← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 68

Sashe 14

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari Abbah da mai martaba su biyu suka tafi ƙasar U.S, Chief ya yi matuƙa mamakin ganin Abbah, cikin farin ciki ya ƙarfe su hannu bibbiyu, anan Abbah ya sanar masa yanda akayi yaji duk maganganunsa sannan ya sanar masa cewa yazo neman yafiyar sa ne akan abinda yayi masa...

Chief ya nuna masa ba komai, komai ya wuce sannan ya ce "yayi mamaki da Razhdeen ya yi recording amma yayi farin ciki tunda ko ba komai yayi sanadin shiryawar su...

Su Abbah sun gama fahimtar juna komai ya zo ƙarshe na ƙiyayyar su kuma daman Abbah ne ya ɗau abun da zafi,
Har suka dawo basu sanar musu cewa É—iyarsu Amreesh tana hannunsu ba, shi Abbah baya son iyayen ta su tarar da ita a cikin wannan hali na cutar da take fama da shi na kukan jini, so yake sai ta warke ta dawo cikin hayyacinta tukun....

Bayan sati guda da dawowar su Abbah daga ƙasar U.S suma su Chief Suraj da matar sa Madam Parveen da Rakesh ne suka zo Nigeria duba jikin Razhdeen, Madam Parveen har da kukan ta domin jikin Razhdeen ba sauƙi tinda har zuwa yanzu bai farfaɗo ba,
Abbah ya nuna wa Baiwar ALLAH iyayenta amma su ba'a sanar musu ba har yanzu, Baiwar ALLAH kawai jure wa tayi amma taso taje yanda suke, kuma taga Madam Parveen ta gane ta, tayi mamaki sosai da taga itace mahaifiyar ta, da haka har suka koma ƙasar U.S...

Baiwar ALLAH tasha kuka sosai ganin sun tafi, amma ta wani ɓangare tayi farin cikin ganin iyayen ta....

★★★

Bayan wata uku da Auren Roshan, har ila yau bai je ya dubo Razhdeen akan gadon asibiti ba itama Baiwar ALLAH anyi da ita akan taje ta gano Razhdeen fur taƙi domin bata ƙaunar ganin fuskar sa,
Ita kuwa likita ya duba ta ya sanar cewa Depression ne, tsananin damuwa ne yasa har take kukan jini ga rashin bacci da cin abinci da kuma samun sukuni....

Fito wa falo tayi ta tarar babu kowa, dake ba fito wa cikin mutane take ba, Hajiya Kilishi tana ɓangaren ta, ita kuwa Ammy da Aunty Yolash su suke jinyar Razhdeen a asibiti,
Maamie da Aunty A'isha suma part ɗinsu daban a cikin gidan Abbah, acan Maamie take tsula tsiyar ta, dake Aunty A'isha ta rigada ta saba da halin ta haka suke zaune kafin lokaci komawar su ƙasar Jidder.
Har tsawon watannin nan basu koma ba, domin Mai martaba bazai iya koma wa yana ganin Razhdeen ko farfaÉ—o wa bai yi ba sakamakon dogon suma da ya yi....

Baiwar ALLAH Ummy kawai ta tarar ta fito a kitchen, har zata haura room É—inta da plate É—in abinci a hannunta Baiwar ALLAH tayi saurin tsayar da ita tana faÉ—in "Amm Ummy dan Allah..."

Ummy juyo wa tayi tana kallon ta ba tare da ta ce komai ba,
jin Baiwar Allah tayi shiru ne yasa ta cewa "inada abun yi fa domin yunwa nake ji..."

Baiwar ALLAH wacce gaba ɗaya ƙashin wuya yayi mata sarƙa duk idanuwanta sun faffaɗa, fuskar nan tayi fiyau ga wani irin fari da tayi kamar ba jini a jikin ta, ta ce "daman akwatin kayana nake so ki ɗan ɗauko mun a can part ɗin Yaya Roshan..."

Ummy ta ce "ƙafar ki jinin haila take da bazaki je da kan ki ba? ...."

Baiwar ALLAH ta ce "shikenam je ki kawai..."

Ita kuwa Ummy wucewar ta tayi, a yayin da ita Baiwar Allah ta nufi hanyar waje,
tana fita ganin part ɗin Roshan da ɗan nisa kaɗan yasa ta cewa a security ya kaita da mota, shiga tayi ya kaita har bakin gate ɗin Roshan sannan ta sauƙa ta fara knocking a hankali...

Shi kuwa Roshan da Ramlat suna filin gidan a jikin mota, Roshan ya fito zai fita ita kuma ta rako shi, tana rungume da shi a jikin mota a tsaye suna shan love É—in su kwatsam suka fara jin knocking,
Basu yi tunanin Baiwar ALLAH bace domin shi Roshan rabon da yayi ido huÉ—u da ita tin ranar Auren sa da daddare, haka itama Ramlat,
Ramlat tana rungume da shi hannunta riƙe da fuskar sa kamar wacce zata yi masa kiss,
ta kalli bakin gate ta ce "waye turo gate É—in a buÉ—e yake...."
still suna rungume da juna, Baiwar ALLAH ce ta turo da sallama a bakinta, ganinsu yasa ta dakata tana kallon su, zuciyar ta kuwa haka yake bugun uku-uku,
Roshan ido ya haÉ—a da Baiwar ALLAH ji yayi gabansa ya yanke shima haka yake jin bugun zuciyar nan idonsa akan ta,
Ramlat fuska É—auke da murmushi ta ce "shigo mana, yau kece a part É—in nan...?"

wani irin yawu Baiwar ALLAH ta haɗiya tana jan ƙafa daƙer ta shugo, ba tare da ta isa yanda suke ba ta tsaya,
Roshan kawar da kansa yayi gefe, sai lokacin Ramlat ta rabe jikinta da na shi tana faɗin "nima na rako mijina zai fita ne, yanzu nake shirin zuwa can part ɗinku, mu ƙarasa ciki koh...."

Roshan yayi saurin katse Ramlat da cewa "ki tambaye ta me tazo yi tukun..."

Ramlat kallon Roshan tayi ta ce "ta zo ziyara mana..."

Baiwar ALLAH ta ce "nazo É—aukan kayana..."

Ramlat ta ce "oh daman kina da kaya ne? okay ki je ki É—auko a room É—in da kika zauna, kinsan ni tinda nazo ban shiga ba..."

Baiwar ALLAH gaba tayi zata shige falo Roshan ya ce "bana son ƙara ganin ƙafar ta a cikin room ɗina, ke kije ki ɗauko mata..."

Ramlat ta ce "toh shikenam Rabin Rainah an gama..." murmushi ya sau mata ita kuwa ta shige...

Baiwar ALLAH kuwa idonta akan Roshan, shima idonsa yakai kanta tare da jefa mata wani irin kallo na harara, ganin bazata iya fita ba tare da tayi masa magana ba yasa ta nufi yanda yake a tsaye yana jiran fitowar Ramlat kafin ya fita,
Ganin ta tsaya masa a gaba yasa shima ya ƙura mata ido, tasau murmushi sannan ta ce "Yaya Roshan na taya ka murnar ƙara Aure, amma ina so ka sani cewa nasan har yanzu akwai soyayya ta a cikin zuciyar ka, haka nima, soyayya takan koma wa ƙiyayya amma ita ƙauna har abada tana nan a matsayinta, to ƙaunar juna muke, duk abinda zaka yi nasan sai dai kayi don ka ɓata mun amma ba har cikin zuciyar ka ba......"

Kafin ta ƙarasa maganar ya katse ta da cewa "ki daina wannan shirmen domin yanzu babu ke a cikin zuciyata, wacce ta fiki muhimmanci ta mamaye wurin, don haka bazaki samu shiga ba..."

Baiwar ALLAH buɗan baki tayi zata yi magana ya katse ta tare da darara mata tsawa yana faɗin "na tsane ki, dan Allah ki fita daga cikin rayuwa ta, kije ki kama wanda ya fini muhimmanci a wurinki, wanda zai baki kulawar da bazan iya baki ba, wanda kika mallaka masa kan ki da Auren ki saboda tsananin ƙaunarsa da kike...."

Bai ankara ba yaji ta ci kwalar rigar sa tare da jawo shi jikinta ta riƙo kanta da hannu ɗaya tare da haɗe musu baki wuri ɗaya,
Dai dai lokacin da Ramlat ta fito ganin su yasa tasau akwatin hannunta ƙasi tare da zaro ido waje,
Roshan yana jin sauƙar akwati ƙasin floor a ruɗe zai ɗago Baiwar ALLAH ta ƙara ƙanƙame shi bakinta a cikin nasa, itama tasan Ramlat ce ta fito hakan yasa ta ƙara shige wa jikinsa, sai da ta gama sumbatar sa kusan minti guda tukun ta sake shi, tana ja da baya idonta akan sa shima haka yake binta da kallo ko ƙibtawa baya yi, Baiwar ALLAH cikin barikanci ta ƙibta masa ido ɗaya sannan ta juya baya jin alamun ta iso dab da Ramlat, idonta akan Ramlat da murmushi akan furkarta ta ce "au har kin ɗauko akwatin? sannu fah..."
ta durƙusa ta ɗauki akwatin a ƙasi ta ɗago tana zaro harshe tare da ɗage harshen saman lips ɗinta ta juya ta nufi bakin gate, tana fita ta shiga mota security da ya kawo ta ne ya juya da ita part ɗin Abbah...

Ramlat idonta ta sauƙar kan Roshan idonta duk ya cicciko da hawaye ta juya da gudu cikin falo tana rera kuka,
Gaba ɗaya jikin Roshan ne yayi sanyi ganin Ramlat ta juya tana kuka yasa shima ya bita ciki yana ƙiran sunanta.....

Baiwar ALLAH tana isa part ɗin Abbah ta tarar da wasu manya-manyan motoci na alhurma a jere alamun anyi manya-manyan baƙi ne, dake kuma gidan basa rabuwa da baƙi masu zuwa duba jikin Razhdeen, har daga ƙasar waje ake zuwa, yanzun ma tasan masu zuwa duba Razhdeen ne...

Haka ta shige falo jikinta na ɗar ɗar domin a rayuwar ta tana tsoron baƙi, daman can ba son zaman cikin mutane take yi ba,
tana shiga ta tarar da wani babban mutum asalin mai kuɗi yana zaune a 3 seater, sai kuma a gefensa wata hamshaƙiyar mata ce fara tas alamar matarsa ce, a ɗayan kujerar kuma wani zankaɗeɗen saurayi ne zaune sai sakin murmushi yake, kallo ɗaya Baiwar ALLAH tayi mishi idonta ya sauƙa akan sarƙar wuyansa, ƙirjinta ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ganin irin sarƙarta ne banbancin colour ne kawai,
a ciki ranta tayi farin cikin ganin su saboda su ne wanda Abbah ya nuna mata cewa iyayenta ne,
Ƙara kallon Madam Parveen tayi bata san lokacin da ta saki murmushi ba...

Abbah ne ya ce "Daughter ƙaraso mana ya na ganki da akwati?..."

Baiwar ALLAH shugowa tayi tana binsu da kallo hannunta É—auke da akwati, murya na kakkarwa ta ce
" zan kai kayana ciki..."

Abbah ya ce "to je ki dawo yanzu..."
Baiwar ALLAH gudu-gudu sauri-sauri ta shige room É—inta domin tana muradin ganin iyayenta...

Abbah ne ya ciro wayar sa ya ƙira wayar Roshan, bugu ɗaya aka ɗauka Abbah ya sanar masa cewa yazo yanzu anyi baƙi,
Roshan ya amsa masa sannan suka katse wayar...
Chapter 14 · 0% Book details