← Book details My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 68

Sashe 11

My Enemy Takun Karshe Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka likitoci suka kwantar da shi akan gado suka shiga dashi emergency room shima, domin ciwon zuciyar Roshan ba ƙaramin hatsari ne da shi ba,
Sai dai kowa da ɓangaren sa, wannan yana part ɗin heart emergency shi kuma Razhdeen yana ɗakin operation domin ana duba masa ƙwaƙwalwarsa ne...

Abbah gaba É—aya ya rasa ya zai yi, ibtila'i dai gashi yana cikinsa, haka ya cigaba da zama a asibiti yana zaman jinyar twins É—insa...

Itama Baiwar Allah a wannan ranar Aunty Yolash ce ta taya ta kwana...

__________★★★★★

Bayan kwana biyu.

A yau ne ranar É—aurin Auren Roshan da Ramlat, jikin Roshan Alhamdulillah domin a yau aka sallame shi daga hospital bayan kwana biyu da yayi, Abbah ne ya sanar masa cewa "Razhdeen yana kwance har yanzu bai farfaÉ—o ba sakamakon hatsarin motar da yayi...

Abbah ya sanar wa Roshan ne saboda yasan Roshan bai san Razhdeen ya samu hatsarin ba saboda a ranar da yayi hatsarin shima Roshan baya cikin hayyacinsa, kuma sai jiya da daddare ya farfaÉ—o yau kuma da safe aka sallame shi,

Roshan ne ya kalli Abbah da rinannun eyes É—insa wanda har yanzu bai dawo normal ba tsabar kukan da yasha, jin Abbah ya sanar masa Razhdeen yayi hatsari ne yasa shi cewa "Dad I need to go home..."

Abbah ya ce "Roshan na ce Razhdeen yana kwan....."
Kafin Abbah ya ƙarasa maganar Roshan yayi saurin katse shi da cewa "i don't care Dad, he is not my brother, na yanke alaƙata da shi, ba ni ba shi ganin fuskar sa ma bana buƙatar gani, domin bana shiri da maciyi amana..."

Cike da mamaki Abbah yake kallon Roshan ya ce "Anya Roshan baka fara shaye-shaye ba kuwa? shin kasan me kake faÉ—i kuwa? shi twins É—inka ne kake...."

Nan ma Roshan ya ƙara katse shi da cewa "Yes naso ace mahaifiya ta daban ta haifeni, ban taɓa jin na tsani mutum ba sai akan Razhdeen da Ammata, na tsane su, sun ci amana ta...."

Abbah ya ce "ka gaya mun me yake faruwa ne?..."

Girgiza kai Roshan yayi sannan ya ce "ba komai, banaso a É—aga mun Aure na, a yau nake so..."

Abbah ya ce "Roshan idan baka sanar mun abinda ke faruwa ba taya zan sani har na shiga cikin lamarin..."

Roshan ya ce "ai banaso kowa ya sani saboda kar a ƙara haɗani da maciya amana, nafi son yanda na yanke alaƙata da su ta wuce har abada, bana son sasanci..."

Yana kaiwa ƙarshe ya miƙe tare da nufan hanyar waje, Abbah bayansa yabi suka fita tare domin yanda yake lallamin Roshan tamkar ƙwai domin yanada rauni sosai, abu kaɗan ne zai kwantar shi akan gadon asibiti shiyasa Abbah yake son bin komai a hankali...

Abbah da Roshan ne suka shiga mota wani soja yake driving É—insu zuwa gida domin a yau ne ranar Auren sa...

Razhdeen kuwa har yau kwana biyu kenam ko motsi babu, balle asa ran zai farfaÉ—o kwana kusa, ga yanda aka Aske masa sumar kansa sakamakon aikin da aka masa, sai ya fito kamar ba shi ba, domin sumar gaba É—aya aka Aske..

Ammy Amaryar Abbah ita aka bari take jinyar Razhdeen domin tamkar uwa take a wurinsu, ko ba Auratayya a tsakaninta da mahaifinsu Ammy ƙanwar mahaifiyar su ce uwa ɗaya uba ɗaya...

Su Abbah suna komawa gida ya shirya tsab zai je ƙasar jidder acan za'a ɗaura Auren sai a tafo da Amarya, da su mai martaba da matan sa gaba ɗaya...

Roshan kam ƙin zuwa yayi saboda baya son hayaniya,
Kai tsaye part É—insa ya nufa saboda akwai mutane acan part É—in Abbah kowa sai tambayar sa yake da jiki shi kuwa ba son yin magana yake ba,

Yana shiga falo yaga falon wayam ba kowa, zuwa yayi zai wuce idonsa ya sauƙa akan Baiwar ALLAH dake zaune a ƙasin bayan kujera ta kifa kanta da gwiwa,
tsayawa yayi tare da kawar da kansa gefe domin idan yana ganinta zuciyar sa hargutsuwa yake, murya ciki-ciki ya ce "meya zaunar dake a part É—ina?..."

Ɗagowa tayi tana kallonsa daƙer ta tashi sakamakon rashin ƙwarin jikinta da kuma rashin cin komai, hatta ruwa ta kasa sha duk leɓɓerin bakinta ya bushe yayi fari tass kamar wacce tayi shekara tana jinya, zuwa tayi ta tsaya a gabansa tana ƙiran sunansa cikin sassanyar murya ta ce "D......"

Roshan yayi saurin katse ta da cewa "D ya mutu, wannan Roshan ne..."

Haɗiyar yawu tayi duk baki ya bushe babu yawu ko ɗis ta cigaba da cewa "dan Allah kayi haƙuri, wallahi ban san ya akayi hakan ta faru ba, inasonka Yaya Roshan, Dan ALLAH kar ka rabu da Ni..."

Roshan ji yake kamar ya shaƙe mata wuya domin wani irin takaici yake ji idan yana sauraron Muryar ta,
ɗaga hannu yayi yana nuna ta da yatsa tare da faɗin "ke kinada bakin da zaki bani haƙuri? meye haƙuri? yanda na tsani shaiɗan haka na tsane ki domin ke babbar shaiɗaniyar cikin gidan nan ne, bana hulɗa da maciyar amana da kuma mazinaciya, ke babbar kafura ce marar imani wacce a ranar alƙiyama zaki dawwama ne a cikin wutar jahannama, la'ananniya mazinaciya wacce Allah ya kwashe miki kaya daga gaban ma'aiki....."

Wani irin mari Baiwar ALLAH ta zabga masa, ƙara ɗagowa tayi zata mare shi yayi saurin riƙe hannunta yana huci, idonsa akan ta...

Kuka ta fara yi tana faÉ—in "Ni ba mazinaciya ba ce sannan ni ba shaiÉ—aniya ba ce, haka kuma ni ba kafura ba ce sannan ina tare da Manzon Allah, ina kuma neman tsari daga faÉ—awa wutar jahannama....."

Kukan jinin da ta saba yi shi take yi yanzu domin ya rigada ya zamo shine hawayen ta....

ganin hawayen ta na jini ne yasa yayi saurin kawar da fuskar sa daga kallon da yake mata domin bazai iya juran ganin wannan kukan ba, haka yasau mata hannu sannan ya wuce ta gefenta ya nufi part É—insa, yana shiga ya saka sakata ....

Baiwar ALLAH durƙusawa tayi tana ƙara sabinta kukan ta....

★★★★★★

Ƙasar Jidder an ɗaura Aure cikin ƙoshin lafiya, Roshan da Ramlat R+R😍...

Gaba É—aya zasu tafo Nigeria Maamie da kuma Aunty A'isha sai Amarya Ramlat, da shi kan shi Mai martaba, shi zai zo ne saboda duba jikin Razhdeen, har da sauran gaba É—aya,
Abbah ma yana tafe da su tare da wasu Æ´an uwa...

Bayan sun isa Nigeria a É—aki na musamman aka ajiye Ramlat kafin a kaita can part É—in Roshan, dole sai ta fara zama a yankin Abbah,
Ana kawo Amarya duk baƙin fuskoki suka tattafi domin an sanar cewa babu wata hidimar da za'ayi sakamakon anada marar lafiya, kowa babu sukuni a cikin zuciyar sa...

Misalin ƙarfe 8 na dare kowa na gidan ya hallaru a falo, bayan tafiyar baƙi, waɗanda suke gidan yanzu sune Hajiya Kilishi da yaranta huɗu a falon Pinky da Rukky da Ummy sai Ƴar tinny, sai kuma Aunty Yolash da kuma su Maamie da Aunty A'isha matan mai martaba da shi kansa mai martaba sai Abbah da kuma Amarya Ramlat duk sun hallaru,
Abbah ne yayi gyaran murya sannan ya ce " ma sha ALLAH, anyi Aure lafiya ga Amarya sai dai babu Ango da uwar gida Kuma ina son ganin su suma,
Bayan haka akwai wani babban al'amarin da yake faruwa a cikin gidan nan wanda babu wanda yasan meke faruwa hatta Ni kaina, Roshan da Razhdeen a halin yanzu wani irin ƙiyayya ne yake wakana a tsakanin su, amma a yau nake son jin abinda yake faruwa, shi Razhdeen yana can kwance a gadon asibiti rai a hannun Allah, dan haka yanzu nake son ganin Roshan da kuma Daughter domin abun ya shafe ta...."

Ummy tana zaune tana jin Abbah domin tasan dalilin samun matsalar Roshan da kuma Razhdeen da Baiwar ALLAH....

Pinky da Rukky suma kallon juna suka yi domin sun san matsalar...

Abbah ne ya kalli uwar masu gida sannan ya ce "kije part É—in Roshan ki ce ina nemansa shi da matar sa..."

Ummy amsa masa tayi tare da miƙewa tsaye ta fice...

Ummy mota ta shiga security ya jata suka nufi part ɗin Roshan, tana isa ta fara knocking ƙofar falo, ganin shiru ba'ayi magana ba yasa ta tura ta shiga, kai tsaye room ɗin Roshan ta nufa, tana isa ta tarar da Baiwar Allah zaune a baƙin ƙofar ɗakin Roshan...

Ummy kallo É—aya tayi mata ta kawar da kanta gefe tayi kamar bata ganta ba domin a halin yanzu Baiwar Allah ta fita mata a rai,
Ummy tinda ta tsani mahaifiyar ta akan yawon bin hotel da Auren ta to babu wanda bazata tsana ba, ganin itama Baiwar Allah tabi layin nan yasa itama yanzu ta tsane ta...

Ummy buga ƙofar ɗakin Roshan take tana ambatar sunansa "Yaya Roshan Ni ce Ummy..."

Daga ciki ya ce "meya faru ne?..."

Ta ce "Abbah ne yake ƙiran ka ..."
Ya ce "ok I'm coming..."

Ummy kallon Baiwar Allah tayi wacce take ƙasi a zaune sai kuka take tayi kamar zata ce mata taje itama ana ƙiranta taji ranta a ƙone yake bazata iya ɓata bakinta wurin mata magana ba, haka ta wuce bata kulata ba, barin falon tayi taje ta shige mota aka komar da ita part ɗinsu...

Roshan ne ya shirya tsab cikin baƙar jallabiya ya fito zai je ƙiran Abbah yana buɗe ƙofa kwatsam ya tarar da Baiwar Allah zaune a bakin ƙofar ɗakin sa, jin fitowar sa ne yasa tayi saurin tashi tana fuskantar sa,
Haɗe rai yayi fuska ba annuri ya rufe ƙofar ɗakinsa sannan ya riƙe hannunta yana janta suka fice daga falo, suna isa wurin mota ya buɗe back seat ya wurgata ciki, sannan shima ya shiga ya ja motarsa ya nufi part ɗin su Abbah..

Suna isa ya fita tare da buɗe back seat ya sake riƙo hannunta yana fizgarta da haka suka nufi babban falon Abbah,

Suna shiga ya tarar da kowa da kowa a falon ko sallama bai tsaya yi ba cikin fushi yayi wurgi da Baiwar ALLAH kan tsakiyar carpet É—in falon.

Baiwar ALLAH a yanda ta kife ko ɗagowa bata yi ba haka ta fara rera kuka kai a kife a ƙasin carpet...

Abbah da mai martaba ganin haka yasa suka miƙe tsaye suna faɗin "miye haka Roshan?..."
Chapter 11 · 0% Book details