← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 68

Sashe 15

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowa ya hallaru a falon har da mai martaba da matansa da kuma Abbah shima da matansa domin Ammy ta dawo itama sai Aunty Yolash da yaran gidan, shima Roshan ba jumawa ya shigo da matar Ramlat wacce tasha kuka, itama Baiwar ALLAH fito wa tayi tana sanye da dogon hijab har ƙasi,
Razhdeen ne kawai baya nan yana can kwance a gadon asibiti sai sojojin da suke gadin sa...

Abbah ya kalli mutanen falon sannan ya fara magana kamar haka "a yau ne ranar farin ciki na da Allah ya kawo mun babban aminina wanda muka É—au tsawon shekaru muna zaman gava sai a wannan lokacin Allah ya bayyano mana haske cikin lamuran mu, Allah na gode maka, a cikin Æ´aÆ´ana akwai waÉ—anda basu san Chief Suraj Mahendra Marka ba to wannan shine, mahaifin Mohandas da ya Auri É—iyata Amina...."

Abbah ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "Daughter kiyi haƙuri yau zan bayyana wa iyayenki ke ...."

Baiwar ALLAH hawaye ne ya fara cicciko wa daga cikin ƙwayar idanuwanta, domin ta tabbata abinda mutanen gidan marayu suke faɗa gaskiya ne, na cewa iyayen ta Christal ne tunda take ɗaure da sarƙa irin nasu....

Madam Parveen haka jikinta ya É—au rawa tana bubbugan cinyan mijinta tare da faÉ—in "Please me suke nufi ne?..."

Chief ya riƙe hannun madam Parveen yana faɗin "wait ki kwantar da hankalin ki, nima kaina ban gane mai suke nufi ba..."

Abbah buɗan baki yayi zai yi magana sai suka ji bugun ƙofa,
Abbah ya ce "come in..."

Duk bakin ƙofa suke kallo suna son ganin waye domin a cikin gidan nan babu wanda ya rage duk an taru a falo sai Razhdeen da baya nan, sannan duk wanda zai shigo gidan sai Soja ya ƙira waya ya sanar,
A wannan lokacin kuma ba'a yi hakan ba...

Ganin Minal ta shigo yasa duk mutanen falon suka mimmiƙe tsaye,
gani suka yi shima Mohandas ya shigo yana É—auke da yaro a hannunsa mai kimanin shekara É—aya da rabi...

Madam Parveen jiki na rawa ta buÉ—e baki tana faÉ—in "M m m Mohandas my son...." ta nufi wurin su da gudu ta rungume shi tana dariya haÉ—e da kukan farin cikin ganinsu.
Hajiya Kilishi itama cike da farin ciki ta nufo su da sauri ta rungumi Minal sosai a jikin ta tana faÉ—in "Minal, Minal kin dawo gare ni Allah na gode maka...."

Abbah kasa magana yayi ya koma ya zauna, shima Chief É—in zama yayi idonsa akan su, Mai martaba ne ya ce "ku shigo mana..."

Pinky da Rukky da Ummy da Ƴar tinny haka suka je duk suka rungumi Minal suna farin cikin ganinta, tare duk suka ƙaraso cikin falo, aka basu wurin zama,
Minal bata zauna ba haka taje gaban Abbah ta durƙusa a gabansa tana kuka ta ce "Abbah dan ALLAH kayi haƙuri ka gafarce ni, nasan banyi maka adalci ba amma naga hakan shine mafita a gare ni, ina matuƙar ƙaunar Marshall Mohandas, mun yanke shawarar guduwa domin munga baku da niyar kawo ƙarshen ƙiyayyar ku, yanzu kuma mun san komai ya dawo dai-dai hakan yasa muka dawo gare ku..."

Abbah ya ce "aina ku ka san da wannan maganar?..."

Minal tana kuka ta nuna Roshan da yatsa ta ce "shine ya sanar mana cewa mu dawo gida..."

Abbah idonsa yakai kan Roshan, Roshan kuwa ganin sun haɗa ido da Abbah yasa yayi saurin kawar da kansa gefe yana sosa ƙeyar sa....

Abbah ya ce "daman kasan a yanda suke shine baka sanar mun ba? ...."
Roshan ya ce "kayi haƙuri Abbah hakan shine zaman lafiyan kowa..."

Jinjina kai Abbah yayi tare da kallon yanda Minal take sannan ya ce "shikenam komai ya wuce, ki tashi kije ki zauna..."

Minal share hawayen ta tayi ta tashi taje ta zauna, shima Mohandas neman yafiyar iyayensa yayi sannan ya sanar musu cewa "ya musulunta ba tare da sanin su..."

Shima iyayensa sun lamunce masa, Rakesh tashi yayi ya rungumi Yayansa yana farin cikin bayyanowar sa...

A wannan ranar kowa ya kasance cikin farin cikin cikar ahali, Ummy ganin yaro kyakkyawa yasa ta karɓe shi take rungume da shi, ta tashi ta miƙa shi a Abbah,
Abbah ne ya karɓi yaron yana masa wasa dake yaron yayi wayo sosai domin har an yaye shi,
Abbah ya ce "meye sunansa?..."

Mohandas ya ce "Muhammad Afif...."

Abbah ya yi murnan jin sunan...
Chief ma miƙa masa yaron akayi kowa sai da yaron ya shiga hannun kowa na falo...

Baiwar ALLAH kam duk wannan hidimar da akaita yi idonta akan Madam Parveen da kuma Chief da Rakesh, haka ta shiga tunanin lokacin da suka fara haɗuwa a hospital da madam Aliya, a lokacin madam parveen tana kukan ɓatan ɗiyar ta...."
Lokaci guda Baiwar ALLAH ta fashe da kuka tare da miƙewa tsaye ta nufi wurin Madam Parveen ta rungume ta sosai tana kuka...

Madam Parveen ganin ana cikin farin ciki kuma taga Yarinya ta rungume ta tana kuka yasa jikinta yayi sanyi, sai kuma ta tuno da maganar Abbah da ya fara yi wanda bata gama fahimta ba,
Itama Madam Parveen rungumar ta tayi tana rarrashinta ba tare da sanin ko ita wacece ba, amma tabbas ta tuna yarinyar, tayi tunanin saboda mutuwar Madam Aliya ne yasa ta ke kuka...

Kowa hankalinsa ne ya karkato kansu, da murmushi akan fuskar Abbah ya ce "kinga Daughter ki nutsu ki saurari abinda zan gaya miki..."

Madam Parveen itama kukan take idonta akan Chief, shima idonsa akan Baiwar ALLAH domin jikinsa yana bashi wani abu.
sai da kowa ya nutsu kafin Abbah ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "tinda ke kin fahimci komai sauran su zan musu bayanin komai..."

Anan Abbah ya sanar musu cewa "wannan yarinya ita ce Æ´arku wacce ku ka rasa tin tsawon shekaru wato Amreesh..."

Chief girgiza kai yayi tare da faÉ—in "tayaya hakan zata faru?..."

Madam Parveen sake baki tayi tare da zaro ido waje tana kallon Baiwar ALLAH..."

Itama Baiwar ALLAH ita take kallo tana kuka, yanzu ba kukan jini take ba abun yayi sauƙi sakamakon ɗorata akan magani da Doctor yayi ...

Abbah ya ce "idan kuna tunanin Ƴar ku Amreesh tana da wata shaida a jikin ta to ku bincika, idan ba ita bace shikenam...."

Madam Parveen fuska a wanke da hawaye take kallon Chief, Chief jinjina kai yayi sannan ya ce "ina ji a jikina cewa ita ce Daughter na Amreesh...."

Rakesh ne ya taso gadan-gadan yayo kan Baiwar ALLAH dake rungume da Madam Parveen yazo ya riƙo hannunta tare da ɗagota tsaye yana shirin cire mata hijab, Baiwar ALLAH ihu ta fara kurmawa tana ƙanƙame da hijab, Madam Parveen ce ta jawo Baiwar ALLAH jikinta tare da rungumar ta sosai tana faɗin "ka ƙyale ta bana son jin kukan ta..."

Rakesh ya ce "idan bamu ga shaidar dake jikinta ba taya zamu san Amreesh É—in mu ce?..."

Mohandas a ruÉ—e ya ce "Amreesh kuma?..."

Abbah ya ce "No ai komai a hankali ake binsa, da rarrashi zaku duba mata..."

Aunty Yolash ce ta taso da murmushi akan fuskar ta tayo kan Baiwar ALLAH wacce take rungume da Madam Parveen, zama tayi a kusa da ita tana faɗin "Daughter kiyi haƙuri idan basu ga shaidar haka a jikin ki ba babu yanda zasu yadda cewa ke ƴar su ce, ki yi haƙuri kinji ko..."

Baiwar ALLAH tana kuka ta ce "ni bani da wata shaida, ku kyale Ni...."

Furr Baiwar ALLAH taƙi yadda ta cire hijab ɗinta, Chief ya ce "ku barta domin naji hakan a jikina cewa Daughter ɗina ne Amreesh...." ya ƙarisa maganar yana murmushi,

Itama Madam Parveen jinjina kai tayi tana faɗin "Nima na yadda..." ta ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka...

Mohandas da Rakesh babu wanda ya ce komai domin har yanzu basu tabbatar ba...

Roshan ganin yanda Mazan basu yadda ba yasa ya tashi ya nufi wurin Baiwar ALLAH yasa hannu ya ɗagota, ganin Roshan yasa ta ƙafe idonta akan sa, shima ɗin ita yake kallo fuska ba annuri bata san lokacin da ya zamar mata da hijab ɗin ba, sannan yasa hannu ta bayanta ya zuge mata zip ɗin riga, still idonsa a cikin nata haka suke kallon juna, yana tsaye a ta gabanta ya buɗe musu bayanta kafin ta ankara,
Chief a ruɗe ya miƙe tsaye yana zaro ido waje ganin zanen bayanta, itama Madam Parveen miƙe wa tayi jikinta har wani kakkarwa yake idonta akan zanen bayanta itama,
Mohandas da Rakesh su ma a ruÉ—e suka tashi, domin ko wannen su yana É—auke da wannan zaunen a bayansa kuma sak iri É—aya babu banbanci,

Madam Parveen hannu takai sai tin wuyan Baiwar ALLAH tana shafa tawadar baƙin wurin wanda da shi aka haife ta,
Kowa a cikin su sai da ya duba wannan tawadar bayan zanen...

Roshan ganin irin kallon da take masa ne yasa shi sakin murmushin da bai san yayi mata shi ba, sai kawai ya tuna sunbatar sa da tayi da taje part É—insa...

Mohandas da Rakesh kallon juna suka yi tare da sakin murmushin farin ciki baki a haÉ—e suka ce Amreeeeshh...."
Baiwar ALLAH jin an ambaci sunan Amreesh da ƙarfi yasa ta firgita ta dawo hayyacinta, haka take bin kowa na cikin falon da kallo, Madam Parveen kam yankan jiki tayi ta faɗi sumammiya, kafin takai ƙasi Chief yayi saurin riƙo ta,
Baiwar ALLAH ganin haka yasa kanta yayi mungun sarawa, a firgice takai hannu ta dafe kanta itama tayi ƙasi luu zata faɗi Roshan ya yi saurin riƙo ta tare da mannata a jikinsa yasa hannu yayi mata ɗaukan luɗa,
Ramlat kam ƙirjinta kamar zai faso tsabar bugu da tsananin kishi, kai tsaye room ɗinta ya nufa da ita, yana zuwa ya tura ƙofa ya shige yana zuwa ya kwantar da ita akan gadonta...

A wannan ranar kowa ya kasance cikin farin ciki, Madam Parveen bata tashi farfaɗowa ba sai dare misalin ƙarfe 8 ta farka tana ambatar sunan Amreesh,
"Amreesh! Amreesh!! tana ina Amreesh ɗina, ta fito falo tana Dube-dube domin daga cikin bedroom take yanda aka kwantar da ita akan gado, mutane ta samu a falo kowa a cikin farin ciki especially Chief Suraj bashi da wata damuwa yanzu da ya wuce Razhdeen ya farfaɗo domin yana matuƙar ji da shi...
Chapter 15 · 0% Book details