← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 68

Sashe 44

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan kowa ya hallaru duk a dinning suka zauna sai da kowa ya ci ya sha tukun aka sake haÉ—a sabon hira,
Razhdeen a wannan ranar wuni ya yi yana wurwurga ƙwayar idanuwansa ta ko ina, yana son ganin Amreesh amma bai ganta ba shi kuwa ya kasa tambayar ta, duk halin da yake ciki kuwa Roshan duk ya fiskanta, shi dai murmushi kawai yake sa ki sai daga baya Roshan ya tashi, ɗakin Reemah ya nufa idon Ramlat akan sa domin ta tsani taga Roshan ya shiga room ɗin Reemah duk da saboda Afaf yake zuwa,
yana shiga ya tarar da Reemah a tsakiyar gadonta ita da Afaf suna wasa, shima zama ya yi a bakin gado idonsa akan Afaf ya ce "Biju Mama wasa ne?..."

Ɗagowa tayi tana kallon sa da sumar gaban gashin ta duk ya rufe masa goshi har zuwa girar ta, ta baya kuma ya sauƙa mata har gadon bayan ta, ta ce "Daddy..."
Shafa sumar kanta Roshan yayi tare da faÉ—in "zo mu tafi ko..."

Da sauri Afaf ta miƙa hannun ta Roshan ya ɗauke ta, ya kalli Reemah ya ce "bazaki zo ki gaishe da Uncle Deen ɗin ki ba?...".
Yamutsa fuska tayi ta ce "bana buƙatar sa..."

Girgiza kai Roshan yayi sannan ya fita da Afaf a hannunsa...

Roshan bayan ya sauƙa falo ya tarar da Razhdeen baya nan sai iya Abbah da matansa da kuma Ramlat,
Roshan zama yayi Afaf akan cinyar sa ya ce "ina baƙin suke?.."

Abbah ya ce "ya fita raka abokansa zasu koma..."

Suna zazzaune a falo sai ga Razhdeen ya shigo, idonsa ne ya sauƙa akan yarinyar hannun Roshan ƙirjinsa ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske har sai da ya dafe gefen ƙirjinsa ta saitin zuciyarsa,
Abbah ganin haka ya sa shi cewa "lafiya kuwa Razhdeen?..."

Roshan kuma idonsa akan Afaf wacce itama dafe ƙirjinta tayi yanda Razhdeen ya yi, lokaci guda ta fashe da kuka,
cike da mamaki yake kallon ta sai kuma ya ɗago ya kalli Razhdeen still hannunsa akan ƙirjin,
Shima Razhdeen idonsa ya sauƙar kan ta ganin yanda yayi itama tayi yasa shi shiga mamaki, haka kowa ya fahimci haka..

Abbah ne ya ce "Razhdeen zo ka zauna mana..."
Razhdeen idonsa akan Afaf haka yaje ya zauna, cike da mamaki ya ce "Dad wannan yarinyar fa? daman twins ka samu Daughter baka sanar mun ba?..."

Girgiza kai Abbah yayi sannan ya ce "Razhdeen kun samu Daughter gashi yanzu tana da shekara 1 daman kai muke jira ka dawo sai a mata birthday...."

Razhdeen kallon Roshan ya yi tare da faÉ—in "congratulation my twins..."

Roshan cije lips ɗinsa na ƙasi yayi sannan ya ce "is your Daughter..."

Razhdeen murmushi yayi sannan ya ce "Yes your Daughter is my Daughter and than my Daughter is your Daughter too..."

Roshan ya ce "Yes i believe it but this girl is your real daughter from Amreesh...."

Razhdeen zuciyarsa ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske yana zaro ido waje ya ce "what?..."
ya maida idonsa kan Abbah yana karkaÉ—a kai alamar bai yadda ba..

Abbah ya ce "da gaske Razhdeen abinda Roshan ya faÉ—a gaskiya ne, Æ´arka ce ta cikin ka, abinda ya faru a tsakanin ka da Amreesher Allah ya baku rabon wannan yarinya..."

Razhdeen a ruÉ—e ya zura zara-zaran yatsunsa a cikin sumar kansa yana cakuÉ—awa tare da faÉ—in "oh my God, innalillahi wa inna'ilaihi raju'un...."

Itama Afaf hannunta biyu ta tusa a cikin sumar kanta tana hargutsawa kamar yadda Razhdeen yake,
Ɗagowar da Razhdeen zai yi idonsa ya sauƙa akan ta ganin yanda take hargutsa sumar kanta kamar yanda yake yi,
Shima Roshan ita yake kallo hatta su Abbah,
Roshan girgiza kai yayi yana murmushi ya ce "Abbah a koda yaushe ina sanar muku duk ɗabi'un yarinyar nan irin na Razhdeen ne amma baku taɓa yadda ba, wasu abubuwan da yake yi itama takan yi su sa'in-sa'in, wani abu idan tana yi nasan shima a lokacin yana irin sa ne, yanzu gashi kun gani da idon ku, she do something like him..."

Sai yanzu Abbah ya gaskaka tare da faÉ—in "ikon ALLAH kenam, ga kamanni sak kamar an tsaga kara, komai da komai iri É—aya..."

Kowa ya gama tofa albarkacin bakin sa, daga baya Roshan ya kalli Afaf sannan ya ce "Biju Mama waye wancan?..."
ya nuna Razhdeen..

Kallon Razhdeen tayi sannan ta yi dariya da hakwaranta da basu gama fitowa ba, ta ce "Abiiii...."

Razhdeen bai san lokacin da ya sau ƙayataccen murmushi ba idonsa akan ta..
Roshan ya ce "to je ki wurin Abi koh..."
ya sauƙe ta tana takawa a hankali irin tafiyar bai gama nuna ba, tana sanye da doguwar riga na kanti ta ƙasi ta baje sosai da ƴar takalmin thorns ɗinta,
ta ƙarasa wurin Razhdeen da gudu-gudu yayi saurin ɗaga ta ya rungume ta sosai a jikinsa bai san lokacin da ya fara zubda hawaye ba, haka ya ɗago ta tare da sumbatar ta akan goshi yana shafa sumar kanta..

Reemah kuwa tana tsaye a bakin matakalar beni ta kasa ƙarasowa falon idonta akan Razhdeen, ganin yanda ya damu da yarinyar ga yanda ya rungumeta sai sunbatar sumar kanta yake yana hawaye itama bata san lokacin da hawaye yake zubo mata ba, tsananin tausayinsa ne ya kama ta sai sakin murmushi take tana goge hawaye.

Razhdeen ne ya sauƙe idonsa akan Reemah, miƙe wa yayi tsaye yana ɗauke da Afaf ya ce "Sarah zo..."

Reemah tafo wa tayi wurinsa, tana zuwa ta rungume shi, shima rungumarta yayi da É—ayan hannu yana faÉ—in "my fine girl an girma, to meye na kukan..."

Reemah tana kuka ta ce "My super man..." ta ƙira sunan tana dariya...

Shima dariyar yake ba ƙaramin kewar juna suka yi ba,
sai da suka gama koke-koken su tukun kowa ya samu wurin zama,
Razhdeen yana zaune Afaf akan cinyarsa sai kuma Reemah a gefen sa tana riƙe da hannunsa kamar wanda zai gudu....

Abbah fuska ɗauke da murmushi ya ce "Deen tunda Allah ya dawo mana da kai lafiya yanzu abinda zai faru shine dole zaka bi mana bayan Amreesh, domin yarinyar nan bazata taso ba tare da mahaifiyar ta ba indai tana raye, Amreesher mallakin ka ce an riga da an baka ita tin kafin a haife ta don haka zaka amshi matar ka, ba tare da ɓata lokaci ba za'a ɗaura muku Aure..."

Razhdeen jin zuciyar sa yake kamar ana sukar sa domin ba ƙaramin son Amreesh yake ba, kamar zai yi kuka ya ce "Abbah Amreesh bazata taɓa aminta da ni ba, gani take laifi nane abinda ya faru but ina ƙaunar ta sosai..."

ya ƙarasa maganar yana kai idonsa kan Roshan, wanda shima Roshan idonsa akan Razhdeen yake, haka kawai yake jin tausayin Razhdeen domin ya sha wahala akan Amreesh, inda ace an gado Amreesh tin wuri da bazai yi garajen Auren ta ba,
Roshan cikin tausayawa ɗan uwansa ya ce "My man kar ka damu idan ka tashi tafiya zan raka ka zuwa wurin Amreesh, zata yadda da kai sannan zaku zauna da ƴarku cikin aminci da ƙaunar juna...."

Wani irin kallo Reemah ta watsa wa Roshan jin za'a raba ta da Afaf,
A gigice Reemah tasa hannu ta karɓi Afaf daga hannun Razhdeen..

Razhdeen ji yayi an fizgi Yarinyar daga hannun sa da sauri ya waiwaya yana kallon Reemah,
Reemah rungumar Afaf tayi sosai tare da miƙe wa ta nufi room ɗinta da gudu..

Roshan kallon Abbah yayi sannan ya ce "Abbah! ya za'a yi da wannan al'amarin? ina tunanin matsalar da za'a samu idan uwa ta buƙaci ƴarta..."

Abbah jinjina kai yayi ba tare da ya furta komai ba..

Razhdeen cike da mamaki ya ce "me yake faruwa ne?..."

Roshan ne ya sanar masa halin da ake ciki,
Razhdeen lumshe ido yayi tare da luma yatsun sa a cikin sumar kansa sai da ya ɗan juma kafin ya buɗe idon yana sauƙe numfashi ya ce "indai yarinyar ce babu matsala za'a iya bar mata, babban matsalar shine haɗa alaƙa da jinn, bana son su shafi yarinyar, itama Sarah inaso a rabata da su..."

Ammy tana zaune sai yanzu tayi magana ta ce "to kai banda abinda Razhdeen ai yarinyar ce tasa suka bar jikin ka..."

Razhdeen ya ce "eh ina so su bar jikin ko wacce a cikin su, bana buƙata..."

Abbah ya ce "tayaya kenam?..."
Roshan ya ce "Addu'a shine makamin mumini don haka zamu tsayar da addu'a sosai, zamu gayyato manyan malamai..."

Ammy ta ce "ba masu cutar wa bane, sai ma kariyar da suka basu don haka ban goyi bayan a tada su ba saboda ba'a san irin matsalar da za'a fuskanta ba, tinda ba ƙaramin ƙarfin iko gare su ba, matsalar shine kada su raba ƴa da uwa da kuma uba...."

Abbah ya ce "to ke taya kika san da haka?..."

Ammy ta ce "ta hanyar yin magana da su, saboda haka Ku bar su kawai, mutanen kirki ne kuma zasu cigaba da basu kariya babu wani abun citarwar da zai same su, sai dai abu ɗaya ne za'a nemi alfarmar su shine su damƙa yarinyar a hannun mahaifiyar ta..."

Roshan idonsa akan Ammy ya ce "babu wata alfarmar da za'a nema daga wurin su, indai ba zasu cutar ba to a bar su kawai, ita uwar yarinyar ai bata son ƴar, inda tana sonta da bazata kama hanya tabar jaririyar yarinya tana kuka ba, bata ji tausayin ta ba har ila yau shekara guda da watanni bata tako ƙafa tazo ganin ƴarta ba ko a photo bata taɓa neman ganin ta ba, to akan da wani dalili zaku damu kada a raba uwa da ƴa? in aljanun basu raba ba ai ita uwar da kanta ta raba alaƙar ta da ƴarta, saboda haka Reemah tana son yarinyar kuma an bar mata ita babu wanda zai raba ta da ita saboda tin tana Jaririya take riƙe da ita...."

Razhdeen idanuwansa ne suka yi ja jin abinda Amreesh ta aikata wa É—iyarsa, tana hukuntata saboda shi,
dafe goshin sa yayi yana tunanin ta yanda zai fara tinkarar Amreesh, gashi Æ´ar da ta haifa ma ta hukuntata saboda shi balle shi da kansa...
Chapter 44 · 0% Book details