Sashe 56
My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Roshan hannu yasa zai ture ta gefe Dai-dai lokacin da Ƴar Amana tasa hannu itama ta hankaɗata, lokaci guda Salma tayi gefe ta doku a ƙasin floor nan take ta gurɗe a hannu dake akan hannu ta faɗi,
Roshan cike da mamaki yake bin ta da kallo domin shi ba wani ture ta da har zata faÉ—i ya yi ba, É—ago hannunsa ya yi yana dudduba wa,
Ƙawar ta da take gefe ta tafo da gudu zata yo kanta taga Roshan ya miƙa mata hannu zai ɗagota,
Salma miƙa masa hannunta marar ciwo tayi tana murmushi domin ita damuwar ta ba ciwon ba,
haka ya É—ago ta yana faÉ—in "sorry! fatan baki ji ciwo ba..."
Ƴar Amana wani irin kallo ta watsa mata cike da takaici da baƙin ciki domin ta tsani wata budurwa ta raɓi jikin Roshan,
Salma miƙa masa hannun da taji ciwo tayi ta ce "naji ciwo a hannu na..."
Roshan riƙe hannun ya yi ya ce "Ok muje na duba miki...."
har sun juya zasu nufi cikin hospital Ƙawar Salma ta taɓa ta baya, juyawa tayi tana kallon ta da murmushi akan fuskar ta anan ƙawar take nuna mata rubutun bayan sa, bayan ta karanta itama zaro ido tayi baki a sake ta tsaya cak, shima tsayawa ya yi ya ce "muje mana..."
Girgiza masa kai tayi ta ce "a'a ka je kawai zan zo daga baya..." ta ƙare maganar murya na kakkarwa...
Ya ce "Ok shikenam.."
yayi gaba abinsa...
Salma rungumar ƙawar ta tayi tana sauƙe numfashi ta ce "mijin Aljana kuma? akwai alamar tambaya akan Roshan daman Wayyo Allah..."
Ƴar Amana murmushi tayi sannan ta buɗe wa Salma kunne yanda zata ji duk abinda zata ce, anan ta fara magana tana faɗin "wannan tsoritar da kika yi kaɗan kenam..."
Salma jin an furta haka yasa ta É—ago tana kalle-kalle domin jin maganar take kamar daga sama,
Ƴar Amana ta cigaba da cewa "zan yi miki gargaɗi na ƙarshe akan Roshan domin shi ɗin rayuwata ne, duk wacce ta raɓi jikinsa da niyyar soyayya to ta fara ƙirga kwanakin barin ta duniya nan da kwana ɗaya ko a cikin na biyu, Roshan rayuwata ne na ƙara maimaita miki, duk wacce kika ji tana son yin soyayya da shi to ki bata shawara idan ta ƙi to wallahi zata bar duniyar nan, Roshan nawa ne, Roshan nawa ne ni kaɗai..."
Haka Salma ta toshe kunnen ta domin jin muryar take kamar zai fasa mata kunne domin muryar tana fita ne da bibbiyu, ba abinda take faÉ—i illa "wallahi indai Roshan ne na rabu da shi duniya da lahira, bazan sake shiga sabgar sa ba amun afuwa dan Allah kar ku kashe ni..."
Ƙawar ta kuwa rirriƙe ta take tana tambayar ta "wai me yake faruwa ne? kodai Aljanar Roshan ce ta bayyana miki?..."
Salma ɗagowa tayi tana kallon ƙawar ta cikin kuka ta ce "wallahi ita ce, na shiga uku yau Aljana ta fito mun da muryar ta..."
ÆŠayar ta ce "ai kaÉ—an kika gani indai baki rabu da shi ba nan gaba zata fito miki a zahirance ne..."
Cikin tashin hankali Salma ta ce "mai zai sa bazan rabu da shi ba? ai na rabu da shi an gama, kinga tashi mu bar wurin nan..."
A ruɗe Salma ta miƙe tsaye wanda jin muryar aljana yasa ta durƙusawa haka suka bar wurin da gudun gaske...
Roshan yana shiga duk wanda ya karanta rubutun bayansa sai ya gudu, wasu kuma suyi ta dariya har da masu furtawa a fili suna faÉ—in "Mijin Aljana! Mijin Aljana..."
Roshan gaba ɗaya ya gama tsarguwa duk da ba wanda ya tuntuɓe shi da maganar, da ma'aikatan da waɗanda suka je duba majinyata kowa haka ake nuna shi da yatsa ana maganarsa, duk ba wanda bai ga rubutun ba, sai wani abokinsa ne ya miƙa masa hannu alamar gaisuwa yana faɗin "Congratulation Mijin Aljana yaushe aka yi Auren ne ba gayya?..."
Sai yanzu Roshan ya gama tabbatar da cewa duk gurmin da ake yi da shi ake, cikin rashin fahimta haka yake bin mutumin da kallo har ya tafi, haka yake bin mutane da kallo É—aya bayan É—aya yanda suke ta masa dariya wasu kuma suna faÉ—in "Mijin Aljana..."
Roshan ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba ganin an maida shi mahaukaci, a fusace ya nufi office ɗinsa ya shige, yana zuwa ya zauna akan kujerar sa ya kifar da kansa akan table ɗin gabansa wanda yake ɗauke da takardu da computer, tsabar takaici bai san lokacin da hawaye yake zubo masa ba, shi takaicin sa yana matsayin shugaba a cikin hospital ɗin nan amma mutanen da basu kai ba har da su ake masa izgilanci da yaransa ma'aikata, ya daɗe yana tunanin meyasa suke ƙiransa da mijin Aljana,
Jin yayi an knocking É—agowa ya yi yana goge hawayen sa da handkerchief daga bisani ya bada umarnin a shigo,
wata mata ce ta shigo zata faÉ—i matsalar da ke damunta, ganin Roshan yasa ta juya da gudu tana faÉ—in "Wayyo Allah mijin Aljana ne daman a cikin office É—in? wallahi na yafe..."
Roshan abun sai ya ƙara ɗaure masa kai, yana cikin tunani sai yaji an turo ƙofa da sallama, ɗagowa ya yi yana kallon wanda ya shigo yana tunanin shima da nashi izgilanci yazo masa, wani babban Abokinsa ne mataimakin sa a wurin aiki, zuwa ya yi ya zauna yana kallon Roshan wanda shima Roshan tagumi ya yi yana binsa da kallo..
Doctor Aliyu ne ya fara yin magana ya ce "Good morning Doctor Roshan..."
Roshan É—aga masa kai kawai ya yi ba tare da ya furta komai ba domin shi kaÉ—ai yasan abinda yake ji a ransa.
Doctor Aliyu ya ce "Doctor Roshan kasan abun zai dame ka meyasa ka rubuta hakan? meye dalilin rubuta mijin Aljana a bayan rigar ka kuma? kasan dole mutane sai sunyi magana wasu kuma su tsorita..."
Roshan cike da mamaki yake bin Doctor Aliyu da kallo cikin rashin fahimta, murya ciki-ciki ya ce "ban fahimci abinda kake nufi ba..."
Doctor Aliyu ya ce "Oh kana nufin kace baka san da rubutun bayan rigar ka ba?..."
Roshan cike da mamaki ya fara ɓalle bottle ɗin gaban rigar sa ya cire rigar dake akwai wani T-shirt mai gajeren hannu ta ciki, yana juya bayan rigar ya ga an rubuta Mijin Aljana, a ruɗe ya furta "what! who do this for me?..."
Doctor Aliyu ya ce "indai baka san da shi ba to wani ne ya rubuta maka..."
Roshan ya ce "amma lokacin da zan saka rigar babu rubutun nan, sannan lokacin da zan yi breakfast duk ƙannena a zaune suke har iyayen kuma nine first ɗin barin wurin, still motar da na shiga ni kaɗai nayi driving ban tsaya a ko ina ba sai anan hospital..."
Doctor Aliyu ya ce "akwai matsala to, amma ka tuntuɓa shin tin daga gida hakan ya faru ko kuma sai da kazo nan..."
Roshan ɗaukar wayansa ya yi ya danna ƙiran wayan Razhdeen, bugu uku ya ɗauka domin Razhdeen baya saurin ɗaukan ƙira ko wayar tana hannunsa sai ƙiran ya kusan yanke wa tukun yake ɗagawa, already Roshan yasan hakan shine halinsa shiyasa bai damu ba saboda yasan zai ɗauka, bayan Razhdeen ya ɗauki ƙira abinda ya fara furtawa shine "ya akayi ne mijin Aljana..."
Roshan ya ce "kana nufin kace tin a gida rubutun yake bayan rigana?..."
Razhdeen ya ce "ina kai ka rubuta hakan da hannunka meyasa zaka tambaya alhalin kasan kowa zai kalla..."
Roshan kamar zai yi kuka ya ce "My Man wallahi ban san da wannan rubutun ba, bani da rubuta ba kuma lokacin da na É—auko rigar babu rubutun nan..."
Razhdeen yana kwance sai da ya tashi zaune yana faÉ—in "what? kana nufin kace ba kai ka rubuta ba? Oh my God akwai matsala Please twins come back to home now, we've to do something..."
Roshan amsa masa ya yi da "okay..." Idonsa gaba É—aya ya kaÉ—a ya yi ja tsabar damuwar da ya shiga lokaci guda...
miƙe wa ya yi idonsa akan Doctor Aliyu ya ce "i need to go home..."
Yana kaiwa nan yayi ficewar sa da rigar a hannu,
Doctor Aliyu girgiza kai ya yi ba tare da ya ce komai ba domin shima abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba...
Kafin Roshan ya koma gida har Razhdeen ya sanar wa Abbah halin da ake ciki, shima Abbah hankalin sa ba ƙaramin tashi yayi ba,
cikin ƙanƙanin lokaci Roshan ya isa gida, a falo ya tarar da su Abbah,
Abbah yana ganinsa ya miƙe tsaye tare da yowa kansa yana faɗin "Roshan da gaske ne abin da nake ji?.."
Roshan ya ce "Abbah seriously ban san da wannan rubutun ba kuma ba mutum bane ya rubuta ba..."
Razhdeen karɓan rigar hannunsa yayi yana duba rubutun rigar, yana gani ƙirjinsa ya buga da ƙarfin gaske domin sai yanzu ya lura irin rubutun Ƴar Amana ce, domin rubutun ta tana yi ne haɗi da design kafin ta tsara, a ruɗe ya ce "Dad wannan ai rubutu Sarah ce..."
Abbah ya ce "rubutun Shalele kuma?..."
Roshan shima maimaitawa ya yi "Shalele?..."
Ummy dake wurin itama ta ce "tabbas wannan rubutun Reemah ce..."
Itama Baiwar ALLAH ƙarewa rubutun da kallo tayi sannan ta ce "wannan rubutun Ƴar Amana ce..."
Abbah ya ce "Razhdeen meye mafita? ya zamu yi mu samo Shalele? ta wani hanya zamu bi ta dawo gare mu, hakan na nufin ta koma aljana kenam? yanzu idan Mahaifinta yasan da wannan maganar wani irin hali zai shiga? muna buƙatar ta..."
Ammy ta ce "gaskiya idan a haka zamu zauna bazata taɓa dawowa ba sai mun miƙe tsaye, duk da muna kan yin Addu'o'i amma kamata yayi a tara malamai a tsaya akan al'amarin..."