← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 68

Sashe 42

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty Habiba ta ce "na taya ki murna sosai Baiwar ALLAH, kinyi babban Sa'a a rayuwa, da ke da Ƴar Amana ashe ku ɗin ba ƙananun yara bane shiyasa jinin ku ya haɗu sosai, ita ƴar sarkin ƙasar Jidder ke kuma ƴar shugaban sojojin ƙasar U.S, Allahu Akbar..."

wata ce a ciki ta ce "Amma Baiwar ALLAH shin abinda ake faÉ—i lokacin cewar iyayenki Christal ne shin gaskiya ne?..."

Baiwar Allah kallon ta tayi tare da jinjina kai ta ce "gaskiya ne amma sai dai yanzu sun musulunta..."

Duk cewa suka yi Alhamdulillah cikin nuna farin cikinsu,

Suka ɗauko hirar Yallaɓai anan Baiwar ALLAH take jin labarin abinda ya faru da shi kuma har ya mutu,
Sun jajanta sosai sannan idan suka tuno da labarin abubuwan suka wakana a baya gaba ɗaya sai su tintsire da dariya, musamman labarin Ƴar Amana da Yallaɓai, sannan suka yi jimamin mutuwar Madam Aliya,
A wannan lokacin ne suke sanar da Baiwar ALLAH cewa yanzu komai Alhamdulillah, sun samu Æ´anci sosai, suna samun wadataccen abinci da komai na rayuwa amma har yanzu akwai dokan hana fita...

A wannan ranar sun juma suna shan hira, anan Baiwar ALLAH ta kwana....

★★★★★★

Washe Gari da hantsi sai ga sauƙar mutanen U.S, motoci ne sun kai 15 na sojoji waɗanda suka je ɗaukar su a airport,
Abbah da mai martaba da matan su da Ummy da Reemah da Ramlat sai Roshan duk suna zaune a falo, basu ankara ba suka ji shugowar su Chief cikin farin ciki, da Madam Parveen da kuma Minal da Rukky da mazajen su, ganin kowa a cikin tagumi yasa jikin su yin sanyi, cikin yaƙe Abbah ya tarye su,
Chief da ya gaza yin haƙuri ya ce "me yake faruwa ne naga kamar ba lafiya ba?..."

Murmushi takaici Abbah yayi sannan ya ce "babu lafiya kam..."

Madam Parveen ƙirjin ta ne yayi wani irin bugawa, tana ganin jaririya amma hankalin ta yana kan Baiwar ALLAH ganin bata tarar da ita ba,
bata san lokacin da hawaye yake gangaro mata ba, ta ce "ta mutu ko?..."

Abbah girgiza kai yayi sannan ya ce "ba mutuwa tayi ba, ta tafi bamu san ina tayi ba sai letter da ta bari..."

Abbah ya kalli Aunty Yolash ya ce "ki basu..."
Aunty Yolash ce ta tashi taje ta bawa Chief, Chief ya ce "indai rubutun Hausa ne ki karanta mana..."

Jinjina kai Aunty Yolash tayi jiki ba ƙwari ta karanta musu abinda yake cikin takardar...

Hura iskar bakinsa Chief yayi yana faÉ—in "why Daughter, why! why my Daughter..."

Madam Parveen ta ce "ta tafi tabar Baby?..."

suna cikin jajanta wa sai ga wasu sojoji su uku sun shigo tsayawa suka yi suka sanar wa Abbah cewa "Sir mun duba ko ina babu labarin ta..."

Abbah ya ce "ku tafi ku ban wuri..."

Chief ya ce "kar ku damu za'a same ta Insha Allahu, ku jinkirta nemanta yanzu domin bazaku same ta ba, na tabbata ta samu wani wuri ta zauna kaga kuwa samun ta zai yi wuya..."

Ammy ce ta taso ta kawo wa Madam Parveen jaririyar tana faÉ—in "ganan jikar ki"
Madam Parveen karɓan ta tayi tana murmushi haɗi da hawayen baƙin cikin tafiyar Amreesh...

★★★★★

Baiwar Allah kwana ɗaya tayi a gidan marayu ta shirya tafiya, suna kuka haka suka rabu ba'a son ransu ba amma Baiwar ALLAH tayi musu alƙawarin wata rana zasu sake ganawa da tare da ƴar Amana, daga nan ta tafi....

Su Madam Parveen kuwa basu tashi komawa ƙasar U.S ba sai da Jaririya tayi sati guda da zuwanta duniya, akayi suna ba tare da anyi hidima ba sakamakon rashin uwar yarinya,
Roshan ne ya raÉ—a wa jaririyar suna ta ci sunan Mahaifiyarsu wato Fateemah (Afaf)...

Ƴar Amana kullum yarinyar tana hannun ta, domin yanda take ji da yarinyar nan ko uwar da ta haife ta bata kaita ba, bata barin kowa ya ɗauke ta hatta madara yanzu ita take bata,
Shima Roshan gaba ɗaya ya ɗora ransa akan Afaf domin idan bata hannun Reemah to tana hannun Roshan to idan tana hannun ɗaya daga cikin su to ya kuwa suna tare ne domin indai Afaf tana hannun Roshan Reemah bata barin wurin sa, haka nan idan Afaf tana hannun Reemah to Roshan sai ya yi zarya wurin Reemah ya kai sau nawa, hakan yasa yanzu alaƙar ta dawo tsakanin Roshan da Reemah ta silar Afaf, bugu da ƙari kuma Roshan ya bata haƙuri akan abinda yayi mata sannan jin abinda Baiwar ALLAH ta rubuta a letter ta yasa ya fara saka abun a ransa domin a rayuwa babu abinda Baiwar ALLAH zata nema a wurinsa ta rasa indai bai fi ƙarfinsa ba, amma har yanzu bai nuna hakan ba, sannan kowa ya bar zancen a gefe saboda halin da Ramlat zata shiga idan taji zancen, domin ɓoye mata ake kuma daman ba shiri suke yi ba..

Roshan sunan da yake ƙiran Afaf shine *BIJU MAMA* ma'ana Manana...
hakan yasa kowa yanzu yake ƙiranta da haka, duk wata gata da nuna ƙauna ana mata domin yarinyar da shiga rai take...

A lokacin da Madam Parveen zasu tafi taso a bata Afaf amma Abbah ya ce "abar masa ita zasu raine ta..."

Babu yanda Madam Parveen bata yi ba akan abata ita domin hankalin ta ya kwanta tinda babu Amreesh, har Abbah ya amince akan ta tafi da ita tinda ta nuna damuwar ta akai amma fur Reemah ta ƙi bayar da Yarinyar, har da kukan ta wai ita baza'a rabata da Afaf ba,
Babu yanda ba'ayi ba amma Reemah ya ƙi,
Madam Parveen har da hawayen ta...

Kuma shima Roshan baya so a tafi da ita, kowa ma baya so domin suna matuƙar ji da yarinyar, daƙer aka karɓe Afaf daga hannun Reemah aka damƙawa Madam Parveen...

Babu wanda yasan Reemah tanada Aljanu na al'ajabi sai yau,
Bayan an karɓi Afaf, Reemah tsayawa tayi kai a sunkuye...

Madam Parveen da iyalanta sallama sukayi da kowa cikin kewar juna zasu tafi har sun nufi bakin ƙofa suka ji wani irin ƙarar murya mai toshe kunne kamar daga sama an darara tsawa, duk babu wanda bai firgita ba, Madam Parveen ƙanƙame Afaf tayi sosai jikinta na kakkarwa kowa ya maida idonsa kan Reemah,
Ganinta yasa kowa jikinsa ya fara kakkarwa, kowa ya ƙanƙame na kusa da shi banda Abbah da Mai martaba da suke ta faman jero Addu'o'i,
Roshan zaro ido waje ya yi yana kallon Reemah cike da mamaki,
Chief shima bakinsa ne yake ta motsi alamun addu'a yake domin abun da abin firgitarwa da al'ajabi...

Ƴar Amana ce ta ɗago da dara-daran idanuwanta waɗanda suka kaɗa suka yi jawur, fuskar da gangan jikin duk ya canza launin yellow kamar ba jikin bil-adama ba, sumar kanta da yake kwance har gadon baya yanzu duk sun mimmiƙe tsaye kamar wanda aka tsayar da su, wani irin haske ne ya zagaye ta, a tsawace ta fara magana tana faɗin "Duk abin da ku ke a tafin hannun mu kuke, muna yin abu bakwa mana uzuri to ku sani cewa ƙyale ku muke, kuna yin abinda ranku yake so muna zuba muku ido alfarma muke muku saboda ku ɗin iyaye ne kuma a'hali, kuyi duk abinda ku ke so babu ruwan mu amma kada a shiga gonar mu, abinda muke so namu ne don haka a bar mana kayan mu....."

Mai martaba cikin damuwa ya ce "ku É—in su waye? sannan wa ya turo ku? daga ina kuke? sannan ku nawa ne?..."

Dariya Reemah tayi sannan ta ce "mu É—in jinin jikinta ne, muna tare da ita ne tin daga lokacin da aka haife ta, ita É—in Amanar mu ce, muna son abunda take so, bama cutar wa don haka kada a cutar da mu, babu wanda ya turo mu kuma..."

Mai martaba ya ce "yanzu mai kuke buƙata?..."

Ta ce "Abinda take so shi muke so don haka a bata Jaririya, muna tare da jinin Razhdeen don haka muna son ganin Jaririya a kusa da mu...."

Mai martaba ya ce "meye haÉ—in ku da Razhdeen kuma?..."

Ta ce "jini biyu muka ɗaukaka a doron duniyan nan, Razhdeen da kuma Reemah hakan yasa muka haɗa jinin, amma mun haramta yin Aure a tsakanin su, yanzu kuma tinda ga jinin Razhdeen na biyu mun ɗauke ta, mun damƙata a hannun Reemah, raba ta da jaririyar zai haifo babbar matsala..."

Mai martaba ya ce "idan kuma Uwar jaririyar ta buƙaci ƴarta fa?..."

Ta ce "tayi haƙuri wannan ta zamo tamu kuma mun damƙa amanar ta a hannun Reemah, da zata haifo yara 100 a gaba to babu ruwan mu da su amma kuma zamu ɗaukaka yaran in har jinin Razhdeen ne,
wannan ta farkon tamu ceeee, in kuma zaku karɓe amanar da muka damƙa wa Reemah to kuwa zamu ɗauke jaririyar mu tafi da ita can duniyar mu...."

Abbah ne yayi saurin cewa "a'ah! a'ah!! dan ALLAH kar ku tafi da yarinyar gwara ta zauna a hannun Reemah tinda Reemah tana tare da mu zamu kula da su gaba É—aya..."

Reemah tana tsaye a cikin wannan yanayin sai yanzu kowa ya lura da ƙafarta ba'a tsaye da ƙasi take ba, an ɗan ɗagata sama, an rabata da ƙasi kaɗa,
Ta ce "Kada mu ji! Kana mu gani!!!...."

Tana kaiwa nan hasken nan ya ɓace aka sauƙar da Reemah ƙasi sai yaraf ta faɗi ƙasin carpet sumammiya, sumar gashin ta ne ya dawo yanda yake ya kwanta sannan launin Fatar ta ta koma yanda yake...

Mai martaba ne ya nufi yanda take da sauri ya É—ago ta saman cinyar sa yana hawaye yana shafar fuskar ta..
Abbah zama yayi ya dafe kansa da hannu biyu yana jinjina lamarin,

Madam Parveen hannu na rawa tazo gaban Mai martaba da yake ɗauke da Reemah ta miƙa masa jaririyar hannu na kakkarwa, lips ɗinta ma haka yake kakkarwa ta ce "ga ga ga Baby..."

Gaba É—aya ta gama tsorita,
Mai martaba ne ya karɓe ta, da sauri Madam Parveen ta ja da baya taje ta riƙo hannun Chief tana faɗin "ku zo mu tafi dan ALLAH, bana so ina nan ta tashi ta same ni..."

Mai martaba É—agowa yayi yana kallon ta ya ce "kar ki damu babu abinda zai faru..."
Chapter 42 · 0% Book details