ina buƙatar ki a kusa da ni..."
Ƴar Amana gaban mirror taje itama tayi facing ɗin mirror sai ga ta ta bayyana a jikin madubi, a ruɗe Roshan ya ja da baya ganin Ƴar Amana ta bayyana, muryarsa haka yake kakkarwa ya ce "Shalele..."

Ƴar Amana tana kuka ta ce "Yaya Roshan na kusa na rasa ka, an yaudare ni Yaya Roshan, sunce zasu dawo dani da zaran ka bayyana soyayya ta sai kuma suka canza magana, daman so suke su ɗauke ni sai ga shi dama tazo musu, ban san ya zanyi na kuɓuce musu ba, dan Allah ka taimake ni Yaya Roshan, gobe da yamma suke son mayar ni Aljana domin rana ce ta musamman a wurin su, inason kafin lokacin ka cece ni ina cikin tashin hankali..."

Roshan yana kuka ya ce "Shalele ta wani hanya zan bi na ceceki?..."

Ta ce "akwai mafita guda ɗaya kana yin wannan shikenam sauran ƙwatoni..."

Roshan ya ce "meye mafita?..."

Ƴar Amana ta ce "yau da misalin ƙarfe 2 na dare zaka ga wani haske ya bayyano maka, cikin wannan hasken zaka shiga daga nan za'a kai ka yanda nake, Amma muddin baka yi bacci ba, idan hasken ya bayyana ya same ka kana bacci to ɓace wa zai yi daga nan babu wata hanyar da zaka same ni..."
tana kaiwa nan tayi ɓacewar ta,
A gigice Roshan ya fara ƙiran sunanta "Shalele! Shalele!! Reemah!!! Reemahhh!!!!...."

Haka yake ambatar sunan ta Dai-dai lokacin da Abbah da Razhdeen suka shigo, da hanzarin su suka ƙarisa wurin da Roshan yake..
Abbah da Razhdeen ne suka riƙe shi suna faɗin "meya faru Roshan..."

Roshan cikin tashin hankali yake faɗin "Abbah zasu mayar ta Aljana shikenam zan rasa abar ƙaunataa..."

Abbah ya ce "insha Allahu bazaka rasata ba, zata dawo da yardar Allah..."

Daƙer suka samu su ka rarrashe shi...

★★★

Misalin ƙarfe 12 na dare Roshan yana nan da idonsa sai zarya yake a cikin room ɗinsa, ko zama bai samu damar yi ba duk da yasan ba baccin zai yi ba domin yanzu kusan kwana yake baya bacci sai da safe yake baccin safe, jira yake yaga zuwan hasken da Ƴar Amana ta sanar masa zai zo, domin a halin yanzu a shirye yake da ya rasa rayuwar sa saboda ita, haka ya cigaba da zirga-zirga a cikin ɗakin idan ya gaji sai ya zauna a bakin gado, da haka har lokaci ya yi, yana duba agogo ya ga ƙarfe 2 dai-dai miƙewa tsaye ya yi yana son ganin bayyanar hasken domin yana muradin ganin Reemah...

Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga hasken nan ya bayyana kamar walƙiya, haske ne na kashe ido sai da Roshan ya rufe idonsa da hannayensa, haka yake tafiya a hankali idonsa a rufe yana yowa wurin hasken tare da ambatan sunan Allah, ba abinda yake sai jero Addu'o'i da haka ya shige cikin hasken, nan take hasken ya ɓace da shi...

Wani wuri ne shi ba kogo ba sannan shi ba É—aki ba, wurin a gewaye babu ko hanyar fita bare window, ga haske ta ko ina shi kaÉ—ai ya bayyana babu motsin kowa,
Roshan ganinsa a wurin da hasken ya ajiye shi ne yasa shi faÉ—in "Reemah! Reemah!! gani nazo yanda kike ki bayyana mun kan ki, kina inaaa...."

Roshan yana magana haka wurin yake ɗaukan maganar sai muryar sa take fitowa bibbiyu, sautin muryarsa ne yake fita da ƙarfi haɗi da rarrabe wa,
Haka ya cigaba da magana yana ƙiran sunan Reemah amma babu wanda ya bayyana a wurin, sai da ya ɗau tsawon lokuta yana zarya a filin wurin kafin ya ji an ambaci sunan sa ta bayan sa "Yaya Roshan..."

Dasauri ya waiga ganin Ƴar Amana yasa shi sakin murmushi yana faɗin "Allah na gode maka daka bayyanar mun da farin ciki na..."

Da hanzarin sa ya nufi yanda take kafin ya isa yaji an ƙara ƙiran sunan sa ta bayan sa "Yaya Roshan.."
dakatawa ya yi da tafiyar ya ƙara juya ya kuma ganin Ƴar Amana cike da mamaki yake bin su da kallo su biyu siffar su iri ɗaya hatta kayan jikinsu komai da komai, kamanni kamar an tsaga kara, haka ya shiga cikin zulumi idan ya kalli wannan sai ya juya ya kalli wancan gaba ɗaya sun kasa masa tunani, juyawa yayi zai koma kan wacce ta zo daga baya still ya ji an ƙara ƙiran sunan sa "Yaya Roshan..."
kuma du ta ukun ta bayyana kuma duk kamannin su É—aya, Roshan tsayawa yayi yana binsu da kallo kuma du ta huÉ—u ta sake bayyana tare da ambatar sunansa "Yaya Roshan..."
Haka ta biyar ma ta bayyana sai da Ƴar Amana ta kasu kashi goma ko wacce tana ƙiran sa da Yaya Roshan...

Gasu nan kashi-kashi ko wacce tana tsaye a wurin ta babu abinda ya banbanta a jikinsu komai nasu iri ɗaya hatta sumar gashin bazaka iya tantance wannan Ƴar Amana ce ba,
Roshan gaba ɗaya hankalinsa yayi matuƙar tashi ganin wannan al'amarin,
Ji yayi sautin ƙatuwar murya ta bayyana ana faɗin "Roshan a cikin ƴan matan nan masu kamanni ɗaya ka zaɓi Reemah ka, idan ka zaɓi wacce ba asalin ita bace to duk zasu ɓace ne kuma ka rasa ta har abada, idan kuma ka zaɓe ta to duk sauran zasu ɓace su bar maka ita amma bazaka tafi da ita ba a halin yanzu ba amma zamu kwatanta maka a yanda zaka same ta a matsayin mutum, kuma zamu zare hannun mu akanta wannan alƙawarin mu ne..."

Daga nan aka daina magana...
Su kuwa Ƴan matan duk suka fara kuka suna faɗin "Yaya Roshan ni ce Reemah ka taimake ni, wallahi ni ce Shalelen ka..."

Haka muryoyi suke fita daga bakinsu, kuma duk muryoyin iri É—aya, lokaci guda duk suka yi shuru daga nan ko wacce ta fara maganar ta da ban, ta farkon ce ta fara tana kuka ta ce "Yaya Roshan ka taimake ni ina cikin tashin hankali ni ce Reemah..."
ÆŠayar ma ta fara kuka ta ce "Yaya Roshan kar ka yarda da su ni ce Shalelen ka..."
ÆŠaya ma ta ce "Yaya Roshan Dan ALLAH ka taimake ni wallahi ni ce Shalelen ka..."
ÆŠayar ma ta ce "Yaya Roshan ashe akwai lokacin da bazaka iya tantance jikinka ba? Shalelen ka ce fa take magana..."
ÆŠayar ma ta ce "Yaya Roshan kar ka yarda da su duk yaudarar ka zasu yi ni ce asalin Reemah kuma Shalelen ka..."
Duk haka suka kasance cikin launa magana, ko wacce tana magana ne yanda zai yadda akan Reemah ce...

Roshan hannu ya É—ora akansa yana faÉ—in "Oh my God! Shalele meyasa zaki mun haka, dan Allah ki mun wani alamar da zai nuna mun cewa kece Shalele nah..."

Duk hawaye suka fara yi ko wacce ta fara faɗin "Yaya Roshan nace maka ni ce Shalelen ka amma kaƙi yadda wata alama zan nuna maka, ka yadda da ni dan Allah..."

Roshan gaba ɗaya hankalinsa ne yake shirin barin jikinsa, suna shirin rikirkita masa ƙwakkwalwa, domin babu wata alama da zai nuna cewa wannan ce Reemah,
ba shi da wata mafita haka ya durƙusa da gwiwowinsa ya yi sujjada anan ya kaiwa Allah kukan sa da neman taimakon Allah,
"Ya Ubangijina na kawo kuka na gare ka domin kai kaÉ—ai zaka iya magance mun damuwa ta, Ya Allah ka taimake ni, ka kawo mun agaji, ka ceci baiwar ka tana cikin wani hali...."
Sai da ya gama Addu'o'in sa da neman taimakon Allah kafin ya É—ago a hankali ga yanda idanuwansa suka yi jawur,
Haka yake bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya cikin ikon ALLAH idanuwansa suka sauƙa akan ta tsakiya wacce alamu ya nuna cewa Reemah ce ta hanyar ganin inuwar ta, wanda sauran kuma inuwarsu bai bayyana ba sai ita kaɗai, zaro ido ya yi waje cike da farin ciki da gudun gaske ya miƙe ya nufi yanda take, a kiɗime ya rungume ta tare da ɗagata sama yana juyawa da da ita tsabar farin ciki...

Su kuwa sauran duk tsaya kallonsu suka yi lokaci guda duk suka ɓace, sai ya rage daga Roshan sai Ƴar Amana, har zuwa yanzu suna rungume da juna cikin farin ciki daga bisani suka rabe a ruɗe Roshan ya kama fuskar ta yana faɗin "Shalele nah kin bayyana, Allah nagode maka daka bayyanar mun da matata, Allah nagode maka, Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!..."

Ƴar Amana kuka take haɗe da dariya ta ce "Yaya Roshan taya ga gano ni? ina so na nuna maka alamar da zaka gane ni amma sai dai duk abinda nayi suma yinsa suke, nagode sosai, ka ceceni daga hannunsu Yaya Roshan..."

Roshan ya ce "yanzu abinda zai faru shine ki nema mana hanyar fita daga nan, ina so na koma da ke gida..."

Murya suka ji daga sama an furta "Bazaka tafi da ita ba, yau ƙarfe 6 na safe zamu turo maka wani ɗan maƙullo wato wani ƙaramin aljanin mu shi zai nuna maka hanyar da zaka bi kaje wurin da zaka samu Reemah, bil adama basa shiga wurin da daddare sai da safe, don haka ka shirya zuwa wurin da safe ƙarfe 6, don haka yanzu zamu mayar ka yanda ka fito..."
Chapter 57 · 0% Book details