← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 68

Sashe 20

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itama Baiwar ALLAH fara magana tayi tana faɗin "a lokacin da na karanta saƙo na fita ne akan naje na samu Razhdeen da maganar sharrin da ya mun, nayi tunanin shine ya ajiye mun saƙon...."

Nan ma Abbah jinjina kai yayi sannan ya kunna suka cigaba da kalla,
Showing wurin da Razhdeen yazo akayi ka yanda suka tsaya a falo suka yi rikici akan ta bayyana masa yanda Reemah take, a wurin har Razhdeen ya mare ta..

Sai a lokacin Roshan ya gane cewa anan Razhdeen yasan cewa Baiwar ALLAH Amreesh ce, domin a lokacin da Razhdeen yasan ita ce Amreesh fita yayi jiki ba ƙwari ya fice,
daga nan Razhdeen bai ƙara zuwa ba sai ƙiran da Baiwar ALLAH tayi masa, duk akwai video anan,
a cikin video bedroom ɗinta ne kawai babu CC Camera, amma bayan Baiwar ALLAH ta ja shi ciki acikin video ba da wata manufa suka shiga ciki ba domin tana kuka tana masa magiya akan ya bata sarƙar har suka shiga ciki, kuma alamun abu zata nuna masa,
daga baya sai ga su Pinky da Rukky suka shigo hannunsu riƙe da wani kwalbar turare, ana kallonsu suka tsuguna ta ƙasi suna feffeshe turare ta cikin ƙasin ƙofa fuskar su ɗaure da facemark...
daga nan suka gudu, bayan awa sai ga Roshan da Ummy sun shigo tare anan ake kama su...

Abbah ya tsayar da video idonsa akan su Pinky ya ce "meye abinda ku ka fesa musu?..."

Rukky ta ce "feeling fresh..."
Abbah ya ce "ku je ki É—auko mun na gani..."
Rukky ce ta miƙe jiki ba ƙwari taje ta ɗauko ta miƙawa Abbah,
Abbah karɓa yayi tare da karanta ƙarfin yanda turaren yake da ƙa'idojinsa,
Kowa sai da ya karɓa ya duba, duk sun san amfanin wannan turaren bashida kyau wurin fitar da mutum a cikin hayyacinsa, mungun abu ne, yanzu haka kana feshe falo cikin ƙanƙanin lokaci zai fitar da kowa daga cikin hayyacinsa, kowa zai nemi ɗan uwansa ne ba tare da an sani ba....

Roshan wani irin yawu ya haÉ—iya cikin takaici yake bin yaran da kallo,
Kowa sai da yaji haushin su,
amma ta wani ɓangaren Roshan ya yi magana akai,
cewa "Amma Abbah shiga É—akin da suka yi ne ya bawa yaran damar aiwatar da abun, me zai sa su shiga bedroom ba muharraminta ba?..."

Abbah ya ce "zan ɗau ƙwaƙƙwaran hukunci akan wannan al'amarin, zaku gane kuran ku, ina dai ku iblisai ne ko? zan yi maganin ku..."

Rukky ce ta fara kuka tana faɗin "dan ALLAH Abbah kayi haƙuri wallahi Pinky ce take sawa ayi..."

Bata ƙarasa maganar ba Abbah ya daka mata wani irin gigitaccen tsawa tare da faɗin "ki mun shuru, ku jira sakamakon ku..."

Sannan Abbah ya kalli Baiwar ALLAH ya ce "Daughter kiyi haƙuri kinji, ni dai nasan bazaki taɓa aikata wannan da saninki ba, amma zan ɗau mataki akan su kar ki damu...."

Baiwar ALLAH tana kuka ta ce "ba komai Abbah ni na yafe musu kawai abar su, komai ya wuce....."

Abbah ya ce "bazan taɓa barin su ba domin sun aikata laifin da basu cancanci yafiya ba...."

Ƴar Amana itama kukan take ganin abinda ya faru tsakanin Baiwar ALLAH da Razhdeen, taji ƙuna sosai a ranta da kuma bugun zuciya, jure wa kawai take gaba ɗaya idanuwanta sun kaɗa sunyi jawur..."

Iyayen Baiwar ALLAH kuwa ganin abinda ya faru da Razhdeen ne yasa basu wani damu ba, daman can ita ɗin nashi ne, amma tinda yanzu bata tare da Roshan sun mayar da alƙawarin da suka ɗau na haɗa Baiwar ALLAH da Razhdeen...."

Duk kowa babu wanda yaji daɗin abinda ya faru amma ƙaddara ta riga fata...

Ƴar Amana ganin bazata iya jure wa ba yasa ta miƙe tare da nufan hanya zata koma ciki tabar falon, tazo wuce wa tayi tuntuɓe da ƙafar Maamie ta kife a ƙasin carpet...

Maamie a fusace ta cire earpiece ɗin kunnen ta takai hannu ta ɗago Ƴar Amana ta zabga mata mari...

Kowa na falon a ruɗe suke bin Maamie da kallo cikin ɓacin rai,
Ƴar Amana ɗagowa tayi takai idonta kan Maamie wacce take ta zuba masifar ta, haɗa ido suka yi ana Maamie kamar an ɗauke mata wutar kanta ta tsaya cakk, idonta a cikin ƙwayar idanun Ƴar Amana,
Maamie gani take wani hayaƙi yana fita daga cikin idanuwanta kuma ta kasa ɗauke kanta daga kan Ƴar Amana, itama Ƴar Amana idonta ne ya ƙafe wuri ɗaya a cikin na Maamie hayaƙi yana fita, idanuwanta sun zama jajawur hatta ƙwayar baƙin idanun ya ɓace sai zallar jaaaaa.........

Typing ✍️

*MY ENEMY*

*TAKUN ƘARSHE*

*BOOK 3*

31 to 35

Gaba ɗaya mutanen falon miƙe wa tsaye suka yi suna kallon ikon ALLAH,
Banda Razhdeen dake zaune babu halin tashi, cike da mamaki suke kallon Maamie da Ƴar Amana ga yanda ko wannen su suke ƙafe guri guda, Ƴar Amana idanuwanta ne suka yi jawur bayan hayaƙin nan ya gama fita a lokacin Ƴar Amana ta yanki jiki ta faɗi sumammiya...

Maamie a ruÉ—e ta dafe goshin ta tare da faÉ—in "wayyo kaina, kaina ciwo, zai fashe wayyo Allah Boka kar ka bar hakan ta faru, Boka! Boka!! Boka!!! ka taimake ni, wayyo ka taimake ni Bokaaa...."

Nan ta tintsire da dariya tana tafa hannayen ta tare da faÉ—in "haba! haba Ghali ni da nace ka je ka bisine Reemah da ranta shine ka barta a raye? Boka fa ya sanar mun cewa duk lokacin da na haÉ—u da Reemah zan haukace, wayyo Allah Ghali ka cuce ni, Reemah dana rufe mata baki shikenam yau asiri na zai tonu, Reemah ta bayyana mun a gaba na...."

Baiwar ALLAH tafo wa tayi da gudu ta tsuguna a yanda Ƴar Amana take a kwance bata san halin da take ciki ba,

Jin yanda Maamie take ta ɓare-ɓaren maganganu yasa Abbah faɗin "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Allahumma ajurni fi musibati wa akhlifli khairan minha...."

Mai martaba kuwa idanuwan sa a waje yanda yake da zazzaro su sai bin Maamie yake da kallo jin irin aika-aikan da tayi wa É—iyar sa Reemah,
kuma sai tonawa kanta asiri take tayi...

Duk abinda ya faru da Ƴar Amana tin haihuwar ta Maamie bata ɓaye ba, har sawa da tayi a cire wa Aunty A'isha mahaifa da tayi duk sai da ta faɗe su...

Daman Boka ya sanar cewa duk lokacin da suka haɗa ido huɗu da Reemah toh hankalinta zai gushe duk wata gaskiyar da ta ɓoye sai ta faɗe su....

Kowa a falon sai da ya jinjina wa mugunta da makircin Maamie,
Aunty A'isha tsabar yanda zuciyar ta yake bugawa da harbawa da ƙarfin gaske yasa gaba ɗaya ta fita hayyacinta, har ƙoƙarin shiɗewa take, numfashi yana shirin ɗagewa..
Aunty Yolash ce tazo yanda take zaune ta zauna kusa da ita tare da rungumar ta a jikin ta tana rarrashinta,
Duk babu wanda yaji daÉ—in wannan al'amarin, duk zama sukayi suna sauraron abubuwan da Maamie take faÉ—i na makircin ta...

Madam Parveen mahaifiyar Baiwar ALLAH da sauran ƴan uwan ta duk jin labarin suke kamar a Film domin basu taɓa ganin irin wannan al'amarin a zahiri ba...

Yanzu ta tabbata Ƴar Amana ita ce Reemah, tana kwance akan cinyar Baiwar ALLAH tana shafa mata sumar kanta...

Mai martaba jikinsa ne yake zaƙami gaba ɗaya ya rasa yanda zai sa kansa, ji yake kamar ya kashe Maamie a yanzun nan...

Maamie bayan ta gama maganganun ta ba tare da ta san abinda take faÉ—i ba, tayi shiru tana kuka domin ba'a son ranta ta faÉ—i duk waÉ—annan maganganun ba, kamar wanda ake matsar bakin ta...

Falon tsit akayi sai ƙaran kukan Aunty A'isha kake ji, daga baya suka ji an turo ƙafar falo, duk kallon bakin ƙofar suka yi, wacce suka gani ne yasa Mai martaba yayi saurin miƙe wa tsaye idanu duk sun kaɗa sunyi jawur,
A ruÉ—e ya furta "Maimuna...."

Itama Maamie tashi tayi tsaye tana nuna bakin ƙofa da yatsa murya na kakkarwa take faɗin "wayyo fatalwa! fatalwa!! fatalwa!!! innalillahi ta mutu fa, meyasa kika dawo? au kin zo ne ki tona mun asiri? to a hir ɗin ki..."

Maimuna ƙarasa shugowa tayi cikin falon tana murmushi zuciyar ta fari sol, ranar da take jira yau gashi ta zo kuma tazo a dai-dai...

zama tayi akan kujera tana kallon Mai martaba sannan ta ce "ka zauna mana king..."

Mai martaba zama yayi itama Maamie zama tayi hawaye ya gagara tsayuwa, idonta akan Maimuna gaba ɗaya hankalinta ya kasa dawo dai-dai, jikinta har wani ɓari yake cike da tsoro da fargaba..

Maimuna kallon kowa tayi na cikin falon da wanda ta sani da waɗanda bata sani ba duk suna nan, sannan ta ce "kuyi haƙuri kunyi mamakin gani na ko?..."

Abbah jinjina kai yayi tare da faɗin "dole zamu yi mamaki, tsawon shekaru kin ɓata babu labarin ki sai daga baya muka ji cewa guduwa kika yi sakamakon kama wani namiji daban akan gadon Auren ki, yanzu kuma wannan la'ananniyar matar tana ƙiranki da fatalwa, bamu sani ba ko mutuwa kika yi..."

Murmushi Maimuna tayi sannan ta ce "Ghali ka shugo mana..."
Sai ga wani ya shugo jiki ba ƙwari haka ya ƙaraso cikin falon ya zauna akan carpet, Mai martaba yayi mamakin ganin yaron gidansa a cikin wannan al'amarin, daman shine ɗan hannun daman Maamie, ita take saka shi yayi duk abunda tace...
Chapter 20 · 0% Book details